Follow us on social media

Showing 72001 words to 73194 words out of 73194 words

Chapter 25 - Furuci Magana Mai Tsada by Mamyn Zarah

19 Aug 2026

132

cikin tashin hankali Kaka mama Sarki Zaid Umma Ammin dasu Aunty kurrat kowa yamiqe cikin matuqar mamaki darajana kowa yadubi Maher saurin kawar dakanshi yayi sabida bayason su kashemai gyuwa wajan gabatar da shari'ar "

Bayan Alqali yazauna akafara gabatar da shari'ar kamar haka

Barrister Maher yamiqe yace " yamai girma mai Sari'a ayau inatafe da manyan hujjojin dazasu tabbatar da wa'inda sukayi wannan kisan idan kotu tabani dama zanyima Alhaji Tukur wasu tambayoyi " kotu tabaka dama juyawa yayi ya'isa gaban Alhaji Tukur duban shi yayi sosai cikin damuwa Alhaji Tukur yajuya yadubi Ammin sannan yadubi yaranshi yaduqar da kanshi cikin tsananin nadama ajiyar zuciya Barrister Maher yasauke yace

" Alhaji Tukur kasanar da kotu dalilin dayasa kuka kashe baby Kuma kai dasuwaye ? " Cikin raunin murya yace

" Nikam babu tsarin kashe baby cikin shirina ni matar ka da yaranka nikeson kashewa Kai Kuma nasaka rayuwar ka cikin tashin hankali kamar yadda nayi abaya dani da Hjy Himla dakuma wadda baikamata nafad'i sunanta ayanzu ba sabida tuni ita tatuba tunkafin zuwan wannan ranar ta tonon asiri agaremu dan haka babu buqatar sake sakota cikin lamarin mune muka sakaka cikin wannan muguwar lalurar Maher tasanadinka nakashe mutane dayawa nazama sanadin kwantawa ciwon kakanka nine nasaka aka kashe doctor darman Kuma nasaka aka kashe mahin wato wanda yakashe doctor darman bayan ankamashi anbashi wuya sosai amma Koda sunana yaqifadi har nakwanta ciwo bayan nawarke nasaka aka kasheshi duk dan dalilin abu 1 shine Mahaifiyar ka nasota so mai tsanani amma taqini taje ta auri mahaifin ka hakan yasa naqudiri niyyar sakata cikin masifa da tashin hankali nine nayi asirin dabata sake haihuwa ba tun daga kanka

Maher nine nasaka aka rabamin qwaqwalwar ka biyu tahanyar tsafi itakuma Hjy Himla ta turomaka manyan aljanu sannan nahad'a Kai da doctor darman yake canza allurar da akeyimaka sannan nine nasaka akamaka muguwar allurar datasaka kayima Iftahal wannan mugun fyad'en Kai Kuma nasaka ayimaka wannan allurar wadda zata kashe qwayoyin halittar haihuwar ka amma se matarka tasauya allurar bayan ta amshi ta hannun Doctor darman tabada ta bacci akayimaka

Bayan na warke muka had'a Shirin sake tarwatsa farincikin dakuke ciki nida Hjy Himla ananne shirin kashe baby yashigo sabida Hjy Himla tayi alqawarin kuntatama gimbiya Bahijjat shiyasa tafara takanta kafin mudawo kan ku munyi amfani da Ayna ne sabida qiyayyar damukaga tanayima gimbiya Bahijjat tabbas batasan suwaye muba waya kawai mukeyi nine wanda yanemo gubar Hjy Himla kuma itace tasaka wannan gubar cikin yoghurt d'in sannan akabama qawarta taje tasaka cikin motar Ayna itakuma Ayna taje tabama baby yoghurt d'in tasha kagin kagano komi yasa mukasaka a harbe mana Ayna dan kar asirinmu yatonu bayan nan mukasaka aka sacemin yaranka biyu wannan shine gaskiyar lamarin Ina roqon kotu datayimin sassauci natuba bazan sakeba

" Sosai kotu takaure da la'antar su Alhaji Tukur su Kaka kuwa kuka kawai sukeyi sabida mugun baqin ciki Ammin kuwa tafi kowa kuka Sabida jitakeyi duk tasanadinta ne komi yafaru duban Hjy Himla Barrister Maher yayi yace " Momy kinadaja akan abinda Alhaji Tukur yafad'i ? "

Cikin matsanancin kuka tace " a a babu gaskiya ne duk abindayafadi dan Allah Saraki kayafemin nacutar dakai nasan nima ayanzu kasheni za'ayi dan Allah ga Abdul nabaka amanar shi nasan Kai Mai maida alkairi ne akan sharri yaciyo bashin banking dan Allah kabiya mishi kagyaramin rayuwar shi Ni nakasayin haka kwad'ayin abun duniya yamakantar dani Maher katayani roqon su mama da Yaya Zaid da Mahaifiyar ka suyafemin dan Allah sannan tabbas nasan Zaffar da Bahijjat bazasu iya yafemin ba amma dukda haka dan Allah kace suyafemin "

Allah sarki zuciyar dake cike da imani tana saurin manta sarri rungumai ta Barrister Maher yayi yana kuka yace " nayafemiki Momy duniya da lahira suma zasu yafe Miki in Sha Allah Kuma nayi miki alqawarin biyan banking wannan kud'ad'an Koda duka dukiyata ne zanbayar Momy har abada ke uwace agareni har namutu bazan ta'ba kallon Abdul amatsayin maqiyiba har abada shid'in Yaya nane " kuka Abdul yasaki sosai yadubi Hjy Himla amma yakasayin magana tashi Kaka da mama sukayi suka fita dan Kam bazasu iya kalloba gyaran murya Alqali yayi yace

" Duba da kwararan hujjojin dakuma fad'in gaskiya damasu lefi sukayi wannan kotu Mai adalci zata yanke hukunci kamar haka " Alhaji Tukur kotu tayanke mishi hukuncin kisa tahanyar harbi da bindiga Hjy Himla kotu tayanke mata hukuncin d'aurin rai da rai a gidan yari tareda ayki mai wahala Ayna da 'kawar Hjy Himla kotu tayanke musu hukuncin d'aurin 20 yrs agidan yari kooooooootuuuuuuuu "

Ihu Alhaji Tukur yasaka hakama sauran sunaji suna gani akasakasu a mota Abdul yana kallo katafi da Momy shi durkushewa yayi yasaki kuka mai qona zuciya sosai su Kaka sukayi baqinciki to amma yaya zasuyi

Bayan kwanaki 2 Aunty kurrat tazo ganawa tayi da Maher shi daya tasanar dashi gaskiyar lamari takuma roqeshi yafiya yakuma yafe mata sannan yace tabar maganar iya ita dashi kawai

Sosai Maher yaqarajin tsananin son Iftahal shiryamusu zuwa Nigeria yayi hadda Abdul bayan yabiya mishi bashin banking sosai su Abba da Ummi sukayi farincikin zuwansu sabida tsananin farinciki sunma rasa Ina zasusakasu duban Iftahal Zayyat yayi yace " iyye Iftahal kece haka ah lalle yazama dole nacanzama matata cima dan kam nafiso tafiki " dariya kowa yasaki seda sukayi 5 months a Nigerian alokacin Abdul yasamu mata Yar dan uwan Ummi Kuma akabashi sannan suka koma Egypt

Har gidan yari suka kaima Hjy Himla ziyara tarame sosai tayi duhu kasa kallonta Abdul yayi cikin kuka Abdul yace " Momy kinsoni fiye dakomi hakan yasa Kika manta da aykata Dede dan kawai nakasance cikin daula da farinciki segashi yau kinacikin irin wannan halin amma ni nakasa cireki seyanzu nace kaicona dama kin kuntatamin rayuwa ta dama kince nabar kallon nasama dani dama idan nace inason abu idan baidace danibe dakin dakeni akan nabarshi baki biyemin ba Momy wannan kalmar tayi tasiri akanmu wadda akace son zuciya bacin zuciya nashiga 3 Momy dama baki haifeni ba "

Jin wa'innan maganganun yasa Hjy Himla koma aguje cikin tsananin kuka da kyar Maher yaja Abdul suka bar gurin

Bayan wasu lokuta gimbiya Bahijjat tahaihu lfy tahaifi 'yah mace Akeey Zaffar yamayer da sunan baby Yar kuwa tamkar an tsaga Kara itada baby bayan wasu shekaru sarki Zaid yayi murabus Allah yayarda Saraki yazama Sarki Mai cikakken iko da adalci tamkar mahaifin shi ayanzu Iftahal yaranta 2 ta haifi 2 bayan su Irfan mace da Namiji


TAMMAT BI HAMDULLAH ALHAMDULILLAH 🤲🏻

Ina godiya ga Allah subahanahu wata'ala dayabani ikon kammala wannan book nawa Masha Allah Alhamdulillah alakulli halin ya Allah abinda nayi kuskure acikin shi Allah kayafemin abinda nayi dede Allah kabani ladan shi ameen


Dun bin godiya agareku masoyana Ina jinjina agareku baki daya ana mugun tare semun had'u a saban book Wanda shi na free ne wato JUYI BIYU bayan shi se cigaban Mugun Sartse wato Akwai banbanci Wanda shi ze kasance nakudi ne tabbas zakuji dad'in shi akwai cakwakiya dan haka kowa yashirya

semun had'u ranar Saturday danjin sabon book ☪☪ JUYI BIYU ☪☪

TAKU HAR KULLUM NPEEDY A AJI
MARMYN ZARAH 🤝🏻👌🏻🥰

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login