Follow us on social media

Showing 27001 words to 30000 words out of 73194 words

Chapter 10 - Furuci Magana Mai Tsada by Mamyn Zarah

19 Aug 2026

138

tana buqatar samun kulawa daga mace sannan kullum tanayimaka kukan Ina Momy kaga idan kayi aure baby zatabar kukan rashin Momyn tata Dan Allah Zaffar " ajiyar zuciya yayi sannan yace

" Ammin bawai na'kiyin aure bane sabida kasa yarda da qaddara a a Ammin sedan bazan iya sake son wata 'ya mace ba Ammin banaso nayi aure amma yazama nakasa sauke haqqin matar sabida gaskiya tunda Nuratu tarasu narufe zuciya ta na kulle idanuna daga kowace irin mace ayanzu babu abinda nike kallo naji dad'i kamar baby kuyi ha'kuri Ammin bazan iya sake saka wata mace cikin zuciya ta ba zanjira har namutu naje natadda matata Nuratu ina roqon Allah yahad'a mu cikin gidan aljanna tare "

Ajiyar zuciya Ammin tasauke tace " amin ya Allah amma Zaffar amatsayina na qanwar Mahaifiyar ka ina roqon wata alfarma kuma banaso kayi musu idan har na'isa Zaffar inaso ka auri 'yata Bahijjat " saurin dubanta yayi sannan yadubi hanyar da Bahijjat tabi bayan takawo mishi abun motsa baki bud'e baki yayi zaiyi magana Ammin tace " karkace komi ni zanji da komi Zaffar dan Allah karkace a a tabbas zakasamu tsananin kulawa agun Bahijjat Kuma daga lokacin da Bahijjat tashiga gidan ka baby tabar kukan rashin Mahaifiya idan har dagaskene bakason damuwar baby balle kukanta to kasamar mata da wata Mahaifiyar wacce zata maye mata gurbin tata Mahaifiyar "

Iska Zaffar yafesar yace " shi kenan Ammin amma fa banajin zanso Bahijjat zanyine dan ke Kuma dan baby amma badan ra'ayin kainaba " sosai Ammin taji dad'in hakan tashi yayi yayimata sallama yafita Kiran Bahijjat tayi cikin sanyin jiki Bahijjat tafito tariga duk taji komi zama tayi kusada Ammin cikin wani irin yanayi murya a raunane tace " Ammin Abbee yariga ya amsa cewa Abdul zan aura Kuma Ammin Zaffar basona yakeyiba inajin tsoron auran Wanda bana gabanshi " jawota Ammin tayi jikinta tace

" Kwantar da hankalin ki Bahijjat nasan Zaffar zesoki Kuma zakiji dad'in zama dashi sannan maganar auran ki da Abdul abune mai sau'ki wajan warware shi amma idan Kika sanar da Saraki cewa bakison Abdul ke Zaffar kike so tonasan zeyima mama magana Kuma kinsan yadda mama takeson Saraki duk abinda yakeso zatayimai Babu musu bari zankirashi dakaina muyi magana dalilin dayasa nace ki auri Zaffar idan babu maganar auran wani tofa babu mafita kuma badan Zaffar yana matsayin d'ah agareniba nake son ki aure shi a a kyawun halin shi da kamalar shi tasa nike miki shi'awar auran shi dakuma gujema auran Abdul " murmushin farinciki Bahijjat tasaki sosai taji dad'in abinda Ammin tace amma tana tunanin yadda zatayi zaman aure da Zaffar dan tasan halin Zaffar danuna halin ko in kula damutun

Bayan Bahijjat tatashi Ammin takira Saraki take sanar da shi suna gama waya Saraki yakira mama magana yayi mata a takaice " _mama barka da yau fatan kina lfy naji kince maganar auran aunty Bahijjat to amma mama ni yanzu bankai matsayin asanar daniba ? kema kinyarda ni marar hankalin ne mama ? komade Yaya kuka d'auka ni amatsayina na shaqiqin Aunty Bahijjat tuni nariga nayima akeey Zaffar al'kawarin auran Aunty Bahijjat Kuma itama nasanar da ita kuma ta amince dama jira nikeyi Abbee yazo nasanar dashi to amma ni bazance kucanza ra'ayin kuba amma idan kuka qi to tabbas kund'aukeni marar hankalin nabarku lafiya_ "

Kafin mama tasakecewa komi tuni Maher yakashe Kiran sosai hankalin mama yatashi tuni tasa aka kiramata maimartaba da hjy Himla da su Ammin Babu 'bata lokaci kowa ya hallara cikin parlour bayan kowa yazauna mama tadube su tace " ke Himla akan maganar auran Bahijjat da Abdul ayanzu Kam Babu ita kafin maganar Abdul tuni Saraki ya amshi maganar Zaffar wato d'an wan Batol se yanzu yake sanar dani Sabida haka Abdul yayi haquri yanemi wata mu aura me " wani irin farinciki kowa yaji amma banda hjy Himla data miqe tace

" Amma gaskiya mama hakan beyiba yanzu ace har Saraki yakai matsayin amsarma Bahijjat miji bacin matsayin qani yake gunta gaskiya idan akayi hakan babu adalci yaron da Babu tabbacin yana cikin hankalin shi yake sanar daku k...... " Ke Himla kishiga cikin hankalin ki Mahaifiyar tamu kike yima magana haka tobari kijj Saraki shine magajina duk da yake qarami cikin su to tamkar shine babba sabida shine namiji idan bana guri shine jagoran su dan haka yanada cikakkiyar damar za'bama Bahijjat miji dukda tana matsayin Aunty shi sannan daga yau karki sake fad'in kalmar hauka akan Saraki Shiba hauka yakeyiba lalurace Allah yasaukar mishi Kuma in sha Allah tazo 'karshe mama Ina godiya agareku dakuka babbatar ma Saraki cewa ya Isa dakoma cikin masarautar nan Ammin Saraki kisanar da Zaffar na amince yaturo magabatan shi "

Daga haka Sarki Zaid yafita Ammin da Umma Suma sallama sukayima mama suka bar parlour itako hjy Himla afusace tabar parlour tana shiga cikin parlour ta tad'auki wayarta takira bokan ta yanad'agawa tace " boka akwai matsala fa wannan banzan Saraki yana lalata min komi dan Allah kasheshi nike buqata tuntuni amma kakasa haba boka gaskiya nagaji idan bazaka iyaba to kasanar dani nacanza guri " dariya boka yasaki sannan yace " haba hjy Himla karki bani kunya Mana komi yakusa zuwa qarshe yanzu matsalar mu wannan matar tashice bamu iya yimata komi sabida tanatare da addu'a akoda yaushe Kuma ayanzu haka tafara shayer dashi addu'ar Kuma yafara samun sau'ki amma yanzu matakin dana d'auka shine zamu gigita ta tahanyar bata tsoro zamusa adinga furgitata sosai ta yarda dole zatabar gidan ki saurara kiji Nan kusa zatabar gidan Maher "

Ajiyar zuciya hjy Himla tayi sannan tace " to naji amma inaso kalalata auran Bahijjat da Zaffar da'ake Shirin qullawa " dariya yabushe da ita sannan yace " angama kisaurari ayki kawai amma inajiran ganin saqon Kaya masu nauyi " tsaki hjy Himla taja tace " yaushe na ayko akakawo maka kud'i to kasani inajiran naga ayki yaci kafin nasake ayko dawasu kayan " daga haka takashe wayar "

Zama tayi kan cushion tana huci dede lokacin Abdul yashigo ganin yadda ran Mahaifiyar tashi yake a hatashe yasa Abdul dakatawa tambayar ta yashigayi cikin fushi Abdul yace " Mom wallahi tunda aka hanani auran Bahijjat sena lalata mata rayuwa wallahi senasata taje gidan mijin batare da budurci ba tuni nike kwad'ayin surar jikin Bahijjat Mom zasunan ni suka hana auran Bahijjat " murmushin mugunta hjy Himla tayi tace " kayi duk abinda kake ganin zaisaka kahuce my son " murmushi yasaki yace " zanyi kuwa Mom

USA

Akwana atashi babu wuya ayau ne doctor yake kan hanyar zuwa USA Abbee Kuma yasaka a Nigeria abubuwa dayawa sunfaru kafin wannan lokacin sosai Iftahal tayi muguwar rama sabida ko abinci bata iyaci hatta ruwa idan zatasha inba tayi addui ba seyakoma kamar jini duk tagama furgicewa yauma kamar kullum hankalin ta cikin Matu'kar tashe yake Sabida tayi duk tunanin dayakamata amma tarasa yadda zatayi wajan hana doctor yin wannan allurar shigowar Maher yasa Iftahal saurin zaunawa isowa yayi yazauna kan cushion ciro sigari yayi yakunna yafarasha kallonshi Iftahal tashigayi sosai tanajin matu'kar tausayin shi da tsananin qaunar shi cikin zuciyar ta d'an dubanta yayi se'alokacin yaga tayi wata irin muguwar rama sosai yaji mamakin hakan a hankali yadubeta yace

" Iftiih!!!! meye dalilin ramarki nalura bakison cin aminci sannan kinsan nace idan har kinason nayi miki abinda kike so to yazama dole ki kwantar da hankalin ki amma bakiji magana taba " cikin raunin murya Iftahal tace " bahaka bane Prince kusan 1 week kenan banajin dad'in jikina shine kawai amma Babu wata damuwa " jinjina Kai yayi sannan yamiqe yace " tashi muje Asibiti " daga haka yanufi hanyar fita cikin sanyin jiki tamiqe dan Babu yadda zatayi tabbas batajin dad'in jikinta to amma batason zuwa asibiti d'an tsayawa tayi tace " am Prince nifa banason zuwa asibiti nan naji sauqi sosai " wata irin harara yasakar mata dole tashiga bedroom ta d'akko gyalenta tana fitowa yawatsa mata wani irin kallo yace " bana buqatar shigar banza " duban mayafin tayi ba qarami bane Kuma yarufe mata jiki sosai " dole takoma ta d'akko hijab tafito suka fita

Nigeria

Sarki Zaid da waziri da liman suka sauka Nigeria cikin babban birnin tarayya wato Abuja basusha wahala ba wajan Isa gidan Alhaji Ishaq wato minister kud'i sosai akayimusu tarba tamusamman bayan sunhuta suka zauna cikin ke'bantaccen parlour duban Alhaji Ishaq Sarki Zaid yayi sannan yace " Alhaji kasan daga Egypt muke tun zuwanmu amma zansake sanar dake sunana Zaid Irfan wato Sarkin qasar Egypt ayanzu nine mahaifin Maher wato mijin 'yarka Iftahal Alhaji nataso daga Egypt ne har nan Nigeria dan baka ha'kuri akan abinda Maher yayi shine yakeda lefi ba Iftahal ba sabida ita FURUCI!!!! tayi bada niyar yin aure ba amma FURUCIN!!!! yazama dalilin auran su to mud'auka wannan abun daga Allan ne tunda kaga hakan tafaru to Allah kad'ai yasan dalilin haka iname baka ha'kuri Kuma Ina taya Iftahal da Maher roqon ka akan kayafe musu dan Allah musamman Iftahal kasan fushin iyaye akan 'ya'yan su babbar matsalace dan Allah kayi ha'kuri sannan ayanzu inajiran duk wani bayani akan yadda kuke shirya naku auran zamubi dukkan wata al'ada taku aure de anriga anyi duk mubar wa Allah ikon shi "

Mi'kewa Alhaji Ishaq yayi sannan yace " nayi farincikin zuwanku hakan yasa na tabbatar kai Sarki ne Mai adalci cikin masarautar ka tunda har ka it's tasowa daga Egypt zuwa Nigeria akan bani ha'kuri dakuma neman yafiya nagode sosai amma sede wani abu 1 ni banayin magana nacanza bazan iya maida Iftahal matsayin 'yataba nariga nayafeta gareku nikam banida wata 'ya maisuna Iftahal kusani nayafe mata Amma bana bu'katar sake ganinta arayuwata har abada nagode sosai Maimartaba inatayaka munar samun qaruwar wata 'yar wato Iftahal " mi'kewa Saraki Zaid yayi yace " nagode sosai daga yafe mata Kuma nayi matu'kar farinciki dabani 'yah mai hankali da tarbiyya irin Iftahal muzamu koma fatan alkairi ga sadakin Iftahal Nan " saurin juyowa Alhaji yayi yace banida alaqa da sadakin 'yar daba tawaba dan haka bana bu'katar ganin su " sake Sarki Zaid yayi yafita waziri ne yad'akko kud'in suka fito hotel suka nufa Sarki Zaid sosai yashiga damuwa akan yadda Alhaji Ishaq yayi fushi da Iftahal

USA

Suna Isa asibiti doctor Sera tayima Iftahal tambayoyi sosai bayan haka aka d'ibi jininta akashiga gwadawa bayan wani lokaci doctor Sera tadawo zama tayi tadubi Maher da Iftahal tayi murmushi tace " Prince ina tayaka murna gimbiya tanada ciki tsawon 5 weeks " cikin matu'kar mamaki Maher yadubi Iftahal zaro ido tayi tadafe qirjinta tsayin lokaci yakasa denayimata kallon mamaki itakuma takasa cewa komi kuma takasa d'auke idon ta daga kanshi juyawa yayi yafita afusace batare dayace komiba


Comments please

_Marmny Zarah_ 🀝🏻πŸ₯°
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 23 to 24

Cikin matu'kar razana Iftahal tadubi Doctor Sera tace " doctor wai dagaske cikine dani ? " sake tabbatar mata doctor tayi sosai hankalin Iftahal yatashi d'an dedeta natsuwar ta tayi sannan tace

" Am doctor kibani allurar bacci idan naje gida zanyima Prince sabida bayasamun bacci sosai tambayoyi doctor tashiga yimata sosai sannan tabata cikin mutuwar jiki Iftahal tafito Koda tafito babu ko alamar Maher agurin sosai hankalin ta yasake tashi tunanin mafita tashigayi amma tarasa wasu irin hawaye masu zafi taji suna sakkowa daga cikin idanunta tsayin lokaci tarasa abinyi isowar wata mota tasa Iftahal d'an ja baya cikin sauri Shanwul yafito yanufo inda take ganin tana zubda hawaye yasa Shanwul saurin cewa " gimbiya lfy ? " Saurin share jawayen nata tayi sannan tace " lfy Lau kaina yakeyin ciwo " jinjina Kai yayi badan ya gamsuba cikin girmamawa yace " Prince ne yace nazo nad'aukeki amma nayi mamakin haka sabida naga shima gida yayi " d'an murmushin ya'ke Iftahal tayi tace " kajika sekace bakasan halin Prince ba dubani akatsaya yi shine yace shi bazai tsayaba " jinjina Kai Shanwul yayi kafin yace wani abu Iftahal tanufi mota dan batason sakeyin wata magana cikin sauri Shanwul yabu'de mata motar tashiga a cikin motar Iftahal tahad'a wannan allurar cikin sirinji bayan tagama tadubi Shanwul tace

" Doctor ya iso kuwa ? " Cikin sauri yace tun bayan fitar ku babu jimawa jin haka yasa Iftahal saurin cewa dan Allah kayi sauri ka kaini gida " jin haka yasa Shanwul sake taka mota suna isa tafito cikin sauri tanufi ciki tana shiga tahangi doctor yana neman jijiya zeyimai allurar cikin sauri ta'karasa fige allurar tayi saurin juyowa doctor yayi shikuma Maher yami'ke wani irin kallo yashiga yimata saurin dedeta kanta tayi tace

" Haba Prince kasanfa nace maka daga yanzu nice wadda zandinga yima allura tunda kasan abunda nike karanta kenan amma shine kaqi jirana ? "

Rai 'bace Maher yace " bashi allurar nan tun kafin ranki ya'baci " ganin yadda yahad'e fuska yasa Iftahal miqa mishi tajuya tabar gurin tana shiga bedroom tasauke ajiyr zuciya had'ida fad'in nagode ma Allah Prince yau sede kasha bacci kawai doctor in sha Allah muguwar allurar ka tadena shiga cikin jikin Prince fiddo da allurar tayi tana dubawa alokacin da ta amsa kasancewar hijab ne jikinta yasa tayi saurin canza allurar data baccin data amso a asibiti

Zama tayi bakin bed tashiga tunanin yadda zatayi wajan fahimtar da Maher kuka tasaki Mai tsuma zuciya se ayanzu tayi nadamar rashin sanar da Maher batun fyad'en a parlour kuwa sosai doctor hankalin shi yatashi yayi yazon Iftahal tagane komine amma dayaji abinda tace se yad'an samu natsuwa Yana amsar allurar yayi saurin yima Maher sabida Kar akuma samun wata matsalar ana gama allurar Maher yami'ke yanufi bedroom d'in Iftahal yana shiga tayi saurin mi'kewa cikin zafin rai da dakakkiyar murya yace

" Ke yazama dole kisanar dani uban wannan cikin naki idan kuma kikaqi to wallahi zanyimiki hukunci mafi muni a rayuwar ki sekinyi nadamar sanina ke bama nadamar saninaba har nadamar zuwanki duniya sekinyi " wani irin kuka Iftahal tasaki ta durqushe saman gyuwoyin ta a gabanshi

Tofa danjin mak Iftahal zatace se Allah yahad'a mu a page nagaba gobe in sha Allah kuyi ha'kuri da wannan

Comments please yawan comments yawan typing

_Marmny Zarah ce_ 🀝🏻πŸ₯°πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login