Back to novel

Chapter 11 of 30

NIDA PATIENT DINA Bayan Koma by MRS ISHAM

wani abu."""

"""Kada ka damu girki ne kawai kuma Anjima kaWai zai Waura, kuma ba aikin ka ba ne."""

"""To ba kaya ma su datti da zan yi ma ki wanki?"""

"""Babu."""

Ta fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa.

"""To zan je na zagaya ko Allah zai sa na samu."""

"""Ka huta kawai da yawon gyaran takalmin nan ga rana, kuma ba kudin kirki ba?"""

"""Kin fi so ba zauna ke ce Wauki Wawainiya ta ne, ke ce mijin ni ne matar, ba zan iya ba"""

"""Amma yanzu wanan uwar rana fa, gyaran ma kamar nawa ake gyara takalma?"""

"""Idan tsinkewa ce Naira hamsin nake Winke wa, amma idan sauran gyararrakin ne ya danganta yanayin"

"aikin."""

"""Please ka bar shi ka hutarwa kanka, a ™alla muna da abincin da zai kai mu watanni uku muna ci, to me"

"ye na wahalar da kai cikin wannan ranar ka yi ta yawo, kudin da ba na kirki ba, da babban sama'a ce ma"

"da sau™i. Amma wanann sana'ar ba..."""

"""Kin raina sana'ar ko? Kina ganin kamar asara ce ko? Duk wanda kika ga ya yi nasara a rayuwa, to akwai"

tarin asarori da faWi-tashi da karyewar jari da ya fuskanta waWanda ba ka gani ba. Sai dai asara ba ta

"hana shi ci gaba da neman nasara ba, faWuwa ba ta hana shi sake yun™urawa ba, karyewar jari bai karya"

"masa zuciya ba. Wahalar da kike sha a yau, ita ce farashin nasarar da kake so ta tabbata gobe. Domin"

"duk nasarar da ba a wahala wajen tabbatar da ita ba, ba ta ™arko."""

Ya Wauki kayan aikinsa ya fice ba bishi da kallo.

"HuWubar mahaifiyarta take tunawa, in da take cewa ."

"""Ya ke ΄ata Ki zaSi namiji mai kyakkyawan zuciya, komai matsayinsa, komai kuWinsa ko rashin kuWinsa."

"A cikin gaskiyar rayuwar aure, za ki gane cewa kasancewa cikin babban gida ko tarin kuWi mai yawa ba su"

da muhimmanci kamar yadda ake tunani.

"Za ki fi son wanda za ki iya tattauna komai da shi, wanda kuma zai zama uba nagari ga  yayanku, wanda"

"ba ya yaudara, wanda za ki iya amincewa da shi."

Iyali masu farin ciki ba su da farashi. Kada ki ji tsoron auren namiji da ke cikin hanyar gyara kansa. Amma

"ki guji na miji marar sana'a kuma bai damu ya tashi ya nema ba."""

Wayarta ta ji yana ringin ta duba ta ga ™awarta ce Nasreen Ibrahim. Tana Waga wa ta ji muryarta cikin

tashin hankali tana cewa.

"""˜awata kina ina?"""

Šan jim ta ji kafin ta ce.

"""Lafiya?"""

"""Na zo gidanku ne nake jin wani zancen da ya ruWa ni akan kin yi aure."""

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce.

"""Kina ina yanzu?"""

"""Ga ni a ™oafar gidanku ."""

Ta cikin wayar ta ji muryar Laila na cewa.

"""Nam ba gidansu ba ne ki je can in da take yanzu ita da musakin fa™irin mijinta can ne gidanta yanzu."""

"""Laila kika dake ma ni wanta magana anan wallahi dai na ci uwar ki a wajen nan."""

"""Ba dai uwa ta ba Wallahi, cire wayar Nasreen ta yi za ta yi cikin Laila sai ta gudu ciki tana cewa ."

"""Shegiya ce ni da zan tsaya ki dake ni? Mai ™irar samudawa ai sai ku kashe ni. Wacce kike zuwa wajen ta"

yanzu ba ta nan dai a koma in da take mun kora ta ni da uwata.

"""Ku jira na ku sakamakon."""

Cewar Jamil yana watsa ma ta wani mugun kallo. Tura ba ki ta yi tana cewa

"""Yaya Jamil kawar Aunty Ma'eesha ce za ta dake ni."""

Bai ko saurare ta ba ya nufi motarsa. Jin Muryar Nasreen na cewa.

"""Ma'eesha ban gane wannan kwatancen naki ba, idan na kawo titin zan kira ki sai ki fito ki shiga da ni"

"cikin layin, don ban zo da Driver ba ni nake yin driving Win."""

Jin haka ya saka Jamil tsaya wa yana kallon tana yana cewa.

"""Ba ni ita Please ta yi Mani kwatancen sai mu tafi tare."""

""""

Jin haka ya saka Ma'eesha cewa

"""Wallahi kuka zo da shi gidana ba zan yafe ma ki ba."""

Jin haka ta ce.

"""Ba zan zo da shi ba kar ki damu."""

Daga haka ta kashe kiran ta kalli Jamil ta ce

"""Ka yi ha™uri ba ta yarda na je da kai ba, amma next week zan kira ka sai ka zo mu tafi tare ka ga ni yanzu"

"ba ta yarda na je da kowa ba."""

"""Ba damuwa ki gaishe ta zuwa next week ina jirab kiran naki."""

Daga haka ya shige motarsa ita ma ta shiga tata motar suka bar gidan a tare.

"Horn ya danna ya tsaya kasancewar shi ne a gaba, ita ma ta tsaya ."

"""Ban lambar wayar taki ko?"""

Ya fada bayan ya sauke glass din mota tasa.

Ta karanta ma sa lambar sannan ta ja motarta ta bar wajen zuciyata cike da tarin tambayoyi.

"Kwatancen da ta faWa ma ta nan ta je ta tsaya a gefen titin, ba ta ga Ma'eesha ba, can ta hango ta tana"

™arasowa wajen motarta. Sai dai kallo Waya ta yi wa ma'eesha ta ga ta rame ma ma ta a cikin kwanaki biyun da ba su haWu ba.

Tana zuwa ta buWe front sit ta zauna tana yi ma ta sallama.

"Amsa wa ta yi tana ma ta kallon mamaki,sai dai ta haWiye tambayoyin ta ta yi wa motar key ta ni hanyar"

da ta ga Ma'eesha ta fito.

Tana nuna ma ta hanyar tana bi har suka ™arasa ™ofar gidan.

"A tare suka fito ta ga Ma'eesha ta buWe ™ofar ta shiga, ita dai Nasreen mamakin ta ™ara hausawa yake yi ."

"""Bismillah shigo ciki."""

Ta yi magana lokacin da ta shiga Wakin.

"Da sallama Nasreen ta shiga cikin Wakin, ta tsaya tsaye tana ™are wa Wakin kallo."

Ba ta zauna ba duk da Ma'eesha ta ce ta zauna saman katifar.

"""Zaman me kike yi a nan, wannan kangon wanda bai kai na a ce kina kiwon karnuka a ciki ba?"""

"Ta yi maganar tana karewa Wakin kallo, sannan ta fito taskar gidan tana kare ma sa kallo, hatta banWaki"

da kitchen Win fale-fale dake tsakar gidan sai da ta le™a.

Sannan ta dawo ta kalli Ma'eesha dake zaune a bakin katifa ta ce.

"""Lafiya kike zaune a wannan kangon kuma me kike yi?"""

"""Zaman aure nake yi ."""

Da mamaki take kallona ta ce.

"""Zaman aure kuma?"""

"""Eh."""

Ta ba ta amsa ba tare da ta kalle ta ba.

"""Wani irin zaman aure kuma da waye mijin naki?"""

"""Zaman aure da kowace macen aure take yi a gidan mijinta."""

Dafe kai ta yi tana cewa

"""Am confused about how..."""

"Kukan da ta saka ne ya saka Nasreen kasa ™arasawa maganar da ta yi niyyar faWa, domin kuwa tausayin"

™awar tata ce ta saka ita ma ta rungume ta suna yin kukan tare ba tare da ta san komai ba.

"Tsawon mintuna suka Wauka suna kuka ba mai rarrashin wani, kafin Nasreen ta zame jikinta daga na"

"Ma'eesha, tana goge ma ta hawaye ta ce."

"""Me yake faruwa ne, na san ni da ke ba mu Soye wa juna komai, don Allah ki sanar da ni kar ki saka"

"kaina ya buga."""

"Nan Ma'eesha ta ba ta labarin komai, tun daga farko kar karshe. Ba abinda Ke tashi sai sautin kukan"

Nasreen tana tausayin ™awarta.

"""Amma Allah ya tsine wa Mamy albarka. Allah ya sa ta shiga wuta, wallahi wannan matar ba za ta ga"

"annabin rahama ba. Gabadaya ta juye wa Daddy tunani sai abinda ta ce. Allah ya jikan Mummy."""

"""Amin ya Allah."""

Ma'eesha ta faWa tana goge hawayenta.

"""Yanzu shi wanann makahon ne zai iya ri™e ki?"""

"Ma'eesha ba ta ce komai ba, don ba ta san amsar da za ya ba ta ba."

"""Yanzu ke sai kika yarda?"""

"""To ya zan yi Nasreen?"""

"""Ai ba yadda za'ayi a haWa ki da wannan nakasashen talakar musaki. Haba ke ba za ku nema wa kanki"

"΄anci ba?"""

Murmushin takaici ta yi ta ce.

"""To ya zan yi tun da mahaifina ya aurar da ni ga wanda ya ga dama, ba na da wani zaSin da ya wuce"

"rungumar kundin ™addarata."""

"""Haka ne, amma wannan ai bai dace da ke ba, ta ya ya za'a aurar da ke ga wanda na san ko kuWin kayan"

"kwalliyarki ba zai iya siye ba ballantana abincin da za ki ci, abun takaici wai sadakinki dubu uku kacal ko kaza yanzu ai ba za'a ce dubu uku ba ballantana mutum, ba kayan lefe ba komai, wanann ke ce kika sigar da wayarki kika kama haya kika siyo abincin da za ki ci kin san wannan auren ba alkhairi a cikinsa. Don haka ki tattara kayan ki yana zuwa ku ci mutuncinsa ki saka ya yi ma ki saki uku, ki zo mu tafi gidanmu ki zauna a can na san iyayena za su karbe ki, kin ga ba ki da kowa a garin nan ba ki san dangin mahaifiyar ki ba, sannan yanzu tun da hakan ya faru ba ki isa ki tafi wajan dangin Daddy ba, don sai abinda ya fada a"

"family suke Wauka."""

"Ta yi maganar tana tattara kayan Ma'eesha da ta gani a waje, tana saka wa a cikin trolly Win ta."

"""Ba in da zan je."""

Da mamaki take kallonta.

"""Da gaske ba in da za ki je?"""

"""Eh haka na ce."""

"""Saboda me?"""

"""Saboda zaman ibada nake yi."""

Nisa wa ta yi kafin ta ce.

""" Duk talaucin mijina zan yi ha™uri na zauna da shi cikin kwanciyar hankali da soyayya. Mijin wata bai fi"

"nawa ba duk sunansu mazajen aure, zan yi alfahari da nawa ko a ina ne, domin nawa shi ne nawa, mijin wata ba nawa ba ne. Zan zauna da nawa cikin nutsuwa da kulawa. Ba zan dinga hangen na wasu ko kallon irin abubuwan da yake musu, domin kowacce tana da nata jarabtar. Zan fito in nuna alfahari da nawa, kamar yadda wasu ke yi da nasu. Kila ma na fi su samun kulawa da soyayya. Talauci ba laifi ba ne. Amma boye shi, da zama cikin kima da mutunci, shi ne alkhairi, Idan mijina yana bakin ™o™arinsa wajen kula da ni, to zan ri™e shi da kyau. Idan na bar shi, ban san wanda zan haWu da shi ba, ba kowanne namiji ne zai iya daraja ni ba zan yi ha™uri na zauna da abina. Da dama daga cikin matan da ake ganin suna"

"rayuwa cikin jin daWi, lokacin da suka auri mazajensu ba su da komai. Sai bayan aure Allah ya buWa musu."

"Ba zan fitar da rai daga rabona, arzi™i na Allah ne, kuma kowa rabonsa ba zai kauce masa ba. Ko ba a"

"sami duniya ba, insha ALLAH za a sami mafi alkhairi a lahira."

"Zan kula da mijina, danginsa sun zama dangina, zan kama darajata mu rufawa juna asiri. Mu kula da"

juna cikin mutunci da biyayya.Rayuwa cikin tausayawa da kulawa da juna cikin soyayya da farinciki yafi

"na rayu cikin arzikin da babu kulawa bare nuna ™auna."""

*Maman Ihsan ce*

09065327995

Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z

*MAKAHO NE*

*NA*

Maman Ihsan ce

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=15969875

11055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

(J.W.A)

"_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ™asaitacciyar baiwa su sauya"

tunanin al'umma cikin sau™i_.

page

"""Duk talaucin mijina zan yi ha™uri na zauna da shi cikin kwanciyar hankali da soyayya. Mijin wata bai fi"

"nawa ba duk sunansu mazajen aure zan yi alfahari da nawa ko a ina ne, domin nawa shi ne nawa, mijin wata ba nawa ba ne. Zan zauna da nawa cikin nutsuwa da kulawa. Ba zan dinga hangen na wasu ko kallon irin abubuwan da yake musu, domin kowacce tana da nata jarabtar. Zan fito na nuna alfahari da nawa, kamar yadda wasu ke yi da nasu. Kila ma na fi su samun kulawa da soyayya. Talauci ba laifi ba ne. Amma Soye shi da zama cikin kima da mutunci shi ne alkhairi. Idan mijina yana bakin ™o™arinsa wajen kula da ni to zan ri™e shi da kyau, Idan na bar shi, ban san wanda zan haWu da shi ba. Ba kowanne namiji ne zai iya daraja ni zan yi ha™uri zauna da abina. Da dama daga cikin matan da ake ganin suna"

"rayuwa cikin jin daWi, lokacin da suka auri mazajensu ba su da komai. Sai bayan aure Allah ya buWa musu."

"Ba zan fitar da rai daga rabona arzi™i na ALLAH ne, kuma kowa rabonsa ba zai kauce masa ba. Ko ba'a"

"sami duniya ba, in sha ALLAH za a sami mafi alkhairi a lahira."

"Zan kula da mijina da danginsa sun zama dangina. Zankama darajata mu rufawa juna asiri,zani kula da"

iyalanki cikin mutunci da biyayya. Rayuwa cikin tausayawa da kulawa da juna cikin soyayya da farin ciki

"yafi na rayu cikin arzikin da babu kulawa bare nuna ™auna."""

"Gabadaya kalaman ta Win sunana kashe wa Nasreen jiki, don haka ta ce."

"""Kina son sa kena?"""

"""Ba sonsa nake yi ba, ina tausayinsa ne."""

"""Kin tabbata iya tausayi ne kawai?"""

"""Na tabbata don ba na jin komai a zuciyata game da shi, abu Waya na sani shi ne tausayinsa da nake ji a"

"zuciyata."""

"""Ke ce abar tausayi ba shi ba."""

Kafin ta fuskanci Ma'eesha da kyau ta ce.

"""Tausayi rabin soyayya ce, amma muje zuwa."""

Ta yi maganar tana ciro wayarta ™irar iphone a cikin handbag Win ta. Sannan ta ce.

"""Ya maganar cousin brother na, da kika yi wa al™awarin aure, kin dai san irin son da Abdul yake ma ki, ya"

"ki kowace mace yanzu haka gobe zai dawo daga ™asar Canada da mararin zuwa ganin ki, kin san kin yi"

ma sa alkawarin yana dawowa za ki gabatar da shi a wajen Daddy. Kin san ba kasar nan zai ajiye ki ba

"can ™asar..."""

Dakatar da ita ta yi ta hanyar Waga ma ta hannu.

"""Ya isa haka nan Nasreen, ya za ki zo kina ma ni wani zancen tsohon saurayina bayan kin san cewa yanzu"

"ni matar aure ce, ko mace Waya na auren maza biyu ne?"""

"""Ba ta auren maza biyu kuma ina son na ceto rayuwar ki daga halakar da kike ciki ne, ki auri attajiri Wan"

"attajirai wanda ya mutu a ™aunar ki wanda zai jiyar dake farin ciki da jin daWi ba wai in da za ki zauna kika wahala ba. Look at you yadda kika koma a kwana Waya duk kin bi kin fita hayyacinki, nan da wata Waya ba za ki ganu ba. Na tabbata har yanzu ke budurwa ce ba abinda ya shiga tsakanin ki da wanann"

"makahon don haka ki rabu da..."""

"""Nasreen tashi ki tafi sai anjima."""

Kallon mamaki take yi ma ta kafin ta ce .

"""Ma'eesha ni kike kora daga in da kike, duk sha™uwa da amincin dake tsakaninmu?"""

"""Nasreen matukar kika cigaba da fadar mugayen kalamanki tabbas zan yi ma ki abun da ba ki yi zato ba."

Na rungumi kundin ™addarata ban yi jayayya da hukuncin Allah ba na dogara gare shi kuma na san ya

"isar ma ni, kada ki sake yi Mani magana makamancin wannan, idan kuma ba haka ba za mu samu Matsala."""

"""Ki yi hakuri Allah ya huci zuciyarki, me ya yi zafi, duk wanda ya ce zai haWiye gatari Sota zan ri™e ma sa."""

Daga nan suka shiga wata firar daban. Ganin rana ta yi ma'eesha ta ce.

"""Me zan girka ma ki ?"""

"""Duk abin da ya samu."""

Tukunya ta wanke ta Wira girki bayan ta fitar da gas din ta ajiye shi a baranda.

Jallop Win taliya da dafa ma su wanda ya ji kayan lambu da bisashen kifi.

A plate daya ta zuba ma su ta saka fork guda biyu.

Ganin Ma'eesha ta dauko pure water ta zuba a plate ya saka Nasreen kai hannu ta taSa.

"""Ya na ji ba sanyi?"""

"""To a wane fridge zan saka ya yi sanyi? Ke ni fa duk yadda rayuwa ta zo ma ni haka zan rungume ta."""

"""Bari na fita na nemo don wallahi ba zan iya ba."""

Tana fadar haka ta mi™e tana ficewa daga Wakin.

Ma'eesha ta rufe abincin tana jiran dawowarta.

Zuwa can ta dawo bakinta Wauke da sallama.

"""Assalamu alaikum."""

"""Wa'alaiki Salam warahmatullah."""

Shigowa ta yi rike da bakin leda ta siyo bottle water guda biyar da maltina guda biyar ma su sanyi.

Daga nan suka fara cin abincin.

Bayan sun kammala ne sai ma'eesha ta kwashe kayan da aka Sata ta je ta wanke su tas. Ita kuma

"Nasreen dama can a gidansu mahaifiyar ta ba ta saka ta aikin komai , sai dai ma su aiki su yi ma ta komai,"

don haka ba abun da ta iya. Ma'eesha kuwa wani lokacin Mahaifiyarta za ta ce ma su aikin su bari Ma'eesha ta yi saboda mace ce ita gidan wani za ta je wata rana.

"Bayan ta gama wanke-wanken ne ta saka ruwan Wumi a wuta ta ke ta yi wanka, da ta fito ne ta Wauara"

alwala don yin sallar azahar.

"Bayan ta idar Nasreen ma ta fito da niyyar yin alwala, yamutse fuska ta ji lokacin da ta ga banWakin, duk"

da ba datti amma ita gani take yi ta fi karfin ta shiga wannan banWaki.

"Alwala ta yi sannan ga shiga Wakin, don ko da ta shiga har ma'eesha ta idar da sallah."

Nan ta ba ta wuri ita ma ta yi sallar

Mayyukan shafawarta ma ma su kanshi da tsada ta shafa. Sannan ta shafa turare sannan ta shirya cikin

"riga da siket na atamafa, ta yi daurin Šankwalinta mai kyau, ba ta yi kwalliya ba powder kawai ta shafa"

da man leSe.

"""Hmmm yanzu ko kin yi kwalliya aikin banza ne fa, don da wani idanun zai gani ballantana ya yaba ya san"

"cewa kin yi kyau."""

Tsuke fuska ta yi ganin haka ya saka Nasreen cewa .

"""Tuba nake yi. Ba zan sake ba."""

"Daga nan ne wayar ma'eesha ya yi kara, bayan ta duba mai kiran ne sai ta katse kafin ta yi danne-danne"

a wayar kafin ta ajiye wayar gefe.

"Daga nan suka ci gaba da fira, sai wayar Nasreen ta yi ruri. Gani. Mai kiran ya saka ta yi Murmushi tana"

cewa .

"""Barka da warhaka yallaSai."""

Daga cikin wayar ta ji muryarsa yana cewa.

"""Barka dai ya kike ?"""

"""Lafiya lau Alhamdulillah. Tun jiya nake kiran lambar ™awarki tana ringin ba ta Waga wa, sai na sake kira"

"na ji a kashe, yanzu ma na kira ba ta Waga ba da na sake kira ina zato ma ta ji blocking Wina ne. Kuma"

"saboda ita zan shigo ™asar gobe, da ba don haka ba sai nan da watanni uku zan dawo ™asar."""

"""Yaya Abdul ka yi ha™uri da Ma'eesaha kawai."""

"""Ban gane ba, ko dai ta samu wani ne ta yar da Ni?"""

"""Hmmm."""

"""Ban gane hmmm ba talk to me."""

Ya ji maganar cikin wata irin murya mai cike da karaya.

"""Ma'eesha ta yi