Follow us on social media

Showing 51001 words to 54000 words out of 73194 words

Chapter 18 - Furuci Magana Mai Tsada by Mamyn Zarah

19 Aug 2026

76

A AJI TAKUCE HAR ABADA

🅿 51 to 52

Komawa Shukura tayi tazauna cikin takaici tama rasa wane irin tunani zatayi tsayin lokaci tana zaune agurin sannan tamiqe komawa cikin bedroom d'in ta tayi tasaqa wancan ta kwance wancan tunda Zayyat yafita bai dawoba se wajan 10 sannan yashiga yana shiga yarufe qofar part d'in sannan yanufi cikin cikin sauri Shukura tamiqe tasha gabanshi dubanshi tayi tace

" haba Zayyat duba agogo sabida Allah see yanzu kake dawowa tun d'azu dinner take jiranka ga yunwa inaji amma nakasaci sabida inajiran ka kadawo muci shine se yanzu " duban ta yayi sosai cikin mamaki yace " ni kikayima dinner Aunty Ina badai niba kodama danni kikayi tofa bazanciba sabida bansaba da hakanba nariga naci abincina a inda nasabaci sabida haka daga yau karki sakeyin abinci danni " daga haka yabi ta gefanta zai wuce cikin sauri tariqo hannun shi cikin saurin murya tace " haba Zayyat dan Allah muje kaci idan kuma bakaciba tonima bazan ciba "

d'an murmushi yayi yace " nace bazanciba kekuma idan bakiciba matsalar kice tunda nasauke miki haqqin ki " fizge hannun shi yayi zaibar gurin sake kamo hannun nashi tayi tace " hakane amma ay baka gama saukemin duka haqqin nawaba "

Cikin mamaki yasake dubanta yace " haqqi Kuma to sanar dani wanene ban saukeba kinsan shi'anin yaro bakomi nasaniba cikin shi'anin aure " kasayin magana Shukura tayi murmushi Zayyat yasaki yabar parlour yanufi bedroom d'in shi yana shiga yanufi bedroom toilet yashiga yayi wanka yashirya bacci ya kwanta a 'bangaran Shukura kuwa bayan tagama Shirin bacci tafeshe jikinta da turaruka masu kamshi kaiwa da komowa tashigayi cikin bedroom d'in ta tsayin lokaci sannan ta rumtse idon ta tafita bedroom d'in Zayyat yanufa bakin qofar tatsaya tsayin lokaci sannan tashiga ahankali Zayyat yabud'e idonshi ganin Shukura yasashiyin mamaki sosai sake rufe idonshi yayi kamar baiji shigowar taba qarasowa tayi bakin bed d'in tazauna tsayin lokaci sannan cikin qasada murya tace

" Zayyat inasonyin magana dakai " shiru yayi kamar bai jitaba sakeyin magana tayi nan ma shiru juyowa tayi tad'an ta'bashi bud'e idonshi yayi yaja tsaki yace " lfy Kika shigomin bedroom a irin wannan lokacin ? " sassauta murya tayi tace " magana nikeso muyi d'azu kace min wane haqqine yarage baka saukemin ba shine nazo nasanar dakai "

Tashi zaune Zayyat yayi yace " Ina sauraranki " ajiyar zuciya tasauke sannan tace " bai kamata muraba wajan kwanciya ba sabida akwai wani haqqi dayakamata musauke wa juna a wajan kwanciyar Kuma Zayyat kafasan matsalata Kuma kasan abinda doctor yace shiyasa nayanke shawarar cigaba da kwana cikin bedroom d'in ka " taqarashe fad'ar hakan cikin raunin murya "

Sosai Zayyat yadubeta cikin mamaki yace " haba Aunty Shukura yanzu bakiji kunyar yima qaninki wannan maganar ba ? lalle amma nayi mamakin haka to amma dukda haka zan baki amsha naga kece kikace kar nasake zuwa bedroom d'in ki sannan ni yarone ba zaki'iya saukemin haqqoqina ba sannan sanin cewa kinada matsala shiyasa nan kusa zan sauwaqe miki ki auri mijin dakikeso wanda zai iya yimiki maganin matsalar ki nima bazan iya aywatar dakomi akan kiba sabida ina matuqar jin kunyar Aunty na "

Yana gama fad'ar hakan yajuya ya kwanta sosai maganganun Zayyat sukasa Aunty Shukura kasacewa komi zuwa can sannan tace " shikenan bazan hanaka yanke duk abinda kakesoba amma kasani daga yau anan zandinga kwana "

Tana fad'in haka tajuya ta kwanta kusadashi murmushi yayi sannan yace " hakan ba haramun bane tunda matsayin mata kike aguna amma bakiji kunyar kwanciya a bed d'aya da qanin kiba ? " shiru Aunty Shukura tayi dan batasan mai zatace mishiba tun daga wannan lokacin Aunty Shukura takoma kwana cikin bedroom d'in Zayyat amma ko sau 1 baiko ta'ba saka hannun shi akan jikinta ba ita kuma tanajin nauyin tunkarar shi da wannan buqatar

Egypt

Yau akeyin gagarumin biki cikin masarautar Sarki Zaid wato bikin Aunty Sumeer da Aunty Bahijjat sosai akatara manyan baqi ciki haddasu Maher karo nafarko dayazo Egypt tunbayan tafiyar shi USA sosai aka shiryamusu tarba kamar dansu ake wannan babban bikin Mama kuwa kamar ta'bace ta ganta a airport wajan tarbar su Maher dole akaje da ita airport sabida tace bazata iya jira sesunzo ba tun kwanaki biyu kafin wannan ranar akaso suzo amma sabida sunada Exam shiyasa se yau ranar bikin d'inbin jama'a ne sukaje tarbar su jirgin yana sauka kowa yazuba ido yanajiran ganin Maher da Iftahal sune farkon sakkowa Maher yana rungumai da Iftahal suna sakkowa ahankali sabida yadda cikin nata yayi girma kamar ba 5 months ba

Zaro ido Mama tayi tayi saurin nufarsu cikin farinciki ta rungumo Iftahal tanayimata sannu sannan tadubi Maher tace " Saraki yau kaina cikin qasar Egypt bayan wasu shekaru nayi kewarka sosai Saraki sannan Ina matuqar farincikin shigowar ka Egypt batareda wannan mugun ciwon ba Allah muna godiya agareka Allah katashi kafadar Alhaji shima yaga wannan farincikin danasanar dashi kayi aure har ma munsamu qaruwa har kuka yayi sabida farinciki g......."


Kafin tasakeyin magana hjy Himla cikin qufula tace " Wai mama su Saraki kawai kika gani ? " dubanta mama tayi tace " ayya Himla ay bazan gankiba kefa iya wata 3 kawai kikayi bakinan amma Saraki shekaru yayi sannan itakuma matar shi banko ta'ba ganin taba gashi dama Ina matuqar son ganinta sabida silarta munsamu nasarori dayawa " sosai hjy Himla taji haushin maganar Mama cikin zuciyar ta tace " habawa yadda yazo bazai komaba daga shi har ita wannan damace nasamu nakashe su cikin hidimar bikinnan babu wani zargi akaina sabida akwai mutane dayawa " amma a fili sakin fuska tayi tace

" Gaskiya ne mamana dama zolayarki nayi Wai nikam Ina Abdul wato koma yazo tarbana ko ? " Murmushi mama tayi tace ay kinsan halin rigimar Abdul tun safe yana cikin part d'in ki yaqi yafito idan kika isa Kya sashi ko wanka yayi " daga haka taja hannun Iftahal suka nufi mota suna isa gida akashiga bushe bushe da kirari seda sukayi dagaske sannan suka samu wucewa ciki sabida yawan jama'a Kai tsaye part d'in Ammin Maher yanufa yana shiga yarungumai Mahaifiyar tashi sannan yarungumai Umma dake gefanta duban Aunty kurrat yayi yasaki murmushi yarungumai ta sosai yace " I miss u my big Aunty kullum kina cikin raina nayi missing hararar ki " sakinta yayi yakoma wajan Aunty Faheemat yarungumai ta sosai yace " wayyo Allah My Sweet Aunty nayi kewarki sosai Ina yunwar wannan daddad'an abincin naki sosaifa Sweet Aunty " sakinta itama yayi yarungumai Aunty Sumeer yace " Alhamdulillah my Dear Ina mugun kewarki nayi missing wannan zolayar taki yauga qanin naki yayi miki murmushin dakika dad'e kinaso congratulation for wedding my dear "

Fad'ad'a murmushin shi yayi yanufi wajan Aunty Bahijjat sumbatar goshinta yayi sannan yayi mata runguma tamusamman sannan yace " dama nace rayuwa zatazo da sauyi My little Aunty yau gashi zakitafi kibarmin Ammin nima kibarni dukda ayanzu kinsaba cin abinci babu Saraki kinbar kukan yin nesadani amma yau gashi nadawo cikin qasar Egypt cike da kewar cin abinci tareda My little Aunty na sekuma gashi ke zakitafi Ina roqonki da kijuyar dayin hakan wa Akeey na Ina matuqar farincikin wannan auran haqiqa Aunty Bahijjat banida tamkarki duk cikin 'yan uwana kece idan kikaga inayin kuka kema kikeyi idan nakasacin abinci kema kike kasaci idan banyi bacciba kema baki iyawa tabbas kin cancanci nasadaukar dakomi danke "

Kuka Aunty Bahijjat tasaki hakama wasu daga cikin 'yan parlour sabida kalaman sun ratsa cikin zuciyoyin su itako Aunty kurrat cikin zuciyar ta tace " lalle ashe duk irin kallon danikeyima Saraki yanasane dani lalle ashe nagode ma Allah dayasa Umma tayimin katanga daga cutar dashi Suma sauran godiya sukayima Allah dabasu d'auki shawarar Aunty kurrat ba sabida ayau sun sake tabbatar da Saraki yanayimusu so mai tsanani kuma na tsakani da Allah haka akacibaga da hidima Iftahal kuwa tanagun mama tacikata da duk wani nauyin ciyeciye misalin 5 ankusa zuwa d'aukar amare wani yaro cikin yaran baqi 'yan biki yashigo yace wai ance amarya Bahijjat tazo wai zasu gaisa da abokin Zaffar jinjinawa tayi itama Ammin haka zuwa can sannan Ammin tace aboki Kuma amma tashi kije qila saqone tashi Aunty Bahijjat tayi tafita cikin sanyin jiki Maher dake kwance cikin bedroom d'in Ammin yatashi zaune yace

" Aboki Kuma na Akeey Zaffar Ina hakan bazai yiyuba " sakkowa yayi daga bed d'in yafita 'bangaran saukar baqi maza yanufa amma basa can kiran wani hadimi yayi ya tambaye shi ina yaga Aunty Bahijjat tayi nuna mishi hanyar part d'in hjy Himla yayi yace nan naga sunbi itada wani yaro " jin haka yasa Maher bin wajan da sauri itako Aunty Bahijjat cikin mamaki takebin yaron ganin sun nufi Part d'in Hjy Himla yasa taji hankalinta ya kwanta tana shiga Abdul dake bakin qofar a la'be yayi saurin janyota tafad'a jikin shi wata irin muguwar dariya yayi yace "

" Dama nayi alqawarin bazakije gidan wancan banzan da budurci ba badai kin qinina to yau zan amshi abinda kika dad'e kinayima wannan ranar tafad'i " daga haka yajata da qarfin ciya zuwa cikin bedroom d'in shi yana shiga da ita yaturata saman bed yarufamata baya cikin sauri dede lokacin Maher yashiga cikin parlour kuma a dede lokacin Aunty Bahijjat tasaki qara saurin shiga cikin bedroom d'in Maher yayi abinda yagayi yasashi matuqar harzuqa cikin zafin rai yashago wuyan Abdul tabaya yafito dashi parlour wani irin mugun duka Maher yashiga kaimai da d'ayan hannun shi duk inda yasan zaimai illa nan yake bugu kafin wani lokaci tuni Abdul yayi laushi gashide shine babba amma abin mamaki yakasa ta'buka komi akan Maher dede lokacin hjy Himla tashigo ganin Abdul cikin mawuyacin hali yasata sakin fuler din hannun ta yawatse kafin tayi magana cikin fusata Maher yace

" nakamashi da yunqurin yima Aunty Bahijjat fyad'e dan haka zanje narufeshi kafin ya amshi kuhunci " zaro ido Hjy Himla tayi sannan tace " Abdul d'in sekuma tasaki kukan munafurci cikin kissa tace jeka dashi she Sha Sha kawai kayime duk hukuncin dakaga yadace amma Saraki dan Allah kaje part d'in ka kakira Iftahal nashirya muku abinci tun d'azu wucemin dashi Saraki banason ko ganinshi " juyawa tayi kan Aunty Bahijjat tana bata haquri bayan fitar su Maher hjy Himla tayi qwafa tace gara Abdul nasan zuwa gobe zai fito Kai kuwa da waccan shegiyar matar taka da cikin dakowa yakeyin murna akan shi yau zaku mutu dazaran kunci wannan abinci Kuma babu wanda yasan hjy Himla tashiryashi

Comments please 👏🏻

_Marmyn Zarah Ce_ 🤝🏻🥰
🗡 *!!!FURUCI!!!* 🗡
💔💔💔
💔
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* 💓❣💘

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... 📖🖊

🗡💔 FURUCI!!!!!💔🗡


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

🅿 53 to 54

Daga haka tashiga bedroom zama tayi bakin bed tanajin mugun haushin Maher akan dukan dayayima Abdul shiko Maher yanafita yasaka dogarawa sutafi da Abdul surufeshi itako Aunty Bahijjat har zuwa wannan lokacin jikinta rawa kawai yakeyi sabida sosai ta tsorata part d'in Ammin takoma cikin matuqar tsoro shiko Maher daganan part d'in kaka yanufa ganin babu kaka bakuma Iftahal a parlour se baqi yasa Maher nufar bedroom d'in Mama yana shiga yahangi Iftahal kwance saman bed d'in mama cikin sauri yaqarasa gareta hawa saman bed d'in yayi yarungumai ta tabaya yasaki wata irin ajiyar zuciya yakai hannu yashafa cikinta yace

" shine kika maqale wajan mama ko ? bakiko tunanin halin da dadyn Babyn zaishiga ko Sonahh hakan yayi kenan zuciya ta da ruhina hadida gangar jikina suna kewarki iya wasu awanni kad'an amma naji natsuwa ta tana neman barin jikina tashi muje part d'in mu dan kinsan bazan iya jure wasu a wanni batare danaji lafiyar babyna ba " cikin shagwa'ba Iftahal tayuyo kallon cikin idon shi tayi tad'an sake kashemai ido tace " haba kafasan duk agajiye nike shima babyn yana buqatar hutu "

Marayrayce murya Maher yayi yace " haba Sonahh please bazan iya haquri ba ko kinfara gajiya da buqatata ne ? " saurin sakamishi yatsa tayi saman lips d'in shi tace " karka sake fad'in haka har abada bazan gaji dabama mijina kulawaba tashi muje nima Ina farinciki da hakan "

Dede lokacin Mama tashigo murmushi tasaki tace " lalle Saraki yau kaine har cikin bedroom d'ina sabida gimbiya ko ? tobari kaji babu inda zata tana Nan bangaji da ganin taba " murmushi Maher yayi yace ayko Kaka sede kiyi haquri dan bazata iya dawannan hayaniyar tacikin part d'in kiba duk kintara baqi sun cika mata kunnuwa " miqewa Maher yayi yakamo hannunta suka nufi hanyar fita dariya mama tasaki tace " amma shine da kake renamana hankali Wai Kai babu ruwanka da mace to yau gashi duk kabi ka rud'e akan macan " murmushi Maher yayi yace " dama kaka bansamu sarauniyar mata bane kuma Sonahh ta cancanci narud'e akanta "

Daga haka yayi gaba riqeda hannun Iftahal suka fita Kai tsaye part d'in shi suka nufa suna shiga abin mamaki komi sabone cikin part d'in ankashe dukiya metarin yawa ko'ina abin kallone cikin part d'in qarasawa sukayi cikin bedroom d'in farko abin mamaki kayan lefan Iftahal sukayi musu maraba cikin mamaki Iftahal tace " wa'innan kayanfa ? " Murmushi yayi yace naki mana kina tunanin bikin su Aunty kawai akeyi ay hada namu ga dukkan alamu nan bedroom d'in kine zomuje nawa dan nafiso nagaisa da babyn cikin bedroom d'ina nacikin masarauta ta akaro na farko "

Baijira mai zataceba yasureta suka fito yanufi d'ayan bedroom d'in da ita yana shiga yanufi saman bed da ita sosai yashiga kallon bedroom d'in nashi komi yatsaru kamar basusan ciwon kud'i ba hawa saman bed d'in yayi nan yashiga sarrafata kamar wanda yayi kwanaki basa tare tsayin lokaci sannan yarabu da ita tare sukayo wanka shida kanshi yafito yaje bedroom d'in ta yaza'bo mata kaya yakoma da taimakon shi tagama shiryawa sannan suka fito yana rungumai da ita suka nufi dining shida kanshi yaja mata kujerar tazauna suna zama wata kuyanga tashigo cikin sauri tarisina ta gaidasu sannan tace "

Sunana Jamila nice mai kulada cin abincin ku idan kungama na kwaishe kayan shine nazo nazuba muku " murmushi Iftahal tayi tace " ok sannu Jamila Amma kibarshi kawai idan mungama Kya kwashe kayan sabida mijina baya iya cin abinda wata mace ta ta'ba idan ba niba sede ko su Ammi kije idan mun kammala Kya gayara gurin kinji nagode sosai Jamila " amsawa tayi cikin girmamawa tafita wani irin kallo namusamman Mai cike da soyayya Maher yakema Iftahal saurin bud'e kulan yayi yace to yau ni dakaina zanyima matata hidima wajan cin abincin nan "

Zuba abincin yayi cikin fulet yasa Spoon yad'iba yakai mata zuwa baki saurin kauda kai Iftahal tayi sabida yadda taji wani irin amai yataso mata dataji kamshin abincin kafin wani lokaci tuni tafarayin amai cikin sauri Maher yamiqe hannun shi yaka'be kulan abincin tafad'i abincin ya watse baibi takanshiba yanufi Iftahal dasauri kamata yayi yashiga shafa bayanta har tagama yin aman sannan yakamata suka nufi bedroom

Shigowa Jamila tayi tashiga gyara gurin bayan Maher yataimaka ma Iftahal ta gayra jikinta kwanciya sukayi misalin 7 akazo d'aukar amare sosai sukasha nasihohi sannan ko wacce aka tafi da ita gidan mijin ta lokacin da Maher zai tafi masallaci Iftahal qin Zama tayi cikin part d'in sede yakai ta wajan Ammin a 'bangaran Hjy Himla kuwa takasa koda zama tanajiran taji labarin mutuwar Maher da Iftahal Amma abin mamaki setagansu sunfito tare sun nufi Part d'in Ammin komawa tayi cikin mugun baqin ciki tanasake tunanin qulla wani tuggun

Murmushi Alhaji Tukur yayi dayaji su Maher sun shigo Egypt tashi yayi daga kishin gid'en dayake yace " lalle kuwa nasha alwashin bazasu komaba dan kuwa zansa akashe Iftahal shikuma nasashi yazama gara mutuwar shi da rayuwar shi nasan ana ciki hidimar biki cikin masarautar to da wannan zanyi afmani nasace matar tashi " kiran wayar dayashiga cikin wayar shi yasashi katse zancan d'agawa yayi abinda yaji yasashi saurin tashi tsaye yanasake maimaita " ankamashi fa kace garin Yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login