Follow us on social media

Showing 138001 words to 141000 words out of 152107 words

Chapter 47 - Duniya Ta Complete Book 2 Complete Complete Hausa Novel by Asma Baffa

28 May 2026

217

fita a toilet din.

"Batasan da gangan yayi ba?,oho amma gaba daya suka zube a gadon yana fadawa samanta. Ya"

aje mata nauyinsa sosai har sai da numfashinta ya fara nauyi

"""Oh. sorry"" Ya furta yana dagata gami da bar mata towel din a tare da ita. Rintse ido tayi tana qin"

"dubansa,bai damu ba ya jawo boxer dinsa dake yashe a gefe tun dazun ya saka,ya sanya hannu ya sauketa zuwa sofa bed ya fara tattare comforter da bedsheets din harma da pillow case din,don bayason anni ta sake dawowa idanunta su gani. Toilet ya koma ya shiga sheqa musu ruwa,jikinsa yayi wani irin sanyi ganin yadda ruwan ke wanko jinin. Da gaske ya shigeta ne da tabbaci da yaqinin ta riga ta saba......ya kuma samu qofar a kulle gam dole taji ciwo koma wanne iri akace masa taji. A yadda"

"yakejin cikakkiyar lafiya a jikinsa ya sani,koda bazawara ce yaje mata da irin yanayin jiya lallai saita"

yabawa aya zaqinta ballantana ita din da take sabon hannu.

"Luggage dinta ya bude,ya fidda mata kaya bayan ya saka wata sassauqar riga a jikinsa over sized"

"shirt da wandonta. Fara ce qal data dace da black trouser dinsa. Sama sama yake jinsa shima,saidai abinda ke gabansa ya shafe komai."

"Da rinannun idanunta ta dubeshi sanda ya aje mata kayan,tana so ne ya matsa ya bata waje ta"

"shirya amma bataga alamun xai matsa din ba,hasalima tsaye yake a kanta ya zube duka hannayensa a aljihun wandonsa kaman zai lasheta,ya zube mata nauyayan idanunsan nan yana jin kamar ya buda"

qirjinsa ya fiddo mata mahaukaciyar soyayyar data sakar masa.

"""Ka fita zan shirya"" Ta fada a taqaice ba tare data kalleshi ba,hannayensa ya fidda daga aljihunsa ya juya"

a hankali ya fita.

"Duk yadda taso ta miqe sosai don ta shirya amma hakan ya gagareta,ba zata iya tsaiwa normal"

"kaman kowa ba,abinda ya sanya hawaye yaci gaba da zuba a idanunta,saita dinga jin data sani ta barshi ya taimaka mata,amma kuma batason komai da zai dinga hadata dashi. Da qyar ta lallaba ta saka underwears dinta ta maida rigar,sannan ta lallaba hannun damanta ta kwanta tana ci gaba da fitar da"

ruwan hawaye.

"A nutse anni ta murda qofar tana shigowa da sallama,wata kunya ta taso ta lullubeta,saita rufe"

"idanunta tamkar me bacci,tana fata annin taji kaman baccin takeyi ta juya ta barta."

"""Sannu "" Anni ta fada a hankali da alama ta fahimci ba baccin takeyi ba."

"""Zaki iya tashi?,doctor zata shigo ta dubaki"". Kai kawai ta gyadawa anni ba tare data iya furta komai"

"ba,ta motsa a hankali tana tunanin yadda zata tashi din. Matsawa annin tayi ta kamata a nutse tana cewa"

"""Yi a hankali"" Tausayinta yana kama annin. Yanayin yanayine bame dadi ba,iya yau kawai ta fahimci"

yaron nata yadda jikinsa ke agine hakama komai nasa

"""Allah ya baki ikon jurewa"" Annin ta fada cikin ranta. Sai a yanzu ta fahimci dalilin da yasa yake kaucewa"

"abubuwa da dama,azumin litinin da alhamis akai akai,harma wani lokaci yakanyi azumin annabi dawud,yau yayi gobe ya huta. Wani lokaci takance"

"""Ka dinga hutawa mana me babban suna. ga azumi ga aiki,shi kansa aikin busy din da kake sakawa"

"kanka pressure din tana yawa"". Sau tari murmushi kawai yakeyi ko ya kafa mata hujja da"

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 78

78

"""Ba isashen time na tsayawa cin abincin,wani lokaci azumin yafi,idanma banyi ba coffee ne sai ruwa"

"sai fura ko yoghurt "". A yau ta fahimci ainihin dalilinsa,saita dinga furta"

""" Alhamdulillah"" Qasan zuciyarta. Da gaske Allah ya tsare mata yaranta gabansu da bayansu kaman"

"yadda take yawaita addua a dukka salllolinta na nafila ko na farilla. Tayi imanin inda wani ne ya samu cikakkiyar dama irinta fu'ad din,tarin dukiya kyau ilimi da suna da yayi a duniya ba irin haramtattun ayyukan da bazai aikata ba,ta sani akwai dubban mata dake a shirye su bada kansu ga irin wadannan mutanen,koda ba zasu samu komai ba a wajensu daukaka ce ace yau suna tare dasu."

Sai data zaunar da sabreen yadda zataji dadin zaman sannan ta juya a hankali tana fita parlor din.

"Minti daya ta dawo tare da baquwar fuskar. Dr fadwa siririya fara tas,duba daya zaka fahimci"

"shekarunta duka duka ba zasu haura arba'in ba zuwa da biyu. Anni tana gaba dauke da tea tray,Dr fadwa na biye da ita."

"Qasa sabreen tayi da qwayar idanunta,ba zata iya kallonsu ba dukka su biyun,har Dr fadwa dake"

"matsayin baquwa a idanunta. Ajiye tea tray din anni tayi tana duban Dr fadwa. Kai Dr fadwa ta gyadawa anni,sai annin ta maida dubanta ga sabreen"

"""Ga likita na.....zata dubaki in sha Allah,ki saki jikinki itama 'yar gida ce"" Kai ta dagawa anni a"

"hankali,tana jin takun anni da fitarta a dakin,ta kuma ja qofar ta rufe musu."

Dubanta Dr fadwa take tana kuma karantarta. Ko ba'a gaya mata ba ta fahimci ita din bame saurin

"sakewa da mutane bace,ta miqa hannu a nutse ta kama hannunta ta sanya a nata,abinda ya sanya"

sabreen daga kanta ta kalleta da risunannun idanunta. Da sassauqan turanci take tambayarta da

sakakkiyar murya.

"""Kinci abinci?"" Kai ta girgiza mata a hankali. Ba zata iya tuna wani abincin kirki da taci ba,tun na dazun"

"kafin su fita,ko acan wajen cin kifi ma bata saki jiki taci komai ba,kasancewar ita ba ma'abociyar cin abinci cikin jama'a bane. Kai tsaye Dr fadwa ta jawo tea tray din zuwa saman cinyarta tana matsawa dab da sabreen"

"""Ki saki jiki kici abinci......sai na dubaki,kada ki damu da yawa. hakan yana faruwa ga 'ya'ya mata da"

"yawa,musamman da yake yadda kowacce mace halittanta daban,haka kowanne namiji shima nashi halittan daban......fashewar budurcin mace yana iya kawo fitar jini amma komai zai zama daidai kinji?"""

"Kai ta daga a hankali,ta kuma miqa hannu tana karbar mug din da anni ta hada mata tea me dumi sosai"

da kauri.

"Ita kanta tasan ba komai a cikinta,ballantana kuma da abun ya faru sai taji kamar anyi mata"

"yasa,kamar an kwashe 'ya'yan hanjinta gaba daya,kamar iska tana turata zuwa gaba."

"Kadan kadan take shan tea din,dr fadwa bata matsa wajen kallonta ko yi mata wata tambaya ba"

"ta daban,ta bata time sosai tana duba wayarta har taga ta ajiye. Wayar ta bari ta daga kai tana kallonta,batasha da yawa ba amma saita qyaleta don tasan lallai yanayin bame dadi bane."

Kauda tray din tayi ta matso kusa da ita tana dubanta

"""Sunana fadwa kefa?"""

"""Ameenatu"" Ta furta idanunta suna dan lumshewa"

"""Sabreen sunan inkiya?"" Kai ta gyada,saita fidda takarda fara ta rubuta sunan akai."

"""Eheennn ina ne yake miki ciwo yanzu?"" Shuru tayi don tamabayar tayi mata nauyi da yawa,uwa uba"

"ma gurare da yawa ciwon suke mata,tun daga lips dinta......qirjinta. hatta da tafukan hannunta da suka"

sha murxa zafi zafi takeji suna mata.

"""Ki sake sosai kiyimin bayani,shi yasa madam ta fita ta bamu guri zai iya zama ciwo me zafi nan gaba"

"idan baki bayani ba"". Hannu tasa ta nuna mata wajen ba tare data iya kallon idanun fadwa ba."

"""Alright. zan duba wajen idan ba damuwa?"" Ta fadi da nufin neman izini. Dif tayi abun yana mata wani"

"iri,shikenan ita kuma jikinta ya zama wani budadden guri?"

"""Kiyi haquri saboda lafiyarki,bazai dauki lokaci ba"" Ta fada da sigar lallashi. Kai ta gyada mata a"

sanyaye.

"""Kin shirya?"" Dr fadwa ta fada tana kallonta sanda ta kwanta kamar yadda ta kwatanta mata. Kai ta"

gyada mata tana rufe idonta saboda kunya.

A hankali ta fara dubata cikin qwarewa da nutsuwa yadda ba zata fama mata ba.

"""Oh my god subhanallah"" Abinda ta fada kenan tana maida mata doguwar rigarta."

"""Kin masa gardama ko musu?"" Dr fadwa ta fada tana kallon fuskar sabreen din da tuntuni ta canza kala"

"zuwa red. Tambayar sai ta zama kaman ta bata license din sabon kuka,ita me zata ce mata?,batasan ma me tayi ba. musu ko taurin kan batasan wanne ne tayi a ciki ba,batasan wanne ne ya faru ba."

"""Irinsu sir.......ba kasafai za'ayi musu musu a irin wannan lokacin a wanye lafiya qalau ba. next time"

"kada ki qara musu ko gardama,mijinki yana da duk wani personality da kowacce 'ya mace zatayi alfaharin samunsa a matsayin miji,. kulawa da tattali yake buqata,ko don gaba kada ki sake matse"

"jikinki da hana masa kanki haka"". Sanda take fadin next time din ji take kaman ta ture Dr fadwa,itakam wacce irin sauna ce da zata yarda taci gaba da zama da mutum irinsa?,wanda bisan ciwo ko darajar dan"

"adam ba?,balle ma har hakan taci gaba da faruwa wai a gaba?."

"Daidai nan anni ta tura qofar ta shigo,da murmushi take tambayar Dr fadwa"

"""Kin gama?"" Kai ta girgiza tana dan murmushi itama"

"""Aah fa......madam yaronki aiki ya baro.....bleeding din data dinga yi ta samu tier ne. so dole sai an"

"mata stitches. "" Idanu kadan anni ta fiddo,har jikinta tana jin wani iri. Lallai Allah kadai yasan azabar da"

tasha tunda har an kai ga batun dinki.

"""Gurin yayi ciwo sosai gaskiya. harda bruises banda tier din,dole a dinki wajen,inda first degree tier ne"

"da sauqi....so amma yanzun ma idan kina ganin a bari """

"""No a dinke Dr"" Anni tayi saurin dakatar da Dr fadwa din. A yadda taga yanayin fu'ad din da idanunshi"

"ba yadda zata bari a bar sabreen din a bude,tun sanda momma ta gaya mata marainiya ce takejin kamar kula da sabreen din wani haqqi ne daya rataya a wuyanta."

"""Kiyi haquri a dinke sabreen kinji?,wannan gurin shine mutuncin duk wata d'iya mace a wajen"

"mijinta. akwai zafi amma zai wuce kaman bai faru ba,wannan shi ake kira da cikakken mutunci mijinki"

ya zamana shi ya karbi wannan abun ba wasu shashashai a waje ba.....nayi alfahari da hakan na kuma

"yi alfahari dake kaman yadda nasan yake a wajen mijinki"" Anni ta fada a tausashe hannunta saman kan sabreen da kunya ta hanata koda motsawa bare ta bude idanunta."

"Sake fita anni tayi ta basu waje don sabreen din ta sake sosai. Dr fadwa kuma ta shirya komai,ta"

"kuma yi mata allurar da sai data zubda qwalla kafin a gama,batasan azaban yana gaba ba sai da aka fara dinkin."

"Neman sakayya wajen Alla data dinga yi har batasan sau adadin nawa ta fadi ba,saidai duka cikin"

"ranta takeyi,bakinta baya iya furta komai sai ruwan hawaye dake fita Dr fadwa na mata sannu."

"Kasa zama yayi a falon,sai kawai ya tura qofar dakinsu saddiq ya shige. Kwance yayi kawai"

"saman gadonsu,ya kasa tuna komai sai hankalinsa dake can dakin inda ya barosu,yaji shigar dr fadwa da"

"anni da fitowar annin duka,baisan me yake faruwa ba don haka ya kasa samun nutsuwa. Gefe guda wani"

irin sarqaqiya ya shiga.

"""KARUWA"" Sunanta ma farko kenan daya fara zuwa kunnensa,yaci gaba kuma da zuwa masa daga"

"bakunan mabanbantan mutane. Kenan dukka wadannan bincike da shaidun duka shaidan zur ne?,duka shaidan qarya ne?. Idan har hakan ya kasance kuma ganin da yayi mata a hotel fa?,mashkur dake hannunsu a yanzu haka yana nemanta afujajan da sunan wadda ta kwashe masa komai nasa?,ganinta da yayi fa tare da mika'il?,a cikin kamfaninsa tana fitowa daga toilet dinsa?,binciken daya tabbatar kuma ita ta kwashe kudaden asusun kamfaninsa fa?,wannan kuma mene?. Ta yaya zai fahimta?,ta yaya zai"

"gane?,waye zai warware masa?."

"""Ka nutsu fu'ad.......diban kudi yasha banban da bada mutunci.....don tana kwashe kudaden maza. don"

"kana ganinsu tare hakan ba yana nufin tana basu kanya bane,kowanne matsayinsa daban,cakudasu waje daya kuma shine zai sanya ka kasa banbance inda komai ya dosa"" Wani sashe can qarqashin lungun"

zuciyarsa ya gaya masa.

Sau uku yana leqa parlor din ko zaiga ko yaji motsin anni ko wani abu da zai bashi haske amma baiji

"ba. Kunyarsa da kawaicinsa duka suka qare,sai kawai ya buda qofar dakin ya fito kai tsaye yana tunkarar dakin."

Itace ta farko da idanunsa suka fada kanta bayan bude qofar da yayi. Ta wani sake fadawa farat

daya saboda masifar dinkin. Ko baka santa ba tsakanin a wannin nan idan ka kalli fuskarta zakasan tayi kalar kukan da bata taba irinsa ba.

"Idanunsa ya maida kan Dr fadwa,likitan da sai da tazo ya tuna ya taba saninta a Egypt,ta taba"

"dubashi da yayi wani zazzabi,hankalinta kuma da nutsuwarta shine abinda ya sanya ya bata daman bashi magani."

"""Welcome sir"" Ta fada cikin girmamawa. Kai ya gyada yaja kujera yana zama hankalinshi a kanta. Daga"

kallon da yayi mata ta fahimci qarin bayani yake nema. Dama kuma dole akwai buqatar masa qarin bayanin don ta fahimci kaman yana cikin mazan nan marasa haquri akan abinda ya shafi janibin

auratayya.

"""Mun kammala,anyi mata stitches. but please sir,tana buqatar hutu na koda 3to 4 weeks kafin a sake"

"tabata,saboda a bawa dinkin daman warkewa yadda ya kamata"". Ido ya lumshe sannan ya bude yana jinjina kai."

"""Mun gode. ta yaya zaa biyaki?""."

"""Madam ta biya sir. Allah ya qara lafiya"" Kai ya jinjina yana girmama qaunarsu da anni. Tsantsar"

kulawa da qauna irin wadda akasan uwa kadai take da wannan zuciyar. Komai idan ya kama qoqari takeyi tayi musu shi ba tare data jira yin kowa ko cewar kowa ba.

Tatttare kayanta tayi ta fice taja musu qofar.

"*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*"

08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ

_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 2

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 79

79

A hankali ya dauke dubansa daga kan qofar zuwa inda take zaune. Idanunsa ya zuba mata yana jin akwai

"wani boyayyen abu ciki rayuwarta,wadanne irin masharrantan mutane ne tattare da ita haka?,wadanda ba zasu iya fadin alkhairi a kanta ba?,wadanda ba zasu iya suturta aibunta ba a sanda akazo bincike a kanta ba?. Idan bai manta ba,ya samu tabbacin cikin wadanda suka bada shaida a kanta harda matar"

"babanta,sanda yake jaddadawa abdul haleem bayason fake bincike,baya son kuma gurbataccen shaidu."

"""Wacece a cikinsu?"" Ya tambayi kansa da kansa yana takawa gabanta,tausayi da wata irin mahaukaciyar"

"qauna tata tana hudashi. A yanzun yana jin a shirye yake da duk wani mutum da zai taba rayuwarta,a shirye yake ya bada dukkan abinda ya mallaka a kanta. in fact a yadda ta zame masa mahadin"

numfashi a yanxun......ba dukiyarsa kadai ba hatta da rayuwarsa a shirye yake ya bata ita. Yana jin ya

"shirya kame duk wani wanda ya bada shaidar banza a kanta,ya shirya tuhumarsu ko su waye. komai"

yawansu komai kuma kusancin dake tsakaninsu da ita.

"A jikinta takejin wanzuwarsa a wajen,wannan ya sanya ta sake zabar ci gaba da rufe idanunta,har"

"ya iso gefanta,ya zame kan gwiwoyinsa yana aza qarfinsa akai. Hannusa ya miqa ya kamo tattausan tafin hannunta,ta motsa da sauri ta nufin zamewa amma ya rigata,ya kamo hannun nata da daya hannun ya saka tsakiyar hannayensa yana duban rufaffen idonta. Dukka kalamansa sun gama qwace masa,komai ya auno sai yaji bai hau mizanin bada haquri ba. amma hakanan zaici gaba da gwadawa don ya shirya"

karbar ko meye daga gareta hannu bibbiyu.

""" Can you feel any pain or discomfort?"" Ya tambayeta kaman zai maida idanunshi cikin fuskarta. Shuru"

"ne ya zame masa amsa,bata ko motsa ba ballantana ta nuna tasan da ita yake. Sake matsa hannunta yayi kadan a tausashe,ya motsa labbansa yace"

"""Sabrrrrr"" Nan ma shuru ba wani motsi ko amsa. Jawo hannun nata yayi kadan,ya kuma matso dashi ya"

dora tafin hannun nata saman qirjinsa saitin zuciyarsa.

Tabbas har cikin jininta taji bugun zuciyarsa. kaman yadda dumin cikin hannunsa da wanda taji

"cikin qirjinsa ya tabbatar mata da zazzafan zazzabin da yakeyi,amma ko daya sai taji bataji tausayinsa ba."

"""Im filled with regret for what i did,am truly sorry please kice wani abu man"" Ya fadi cikin zaquwar ji"

"daga gareta,amma still ba wani canji. Shurunta sai yaji yana kasheshi har cikin tsokar zuciyarsa,shirunta sai yaji yana masa wani irin ciwo baya fatan ta zama me hukunci da shuru wanda kusan halinsa"

"kenan,ya kuma san ciwon hakan."

"""Sabrrrr......I'll do everything to prevent it on the future nayi alqaw. "" Future din daya fada shi ya"

"sanyata janye hannunta sa wani irin sauri,saidai kuma kash zafin namansa ya qure nata,kafin ta samu daman boye hannun ya sake kamoshi yana jin wani nisa da takeson haifarwa tsakaninsu. Cikin yanayi na karaya ya sake aza tafin hannun nata saman kuncinta,ya kuma dora kansa akai kaman wanda ya samu"

pillow

"""My heart was beaten past sabrrrrr........zata iya bugawa wallahi please sabr say something"

"mana. """

"""Ka qyaleniiiiii "" Ta fada cikin daga murya tare da wani irin sautin kuka wanda yayi daidai da shigowar"

"anni. Tsaiwa tayi cak tana dubansa,kaman zata koma sai kuma ta tuna da zancan Dr fadwa,don haka ta qaraso cikin,amma ta dauke kai kaman bataga abinda ya faru ba. Idanunsa ya aza kan annin,sai ya janye jikinsa daga wajen yana komawa inda dr fadwa ta tashi wajen data ajiye documents din da tayi rubutu a"

ciki.

"""Daughter"" Ta kira sabreen a hankali wadda ke qoqarin boye hawayenta da mode na fuskarta."

"""Naam"" Ta amsa tana murmushi"

"""Akwai ciwo ko ya ragu?,idan akwai tace tayi prescribing wasu magunguna,ta tura ta pharmacy dinsu zaa"

"karbo ko a kawo miki""."

""" Akwai ragowa"" Ta fadi tana jin yadda gurin ya daddaure mata"

"""Zai daina in sha Allah"" Maida kallonta tayi kansa."

"""Ka hada mata kayanta da duk zata buqata. zatayi matsa zuwa dakina,zan kula da ita zuwa sanda"

"ciwon zai warke"" Anni ta fada adan dake. Da mamaki ya kalli annin yana jin rashin dadi yana saukar masa,abun sam bai masa ba,yana ganin kamar shi yafi cancanta a bari yayi jinyarta,yayin da sabreen taji kamar an mata rahama,wani sanyi ya fara sauka saman zuciyarta.....zata matsa daga kusa dashi zata"

"bada rata me yawan gaske kuwa tsakaninsu,tana jin sai taso ma zata bari idanunsa ya hadu da nata,tabbas da wannan damar zatayi amfani tayi nesa dashi,nisan da zai fara tun daga yanzu har kuma"

abada

"_uhmmm sabreen,anya me jadda zai bari kuwa?,to dai zami gani_"

"Kaman yadda ani ta buqata haka ya hada mata kayan,yana kallo anni ta kamata a hankali har suka"

"fice a dakin. Ba jimawa ta dawo ta dauki luggage din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login