Chapter 3 of 45

ZUCIYAR ALIYU CE Zuciyarsa Tata Ce By YUSRAH MUSA

"da nayi me"?.

"Do you want to know why"? Dan rainin wayo na miki tambaya kema ki min ni sa'anki ne"?.

"A'a ba daya amma ai masoyi na ne kai ko ba haka ba"? Ba arziki tasa Aliyu kallonta jin abinda tace yace "waye masoyin naki"?.

Fari tai masa da ido tana murmushi tare da rausaya kai tace "ina wani bayan kai Aliyu kaine da wa kake zato"? Kai ya jinjina sakamakon jin abinda tace wai sonshi take amma ta had'a kanta da aiki babba sannan ta d'orawa kanta damuwa saboda gaskiya bata da gurbi a zuciyarsa shifa yayi kyautar zuciyar tasa taya zai iya saka wata a ciki mutum d'aya ce mamallakiyarta baya jin akwai ta biyun ta...........

"Aliyu baka ce komai ba ya aikin naka fatan ka dawo lafiya sannan abinda na fad'a kasan haka ne kaima shiyasa kayi shiru ko"? Kai ya girgiza mata yana cewa "ki daina zaton haka a ranki ki daina 'bata lokacin ki a kaina Amira" da mamaki tace.

"Me yasa"?.

"Bana so kiga kamar na cuce ki a gaba" girgiza kai tayi da sauri tana cewa "bazan ta'ba gani ba Aliyu ko maye zakai min dan Allah ka aure ni"? Tana rufe baki ya d'aga mata hannu yana cewa "listen up daina ro'ko na Amira karki 6ata lokacin ki a kaina ni ina da wacce nake so kin gane"? Zaro ido tai firgici dimuwa damuwa tashin hankali razana sune sukai mata dirar mikiya lokaci guda tea din data kurba ya 'kwareta ta soma tari mai karfi ba 'kak'kautawa tare da dafe 'kirjinta yana kallon ta baice 'kala ba har ta gama Afifah da ta taho da gudu tana bude fridge ta dauko mata ruwa tana kawo mata kallon da Aliyu ya mata yasa da sauri tabar gurin tana rike baki cikin mamakin wa Aliyu yake so dama yana soyayya amma bai ta'ba nunawa ba lallai kwanan nan zasu samu Aunty.
Kasa d'aukar ruwan Amira tai balle ta sha ga zafin da 'kirjin ta ke mata kamar gidan gasa biredi hawaye ya cika mata ido yana gangarowa amma taga Aliyu kawai breakfast d'insa yake hankalinsa a kwance bai nuna alama damuwar abinda take ba kuka ta fashe dashi tana cewa "Aliyu dama kayi haka da niyya ne a zuciyarka dama son kashe ni ne 'kudirin ka shiyasa kayi min hakan"? Murya a tsawace yace "ke are you out of your sense ni kike fad'awa haka kinyi hauka ne"? Cikin kuka tace "ba hauka ne ya kama niba Aliyu kaine kake neman haukata ni da maganganun ka".

"Da nace miki me"?.

"Kana da wacce kake so".

"Eh zan miki 'karya ne saboda ina gudun 'bacin ranki"?.

"Kuma auren ta zakai"?.
"To da me kika d'auka zan yaudare tane? Kaita girgiza ranta a 'bace tace "kawai ni ka bani amsa aurenta zakai"?.

"Ban sani ba".
Jin abinda yace yasa sabin hawaye suka fara zuba mata da'kyar muryarta na ma'kalewa tace "a ina take"?.

"Meye matsalar ki da inda take"?.

"Had'uwa nake so muyi da ita domin naja mata kunne a kanka ta fita layin da ba nata ba kafin tai asarar rayuwar ta dan wallahi saina kashe ta indai na gano wacece" mi'kewa yai cikin halin ko in kula alamun maganganun ta basu sha masa kai ba yace "look it up on Google madam zaki ga komai nata da adireshin ta da mahaifinta da inda suke sai kije ki sameta tana daidai dake" ganin zai bar gurin yasa a gigice Amira itama ta mi'ke tana shan gaban sa cikin kuka tace.

"Meye sunan ta da ya zan gane ta"? Murmushin ganin haukan ta yai yana d'an girgiza kai yace "never mind 'yan mata karki damu kanki ba sunan ta zaki nema ba ita ya kamata ku had'u tunda wannan ne burin ki ko"? 'Kara ta saki mai 'karfi tana dukan dinning d'in a haukace tace.

"Ka fad'a min sunan ta Aliyu fad'a min wace ita a ina zan sameta"? Lamarin Amira yana mugun bashi dariya matu'ka amma ya dake dan baya son raini ko tace da wasa yake mata yace "sunan ta Mrs. Aliyu Marshall anguwar da take gidan Aliyu d'akin da take rayuwa zuciyar Aliyu na gama fad'a miki komai a kanta da inda zaki sameta tana cikin zuciya ne idan kika sake min wata magana a kanta nan gaba saina 6alla ki" yana gama fad'a mata haka ya bi ta gefenta ya fita a parlon 'kamewa guri daya Amira tai ta daskare ta kasa motsin kirki numfashinta ya d'auke lokaci guda taga duk parlon yayi mata wani irin ba'ki bata ganin komai sai duhu ganin haka yasa Afifah tasowa zata zo gurin ta kafin ta iso taga Amiran ta yanke jiki ta fad'i 'kasa da gudu ta karaso tana kiran sunanta daidai Elham da Fati sun sauko da sauri suma suka zo inda suke.

"Lafiya ita kuma wannan fa meye ya sameta"? Elham tai maganar cikin mamaki Afifah bata bata amsa ba sai kallon su datai tana cewa "ku taya ni mu d'auke ta kar Momy ta fito bansan me zance mata ba dukda nasan komai" du'kawa sukai suna d'ago ta sukai stairs da ita har bedroom suka ajeta akan gado zama Afifah tai tana cewa "Fati mi'ko min ruwa a fridge na shafa mata".

"Ok" Fati tace tana mi'kewa ta d'auko mata Elham da take faman kallon Amiran tace "wai dan Allah Aunty Afifah meke damunta ne"? Sau'ke ajiyar zuciya Afifah tai kamar mai yin rad'a tace.

"Ita da yaya discipline ne".

Zaro ido sukai a tare suna cewa "yaya boss me ya hada su kuma"? Dariya Afifah tai harda tafi tana kallon fuskar Amira dake ri'ke shakaf da ruwa tace "maybe Amira tana son yaya discipline ne shi kuma ya fad'a mata da akwai wacce yake so".

"Wacce yake so!?. Cewar Elham tana mi'kewa tsaye tsabar yadda maganar ta dirar mata kai Afifah ta jinjina irin tabbas d'in nan tace "eh wacce yake so akan haka ta fad'i kunsan ma wani goge hadda irin tasa da tace ina anguwar su take cewa yai tai sacin a Google zata gani ya sunan ta yace Mrs Aliyu Marshall anguwar su wai zuciyar Aliyu kiji fa"? Suma kallon juna sukai basu san lokacin da suka fara dariya ba kai Fati ta girgiza tana cewa.

"Lallai Amira ta sayi damuwa da kud'in ta dan yaya boss ko mutuwa zatai ta dawo tunda yace bai yinta fa'kat karshen magana baya 'karya".

"Kenan da gaske ne da yace yana da wacce yake so"? Elham ta tambaya tana ri'ke baki amsa Afifah ta bata "kai da gaske ne mana Elham mukam ai biki zamu sha koma wacece mu gwangwaje" mi'kewa Fati tai tana cewa "ai ko bari yanzun nan naje na fad'awa Momy dan a bari ya huce yana kawo rabon wani gara taji tunda zafinsa wannan labari ne me dad'i" daidai ta juya zata fita Afifah ta jawota baya tana cewa.

"Da alama ki manta waye Yaya discipline ko gulmar sa zaki kai tab idan rabon shan na jaki ne yake rud'ar ki ga hanya nan Allah ya tsare zan dafa miki ruwan zafin da zaki gasa jikin ki" Afifah na rufe baki da sauri Fati ta zauna kamar an tura ta tana cewa "kan bala'i amma Aunty Afifah na gode kin taimake ni wallahi kin cece ni da naje ina ga yau Yaya boss farfesu na zaiyi a gidan nan".

"Humm lallai yarinya iya farfesu indai ya tsaya iya haka ya miki da 'kauna idan bai saki a inji ya markad'a 'kasusuwan ki ba" dariya Elham tai tana cewa "nikam zaman bedroom d'in nan ya ishe ni bari na koma parlor yasan yanzu baya gidan zamu d'an huta kafin ya dawo" mi'kewa Fati tai tana cewa "nima bari na biyo ki" Afifah data ja bargo ta lullu'be Amira tace.

"To wa zaku bari gadin mai suma wallahi nima gani nan bisa sawun ku muje idan ta farfad'o ta fito" saukowa sukai duk su ukun Afifah tai hanyar library ta dauko littafi ganin momy tana zaune a parlon yasa da saurin su cikin zumud'i suka karaso inda take suna zama kusa da ita TV suka kunna Afifah data fito tana zama a can gefe zatai karatu jin zasu takura mata yasa tace.

"Malamai zaku iya kashe TV nan ko kuma ku sauya ku tafi wani parlon amma baku isa zanyi karatu ku 'kure volume ba" kafin suyi magana suka ji daga bayan su ance "this is not place for reading nan parlor ne gurin hutu zaki iya komawa inda kika fito can ne gurin karatu" d'aga ido Afifah tai ta gano Aliyu tsaye saman balcony yana watso mata kallon gargad'i bata sake magana ba ta aje book d'in alamar ta ha'kura.

"Baza kije ki karatun ba kenan dan nayi magana shine kika aje book d'in saboda ga sa'an wasan ki ko"? Da sauri Afifah ta mi'ke tana d'aukar littafin zat bar gurin dakatar da ita yai "baki iya bada ha'kuri ba kenan ko wato ke jar wuya ce"? Dafe kai tai tana juyowa kamar zatai kuka tace.

"Kayi ha'kuri".

"Repeat".

"Kayi ha'kuri".

"Again".

"Kayi ha'kuri dan Allah Yaya".

"Yaya wa"?.

"Yaya Aliyu".

"Dama haka kike kira na"?.

"Eh yaya kayi ha'kuri".

"Ba discipline Daddy da Momy suka rad'a min ba"?.

"Eh yaya kayi ha'kuri"?.

"Kin iya bada ha'kuri kamar matar aure ta gari 6ace min da gani zan kama kine" wucewa Afifah tai tana d'an yin kasa da murya tace "oh ni naga ta kaina Yaya discipline akwai masifa harda ta saidawa a gurin sa so yake ya d'ora min hawan jini kamar yadda ya dorawa Amira".
ZUCIYAR ALIYU CE

@YMA DUTSE JIGAWA
PAGE 04
Su kam su Elham da suka samu shiga ba'a biyo ta kansu ba yasa suka d'an sake har sun manta da tsayuwar Aliyu ta saman su zasu fara yiwa Momy shagwa'ba kenan suka ji murya ance "can you be quite or not? Which rubbish is this zaku sa min uwa gaba kuna mata ihu dama haka kuke mata saboda kunga bana nan to kusa Allah a ranku yau gani na dawo za kuci ubanku ne" a firgice duk suka kalli kofar palor suga da gaske ne mai wannan maganar ya dawo harda cikin mamaki suka zaro ido kamar yadda nasa suke a zare wanda basuyi zaton gani ba suka ganshi tsaye lokaci guda suka 'kankame Momy suna cewa".

"Innalillahi wayyo Allahn mu wata damuwar is back shikenan d'ayan ma ya dawo yaya Afif" da gudu Afifah ta fito jin abinda suke cewa yayin da su kuma suka mi'ke suma da gudun sukai stairs rikicewa Afifah tai tare da tsayawa ta murtuke ido tana kallon sa tace.

"Afif da gaske dama suke kaine"? Murmushin d'aya bata amsar tambayar ta yayi mata yana kallon Momy da itama murmushin farin cikin ganin sane a fuskarta hannu ya bud'ewa Afifah alamar tazo gare shi wacce da sauri ta buga tsallen murna tana dariya ta rungume shi sosai d'agowa tai har lokacin tana dariyar farin cikin ganinbya dawo tace "gaskiya nayi kewar ka bros d'ina yanzu lokacin mune nima d'an uwa na ya dawo zan sake na wala na sha'ki iska me kyau" ta fad'a tana juyawa ta kallo stairs hango su Elham tai suna faman le'kowa suna kallonsu batasan lokacin da sabuwar dariya ta sake 'kwace mata daidai Aliyu ya sau'ko ya karaso inda suke yana ri'ko hannun Afif cikin so tare da hararar Afifah yana mata nunin zai kamata ne yace.

"Muje ka gaida Momy ke kuma zan ina nan zamu gauraya zan dawo kan kine Afif d'in bazai hana naci ubanki ba" ya fad'a suna wucewa inda Momy take zaune Afifah dake tsaye a gefe jin abinda Aliyu yace yasa tad'an 6ata fuska shiyasa fa tace idan yana gidan nan baya bari su sake gashi yanzu batai masa komai ba yace zasu gauraya aiko bazata yarda su had'u ba balle ya mata wani abu d'agowa tai ta kalle su suna zaune a kusa da Momy suna magana duk su ukun murmushi tai a ranta tace "perfect much gayun gidan sun gama kammala yanzu zaman bedroom ya fara gare min ni zan samu sauki ta bangaren Afif tunda Hassan d'ina ne saidai naji da takurar yaya discipline amma su Fati duk inda sukai ba sauki bari naje naga a wanne halin suke sarakunan matsorata" eucewa tai tana dariyar mugunta a ranta da yadda zata ga su Elham a d'aki tasan suna nan sun zubowa kofa ido kamar zasuyi kuka abinda tai zato ta gani domin tana bud'e kofa duk suka mi'ke a rud'e kowa ta rikice domin Elham kam har taje kofar bathroom ta bud'e zata shiga dariyar da Afifah tai yasa ta juyo taga ba Afif ki Aliyu bane sauke numfashi tai tana dawowa tace.

"Kai dan Allah Aunty Afifah me yasa zaki tsorata mu wallahi na d'auka Yaya Afif ne ya shigo fa yadda yayi mana wannan tsawar da ace ba a lokacin ya dawo ba nasan sai yaci uban mu ba bedroom ba ko ramin gyare zamu shiga sai ya bimu" ta karasa maganar tana zama murmushi Afifah tai tana cewa "ai kuma duk da haka baki sani ba ko idan ya gama gaisawa da Momy nan zai taho tunda kinsan shi Afif kamar kurma yake fad'an sa baya mutuwa balle yaga Kuna neman d'orawa Momy hawan jini".

"Humm insha Allahu babu abinda zai mana bari Daddy ya dawo muje gurin sa kawai a kashe maganar" Fati ta fad'a itama tana baro gaban mirror ta dawo bakin gadon su ta zauna kallonta Afifah tai tana jinjina kai tace "humm Allah yakai damo ga harawa idan baici ba yaci mugun duka wato baiyi miki wani abu ba zaki kai 'kararsa daga dawowarsa yau ko wallahi shawara zan baki ki rufawa kanki asiri kiyi shiru da bakin ki karki fad'awa Daddy".

"To yanzu tsakani da Allah Aunty Afifah me mukai masa dan kawai mun yiwa Momy shagwa'ba har wani abu ne"?.
"Ba wani abu bane a gurin ku amma shi a gurin sa wani abu ne saboda yaga kun girma sannan ko Asma'u bata haka balle ku yan mata ba wacce idan akai aurenta bazata zauna ba" Afifah na rufe baki duk suka zaro ido musamman Elham kamar an tsikareta da sauri ta girgiza kai tana cewa "wayyo please Aunty Afifah dan Allah ki daina fad'a kar d'aya daga cikin basawan nan yaji mun shiga uku kisa ayi auren mu lokacin mu baiyi ba".

"Ba wani lokacin ku baiyi ba wallahi ba wacce idan akai aurenta bazata zauna ba a cikin ku".

"Nidai banda ni" Fati ta fad'a tana sake gyara zamanta ta d'auki littafi ta soma karantawa amsa Afifah ta bata "harda ke man kece ma oganniya wacece a cikin mu take yawan son karanta littafan soyayya idan bake ba kuma anyi maganar aure kince wani banda ke"? Kai Fati ta jinjina tana cewa "kwarai banda ni dan wallahi Aunty Afifah yanzu tsautsayi yasa wani garawayis d'in yace yana sona ko yazo yasa ayi min aure dashi zaiga yadda ake hauka da d'anyan kai bazai iya zaman wata d'aya dani ba saboda damuwar dazan ta d'ura masa".

"Tofa kamar wacce kalar damuwa kenan"? Dariya Fati tai tana cewa "idan yace nayi nace bazan ba idan yace na dafa abinci saiya dawo na d'ebo masa d'anye a plate na kawo masa idan yace ruwa na shiga toilet na d'ebo masa kinga ai ba wanda zai dauki wannan haukan komai son da ya ke min ko"?.

"Tab mai sonki zai d'auka bazai ji haushin kiba duk lokacin da kikai wani abu dan ki 6ata masa rai shi Kuma a wannan lokacin zaiji duk duniya ke kad'ai ce kikai masa babu wacce yake so sai ke ai ance so hana ganin laifi komai zaki masa zai yarda hakan ma wani abu ne na musamma............................

Tarin da Amirah tai shine ya katse maganar da suke yi da sauri suka juya gurin daidai ta tashi zaune tana shirin sauka daga gadon duk kallonta sukai ganin yadda ta mi'ke tana had'a hanya tai toilet can ta fito alamar wanka tai ta wuce gaban mirror zata shirya Afifah ce tace "sannu Amirah" kamar bazata amsa ba saboda takaici sai kuma ta tuna ba itace tai mata haka ba Aliyu ne shiyasa murya a hankali tace "yauwa sannu" daga haka ba wanda ya sake cewa komai harta gama shirinta tasa doguwar rigar atamfa street gown ta d'aura d'an kwalin ta d'auki mayafinta da handbag zata fita tace "Afifah ina wayata"? Kaita girgiza tana cewa "maybe tana dinning ki duba idan kin fita na manta ban taho miki da ita ba" ok kawai shine abinda tace tana bud'e kofa ta fita jikinta gabadaya ba dad'i ya saki haka take jinta kamar mara lafiya irin zazza'bi-zazza6i na shirin kamata saukowa parlon tai a lokacin babu kowa daga Momy harsu Afif d'in wucewa dinning tai ta ganta a inda ta fara cin abinci lokacin da suke magana da Aliyu tuna abinda ya faru d'azu yasa sabon ba'kin ciki da takaici ya sake lullu'be ta da'kyar tad'au wayar tare da jan tsaki ta fita a parlon ba kowa a harabar gidan ma sai iya securities da yake bada mota tazo ba shiyasa kai tsaye ta fita daga gidan hango Aliyu tai sun taho wajen gidan tare da Sameer da alama daga gidan su Sameer d'in suka fito cije lips tayi tana kallonsa har suka karaso inda take.

"Ina zaki je"? Aliyu ya tambaya yana kallonta ganin yadda tai mugun had'e rai fuska ba walwala tace "zan tafi gida ne" kaiya jinjina yana cewa "ok ki gaida Mama amma daga zuwan ki kwana d'aya zaki tafi"?.

"Eh zan dawo akwai abinda na manta shi zan d'auko maybe zuwa magriba na dawo ko zaka kaini dama bada mota nazo ba saidai na tari napep dan Allah ka kaini kaji"? Shiru yai domin shifa bai son yawan wannan abubuwan tunda har yaji ta furta masa kalmar so gara ya ri'ka baya baya da ita saboda kar taga yana sake mata tayi tunanin ko shima yana son nata ne ya sani sun dad'e suna tare sun saba da ita ya d'auke ta tamkar Afifah domin tun bayan kammala secondary d'inta suke tare a school d'aya sukai karatu a India da kuma Spain sun zauna lokaci me tsawo shekaru kusan goma iya sabo dai wanda ya kamata sun yi shi amma bai ta'ba ji a ransa yana sonta da aure ba sannan