Follow us on social media
Showing 3001 words to 6000 words out of 34548 words
Chapter 2 - IDAN RANA TA FITO by Halima Abdullahi K. Mashi
. --Baba ya ce gaskia Gaje ya dace ki dinga yiwa yarinyar nan adalci ita da Hinde dukansu ya yanki ne ta mike tsaye gara ka dake ni ko ka huce, ya ce batun duk bai kai nan Ba, kiyi hakuri ta ce ka ishe ni da batun wani adalci, adalci ban san shi ba,kuma kuluwa da Hinde suna da bambanci don ko kai ma ka nuna, ko ba kuluwanka zaba ba??? Ya ce ba zabenta na yi ba, ina dai tausaya mata ne, ni duk daya na dauke su, tunda ni na haife su. Ta ce ni na bambanta, me ake yi da kuluwa watsattsiya ya dube ta da dai na kowa ne kuma fa ta nagari lamiri ne ya sa kai ya fice ya barta tana cewa, toh ba sai ka sake ni ka zauna da kuluwan ba ta juyo ta zubamin don kwashi a tsakiyar kai koma daddiyar banza tashi mun a kai ni har cikin ya tsana naji rankwashin tamkar in saki fitsari, ...OHHH NI HAANAT NAGA MASIFEFFIYAR MATA. Na koma can gurin kwanciyata na rabe kan yan tsummokaran kayana. Shi ko Ado dakin haja ya koma wato kakarshi mahaifiyar babanshi Dattijuwa mai shekaru taga jiya tana ganin yau, gobe sai Allah haja ta haifi yaya da dama suna rasuwa da mijinta marigayi malam shehu maigari na yanzu Alhaji sallau, sai kanin shi maigari kawo kenan Alhaji sidi sai ko kanwarsu kuma yar auta mai suna Mairo ta yi aure an kai ta Garko mijinta Alhaji Dahiru dagabisani suka koma! Cikin kano,dan shi ma'aikaci ne na gwamnati domin yana daya daga cikin wadanda suka ya boko zamanin ana gudun bokon, gwammaja suka zauna daga bisani ya samu matsayin sakataran gwamnati suka koma nasarawa cikin jerin gidajan masu kudi. Mairo ta rasu gurin haihuwar ta ta biyu, bayan gama zaman makoki haja ta koma kauye tare da jikanta Muhammadu Bello, gurinta ya zauna har shekaru shida sannan mahaifinshi yazo ya dauke shi don saka shi a makaranta. Duki hutu ana kawo shi kauye gurin haja kafin a kai shi kasar waje. Ado ya zauna bakin gadonta ya ce tsohuwa mai dan koko, Allah kashe ki musha gunba. Ta ce raggon namiji daga ina kuma?? Ko gurin budurwarka ka je?? Ya ce Ai kin san dai ni bani da wata budurwa a kauyannan. Ta ce, ka zauna karatun shirme har ka tsufa. Ya ce haja don bakya zuwa birni ne shi yasa da kin ga maza manya ba su yi aure ba suna karatu. Ai ni insha Allah zan kafa tarihi a kauyannan. Haja ta ce burinka kenan kullum tadinka kenan. Ya ce ki taya ni da addu'a. Ta ce, ina yi amma na fita. . Jikina yana rawa na shiga kuka ina cewa sai naje gidanku an biya ni na kwashe kwanukan na nufi gida, koda na shaida ma Baba Gaje ta ce ita fa ba sunanta sarai ba, don haka in je gidan su yaron in amso mata kudin ta ai dama ta kula ba da son Raina na dauki kunun ba, in ko ba haka ba tasha alwashin yau sai ta sumar dani. Cikin kuka na nufi gidan malam bawa da yake nasan yaron,Lanto ta ce bata maganin sisi bare naira talatin, in je in yi hakuri na ce za a dake ni ne ta ce ai shima din zata dake shi. Tun daga nan ban koma gida ba in bi wannan layin in bi wannan soron har dare. Lokacin da na hango yaya Auwalu da musa nasan ni za su kama, don haka da na killa da god sai zauran gidan Maigari. (soro) zaure biyar ne a gidan kafin ka shiga ainihin cikin gidan, zauran farko da dakin baki ciki zaure na biyu har zuwa na karshe duk na samarin gidan ne wato dakunan su na cikin zaurukan, zauran da ke tsakiya wato na uku kenan shine ake cewa zauran duhu. Ko da rana ne dindim yake nan na labe. Tun dana ga yau har da cocilar ta taba su musa don su nemo ni hakika tana nufin aikata abinda ta furta. Ina nan tsugunne sai kawai na ji an yi karo dani sannan aka ce wanene? Ban yi magana ba na kuma lafewa. Ya dallaro ni da yar cocilarshi tare da zuba min idanu, ke daga ina? 6...."Na yi shuru tashi mana, ya doka min tsawa jikinah na bari na mike. Me ya kawo ki nan? Cikin dashasshiyar murya Da ta disashe da kuka na ce za'a dake ni ne ya ce wa zai da ke ki? Na ce Baba Gaje ta ce sai ta sumar dani kuma wallahy zata iya. Ya tuno kwanaki ita ce yarinyar da suka yi karo tayi bari, ya tuna kalaman da take furtawa tana kuka. Ya ji muryar wasu a zauran farko sai ya kashe cocilar ni kuma sai na lafe jikin bango su musa ne ya tare sua zaure na biyu yana tambayar su, wasu ke nema? Suka ce wata yarinya ce kanwarsu ta yi laifi ta gudu ya ce to an ce muka tana nan ne? Suka ce a'a za dai su duba ne ya ce musu to babu kowa su fita, nan suka yi waje ya dawo gurina zo nan,na bishi zuwa wani daki nan cikin zauran duhu, yar katifa ce da filo tasha shinfida kasan kuwa wata leda ce mai santsi sannan bangon dakin yasha ado da farin fenti an yarfa baki a jiki sai wata adaka wato akwati tana dore kan wani dan tebur gaskiya dakin ya tsaru ya zauna kan kujerar katako ita kadai ce cikin dakin sannan ya yi min umarni da in zauna gefen katifar. Ado ya ce min ya sunanki? Na ce sunana kuluwa, amma babana yana kirana jidda, ya ce wanene baban naki? Malam kasim ya dan yi jim, sannan ya ce nan gidan wanzamai? Na ce eh, to ina mahaifiyarki? . Ado Ya ce, ya dace su Baba su taka mata birki. Haja ta kama baki ina aka ta6a jin anyi haka?" Ya ce, To ba shi ne Maigari ba?" ta ce, don kawai yana Maigari sai ya kama shiga harkar gidan wani? Ina ce sai an kawo kara sannan zai yi hukunci? Ado ya ce don dai kauye ne, amma can birni har kungiya akwai me kare hakkin kananan yara." Haja ta ce, to ai su kansu waye yake." Ya mike tare da cewa bari in je in duba wani littafi, ta ce aikinka dai kenan krt, a tsurama littafi ido shi ba kur'ani ba ba Ahalari ba." Ya fita yana dry tare da cewa shima Kur'anin mukan duba shi ta kwanta tare da fadin "karyar banza.... Muna zaune ni da Binto muna hira ina bata lbrn taimakon da wanta Ado ya yi min, kasancewar yau Lahadi domin duk lahadi nakan samu sassauci don Baba Gaje tana zuwa cin kasuwar Lahadin-Makoli, wani sa'in ma har da Hinde take zuwa. Yau kam bata je da Hinde ba, suna zaune can gindin bishiya suna hirarsu ita da su Salame. Ashe zancanmu suke yi. Hinde tana son yin kawance da Binto amma ita Binto a gabn kowa tana nuna cewa ni ce kawai kawarta kuma dalilina take zuwa gidanmu, to ashe suna jinmu lkcn da na ke cewa, Binto Adonko yana da mutunci don ranar ya taimake ni, to bayan tafiyar Binto na dawo daga rakiyarta sai su Hinde suka zo suka sani a tsakiya. "Mun ji kina cewa Adon su Binto yana da mutunci, mu za ki yiwa salo? Me ya hada ku da shi?" Na ce To ni ai da Binto muke hirarmu ba da ku ba."Laminde ta ce, "Dalla can ku kyaleta Ado ne ma zai kula ki ga kyawawan 'yammata cikin kauyannan bai kula su ba sai ke kucaka, kazama, mummuna, baka 'ya matsiyata da ke Na ce "To ni na ce muku da wani abu ne tsakaninmu, in ina ruwana ma da samari. Amina ta ce, "Ina dai ruwan su da ke ai ke bandaro za ki yi, Hinde ta ce, "To wane mahaukaci ne zai aure ki ma dubatta da Allah su Jummala wato mahaifiyar Salame sai sheke dry suke dama suma manyan da kansu ba'ar da suke min kenan. Na bar musu gurin na koma can gefe daya na zauna ina tunani.........10 ...Na sani ni baka ce kuma ba na daga cikin kyawawa, gaskiya ne su Hinde ba karya suka yi ba, sun fini kyau, don haka ban ta6a tunanin cewa za a wayi gari wani namiji zai zo ya ce yana sona ba, bare irn su Ado dangin Maigari, ga kyau ga krtn boko gashi yana zuwa birni yana ganin masu kyau, yanda Binto ke bani lbrn matan birni ina so kafin Allah ya dauki raina ya kawo sanadin zuwana birni,, insha kallo in ga irin hanyar da Binto ke bani lbr wai ko min dare zaka samu titi da haske wai na lantarki da ruwan da ta ce ana matso shi wai na ko famfo! Muryar Baba naji yana cewa. Jidda lafiya ki ka yi tagumi? Na mike tare da amsar jakarshi ta wanzanci na ce "Sannu da zuwa Baba, ina tunanin birni ne, wai Baba kai baka da dangi a birni ne?" Ya yi murmushi bani da kowa a cikin birni sai dai a da mukan je rani ya nufi dakin shi na bishi ina cewa ni dai ina so in je birni ko dan na yi kallon abubuwan da Binto take bani labari ya yi dariya dai-dai lkcn ya zauna gefen 'yar katifarshi ta rimi (wato ta auduga). Ke jidda in ki ka je birni ai sai ki 6ace saboda shegen kallon tsiya na yi murmushi in Binto tana bani labrin birni Baba sai in ji tamkar gani a garin ina son zuwa koda nan kasuwar GARKO, amma Baba kaje ta ki Baba ya dube ni cikin tausayawa, kada ki da mu wata rana za ki je har birnin ma na yi dry bari na dibo maka ruwan sha. *************** Ranar kasuwar Garko ina zuba abinci siyarwa cikin kwanuka ina kallon su Hinde suna ta kwalliya don zuwa kasuwa su da kawayanzu dama duk ran kasuwa Hinde bata zuwa talla. Sha'awarsu nake sunci ado gashi sun jan baki, Hinde har da turaran dan duwala da Baba Gaje ta siyo mata daga kasuwar Makoli ga sabuwar atamfarta gami da gyalanta. A raina ina cewa Allah ka kaini in ga na shafa janbaki koda ba zai min kyau ba in dai ji yanda ake yi saukar dundun na ji a gadon bayana.........
ππππππππ IDAN RANA TA FITO ππππππππ . Book 1 Part 1β£1β£~2β£0Husna ta ce, " yes nima na manta ne wai ka jirata in ka dawo. Ya mike tare da cewa "Allah yasa ta yi sauri don wanka kawai zan yi na fita. "Ya nufi gefenshi, dauke da goran ruwan FARO. Ya fito cikin wando Jeans baki da T-shirt mai kalar sararin samaniya. Yana da kyau namiji mai sufar karfi dogo mai kwarjini da haiba. Sai dai miskili ne wai kafi mahaukaci bn haushi, shi ne dan farko gurin mahaifinshi Alhj Tahir, kuma da namiji kacal, wanda kuma yafi soyuwa a zuciyar mahaifin saboda biayayyarsa da kuma kwazon sa. Ya yi karatun sa na primary a S.S.B. Nursery and primary da ke Nasarawa sannan ya yi secondary dinsa a kasan England har zuwa Jami'a din shi. A son mahaifin nasa ya so ya zama Likita ne amma sai dan nasa ya rikede zuwa Dan Sanda ya halarci-kwasa-k wasai tare da dabru na binciko masu laifuka daban-daban kuma yana durowa gida Nigerai bai sha wahala ba hukumar "yan Sandan ciki ta kasa ta dauke shi aiki, dubuwar farko samun matsayi babba. M.B. Tahir dan Sandan ciki ne yana da kimanin shekaru 28. Hjy Shuwa matar mahaifinsa tana da yara 2 Hunsa 'yar shekara sha 18 da kuma Safina 'yar 14, kyakkyawar mace ce mai ji da kanta 'yar boko ce ma'ikaciya a (NNPC). Alhj Tahir na sonta sosai ya aure ta ne bayan mutuwar mai dakinshi Hjy Maryam mahaifiyar M.B din shi ne Silar da Alhj Tahir din ya kai shi kasan Turai don ya yi krtn shi na gaba da primary, lkcn da ya dawo a matsayin dan sandan ciki kwararre, sai Hjy Shuwa ta 6oye akidarta ta kin nashi nunuwa ta ke yi tana sonsa, tamkar dan da ta haifa nan ko me zata yi ta kan yi shawara da shi nufin ta dole sai ya yarda kaunarshi ta ke tamkar daga cikinta haife shi, shi ko ya jima da harbo jirginta yana dai binta ne sau da kafa da kuma addu'ar Allah yasa nan gaba ta canza hali ita kam cikin zuciyarta matukar kin shi take yi, taso a ce 'ya'yanta maza ne gashi tuni haihuwar ta tsaya cak, nata ra'ayin 'ya'yanta su zama su kadai ne gurin mijin nata su gaji dibn dukiyar da mahaifin nasu dashi ne, mahaifin ta Alhj Shu'aibu Turaki Dan Majalisa ne na Tarayya mutumin Maiduguri ne asali, mahaifyarta Shuwa Arab ce ta rasu duk a fi shekara 3 ba. Su 4 ne gurin mahaifin nata kuma ita ce babba, kannanta guda 2 Nasir da Nazir, sai ko 'yar Autarsu Basma. 12..Kwance yake ruf da ciki a tsakiyar gadonsa, kafafunshi suna zube a kasa, yayinda ya doro cikinshi da hannunwanshi da kuma kanshi a filo. Ya mikar da filon ne tsaye maimakon ya gicciye shi kamar yanda a ka fi yi, bacci yake yi domin duk kwanakin nan wani aiki ya hana shi bacci. kowanne lkc ya fi maida hankalinshi ga yanda zaya binciko wadanda ke yiwa Familyn A.D Biliya tsohon Ministan Abuja kisan mummuke, sai a jiya ne aikin ya kammalu, don haka ya samu wannan baccin. Sama-sama yake jin wayarshi tana rigin, kusan sau 4 kenan cike da bacci ya kalli fuskar wayar, tsaki yaja sannan ya daga wayar Husna ya ya? Hjy ta ce kazo zamu fita ne har da Dady." "Ina zamu?" ya tambaya. Ta ce, "Sai ka zo za ta fada maka." Ya kashe sannan ya yi mika sosai, ya shiga toilet, ruwa ya watsa ya fito, ya yi fes cikin blue Jeans da farar riga, M.B yana son kananan kaya in ka gan shi da shadda ko yadi to Dady ne ya dinka mishi su, kuma ya tilasta mishi sa su in za su je daurin aure ko ziyarar dangi ya same su cikin falon shi da mahaifinshi kawai a ke jira. Cikin girmamawa ya kalle ta, Sannu Hjy cikin murmushi ta ce yawwa MUHAMMAD ka koyi kyau sosai, Safina ta ce, Hjy Bros ya san kaya fa, duk kayan da yasa suna yi mishi kyau sosai, Husna da Hjy suka hada baki gurin cewa tabbas, Guntu murmushi ya yi, na gode. Ya dan yamutsa fuska ina za mu? Za ka gani bari Dady ya fito. Itama haka take kiran Maigidan nata. Muryar Dady suka ji ya ce, "Gani na fito." Ga zaton M.B gidan abokan Dady za su kila ana yin wani abinne, to kuma biki ranar Sunday? Haka dai ya yi ta sakawa yayinda suke tafe cikin jin dadi. Direba ke jan su gefen shi M.B ne baya su Dady da Hjy tsakiya kuwa su Husna. . Cikin mamaki gami da sha'awa Shuwa ta ce, "Kin birge ni, kai Allah ya ba ki 'ya'ya masu zuciya, ni su Husna ba su da kishin kai da kyar in za su bani hadin kai. Yanzun kuma kudin ku na nan dankare?" Kilishi ta dube ta sosai matar ta zo nima haujaciya ce zan bari ya auro matar ta same ni da yara guda 3 ba dadi sannan ta baje wannan ta yi zazzaga haihuwa mata da maza haihuwarta fa 7, Shuwa ta ce tabdi gaskiya bn da wannan dabarar da tuni kudi sai dai a samanku, nima yanzun dabara hada shi nayi da Autarmu BASMA kuma tuni ya shige ciki ma'ana ya soma ruftawa cikin gadar zaren da na hada, domin zuciyarshi ta shagaltu da sonta. Kilishi ta nisa da cewa, "Menene dabarar?" Shuwa ta ce "zan gyara wani kuskure ne da na yi can baya lkcn yaron yana karami, na nuna mishi tsabar kiyayya karara inda na ringa hada shi da shokin in kona shi da wuta cikin tafin hannu ko kuma in zuba mishi barkono a idanu. Tilas ce tasa mahaifinsa ya fita dashi waje ba don yaso ba. Kilishi bai tashi dawo min ba sai a matsayin Dan sandan ciki, shi da ya tafi karatun Likita, kin san dole ne sai da dabaru kafin in cimma burina?" ta dan dakata kafin ta ci gaba "Ina so ne da zarar an daura auransu kafin shi da BASMA, sai in bata guba ta zuba mishi cikin ruwan sanyi ma'ana ba tare da kowa ya zarge mu ba. Yana mutuwa shi kenan daga ni sai 'ya'yana sannan tasu dukiyar ta gada domin yana amsar makudan kudi albashin sa bn da hayar da wasu kasashen suke yi. Hjy Kilishi ta ce, "Kina nufin har wasi kasashen suna hayar shi? Shuwa ta ce,"sosai kuwa, ya kware matuka kan aikinshi kasar da ya yi krt sun so rike shi da kyar suka bar shi ya dawo gida. Kilshi ta yi ajiyar zuciya tare da girgiza kai. Shawarata a nan ki bi sannu ki hana da hikimomi nasan wannan partyn da ki ka hada yana daga cikin dabarunki na son ki nuna kina son shi, sannan ya manta cewa kin ta6a mishi azaba. Shuwa ta ce, "Kin gane kawata, kuma a duk lkcn da na fahimce kwa6ata zaya yi ruwa zan kira ki in nemi shawararki don kina da basira. Suka yi dariya irin ta kawaye, sannan Kilishi ta sure Jakarta Bari in tafi sai na ji daga gare ki. Har gurin mota ta yi mata tattaki inda direba ya ja suka yi sallama ta dawo ciki.********* .14....Ina tafiya na dawo talla na hango BINTO, kira na kwala mata ta juyo sannan ta nufo ni da fara'arta, ta ce gida za ki? Na ce, eh, Yaya ADO yana gida? Binto ta ce, Eh, na barshi gida, na ce, mu dan je ya kara min mana domin na haddace na jiya.