Chapter 4 of 45
ZUCIYAR ALIYU CE Zuciyarsa Tata Ce By YUSRAH MUSA
💓ZUCIYAR ALIYU CE💓
WhatsApp no:+234 8160983083
@YUSRAH MS ABUBAKAR
PAGE 05
"Aliyu" ta fad'a tana kallonsa d'agowa shima yayi yana kallonta nata ya daina wancan tunanin da yake kamar zatai kuka tace "dan Allah ka kaini sai ka shigo ku gaisa da Maman namu" kaiya girgiza mata yana cewa "a'a ba yanzu nake son naje mu gaisa ba bari nasa driver ya kaiki" jin abinda yace yasa ranta na tafasa tace "a'a barshi na samu ne napep kawai nagode" ta d'auka idan yaji haka zai kaita sai taji yace "ok sai kin dawo" ya fad'a yana juyawa ya koma inda Sameer yake da kallo ta bishi hawayen damuwa sun cika mata ido ganin ya karasa rumfar ya zauna kar yaga shi take kallo ko tsaiwar me take a gurin yasa da sauri ta juya musu baya tare da bud'e handbag d'inta ta d'auko dan karamin handkicif ta goge hawayen fuskarta sannan ta wuce batare data sake marmarin juyawa ta kalli inda yake ba ta tari napep d'in ta tafi.
Aliyu kam yana komawa inda Sameer yake ya kalle shi fuska shima sam babu walwala yace "Sameer wai dan Allah meyasa kake min haka ne kasan irin wahalar da zuciyata ta shiga cikin lokutan nan da garari ina cikin tashin hankali amma kai ko a jikinka abun bai dameka ba why"? Ya karasa maganar ransa babu dad'i ko kad'an da mamaki Sameer yace "Subhanallahi Marshall meya faru wani abu nayi maka ban sani ba"? Huci Aliyu ya fitar me zafi yana girgiza kai yace "meye ma bakai min ba Sameer yau kace zaka fad'a min inda zanje na sameta ka'ki ni ka fad'a min garin da tafi kawai zanje na ganta ka gane tunda kai baza kaje ba" dafe kai Sameer yayi alamar sha'afa da maganar da sukai shima yad'an girgiza kan yana cewa.
"Sorry Marshall kayi ha'kuri dan Allah na kira wayarta tun jiya ta'ki shiga yau da safe kafin na fito mu had'u saida na kirata saboda nasan dole zaka tambaye ni ita amma labarin d'aya ne yau kuma wayar na rufe shine dalilin da yasa banyi maka maganar ba".
"Ok sake kiranta yanzu maybe ta bud'e wayar".
"Ok tom bari mu gani Allah yasa tana bud'en" Sameer yai maganar yana bud'e wayarsa ya sake kiranta ta shiga amma bata d'aga ba har kiran ya katse wani ya sake danna mata nan ma dai bata d'aga ba kallon Aliyu daya zuba masa ido yayi yana cewa "ka gani da idonka ko wallahi na kirata d'azun ma maybe bata kusa da wayar ne kayi ha'kurin zuwa jimawa saina sake gwada maka" Sameer na rufe baki Aliyu ya mi'ke yana cewa "bazan iya ba Sameer tashi muje ka tambayi mamarta kawai zanfi samun kwanciyar hankali akan wannan bugun da zuciya ta take yi dole sai naje naga likita ina ji a jikina kamar bani da lafiya" mi'kewa shima Sameer d'in yayi yana cewa "a'a Marshall 'kalau kake ka yarda babu abinda yake damunka sai ciwon so".
"Kuma ciwon son ba cuta bane shine ma babbar illa wacce zata saka zuciyar mutum ta buga ya mutu kamar dai ni ka gane"?.
"Eh na gane sosai".
"No baka gane ba Sameer kuma bazaka gane ba sai ranar da so ya shige ka idan ma zaka fahimta kenan" murmushi Sameer yai yana kallon Aliyu daga baya kuma yace "ok muje gurin Umma d'in saina tambayi yaushe zata dawo d'in" d'an 'karamin numfashi Aliyu ya fitar bai sake cewa komai ba suka wuce saida sukai gaf da shiga gidan sannan ya tsayar da Sameer yana cewa "please Sameer fatan ba wanda yasan da maganar a gidan nan ko"? Kai Sameer ya jinjina yana cewa "tabbas ba wanda yasan kana son Zainab bayan ni domin ko ita kanta Zainab d'in bata sani ba saboda ban fad'a mata ba gara na bari idan lokacin daka d'iba yayi ka sameta da kanka ka sanar da ita hakan zaifi" "ok dama na d'auka ko mamarta ta sani ne amma tunda kace ba wanda ya sani naji dad'i yanzu zan iya shiga kaina tsaye cikin 'kwarin gwiwa" dariya Sameer yai yana cewa "kenan da ace sun sani baza ka shiga ba".
"To Sameer na shiga nayi me indai ba gaisar dasu zanyi ba sun zama surukai na".
"Gaskiyar ka wannan haka yake" Sameer na rufe baki suka ji ance "Yaya Aliyu ina yini"? Duk juyawa inda akai maganar sukai domin muryar mace ce ganin Haulat tsaye da jaka a hannunta alamar wani gurin zataje yasa Sameer sakar mata wata uwar harara yana cewa "gidan uban wa zaki je yanzu"? D'an zaro ido tai cike da rashin gaskiya tace "uhm uhm uhmm" ta kasa magana sai nishi da take kamar me jinya cikin fad'a Sameer yace "uhm me nace gidan uban wa zakije da jakar hannunki waye ya aike ki"? Baya ta matsa da sauri jiki na 6ari bata iya bashi amsa ba saboda ba inda aka aiketa kawai yawonta data saba fita zata tafi tsawa ya buga mata da karfi wacce tasa ta juya da gudu tai cikin gidan tsaki Sameer yaja mai mugun 'karfi alamar ransa ya 6aci sosai ko magana bai sake yiba sukai cikin gidan suma da yake mahaifin Zainab shine 'karami shiyasa kofarsa itace can ciki ta 'karshe lokacin da suka shiga iya mahaifiyar Sameer ce kad'ai tana wanke-wanke da sallama suka shiga ganin Sameer da wanda batai zato ba yasa ta washe baki tana mi'kewa tsaye tace "a'a Aliyu kaine d'an albarka kenan sannu da zuwa an dawo lafiya ku karaso man" ta fad'a tana shiga d'akinta bin bayanta sukai ta shimfid'a musu tabarma suka zauna Aliyu ya gaida ita cikin sakewa ta amsa sai faman jansu take da hira saboda tasan matu'kar suka fita yanzu sai sun had'u da Umma tunda taga bata fita ba amma tayi wanka anguwa zataje mi'kewa sukai zasu tafi itama data mi'ke suka fito tare saboda taji kamar alamun 'karar rufe 'kofa maybe ta fice d'in amma me suna fitowa taga kofarta a bud'e kenan ba d'akin ta ne aka rufe ba d'akin mahaifin su Sameer ne shine ya fita tunda taga ga alamar padlock nan a jikin murfin kofar d'akin nasa ya akai zai fita bai bada abinda za'a dafa ba saboda yau yaga ba ranar girkin Umma bace 'kwafa tai tana hararar murfin kofar kamar shine a tsaye a gurin da har zata bi bayansa sai kuma ta fasa ta zauna a gurin aikinta taci gaba da wanke kwanukan.
D'akin Umma su Sameer suka shiga a lokacin ta gama shiri kenan ta d'auko 'yar kamar purse d'inta taji sallamar su amsawa tai tana le'kowa ganinsu yasa da fara'a tace "tofa sannu da zuwa Sameer karaso dashi man kamar wani ba'ko ka tsaya a waje ku shigo dan Allah" shiga sukai itama tabarmar ta shimfid'a musu suka gaisa sannan Sameer yace "am Umma nikam yaushe Zainab zata dawo ne ta tafi kawai tabarmu yau kusan sati uku ko wata guda zatai ne idan na gaji fa saidai kuga naje na d'auko ta" 'yar dariya Umma tai tana cewa "ayya Zainab nima bansan ranar da zata dawo ba tunda ba waya muke ba amma dai tunda hutu ya kusa karewa watakil ka ganta satin sama ta dawo".
"Ok nayi kewar ta ne balle kamar can d'in babu network sai nayi ta kiranta wayar ya'ki shiga ko kuma idan ta shiga ma bata d'aga ba kodai a gida take barin wayar idan zata fita ne"?.
"To Sameer Allah masani saidai idan ta dawo ka tambaye ta wallahi nima da ka ganni nan na matsu ta dawo saboda d'inkunan mutane wasu suna ta zuwa tambayar idan anyi musu nace bata nan kaga babu dad'i shiyasa nake so ta dawo duk da keken ma ya d'an samu matsala sai takai shi gurin gyara".
"To Umma ta sake wani man ta ha'kura da wannan kwanan gida wunin garejin ba'a wata sai yaga gurin me gyara" murmushi Umma tai bata ce komai akai ba saboda ba kud'in gyaran kuma indai ya sani shine zai bata ta gyaro mahaifiyar sa na ganin kuwa sun shiga uku da zagi da gori iri-iri shiyasa ma batace masa babu kud'in gyaran ma shima daga haka bai sake magana ba sai mi'kewa da sukai ganin anguwa zata tafi karsu 6ata mata lokaci sallama sukai mata daga nan ko 6angaren Hajiya basu le'ka ba kawai sukai waje...........
📌AYI HA'KURI IDAN AN SAMU TYPING ERROR MATSALAR KEYBOARD NE📌
@YMA DUTSE
Ok PAGE 06
Fitarsu baifi da mintu biyar ba a fusace Asiya ta shigo tana buga murfin kofar su tace "ke Asabe ina Sameer yake"? D'agowa daga aiki Asabe tai tana cewa "ban gane Ina Sameer ba lafiya".
"Au tambaya ma kike wai lafiya lafiyar ce ta kawo haka idan yana ji zan furta idan baya ji ki fad'a masa gargad'i na dashi akan Haulat ne daga yau karya kuskura ya sake koro min yarinya kamar wata akuya dan ta fita daga gida ina ruwansa da ita kowa yaci tuwon gidansu itama tana da yayun da zasuyi mata fad'an ai basai yayi mana shishshigi ba idan tsare gidan yake so ina yana da 'kannai shima yayi musu man amma banda Haulat duk inda taga dama zata fita taje bai isa ya hanata ba saboda ba shi zai aureta ba idan ya tare gida yace bazasu fita ba a gidan ubanwa zasu samu mijin auren dan kan uwarsa to ki fad'a masa sa'ko daga ni ba ruwansa da 'yata yaiwa d'an kowa a gidan nan bai dame niba amma banda tawa domin zamu kwashi damben tsiya dashi kin gane idan kunne yaji jiki ya tsira" tana fad'in haka ta juya fuuu tai waje shiru Asabe tai cikin takaici ranta na 'kuna wato da tacewa Sameer ya daina takurawa yaran gidan nan akan fitar da suke baiji ba gashi yanzu ya jawo mata magana bari ta gama wanke-wanke nan taje itama har kofarsu ta tsiyata Asiya sai hankalinta yafi kwanciya idan bata rama wannan cin mutuncin ba ba'kin ciki ne zai kashe ta.
Fitar su Sameer kam basu zauna a anguwar ba mota Aliyu ya d'auko suka fita zuwa wani guri domin ya fad'a masa dama zasu je shiyasa ya fita da shirinsa su Afifah kam yau ranar 'yanci ce a gurinsu tunda gidansu Momy ya tafi maybe sai dare zai dawo musu sun san zasu sha'kata badon Afif yana nan ba.
ANGUWAR HAUSAWA
Saukowa yake daga stairs yana kallon fuskar Maminsa yadda take aiko masa da wani kallo murmushi yayi daidai ya karasa saukowa yazo ya du'ka ta gefen fuskarta ya mata kiss yana cewa "good morning Maah d'ina fatan kin tashi lafiya sorry na makara nasan nayi laifi kiyi hakuri yanzu zan tafi" kaita d'aga tana cewa "toya na iya Shareef ai dole nayi ha'kuri amma kai kamar karamin yaro kullum sai ana fama da tashinka daga barci bayan kasan kana da ayyuka"? Kunnuwansa ya kama ya ri'ke yana cewa "sorry Mami na bazan sake ba daga yau" mi'kewa tai tana nufar hanyar dinning tace "kazo kayi breakfast saika tafi tunda aikin gama ya gama".
"A'a Mami na makara da yawa kawai bari na tafi" juyowa tai da sauri tana kallonsa lokacin da zai bud'e kofa tace "a ina kenan zakai badai abincin waje zakaje kaci ba"? Kaiya girgiza yana cewa "a'a Mami nasan bakya so ai saina dawo".
"A'a indai haka ne tsaya na had'a maka a basket ka tafi dashi zaifi" takarasa maganar tana nufar hanyar kitchen tsayawa yayi yana sake kallon agogon dake d'aure a hannunsa ba karamin makara yayi ba yau gashi yana da aiki sosai idan yaje har gaggauta yayi ta gama had'o masa kamar yayi tsuntsu ya tashi haka yake ji tana kawo masa kuwa ya sake sakae mata sabon kiss yana cewa "thank you Mah d'ina Allah yasa na samu mace mai kyawun dabi'u irin naki" ya fad'a yana juyawa ya bud'e kofa ya fita murmushi tai tana kallonsa sakamakon kofar glass ce harya shiga mota sannan ta juya tana komawa insa ta tashi ta zauna.
Sakamakon yasan ya makara sosai ya kwashi motar da gudu dan yaje da wuri yana parking kuwa yaga Baby a tsaye tana faman le'ke le'ke alamar jiran zuwansa take ganin yayi parking yasa da sauri ta gangaro daga inda take ta taho gurinsa cike da murmushi jin dad'in ganin nasa tana karasowa cikin shishshigi ta kar'bi basket d'in d'aya d'auko daga bayan mota tana shirin amsar sauran kayan dake hannunsa yace "no thank muje ko yau na makara" ya fad'a yana yin gaba da d'an sauri ta bishi har lokacin da murmushi akan fuskarta tace "good morning ya kake fatan ka tashi lafiya"? Bai tsaya da tafiyar da yake ba saboda saurin makarar dayai yace "lafiya kefa"?.
"Nima ina lafiya baka tambaye ni jiya yaushe na tafi gida ba"?.
"A'a wannan bai shafe ni ba akan me zan tambaye ki saboda kawai ina so naji yadda kika 'kare ai nasan ba anan kika kwana ba ko"?.
"Eh man taya zan kwana a hospital niba midwife ba amma sai wajen bayan sallar isha na tafi gida ina zuwa Mom ta hauni da fad'a kamar zata dakeni da'kyar na samu na shawo kanta suka fahimce ni amma da cewa tayi da Yaya Hakim ya shigo zata fad'a masa".
"Uhmmm" kawai shine abinda Shareef yace daidai sun kusa karasawa office d'insa ba zato yaji Baby dake bayansa ta danna wata ba'kar d'anyar ashar wacce yasa shi juyowa da sauri yaga meya faru basket d'in hannunta ya gani a 'kasa ga kayan nan sun tarwatse a gurin sannan ga wata budurwa a tsaye da takarda a hannunta kafin ya tambayi abinda yake faruwa Baby ta d'auke ta da mari cikin 6acin rai da tsawa "mahaukaciya ce ke ko kuma makauniya ce bakya gani ne tsabar shashanci da'ki'kiya kin taho kina kallon 'kasa kina iyayin kinzo ki buge ni da wannan banzan jikin naki yau sai kin biya wannan abincin" ta karasa maganar tana shirin kai mata mari na biyu dakatar da ita Shareef yayi ta hanyar cewa "no don't do that again karki 'kara marinta kin gane ni taiwa laifi bake ba bai kamata ki dauki hukunci a hannunki ba kalli fa itama tayi asara" kallon inda yake nuna mata tayi taga wayarta babba 'kirar Apple a 'kasa screen d'in ya fashe ta'be baki tai tana jan tsuka tace "sai me ni banji komai ba wallahi Allah ya 'kara inama ace idan ta bud'e taga taci secreen nan gaba saita kiyaye ta ri'ka kallon gabanta idan tana tafiya meye amfanin wadannan manyan idanuwan naki gashi harda glass amma a banza".
"Baby kinyi hauka ne meye damuwarki da ita akan abinda bai Kai ya kawo ba sai maganganu marasa dad'i kike fad'a mata Ina ni taiwa idan ma 6arnar ce nace na yafe shikenan komai ya wuce muje" d'aukawa Baby tai tana tattara kulolin sannan ta zuba a basket d'in lokacin data d'ago kamar ta sake sharara mata sabon marin sai kuma taja tsaki ta wuce zuwa office d'insa shiru budurwar tai idonta cike da hawaye ba Marin datai mata ko fashewar wayarta ne ya 6ata mata rai ba kawai zagin datai mata batasan ita 'yar waye ba kawai ka kama zaginta badan bata son tashin hankali ba tana komawa gida saita sanar da Dad d'inta yau Baby bazatai kwanan gidan su ba sannan idan taga dama aikin da take ta'kama dashi sai tasa a cireta ta nuna mata karshen isar wace ita amma ba komai....................
Wayarta dake 'kasa Shareef ya d'auko ya saka 'karamin towel d'insa ya goge mata ya mi'ka mata d'agowa tai tana kallon sa tare da saka hannu ta kar'ba ranta na 'kuna da'kyar tace "na gode" ta fad'a tana juyawa ta wuce sosai ransa ya 6aci jin yadda tace masa ta gode d'in kowa yaji yasan ba kamarin ciwon abinda Baby tayi mata taji ba amma ta danne ta nuna godiyarta ga yar kulawar daya bata a fusace ya shiga office d'insa ganin ta tsaye yasa ya nuna ta da yatsa yana cewa "Baby daga yau kinyi na farko kinyi na karshe kar tsautsayi yasa na sake ganin idan nazo kinje tara ta ki barni komai nauyin kayan da nazo dasu na d'auko da kaina kin gane"? Had'e rai tayi tana cewa "yanzu Shareef saboda wancan yarinyar shine ka d'auki fushi dani ban kyauta ba kenan abinda nayi ban burgeka ba har kazo kana tuhuma ta"? Buga table d'in dake gaban kujerar da yake zama yayi muryarsa na nuni da tsantsan fushi yace.
"How to impress you meye abun burgewar anan wannan jahilci kenan kika nuna ba komai ba" nuna kanta Baby tai tana cewa "Shareef ni ka kira jahila saboda nayi fad'a a kanka"? Sabuwar tsawa ya sake buga mata "you are no one but stupid and let me tell you today i am ending all this burden" ganin yadda yake fad'a yana mata tsawa yasa itama zuciya tazo mata wuya cikin d'aga murya tace.
"Tell that to who is afraid Shareef na gaji da wannan tsawar da kake min saboda nayi wancan abun ne zaka sakani a gaba da fad'a kamar wani ubana na mareta kuma wallahi da nasan ita xaka baiwa gaskiya idan ka shigo saina sake marin ta" kaiya jinjina yana nuna mata hanyar fita yace "get out from my office" tsananin mamaki ne ya kamata har batasan lokacin da tace "Shareef na fitar maka a office kace akan wancan yarinyar ko sonta kakeyi ka fad'a min"? bai bata amsar tambayar ta ba sai sake nuna mata hanyar waje dayai yana cewa "as from today I don't want to see you in my office again har abada indai ba aiko ki akai ba kin gane"? Baki ta bud'e zatai magana ya daka mata tsaya.
"Get of my sight kafin na 6alla ki" tsawar da bata saba jin irin taba a rud'e ta fice da gudu tana zubar da hawaye wani irin 'kak'karfan tsaki yayi tsabar yadda ta 'kona masa rai akan abinda bai kai ace damuwa ta shigo ciki ba tasa ya 'kara 6ata lokacin sa anan aje wayar hannunsa yai yana d'iban abubuwan daya kamata ya d'iba ya fita