Follow us on social media
Showing 9001 words to 12000 words out of 34548 words
Chapter 4 - IDAN RANA TA FITO by Halima Abdullahi K. Mashi
mishi, to da zai karyata duk wanda ya zo mishi da batun cewa da wata manufa suke son auran shi da Basma. Don haka ya bi ya lika security a guraran da bai saka ba, domin kara samun cikakken rahoyan sirrin duk wata makakarkashiya. Akwai fatitiikan da za a yi kafin daurin auren, da kuma bayan daurin auran tun saura kwana 2 biki dangin mahaifiyar M.B da Kakarsa Haja suka bayyana birni cikin su har da Binto da kuma Ado, haka nan dangin Mahaifinshi daga Garko, Binyo kam ta tsinke da lamarin bikin 'yan birni, fadi take ina ma da Kulawa muka zo bikin nan ta sha kallon duniya, , Allah Sarki Haja ta ce wa zai barta? Binto ta ce ai zan kai mata wadannan hotunna ta gani ki ko kai mata in ji Haja, Allah yasa ina son yarinyar na so kwarai Ado ya aure ta, domin yanda yarinyar ke sha wuya nasan Ado zaya rike ta da amana zai kula da rayuwarta, Binto ta ce Baba ya yi saurin yanke hukunci koda yake ya ce shekaru da dama da suka gabata suka kulla alkawarin auran Yaya Ado da Aina, haka ne in ji Haja, amma ban gushe ba ina mata addu'a Allah ya bata wanda ya fini, amin in ji Binto. Hjy ta jawo aminiyarta cikin dai wato Kilishi ta maida kofa ta rufe tare da cewa kin san sirri dukkansu suka zauna bakin gado. Hjy Shuwa ta kalli Kilshi ta ce, "Kawata kinga dai yanda komai ke tafiya min daidai ko?", Kilishi dafa ta tare da cewa "Kawata na ta6a ki da alheri na kula sai dai menene shirinki na gaba?" Shuwa ta ce, "Shirina na gaba kuma na karshe shi ne kashe Bello, ta hanyar sa mishi gabu cikin abinci." Kilishi ta zuba mata idanu. "ZUWA yaushe za ki aikata haka?" Kilishi ta tambaye ta. "Da zaran anyi biki." In ji Shuwa. "Ba ki tsoron a zarge ta in abin ya yi wuri? Sannan Likitoci za su gano cewa ya ci guba wacce amsa a ki bada lokacin da kanwarki ta ji tuhuma ta yi yawa? Ta ce ke ce ki ka bata?" In ji Kilishi. Shuwa ta yi dan jim sannan ta ce,"Haka ne. Na so in yi wauta, zan bari sai sun dan kwana 2. Kilishi ta girgiza kai tare da yin murmushi. "Ya ya za ki yi da cikin da kanwar taki zata samu, musamman in an samu irin natattun cikin nan an yi an yi ya fita ya ki fita? Ina nufin dadewarsu za su kusanci juna kuma ciki zai iya shiga, kinga dan in ya zo duniya in bai gaji Kakanshi ba dole ne ya gaji dinbin dukiyar da ubansa ke da ita wadda ki ke burin kanwarki ta gada daga b.aya ki mallake." Shuwa baya"Haka ne kuma fa, lallai Kilshi kina da baiwa. To yazamuyi?. . 24..... Nan da nan Jami'an tsaro suka nufi gurin da mutumin ya fado, shi kuwa Ango tuni dangi suka zagaye shi don jin me ke faruwa? Lokacin da su Hjy Shuwa suka fahimci M.B ne ya yi harbin ba shi aka harba ba, sai suka cika da mamaki gami da tsoron me zai biyo baya? Lokacin da suka isa guri inda mutane suka yi cincirndo don ganin kowane ne Hjy Shuwa ta riko hannu M.B tana cewa me yake faru ne Bello? Ya ce," An turo shi ne don ya kashe ni?" Ta ce,"Su waye za su mana wannan dayan hukunci?", Ya ce "Sai Allah, shi ne kawai ya sani. Sai dai kada ki damu ko su wanene burinsu bai cika ba, kuma na sani zamu hadu dasu karo na 2. Jikinta na rawa "To bari in kira Dady in sanar dashi. "M.B ya ce "Hjy ki bar shi kawai, wannan Jami'an tsaro za su yi gaba dashi in yana da sauran rai ne ya musu bayanin dalilin sa na son kashe ni, in kuma ya mutu shi kenan sai in mun tsaya a gabn Ubangiji." Hjy Kilishi ta matso,"To ai dama karsa shi kayi domin barin irin wadannan a bayan kasa fitina ne." M.B ya yi murmushi ya kalli mutumin lkcn da Jami'an suke saka shi a mota, sannan ya dubi Hjy Kilishi"Da ina da wata dabara da zan iya yi lkcn da na hango shi wacce zan kama shi kon kare kaina bayan harbin to da ban harbe shi ba. Tilas ke sa mu harbi don mun fi son mu ji bayani daga bakin me laifi, kila ba shi kadai ba ne ta yiwu wasu suka sa shi da makamancin haka kin ga duk zamu ji'." Ya zuba hannuwanshi cikin aljihu "Hjy ku koma ciki lkcn tashi ya kusa, kada wannan ya dame ku, domin IDAN RANA TA FITO TAFIN HANNU BA YA KARE TA. HAKAN NAN ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA KO ANA RUWA MUZURAI SAI FA YA YI." . Cikin sanyi jiki tare da tunaninko ya gano sune? Suka ce "Haka ne." 25.....Amarya dai tana can gurin kawaye suna lallashi ta don ita kuka ta kama riris, sannan ta kasa zuwa gurin suna dawowa gurin ta rugo ta rungume mijinta shi ko ya shiga lallashinta. Hjy Suwa ta kira mai abun magana ta ce ya sanar da kowa an gode za a tashi haka saboda wannan farmaki da aka kawo. Maimakon gidansu za su wuce kamar yanda a ka tsara daga gurin party ango da Amarya za a yi musu rakiya zuwa gidansu sai kawai a ka koma gida gaba daya in da suka iske mutanan gidan cirko-criko. Haja sai kuka take lkcn da su Ado suka zo mata da labarin dukkan su suna falo ne suna jiran zuwan su M.B bayan an gama jajantawa yana rungume da kafadun Haja yana lallashinta ya dubi Hjyr "Ina su Basma su zo mu tafi dare na kara yi." Nan take Hjy Tasa kuka," Gaskiya ba za kuje ba, ka sani ko ba shi kadai ba ne me nemn ran naka? Haka kawai kuma sai ku je can ku kadai su kashe mana kai a banza." Husna da Safina suka gurin Mahaifin su da ke tsaye yana saurarn kowa, Dady kada ka bar Bros ya tafi fa." Ya dubi Hjy." Kada wannan farmakin ya dame ku, don ba zai zama barazana ko tsoratarwa a gurin dan Sanda kamar ni ba, zamana ni kadai ko zamana cikin mutane ba shi ne zai kare ni daga mutuwa ba, ku fahimci wanna ni ba zan canza da komai ba kuma ba zan kasa walwa ba don wannan. Haja ta ce "A'a ka dai zauna tukunna Muhammadu kada su kashe min kai Marayan Allah, me ka tare musu?" Ta sake sushewa da kuka tare da cewa "Ni shi yasa birni bata ban sha'awa, yanzu ka ji an kashe mutum."Su Ado suka ce "Da ka dan saura tukunna." 26... Husna da Safina suka kyale mahaifinsu suka je suka rungume Yayan nasu suna jijjiga shi"Don Allah Bros kada ka tafi ka ji Dady ka ce wani abu mana." Dadyn ya yi gyaran murya sannan ya ce "Hakika Bello ya fiku gaskiya, domin kuwa duk wata kariya da wani dan Adam zai baka tana bayan ta Ubangiji, ku lura mana duk cikar gurin da ku ke da yawunku bai sa kun ga mai harin nashi ba sai shi kansa, Allah ya kare shi kuma ya kare kansa." Dady ya kalli M.B "Bello kai kuma sai ka hakura na kwana 2 saboda an ce masu rinjaye sune sama, kai da ni ne muke tare amma duk falon nan basu amince ka je gidanka yau ba." M.B yana dariya ya daga hannuwa sama na bi, suka kwashe da dariya shima yana murmushi don da wuya kaga M.B yana kyalkyata dariya. . 27...Tana shiga gurin Hajiya Shuwa nan take ta hau ta da zagi"Yar iska me ki ka je yi gurinsa? Ban gargade ki ba ne?" Basma ta ce, "Na je fa gaishe shi ne." Ta ce "To ban ce ki dinga zuwa gurinsa ba, don na gaya miki kada ma ki yarda da shi ko gidan ki ka ji." "To" kawai Basma ta ce amma cikin zuciyarta cewa take yi ai mijina ne kuma ba zaki haramta min abnda Allah ya halasta min ba. Basma zata juya Hjy ta ce "Ina za ki?" Zan je dakin su Husna ne, a'a cewar Hjyn shigo nan ki zauna. Duk da wannan gadin da Hjy ke yi wa Basma ta saka ta a dakinta sun zauna tamkar kurame, bai hana Basma ciro wayarta ba shi ta turawa text tana me shaida mishi irin tsantar son da take mishi tare kuma da shaida mishi cewa ta yi mafarkin tana kwance bisa kirjinsa, le6unnanshi yasa kan nata yana mata sunba ta bn mamaki, ina son ganina haka a gaske zan samu? Lokacin da sakon ya same shi murmushi ya yi duk da ya ji dadi bai hana shi ji a cikin zuciyarshi banbarakwai ba, a son zuciyarshi shi ne zaya fara kai kokon bararshi gare ta matsayinshi na miji duk da addini ba ya hana ba ne matsayinshi na mijinta. Sai ya rubuta cewa, Ni na ki ne Basma yanda na tabbatar da cewa ke tawa ce, daina mafarkina zamu yi zama na har abada insha Allah. Zamu kasance cikin yanayin da yafi mafarkinki. Ya tura mata tana gama karantawa ta yi murmushi tare da cewa, my D kenan, haka nan suka ci gaba da yiwa juna musayar kalaman so da kauna har zuwa lkcn yin Sallah, inda M.B ya fita. 28.... Inda M.B ya fiya. Ranar da suka cika sati daya, ranar Dady ya rike wuta sai sun tare kuma ranar ne suka tare. Kafin a kaita sai da Hjy da kawarta Kilishi suka saka Basma a gaba kan cewa kada ta kuskura ta ba da kanta ga angon nata, wai ta bijire mishi ta wannan fanni. Basma ta dubi Yarta ta ce "Anty har yanzun kin kasa sanar dani dalilinki na hada wannan lamarin?" Kilishi ta ce, "Kin kusan gama aikinki, kuma nan za ki ji komai." Basma ta ce "Shi kenan." Ko kayan gyaran Amarya da ake hadawa ita dai da kudinta ta siya kuma a 6oye. Amarya ta gama sakin jiki yau za su 6arji Soyayya ita da mijinta, amma ga mamakinta 12:30 bata ji shigowar Maigidan nata ba, gashi tuni take neman layinshi amma ya ki shiga, fitowa cikin falon tayi don duba dakinshi kofar na kulle don haka ta daga labulan window shi ta hango kwance rigingine filo manne a kirjinshi yana bacci. Sai kawai ta juya ta koma dakinta cikin sanyin jiki. Washegari bayan ya dawo daga Masallaci dakinta ya nufo ta yi dai- dai bisa gadonta me shegen kyau, ya maida wani abu da ya yi yunkurin taso masa sannan ya yi karfin halin karasawa ya saka hannunshi ya girgiza kafadarta a hankali. Mika ta yi wadda dole tasa shi kau da kan shi gefe, domin ganin yanda surarta ta matantaka ta firgita shi, ta bude idanunta a hankali ta zuba su kan fuskar M.B tare da furta "My D." ya dube ta "Amarya tashi kiyi sallah ko?" Ta tashi zaune cikin yanayi na shagwa6a ta ce, shi ne jiya ka bar ni ni kadai ina ta jin tsoro. Ya dan ware idanu cikin murmushi, sorry my dear, jiyan nan na gaji sosai ban san lkcn da bacci ya kwashe ni ba, yanzun dai tashi ki je ki yi sallah kafin gari ya yi haske, kin ji ko? Ta yunkura ta nufi bayinta da kallo ya bita yana son fantama amarci da abar son tasa amma zuciyarsa ta kasa amincewa da hakikanin son da take masa, ma'ana ya sani tana sonshi amma me yasa ta kasa sanar dashi game da shirin da Yayarta ke yi kansa? Koda yake ya sani bata san rayuwarshi ake nema ba, sannan bai san me zayo biyo baya ba cikin zaman nasu, sam bai ji dawowarta ba sai dai ya ji muryata tana cewa "My D, baka zauna ba." Ya ce dama zan je kicin ne don shirya mana breakfast, ya nufi fita ta ce my D ba mu da masu aiki ne? ya girgiza kai tare da cewa bana son masu aiki masu yi mana gadi kawai sun isa, amma duk aikin cikin gida zamu yi kayanmu ta marairaice fuska ban fa iya aiki ba musamman girki ka kuma sani ya ce ni zan yi mana kada ki damu maimakon mu dauki masu aiki tunda ba dadewa za a yi ba yana fadin haka ya fita. . 29... Sai dai su ba kamar mutan birni ba wai har da kungiyar da suke kwatarwa yara 'yancin kai kamar yanda Ado ya sha bani lbr. Ina cikin wannan halin ne sai na ji muryarshi tana fadin subahanallah, 'yammaya me ya yi zafi..... Na dube shi da jayayan idanuna babu komai ya shiga waige-waige can ya dube ni zo muje karkashin bishiyar can in ji damuwar ki. Wala Allah ko zan iya taimaka miki. Na girgiza kai zai yi wuya ka iya taimaka min sai dai ka taya ni da addu'a ya ce kada ki zama mai gardama a gare ni kila ni ne sanadin fitarji cikin matsalar. Jin haka sai bn kuma magana ba, ya yi gaba na bishi. Komai na karanto mishi har zuwa yau dinnan shiru ya yi cikin tausayawa tare da tunanin ita ina zai fara?" Can ya yi wani tunani kuma ya gamsu da cewa za ya gwada hakan. Sai ya ce Kuluwa zan taimake ki hanya ta farko shi ne zan nemi Baba Gaje in bata kudi masu yawa ta bani ke in tafi dake can birni ki dinga taya matata aiki, zan saki Makaranta Islamiyya da boko kiyi ilimi shi kenan kin zama yar birni sam bn san sanda na shiga sheka dariya ba, na dube shi Allah da gaske ka ke yi kuma?" Shima cikin murmushu ya ce sosai ma na ce wai wa ka ganni a birn?" Ya ce balle kin shiga Makaranta, na yi ajiyar zuciya na yi shiru ina tunanin yanda zan zama 'yar birnu, can kuma na tuna Baba Gaje fa zata iya hana ni zuwa, nan take sai raina ya yi duhu cikin sanyin jiki ya ce menene kuma?" Na dube shi in ta ki yarda fa?" Ya ce sai mu canza dabara. Na ce to Allah ya dora ni a kanta, domin duk kudin da za a bata in ta tuna cewa zan iya jin dadin rayuwa ta zata ki amincewa ya ce kada ki damu Allah yana tare da mu na ce to Allah ya shige mana gaba. Ya tashi tare da cewa ki koma gida kada ki yarda ki daga hankalinki kan wannan insha Allah tare zamu bar garin nan. Ina tsaye ina kallon dan birni ya tafi har ya 6ace wa ganina. . 30. Ya ce kada ki damu Allah yana tare da mu na ce to Allah ya shige mana gaba. Ya tashi tare da cewa ki koma gida kada ki yarda ki daga hankalinki kan wanna insha Allah tare zamu bar garin nan., Ina tsaye ina kallon dan birni ya tafi har ya 6ace wa ganina kai ko wannan ya ishe ni alfahari duk cikin kauyannan akwai wadda dan birninan ya ta6a kallo ma balle magana kazalika babu wadda Ado ya ta6a cewa yana so sai dai ni, don ko Aina'u bashi aka yi. Daga nan bn nufi gida ba na koma gurin su Binto ina tare da su har muka kai Amarya muka fito waje muna ta gada, duk sanda na tuno gida sai na ji tamkar kada na koma, sannan na samu kaina da taurarewa cikin zuciyata ina fadin ai dama yau kawaye gidan amarya suke kwana sai gobe in anyi rufi da budar kai bayan an gama jere sannan kowa zai watse don haka a sai na yi kwanciyata. Da safe muna cikin karyawa Laure ta shigo tana cewa "Kuluwa ga Babanki nan a waje ya zo neman ki na fito da sauri na rusuna ina kwana Baba?" Ya ce lafiya Jidda nan ki ka kwana?" Na ce I ya ce to shi ne ba ki zo kin shaida min ba? Sanin kanki ne zan damu na rike hannunsa to i hakuri Baba jiyan na neme ka bn ganka ba nan na koro masa labarin duk yanda muka yi dasu Baba Gaje har zuwa batun dan birni Baba ya ce anya zan bari kiyi nesa da ni Jdda? Ke ce kurum ki ke kwantar min da hankali, na ce in ba dama ko Baba Gaje ta bari ni sai na fasa, muka nufi hanyar gida yana cewa aure ne ya zama dole Jidda shi ne kurum zai raba mu. Sallamar dan birni ce ta dira a kunnunwanmu, Baba ya amsa masa dan birni ya tsugunna ya gaida shi sannan ya dube Jidda Baba ne wannan ko na ce i shi ne Baba kaga wannan shi ne dan birni da nake fada maka. Baba ya ce af towo yanzu nan take yi min zancanka, dan birni ya shiga sanar da Abbana, nufinshi na son taimaka mini. Baba dai ya yi shiru na sani yana jinjina rabuwa da ni ne can ya ce to bari dai muji ta bakin Babar tata dan birni ya ce to gobe ya zo zaya wuce ya ce shi ba bako ba ne a garin dan gari ne dan Maigari wan mahaifiyarsa ne. Baba ya ce haba yaro ai ni nasan ka kai ne dai baka saniba. .....
๐๐๐๐๐๐๐๐ IDAN RANA TA FITO ๐๐๐๐๐๐๐๐ . Part 3โฃ1โฃ~~4โฃ0โฃ Mb ya dubi sajan yace inafatan bawatamatsala ? Sajan daketukin mota shimayadan dubimai gidan nashitacikin madubi banazaton damatsala sannan yamaida dubanshi ga titi saidai gidan nebasan kozayayimakaba m.b. Yayi Dan murmushi taredacewa awace unguwace sajan sani yace nan dorayi ne sai dai gurinbabu jama a sosai m.b. Yace nafison hakan sai da sukafara zuwagidan yagani yayi masa yandayakeso sannan sukanufi gida yaciro wayarshi yana yiwa basma albishir tare dacewa sunkusa shigowa gidan jikin basma a sanyaye kafa dawasu anty ne ? Eh sunsan na iso takasa dannezuciyarta muryarta tashiga rawar kuka