Follow us on social media

Showing 78001 words to 81000 words out of 152107 words

Chapter 27 - Duniya Ta Complete Book 2 Complete Complete Hausa Novel by Asma Baffa

28 May 2026

198

a kanki sai kuma na bankadawa duniya wacece ke bayan na

"maido kudadena cikin dukiyata. ki rubuta ki ajiye"" Daga haka yayi saluting nata,sannan ya taka motar"

da gudu yana wuceta.

"Bata fasa takawa tana nufar gida ba,kamar yadda bata fasa bin bayan motarsa da kallo ba har ya"

"qurewa street din nasu. Wata mahaukaciyar fargaba tana ratsa zuciyarta,sunan mashkur tare da cikakken sanin wayeshi yana gewa tunaninta,a haka ta isa qofar gidan,ta kuma yi tsaye tana duban dogayen katangun gidan kamar me karantar ilimin zanen gidaje."

Tana wassafa yadda zai iya tsallake wadannan dogayen katangun mansion House din tana

qiyasta ta yaya zai iya wuce wadannan securities din da samudawan dake tsaron kowacce kusurwa ta gidan?. Tsaron gidan kadai ya dan sanyawa zuciyarta nutsuwa. saidai kuma bai kore fargaba ko kuma

ya mantar da ita wanene ASALIN MASHKUR BA.

"Gangar hankalinta bata dawo jikinta ba sai data sanya qafafunta cikin gidan,idanuwanta kuma"

sukayi mata arba luxury cars dinsa dinnan dake ajiye a parking lot na gidan.

"Sai yanzu ta tuna bata nema izinin kowa ba sanda zata fita,don sam ta manta hakan yana cikin"

wata doka dake kan kowacce macen aure.....baya ga haka. a lokacin ba abinda take iya tunawa illa

hanyoyin da zata nesanta rayuwarsu da maamah din.

Da confidence din ba lallai su hadu ba har ta wuce daki ba lallai ma yasan bata a cikin gidan ba

ta tura glass door din parlor din tana sanya qafafunta.

Da bude qofar da haduwar idanuwansu lokaci guda ya faru. Iya kallon data gani cikin rusunannun

idanuwansa sun bata wata fargaba da bata taba jinta akan kowa da komai ba.

"Dakiya ta aro ta azawa ranta,tana jin a ranta a yanzu daidai take da kowa a cikinsu ko shi ko"

"mamarsa. Tana jin lokaci bijirewa dukka wani sharuda nasu yazo,tana jin abinda ya rage mata biyu ne. ta samu tabbacin fitarsu zuwa mali a sannan takejin zaman wannan qallagaggen gidan dama me"

gidan gaba daya ya qare mata.

Cikin dakiya da basarwa taci gaba da takowa kaman bataga kowa zaune a parlor din. Tsaf ya

"gama karanta da kuma fahimtar abinda take shirin aikatawa. Ba za'a fishi sanin miskilanci take taken miskili da kowacce dabi'a tasa ba,sai ya dauke kai kaman bai damu da takunta ba,zuciyarsa na sake matsewa,ransa kuma yana qara baci har zuwa sanda ta raba tsakiyar falon."

"Ba zato ba tsammani ta tsinceshi a gabanta. Tsaiwarsa yayi mugun dab da ita,hucin fitar"

"numfashinsa da wani irin dumi da yake bayyanar da bacin rai da zuciyarsa ke ciki yana sauka saman goshinta. Motsawa tayi da nufin ja baya don bata tazara a tsakaninsu qirjinta na wani irin bugawa,saidai"

da tsananin zafin naman nan nasa ya cafki hannunta yana matsawa da kyau

"""Daga ina kike?!,ina kika fita?,gurin waye kika je?"" Ya tambaya a jere cikin tsawar data ratsa dodon"

kunnenta har sai data runtse idanunta.

"Tattara dukka qarfinta tayi ta sabule hannunta daga nasa,wanda ta samu sauqin hakanne"

"saboda banguls din hannunta ya riqe saita zame ta barshi dasu,saidai ko taku biyu batayi ba ya rufo mata baya,sai ya zamana tana tafiya da baya da baya,shi kuma yana maida qafarsa kowanne gurbi data cira qafartata."

Kowanne taku guda daya sai qwayar idanunta sun gauraya da nashi. Abinda take gani cikin idonsa

batasan wanne iri bane. wani yanayi ne da bazata iya fasaltashi ba. Yana sake kunsatota yana sake

"maimaita mata tambayoyin da suke sake razanata,bata ankara ba taji ta bugi bango,tabbacin kowanne"

"space ya qare mata kenan,sai tayi cak sanda ya iso dab da ita,cikken motsi idan tayi yana iya sata ta kasance cikin jikinsa."

"""Gurin wa kika je?,me kuma kikaje yi nace!"""

"""Ban sani ba"" Ta fada da rawar murya tana qoqarin daidata mode dinta. Ko kusa ko alama bata tanadi"

amsar da zata bashi ba.....shi kuma ya matsa mata da tambaya. tambayar da ba abinda take mata sai

"qara fusatata. GURIN WA KIKA JE?,ME KIKAYI?,idan ya fada din sai taji kamar ha debo garwashin wuta"

ya watsawa sassan jikinta ne. Ba abinda yake tuna mata sai mummunar kalmar yawan mutane musamman na cikin gidansu suke jifanta da ita. kalmar da koda ta nuna ta shanyeta tana iya hana

idanunta bacci da wani matsanancin fushi da bacin rai shima irinta yakeso ya ara ya yafa yayi aiki da

"ita a kanta?,batajin kunnuwanta zasu iya jurar ci gaba da jin ana jifanta da kalmar da bata da masaniyar komai a kanta."

Hannuwansa ya dunqule waje guda yanason hana kansa marinta da zuciyarsa keda muradin yi.

Bayaso yakai hannunsa jikinta. baya so ta zama mace ta farko daya fara mari duk kuwa da yanajin ta

cancanci haka.

"""Karki bari nayita maimaita maganata......ina kika fita ba tare da izinina ba? wajen wa kika je?!!!!"" Yayi"

"zancan da wani irin qaraji daya sanyata curewa waje guda,kowanne sashe na jikinta ya dauki rawa"

"""Banje wajen kowa ba. ni ba wajen wanda naje"""

"""....You're going to regret messing with me,for the last time. ina kikaje?"" Ya sake tambayar yana sanya"

hannuwansa duka biyun dake a dunqule ya daki bangon da take maqale a jiki ta saitin kunnuwanta. Abinda ya sake gigitata kenan ta saka hannuwanta duka biyun tana toshe kunnuwanta gami da rruntse idanunta. Zuwa sannan kowacce jarumta dake jikinta tabi ruwa. ba abinda ya rage mata sai rauni daya

narke zuwa kuka.

Cikin qasa da second biyu ta tsinci hannuwan nata jikin nata hannun dake toshe da kunnenta

"yana saukesu,da wani irin taushi da sanyin murya taji yana fadin"

"""Is okay wanne irin matsoraciya ce ke?.enough,stop crying please"" Bata qara tuna komai ba ta tsinci"

"kanta saman faffadan qirjinsa,ya sanya hannunsa daya ya lullube bayanta,daya hannun kuma yana shafa gadon bayan nata da irin salon da uwa kanyi don lallashin jaririnta."

Wani sassanyan qamshi dake ratsowa daga qirjinsa da kuma kowanne sashe na jikinsa ya cika

"hancinta da wani irin sanyi daya soma qoqarin daidaita yanayinta. Saidai hakan ya gaza samuwa,don qarasa rudata yayi,daga yadda kunnuwanta ke iya jin yadda zuciyarsa take bugawa kadai ya tabbatar mata fusatarsa ta gaske ce. amma me ya sanyashi sauya yanayi haka cikin qanqanin lokaci tamkar"

wahainiya?. To kodai yana da boyayyun aljanu da suke sauyashi haka da sauri?.

Bata gama wannan tunanin ba muryar ma'u ta zame mata amsa

"""Ina neman afuwa ranka ya dade. ayimin afuwa"" Ta furta da tsananin kunya tana sadda kanta qasa."

"Bata taba tunanin zatazo ta samesu haka dab da juna ba,kwata kwata ma batayi tunanin suna nan ba,tasan me gidan dai ya fita. dawowar da tayi kuma tazo dubawa amna ko ta dawo?,don sun hadu ta"

daya qofar sai kawai ta shiga sassanta da taji sabreen din bata nan.

Kai kawai ya gyada yana ci gaba da shafa bayanta kadan kadan

"""Hajiya amna ce tace nazo na duba kota dawo """

"""......ta dawo amma batajin dadi,kice ta qaraso"" Da sauri ma'u ta amsa ta juya tana ficewa a gaggauce."

Kaman yana jira ne ma'u din ta fita ya saka hannunsa ya tureta daga jikinsa. Banda yana kusa da

bangon daya bata kariya ba abinda zai hanata zubewa qasa. Da wani fusataccen kallo yake dubanta.

"""Kada ki dauka na yarda ne da abinda kika gayamin muddin na bincika na samu wani abu na daban"

saina miki mafi munin hukuncin da baki taba tunani ba hakanan duk ranar da kika qara gangancin fita

koda qofar gidan nan ne ba tare da izinina ba......saikinyi dana sanin sani na. nan din gida ne da aka

"gina da tsaftatacciyar dukiya ta halas. ba bariki bane ba ba kuma hotel ko gidan karuwai ba"" Daga haka"

ya juya yana daukan file dinsa dake ajiye saman daya daga cikin kujerun falon yana ficewa da sassarfa.

"Wani irin kuka ne yakeson qwace mata amma tana hana kanta,don idan har kunnuwanta sun jiye"

"mata daidai amna na gidan,kuma zata iya iskota koda wanne lokaci,dole ta tattaro dukka wani bacin rai"

"tana hadiyeshi,saidai kuma abinda takeji yafi qarfin abinda zuciyarta zata iya dauka,sai bacin ranta ya"

"zabi fita ta hanyar fitar hawaye daga idanunta zuwa saman fuskarta,ta lallaba tana neman kujera daya ta zauna a kai tana dafe da kanta."

"""Oh god........ damn it. "" Abinda ya dinga maimaitawa kenan cikin mota yana saka yatsunsa cikin sumar"

kansa.

Ya manta yaushe ne lokaci na qarshe daya fusata irin haka. yaushe rabon da yaji zallar bacin rai

"irin wannan dake ratsa kowanne sassa na jikinsa. Ya alaqanta hakan da tozarta igiyar aure da yake shirin faruwa. Sai ya samu kansa da blaming kansa,me yasa zai daga hankalinsa har haka?,ai duk wanda ya siya rariya yasan zata zubda ruwa. Ransa yaji yana qara baci,sai ya yiwa driver magana ya qara speed na"

motor din.

48

"_An karbo daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace,manzon Allah S A W yace,idan miji ya kira"

"matarsa zuwa shimfida taqi zuwa,mala'iku zasuyita la'antarta har gari ya waye_"

"*_qarqashin wannan hadisin akwai qarin haske,idan a wannan qin da tayi kuma ta samu ciki koda ta rasu"

wajen haihuwa wasu malamai suna ganin bata samu wannan shahadar da mace me naquda ke samu ba idan ta rasu_*

*MAAMAH*

Tunda ta cewa zuwaira taje ta duba mata su taci gaba da kiran wayarta ba qaqqautawa don ta

"matsu taji feedback,saidai kuma shuru ba'a picking wayar. Saita koma kiran wayar laila ita dinma duka"

"sammakal. Kamar ta dora hannuwanta akai tayita rusa ihu haka taji,ta tsinewa zuwaira da laila a ranta"

batasan adadi ba

"""Dukkaninku baku da amfani"" Ta fada da fushi,sai taji kamar ba zata iya zama ba. wannan karon zata"

tafi gidan fuad da kanta ne ta dubo meke faruwa ba tare da damuwa da komai ba.

"Tana taka qafarta kiran zuwaira ya shigo,tayi qoqarin hadiye fushinta tana fatar samun feedback"

"me dadi,saidai amsar da zuwaira ta bata ya kusa sanyata zubewa qasa warwas"

"""Bata gidan ita kanta. kuma akan idanuna ta dawo ita kadai"". Iya haka kadai ya bawa maamah amsar"

"abinda taketa zulumin ya faru. Ta kwashesu,ta tseratar dasu,amma dai bata sare ba,tana da sauran hope,don haka kai tsaye ta fara kiran number huda."

Kiran duniya computer ta gaya mata ta kuma jaddada mata wannan layin a kashe yake. Ta laluba

"wayarta kaf ta rasa number wayar bokanta tana me mancewa da cewa mutumin baya riqe waya,yo mutumin dake rayuwar tsakiyar dajin Allah ina gaya service ma bare waya ta dameshi?,mutumin da yake kewaye da aljanu,suke kai masa saqo kuma ku amso masa ko daga ina ne?,me zaiyi da waya?."

"Hajja harira ce ta fado mata,ba bata lokaci ta danna number dinta tahau kira."

*Hajja harira*

"Tun fitar laila bata iya tashi daga wajen ba,idan tace ta qulla tunani sama da dubu da kwancesu"

"tsaf a wajen ba zatayi musu ba. Duk wani tunaninta idan yaje ya dawo a waje daya yake cakewa,tun tana neman qaryata abinda take zargi har zuciyarta ta gama yin ittifaqin amsar dai itace"

"""Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"" Ta furta da wani matsanancin tashin hankali. Tayi imani muddin abinda"

take zargi ne ya tabbata.....to lallai laila zata qare rayuwarta kaf wajen bautar maamah Asiri ne da

"bashi da makari sai mutuwa. yaci uban bita zaizai,yafi uban tace saidai kafin tace. Ita mariya zata yiwa"

"haka?,wannan shine sakamakon alkhairin da ita tayi mata?."

Kamar tasan itace a gaban tunaninta saiga kiranta ya shigo. Kamar kada ta daga amma kuma wani

tunani daya darsu a ranta ya sanyata gyaran murya ta daidaita muryarta sannan ta daga din.

"""Al'amura kamar suna shirin kwabewa hajja. ina tsoron kada zancan mutumin nan ya fara"

"tabbata. ki taimakeni hajja"". Maamah ta fada da tsananin damuwa,damuwar data saka hajja taji wani"

bangaren na tata damuwar da tashin hankalin suna samun sassauci ko banza ba ita kadai ke cikin

"damuwa ba. ba kuma ita kadai zata ci gaba da zama a cikinta ba,taci alwashin dukka yadda zatayi zata"

"yi don maamah taci gaba da tabbata cikin damuwar ta,waye ya gaya mata yaro yana wasa da kan maciji koda kuwa ya rasa abun wasa?."

"Yanayinta ta daidaita don yayi dai dai da yadda maamah zataso taji,tana mamakin zallar rainin"

"hankali irin nata. Bayan mummunar sakayyar da tayi mata,kuma wai ta nemeta da tata matsalar tamkar ma batasan me ya faru ba?."

"""Me yake faruwa?"""

"""Garkuwata ta subucemin daga yanzu zuwa kowanne lokaci zan iya fuskantar barazana daga wajen"

"abun hari na,kowanne hope nawa kuma ya subuce hajja. meye abunyi?"" Ta qarasa maganar da sigar"

"tambaya cike da damuwa. Iska hajja ta furzar tana dan bubbuga tafin qafarta kadan kadan,a nutse tace da ita."

"""Bani lokaci mariya nayi tunani mintuna kadan nake buqata"". Jikinta a sanyaye ta amsa mata suna"

katse wayar su dukka biyun.

"Wayarta take dan bugawa cikin tafin hannunta cikin salo na tunani. Mariya shegen kai ce,tana"

da nata matsanancin wayon da kai da kake rayuwa da ita kayi kadan ka fahimci komai idan ba ita taso ba. saidai kuma a wannan yanayin da ake ciki mariya tana tafin hannunta ne. Bata isa tayi wani motsi

"cikakke ba ba tare da ita ba,itace ginshiqin itace kuma madogarar. To shin batasan abinda tayi mata"

"bane?,batasan me ya faru ba?,ko tsananin iya bariki ce kawai?."

"""Inaso na samu tabbaci"" Ta furta tana daukar wayarta data aje tun daxun ta sake lalubar number"

maamah din.

"Bugu daya tak ta daga,ta sanya wayar a kunnenta tana kiran sunan hajja."

"""Duk abinda zaka daukoshi ko ka matso dashi don biyan buqatarka. kuma ya gaza yin wannan aikin sai"

"nakega bashi da wani amfani,kau dashi kawai zaifi me zai hana ta gusa daga rayuwar fuad tun kafin"

"matsalolin da boka ya baki a dunqule su fara bayyana har sufi qarfin shawowarki? ga laila nan?,umarni"

"na da naki sune zasu zama abun binta,a azata a bigiren da wannan ke kai,nayi Imani da laila. tabbas ba"

"zata sabawa tsarinmu ba. sirrinmu kuma a lullube""."

"Nauyi maamah taji maganar tayi mata,sannan sam bataji maganar ta kama hankalinta ba. Har"

"cikin jininta da zuciyarta takejin laila bata mata ba,kwata kwata bata dace da wannan aikin ba,bata dace ma ta zama matarsa ba koda na minti guda ne kuwa. Tasan wacce hajja farin sani,tana tunanin ita ko yaronta zasu kubuta daga ayyukanta ne?,sai ta girgiza kai a fili tana jin abun bai kama hankalinta ba. To amma dole sai tabi ta takatsantsan kafin ta fahimtar da hajja din,tafi kowa sanin hajjan akan laila bata"

dagawa kowa da komai qafa.

"""Aah fa hajja harira,laila ni dake duka 'yarmu ce. ba zamj jefata cikin wannan risk din da wahalar"

"ba......qyale bare dai,wanda idan ya sabawa tsarinmu kowanne mataki zai iya fadawa kansa. kamar"

yadda itama wannan din MUMMUNAN SAKAMAKO na rantse miki da Allah zai yita bibiyarta. ba zan

"qyaleta ba,sai na banbance mata tsakanin aya da tsakuwa!"" ."

"Turqashi!. hajja ta fada qasan ranta,kai tsaye a bayyana ko a kaikaice maamah bata qaunar laila"

ta kafa tarihin zama matar muhammad me jadda. wannan shine amsar tambayarta kai tsaye idan aka

cire kauce kauce.

"""Ke yanzun wanne shiri ne na gaba kike ganin ya kamata muyi?"" Ta mata tambayar tana relaxing kanta"

don samun bakin zaren daga inda zata dasa nata aikin.

"""Ki bari tukunna na samu nutsuwa daga wannan,abubuwa su hau kan saiti,zaki ganewa idanuwanki ba"

"tare da nace dake komai ba"". Ta fadi mata kaman yadda ta saba. Tana da boye duk wani shiri nata,zai"

"wahala tana kan shiri ka sani,ko a baya wannan ne ya zama SILA da sanadin da LAILA ta shiga DUNIYAR lissafinta,qila data tsaya neman fashin baqi wajen boka kamar yadda hajja taso suji ba shakka da qila"

yanzun haka laila bata fada wannan BAQAR MASIFAR ba. dukka hajja ke wannan tunanin cikin ranta

tana jin wani bacin rai yana taso mata.

Hajjan ta bude baki zatace wani abu sautin kukan laila ya mamayi kunnuwanta daga cikin wayar.

"Wani abu ya daketa,tayi shuru tana sauraren tambayar da maamah keyi mata kafin kiran ya yanke."

"""Tashin hankali!"" Ta fada a sarari tana miqewa tsaye,ji take kamar ta wuce kai tsaye gidan maamah"

amma wata zuciyar na jan kunnenta

"""Sai kinyi kamar baki sani ba. sai kinyi kamar baki fahimci komai ba,saikin maida komai ba komai ba""."

Wadannan maganganun suka sanyata rusuna ta koma ta zauna wuta naci gaba da balbala a zuciyarta. Daidai sannan nafessa ta shigo da mopper da broomstick tare da sallama a sanyaye cikin girmamawa.

"""Ubanme kika shigo kiyimin?"". Kai ta sunkunyar"

"""Kiyi haquri,haidar ne ya tashi da zazzabin haqori yau shi yasa ban shigo sharar da wuri ba"". Duk da"

"jikanta ne bata tsaya ta nuna kulawa ko alhinin komai ba,hasalima bata fahimci gaya mata take baida lafiya ba yaron,sai ta daka mata tsawa tana fadin"

""" Sharar da bakiyita dazu ba sai yanzu ko?,baqar munafuka,fita ki bani waje"". Tashi sosai hankalim"

"nafeesa yayi,take idanunta suka tara ruwan hawaye,tana tsoron me zata gayawa d'anta a kanta idan ya dawo,tanason aurenta batason ta kashe mata shi,wannan ya sanya ta sulale tana tsugunnawa ta soma"

mata magiya tana bata haquri

"""Ki tashi bani waje kafin na rufeki da duka,sharar ce nace banaso ko ana dole?"" A nan ta fahimci bawai"

"iya rashin sharar bane kawai da ba'ayi ba ya sanyata haka,akwai wani abu na daban da ya bata mata rai,wannan ya bata sassauci sai ta miqe tana sake bata haquri ta bude qofar ta fita gami da rufe mata. A"

qasan ranta tana tafe tana addu'ar

"""Ubangiji ka qara mata damuwa fiye da damuwoyin data sanyawa zukatanmu ya rabbi ka shagaltar"

"da ita da damuwarta ta yadda zata zame mana mu kuma hutun da bamu taba samunsa cikin gidajen mazajenmu ba""."

49

"_Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; ""idan dayanku yazo masallaci,ya duba"

"takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya kawar da ita daga jiki,yayi sallah da takalminsa_"

"*_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin ba najasa ko dauda a jiki_*"

49

"Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login