Back to novel

Chapter 10 of 30

NIDA PATIENT DINA Bayan Koma by MRS ISHAM

ji muryarta tana cewa.

"""Ba ri na je na siyo bread a shagon dake nan kusa da mu."""

Bai tanka ma ta ba ita ma ba ta jira cewarsa ba ta yi ficewar ta.

Ba ya jima ba ta dawo da bread a leda da gwanhwanin milo da na madara.

"Ta ajiye har ga Allah ta ji dadin siyayyar da ta yi, ba don ta yi tunanin siyar da wayar ba su da ba ta san"

"yadda za ta yi ba. Duk da cewar a yanzu ma hankalin nata bai kwanta suka ba, saboda ta san yau da gobe duk abinda ta siyo za su ™are ya za ta yi ne ina za ta samu wasu kuWaWen har ta sake siyo ma su wani ba. Don ta tabbatar makaho ba iya Waukar nauyin gidan zai yi ba, don wannan gyaran takalmin da yake yi ba"

ta tunanin shi kansa zai iya W sa Waukar nauyinsa da shi ballantana ya dauki nata nauyin.

"""Ma',eesha."""

Ta ji ya kira sunanta lokacin da ta kashe Gas Win.

"""Na'am."""

"""Don Allah ki daina yawan fita ko wane lokaci yanzu yai kin fita sau nawa a gidan nan?"""

Shiru ta yi tana kallon da kafin ta ce.

"""Idan ina bu™ata abu za ka aje ma ni yaron da zan aika ne?"""

"""Meye amfanina ina gidan da sai kin fita?"""

"""Na ding aikenk kenan?"""

"""Wa ya fi cancanta ya fito ya nemi abun da ake bukata tsakanin ni da ke?"""

"""Kai ka fi cancanta amma gani nake za ka wahala ga sanda ga kaya a hannun ka."""

"""Kin manta haka nake fita neman na abinci, hannu daya ri™e da sandar hannu daya ri™e da kayan gyara. """

"""Shi kenan dama na mance ban siyo ruwa ba sai ka je ka siyo."""

Ta ciro Wari biyar ta bashi ya karba.

"""Wannan nawa ce?"""

"""Šari biyar ce, yanzu tsarin zai canza kamar yadda rayuwa ta ta canza. A baya bottle water nake sha,"

"amma yanzu ba na da halin da zan cigaba da shan sa, ko da na siya yanzu nan da kwana biyu zai gagare"

"ni don haka yanzi zan koyi shan ruwan pure water. Wannan Wari biyar ka siyo ma na bag Waya wato jaka dayatina tunanin bai wuce dari biyar ba."""

Ya fita don siyo wa ta bi shi da kallo har sai da ya fice sannan ta Wauko ™wai guda huWu ta ta Wan jajjaga

"bayan ta wanke ™aramin turmi ta daka magi ta yanka albasa, sannan ta Wauko fry pan ta wanke sannan ta zuba mangyaWa ta soya."

"Da sallama ya shigo gidan ta amsa tana mi™e wa ta karbi jakar ruwan dake hannunsa, ya ™araso ciki sai"

da ya ji ya taSa tabarmar da sandarsa sannan ya gane ya ™araso wajen.

Bayan ya hau tabarmar ne ya zauna tare da yin Bismillah.

Kofuna biyu ta dauko na shan shayi ta ajiye bayan ya wanke da cokula. Ruwan shayin ta zuba wa kanta

"da nasa ta zuba sugar da milo da madara, ta fifita dai da ya rage zafi ta ajiye ma sa a gabansa da plate Win da ta saka ma sa soyayyen kwai ciki ta ajiye ma sa bread."

"""Ga breakfast Win ka nan a gabanka."""

Sannan ta haWa na ta ta koma kan tabarmar ta zauna a gefensa.

"""Na gode Ma'eesha Allah ya biya ki fa gidan aljanna."""

"""Amin ya Allah."""

Ta amsa tana cigaba da cin abincin ta.

_Nadra_

Tana zaune a falon zuciyar ta cike da mamaki da Wan firgici. Duk abinda take gani a gidan yana gudana

tana Waukarsa ne na yayarta Sidra ba ta taSa tunanin ita ce Amaryar ba.

"Abba dake zaune kusa da kujerar dake kusa da Nadra dake zaune saman Centre carpet, fuskarsa cike da"

tsananin tausayin ΄ar tasa mai biyayya da bin Umarninsa akan komai.

Idanunsa sun kaWa sun yi jajir ya ce.

"""Nadra yau ce ranar da rayuwarki za ta sauya."""

Nadra ta kalli fuskarshi idanunwanta cike da rashin fahimta tana kallon jama'ar falon Waya bayan Waya.

"Idanunta suka sauka akan kakarta mahaifin Abba, sai Gwaggo Maimuna Yar Abba sai Gwaggo Laraba"

™anwar Abba. Sai Yayan Umma wato Alhaji Bashir. Kafin ta mai da dubanta kan Abba.

"""Nadra yau aka Wauara aurenki ba tare da na shawarce ki ko jin ra'ayin ki ba, saboda ina da ya™inin cewa"

"ba za ki taSa watsa ma ni ™asa idanun ba."""

A firgice take kallon su ta ce.

"""Me kuke nufi wace ce Amaryar?"""

Abba ya dube ta cike da kulawa da nauyi ya ce.

"""Sidra ta gudu Allah ya kare ta a duk in da take. Amma ki sani rayuwarki aka Waure yau."""

Nadra ta ji shiru na Wan lokaci zuciyarta ta yi ma ta nauyi kamar dutse. ˜walla ce cike a idanunta ba zato

ba tsammani zuciyarta ta fara fahimtar cewa ita ce Amarya. Ta taSa kafafuwan Abba cikin tsanani ruWani da firgici. Zuciyarta na bugawa da karfi. Sai ta Waga kai ta yi addu'a a cikin zuvuyarta.

"""Allah ka bani ™arfin fuskantar wannan sabuwar rayuwa , ka sa na zama mai ha™uri da biyayya."""

Kuka ta fashe da shi mai tsuma zuciyar mai sauraro. Cikin wannan yanayi Nadra ta san cewa babu koma

"baya, kuma dole ta rungumi a abun da ya zo ma ta. Shin ma waye mijin da aka Waura ma ta auren da shi? Tambayar dake kai komo a zuciyarta kenan. Sai ta ji muryar wan Mahaifiyarta Alhaji Bashir yana cewa."

"""Dama kana naka ne Allah ya gana nasa. Dama can Allah bai ™adarto cewa Sidra ce matar Fahad ba sai ke,"

"don haka ki rungum..."""

Kukan da ta fashe da shi ne ya saka kowa dakata wa yana kallonta. Kuka take yi wanda ke fitowa can a

kasar ranta.

"""Ki yi hakuri Nadra na san za ki ji abin a baibai, amma ki sani ba ni da wani zaSi da ya wuce hakan. Na"

gayyaci jama'a na tara su an zo daga garuruwa mabanbanta gari ya waye ana jiran rana ta yi a daura

aure amma sai Sidra ta nemi tozarta ni da kunyata ni ta nemi zubar ma ni da ™ima a idanun jama'a. Da

"wani idanu zan kalli jama'ar da na gayyata zuwa auren ΄a ta na ce ma su an fasa daurin auren ΄ata ta gudu? Hakan ba zai zubar mani da ™ima ba? Ke kadai ce na san cewa za ki iya kwaso ma ni ™ima ta da ΄ar ki ta nemi zubar wa. Tun da na haife ki daga ni har mahaifiyar ki muna alfahari da ke, ba ki taSa saSa ma na ba, don haka ba na sa ran wannan karon za ki aikata wani abun da ba daidai ba. Na roke ki da Allah"

"ki..."""

Cikin sauri ta ce .

"""Abba ka daina ro™o na don Allah ba abinda za ku aikata akaina ku roke ni Ko da hakan na nufin mutuwa"

"ta ce, Abba dan Allah ka daina ro™o na sai na ji kamar na gaza zama ΄a gagari ce a gare ku. Na amince akan duk hukuncin da kuka yanke akaina. Amma Yaa Fahad fa Sidra yake so kuma ita ma na san tana tsananin son sa idan ta dawo ta tarar da..."""

Abba ya kira sunanta a kausashe.

"""Nadra!"""

Šagowa ta yi ta kalle shi da idanunsa da suka yi jajir saboda kuka ta ce.

"""Na'am Abba."""

"""Daga yau ba na son sake jin sunan Sidra a bakin ki, a cikin gidan nan ma na hana a kira sunan ta, ba zan"

"yi ma ta baki ba amma na cire ta daga cikin mu, ki Wauka ba ki da wata ΄ar uwa a raye Sidra ta mutu a"

"wajen ki."""

Kuka ta saka sosai tana rokon Abba ya yafe wa Sidra amma bai saurare ta ba. Sai ya tashi tsaye ya kalli

Nadra ya ce .

"""Allah ya yi ma ki albarka ya kare ki a duk in da kike, yadda kike wa iyayen ki biyayya Allah ya sa ΄a΄an da"

za ki haifa su yi ma ki fiye da yadda kika yi mana. Allah ya zaunar da ke lafiya da mijinki ki yi ma sa ladabi

"da biyayya kome ya daka ki to kiyi masa matu™ar bai saSawa addinin Musulunci ba, aljannarki na kasan"

"™afansa idan ya daga ki shiga kada ki mance da wannan."""

"Yana fadar haka ya fita daga falon kamar zai yi kuka, don ba zai iya jurar ganin Nadra n kuka tana"

"rokonsa akan wani abu bai yi ma ta ba, amma wanann karon ba ya jin zai saurare ta akan zancen Sidra."

Sauran jama'ar dake falon kowa nasiha sosai suka ji ma ta akan zaman aure da hakuri da rayuwar aure.

"""Dare na yi ya kamata a Wauke ta a kai ta gidan mijinta."""

Cewar Gwaggo Maimuna tana kallon Ammi.

Ammi ta ce .

"""To me kuke jira ku tafi a raka ta ma na ga jama'a can a falo suna jiran ku fito, ga motaci jere a waje."""

Gwaggo Laraba ce ta ja hannun Nadra da ta kudundune cikin babban mayafin da aka yafa mata.

"Part Win Umma suka shiga suka same ta ita da ™awarta Hajiya Turai tana rarrashinta, ganin dunya saka"

Umma ta yi saurin goge hawayenta.

Kukan Nadra ne ya kara tsananta ta nufi Umma ta shige jikinta ta rungume. Kuka suke yi du duka biyin.

"Duk yadda Umma ta so rike kukanta kasa wa ta yi, haka kawai take jin tausayin Nadra ga Sidra da ba su"

"san halin da take ciki ba, damuwa sun yi ma ta yawa. Kula take yi sosai tana ™ankame Nadra kamar za'a ™wace ma ta ita."

Ammi ce ta shiga ganin halin da suke ciki ta ce

"""Me nake gani haka, ke da za ki ma ta nasiha a wuce da ita gidan mijinta shi ne kike kuka?"""

Da ™yar aka SanSare Nadra a jikin Umna suka fita da ita tana kuka tana kiran sunan Umma. Hankalinta ya

tashi musamman da ta ji jikin Umman da zafi alamar ba ta da lafiya.

Tana ji tana gani lokaci daya rayuwarta ta juye sama zuwa ™asa ™asa zuwa sama. Ko da wasa ba ta kawo

"wannan ranar ba, ba ta yi tsammanin nan kusa za'ayi aurenta ba kuka da saurayin ΄ar ta wacce take ™auna yake ™aunarta. Amma yau ita ce za'a Wauka akai gidan Fahad a madadin Aunty Sidra. Kuka take yi sosai tana ji tana gani aka saka ta a Waya daga cikin motocin da suka zo Waukar Amarya."

Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimuna suka saka ta a tsakiya.

"Sauran dangi suka shiga cikin sauran motocin, sai dai ba ™awar amarya ko Waya, kasancewar ba ™awarta"

"da ta san da zancen auren, ko A'isha Humaira da ta zo ta dai zo ne a matsayin bikin Sidra ba wai ta san"

™awarta ce aka aurar ba.

Sauran yan matan na dangi da kowa sai da motacin suka kwashe su zuwa gidan Amarya.

_Fahad_

Kwance yake a bedroom Win sa yana jin yadda abokansa Sadik da mukhatar suke ta yi ma sa knocking

"™ofar, amma bai yanka ma su ba sai ma pillow ya saka ya dora a kansa alamar baya son ™arar ™ofar."

"""Fahad please open the door."""

Cewar Mukhtar yana bugun kofar. Sadik cikin ™uluwa da wula™ancin da Fahad ke yi ma su tun Wazu ya ce.

"""Wai kai wane irin wula™anci kake yi wa mutane ne tun Wazu, sai faman bin ka make yi ka fito mu tafi a"

"raka ka Wakin amarya ka share mu ka mayar da mu ΄an iska idan ba za ka je ba ai sai ka sanar da mu."""

"""Sau nawa na fada kowa ya watse, sauran sun tafi ku ma ku tafi ba in da zan je Allah ya ba mu alkhairi."""

Cikin takaici suka fito kowa ya nufi motarsa suka bar gidan.

_Nadra_

Har suka isa katafaren gidan Fahad ba ta daina kuka ba.

Motacin duka suka shiga cikin compound Win gidan.

Babban gida ne sosai mai girman gaske ga manyan fitilu da suka haska gidan ya koma tamkar rana ne ba

dare ba.

"FaWar kyau da tsaruwan gidan ma Sata lokaci ne, gini ne na alfarma kuma na zamani."

"""Fito da ™afar dama."""

Cewar Gwaggo Laraba tana riko hannun Nadra dake kuka.

A hankali ta yi Bismillah ta fito da ™afar dama.

Tana rike da hannunta suka nufi main door nan ma ta ce ma ta ta shiga da addu'a.

Ta dan jira kafin ta ga ta saka ™afar dama ta shiga ciki.

"""Ma sha Allah."""

Shi ne kalmar da kowanen su yake faWa wasu a zuciya wasu a fili.

Šaya daga cikin manyan kujeru dake downstairs aka zaunar da ita. Yayin da suka dinga shiga suna le™a

ko ina na gidan suna yaba kyawun gidan.

Daga karshe dai suka kai Nadra Wakin da ya kasance mallakinta ne a downstairs.

Saman katafaren gadonta suka zaunar da ita.

Nan suka dinga yi ma ta nasiha sosai da da kuma kara nuna ma ta mahimmancin ha™uri.

"Sannan suka yi ma ta Sallama suka fice, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita. Hakan ya saka suka dawo"

suka dinga rarrashinta. Ganin kukan na ta ba na tsaya wa ba ne ba ne.

Sallama suka yi ma ta suka ce da safe za su dawo. Suka bar gidan suna ta santin kyawun gidan.

_Mama_

Tana zaune ita da Aunty Rahama da ™anwar Mama mahaifiyar Farida wacce suke kira da Aunty Jummai.

Farida na kwance a jikin Mahaifiyarta tana sharar ™walla.

Aunty Rahama ce ta kalli Farida tana cewa.

"""Ki yi hakuri Farida wannan kukan ya isa, Allah ya zaSa ma ki ma fi alkhairi, idan Allah ya nufa ke matar"

"Fahad ce wata rana sai ki ga Allah ya karkato da hankalinsa zuwa gare ki ya aure ki, auren nan nasa ba wai yana nufin ba ya da damar auren ki ba ne, ai namiji mijin mace huWu ne."""

Haka Aunty Rahama ta dinga rarrashinta duk da ta san cewa ba yadda Fahad zai yarda ya auri Farida

saboda ba ya son ta kwata-kwata amma ta faWi haka ne don ta kwantar ma ta da hankali.

Mama ne ta kalli Rahama ta ce .

"""Ki je ki duba ko sun tafi don karfe goma da rabi yanzu, don motocin da suka kai Amarya tuni sun dawo."""

Rahama ta mi™e kenan sai ga kiran Sadik ta shigo wayarta.

Amsa kiran tayi bayan ta ji sallama ta ce .

"""Sadik kin kai abokin maku ne?"""

"""Ina fa Aunty, rashin mutunci ya ma na muka bar shi."""

Nan ya sanar da ita yadda suka yi da shi. Kuma ya kira ne don a je a saka shi ya tafi kada ya bar yarinya

ita kadai a gidan.Bayan sun yi sallama ta kashe kiran wayar.

Nan ta sanar da Mama yadda suka yi sai Mama ta dauki waya ta kira Fahad. Amma wayoyinsa a kashe.

Don haka ta mike fita Aunty Rahama ta bi ta a baya suka nufi part Win Fahad.

*Maman Ihsan ce*

09065327995

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug

*MAKAHO NE*

*NA*

Maman Ihsan ce

* Happy new year*

Ina ma na barkan shigowa sabuwar shekarar 2026 lafiya. Allah ya ba mu zaman lafiya mai Wore wa a

™asar nan.

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=15969875

11055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

(J.W.A)

"_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ™asaitacciyar baiwa su sauya"

tunanin al'umma cikin sau™i_.

page

"Nan ta sanar da Mama yadda suka yi, sai Mama ta Wauki waya ta kira Fahad. Amma wayoyinsa , don"

haka ta mi™e ta fita Aunty Rahama ta bi ta a baya suka nufi part Win Fahad.

Ba kowa a fakon sai sanyin A.C dake tashi a falon.

"Bedroom Win sa suka nufa Mama ta fara buga ™ofar da ™arfi. A tunanin Fahad su Sadik ne ba su tafi ba,"

don haka a fusace ya fara magana.

"""Wallahi idan ba ku rabu da ni ba zan tafka ma ku rashin mutunci idan na fito."""

"""To Bismillah ma ta mutunci kawai."""

Muryar mahaifiyarsa da ya ji ne ya saka shi zaro idanunsa waje.

"""Ya Salam. Mama ce?"""

Tasowa ya yi cikin rashin kuzari ya zo ya bude kofar Wakin.

Kallonsa ta yi fuska a tamke ta ce

"""Me kake yi har yanzu da ba tafi gidanka ba ka bar baiwar Allah ita kaWai."""

Har ya buWe baki zai yi magana sai Mama ta Waga ma sa hannu alamar dakatar wa.

"""Ba na son jin komai, mintuna goma kada ka sake yi a cikin gidan nan ba ka tafi ba."""

"Tana gama fadar haka ya juya ta fice, yayin da Aunty Rahama ma ta mara ma ta baya suka fice a tare."

Kamar zai yi kuka haka yake ji.

"Key Win motarsa ya Wauka, sai system Win sa da wayoyinsa ya nufi hanyar fita zai fice."

Har ya murWa handle Win kofar zai fice sai ya juya yana ™are wa Wakin kallo sannan ya dawo ya kashe

komai na dakin .

Ficewa ya yi zuwa farlon nan na ya kashe duk wani kaya na Elections sannan ya fice.

"Kai tsaye wajen motocinsa ya nufa, ya shiga Waya daga ciki bayan ya ajiye laptop dinsa a kujerar zaman"

banza. Sannan ya yi wa motar key bayan maigadi ya wangale ma A ya bar gidan.

_Makaho_

"Suna zaune bayan sun gama yin breakfast, ruwan tea ya shanye amma bai cinye bread da ™wai ba."

Tattara kayan ta yi ta haWa su a can gefen kayan wake-wake da suka Sata.

"""Ma'eesha me kike yi ne?"""

"""Ba komai wake-wake zan yi."""

Sandarsa ya Wauka ya karasa in da yake jin motsinta ya ce.

"""Ba ri na wanke je ki kawai."""

"""A'a ba za ka iya ba."""

"""Ba abinda za ki iya yi wanda ni ba zan iya ba, domin nakasa ba kasawa ce """

"Lalube ya fara yi har ya ji in da kayan suke , tana kallonsa yana wanke wa yana Wauraye wa har ya"

kammala.

Ta kwashe kayan ta je ta jera su a in da ya dace.

Bayan ya shigo Wakin ne ya ce ma ta .

"""Yanzu me zan yi ma ki?"""

"""Ba komai na gode."""

"""Na san ke ΄ar hutu ca ba ki saba da ayyuka ba, ma su aiki ne suke yi ma ki aiki, to don me ba za ki bari"

"na taya ki ba ?"""

Gajeren murmushi ta yi ta goge ™wallar da ya cika idanunta ta ce.

"""Haka ne, duk da ma su aiki ke yi ma ni aikin komai amma hakan bai saka Mahaifiyata koyar da ni ba. Ta"

"na cewa ba lallai mijin da zan aura ya so a ce mai aiki ce ke yi ma sa gyaran Waki ko girki ba. Wani namijin sai matarsa kawai take yi ma sa hidima."""

Kasancewar ta buga labule ta shimfiWa leda ta ajiye katifar ta gyara. Ba wani aikin da ya rage. Hakan ne

"ma ya sa ta tuna ina z ta damu room freshener spray ko turaren wuta ta turaran wuta da za ya sa a Wakin ya yi ™amshi , dole ta nemo ba z ta iya zama daki ba ™amshi."

"""Ba abun da zan yi ma ki kafin na fita, kada na fita kuma ki bu™ata