Chapter 2 of 45

ZUCIYAR ALIYU CE Zuciyarsa Tata Ce By YUSRAH MUSA

da tasa kudin da Aliyu ya bata domin tasan matu'kar suka gani saita basu wani abu shiyasa take 6oyewa matsowa kusa da ita Bilki ta sake yi tana cewa " "babu komai Hajiya kawai son shi muke dukkan mu" zaro ido tai tana cewa.

"Da gaske kuke yaran nan"?.

"Allah hajiya".

K'asa Hajiya tai da murya sosai gudun kar wani yazo shigowa yaji tace "yauwa 'yan albarka haka nake son ji kwanan nan zan ji'ke da kud'i idan d'ayar ku ta aure shi na tabbata yaron nan zai jiyar dani dad'i ku dage yasan daku yasan kuna son sa idan bai so wata ba zai so wata tunda naga yana da mutunci d'an arziki ne ya gaji halin mahaifin sa" ta 'karasa maganar tana d'auko kud'in daya bata ta nuna musu tana cewa.

"Kun ga yanzu nan Samar ya kawo min shi kalli alherin daya min idan kuma akace yayi aure a gidan nan kullum jalaf d'in taliya da kifi ga zobo mai sanyi nasan shine abinci na dare da rana dan Allah yaran nan kada kumin bakin ciki kun ji"? Kallon juna sukai suna sha'kewa da dariya suka ce "sai hajiyan mu muna yinki za'ai yadda kike so" washe baki tai yauwa ko kufa haka nake son ji".

Cikin wayo Bilki tace "amma hajiya kinsan bazai so mu a haka ba dole sai muna kyawawan shiga irin ta 'ya'yan masu kud'i muna kwalliya kuma ga shi bamu da kud'i yanzu ni saurayi na yayi tafiya" dariya Rasheedat tai tana cewa "nima nawa garan yayi tafiya shekaran jiya kuma banda ko sisi hajiya a cikin kud'in daya baki zaki bamu ko dubu biyar ce muje mu fara rage wasu abubuwan tunda kema kina son shiga cikin tafiyar" zaro ido hajiya tai tana mayar da kud'in ta cikin inda ta d'auko shi tace "caf dubu me zan baku dubu biyar naji kunce lallai yaran nan baku da hankali ko biyar bazan bayar ba balle dubu biyar kuje gurin iyayen ku su baku man dama dan ina so kuma nice zanyi muku jagorancin komai kenan"?.

Hada ido sukai suna 'kiftawa Rasheedat tace "shikenan hajiya zamu nema amma ki sani idan yazo yace yana son mu ya aure mu kada muga yar 'kafar ki a gidan idan ma kinje zamu sa securities suyo waje dake mu nuna bamu sanki ba daga mu sai iyayen na mu tunda haka ne" shiru hajiya tai jikin ta yayi sanyi ganin batai magana ba Bilki tace "kefa Rasheedat ki rabu da ita da alama bata bu'kata dubu goman daya bata zata isheta rayuwa tashi mu je" ganin da Hajiya tai suna kokarin tashi da sauri tace "a'a ku tsaya badai dubu biyar bane gashi" ta fad'a tana d'auko kud'in ta basu badan ranta yaso ba tace "saidai na baku Kowaccen ku dubu biyu nima fa dubu goma ne kawai" kar'ba sukai suna mi'kewa Rasheedat tace "karki damu Hajiya dubu bibiyun ma tayi mana raba arne da makami ibada ce" a hasale Hajiya tace "kuma dan ubanki nice arniyar saboda ke ba 'yar mutunci bace"? Ta'be baki Rasheedat tana kallon ta da gefen ido tace "sai an kula kucaka take yanga ke kike yi mukam munyi nan" ta fad'a suna fita da ashar Hajiya ta raka su tana mi'kewa ta biyo bayansu tana cewa "ubanku ya make uwarku kuzo ku bani kud'i na shegu 'yan iskan yara matsiyata" cin karo da Haulat tai zata shiga gurin nata ganin su Rasheedat sun fita ga Hajiya na rako su da zagi tace.

"Hajiya lafiya ke da waye"? Tsaki Hajiya tai tana cewa "ni da waye kuwa banda fitinannun shegun yaran nan Rasheeda da Balki" cikin gulma Haulat tace "tofa sun zo sun yi miki ha'incin nasu da suka saba ko muje ciki Hajiya rabu dasu dan Allah kinga kifi ne na kawo miki ko Umman mu bai baiwa irinsa ba saboda ina sonki jiya saurayi na ya kawo min da dare shine naci na rage miki" cike da zilama Hajiya tace.

"Ina kifin yake bani shi nan 'yar nan irin ku ake so" murmushi Haulat tai tana jinjina kai tace "to mu koma ciki Hajiya akwai maganar da nake so muyi dake akan Aliyu" juyawa Hajiya tai tana dogarawa akan sandan tace "to kema dai akan Aliyun zaki min magana badai sonsa kike ba"?.

"Eh sonsa nake man akwai wanda ya riga ni ne a cikin 'yan matan gidan nan"?.

"Eh mana wadancan tantiran ma duk sonsa suke yanzu suka gama min lissafin zasu je su sayo kayan kwalliya da kayan sawa saida sukai min wayo d'an kud'in da Aliyun ya shigo ya bani dubu goma sun kar'be dubu hud'u" cikin zuga Haulat tace "kai ji mugaye 6arayi kuma kin basu"? Cikin takaici Hajiya tace "bayarwa na nawa saidai kar a 'kara a gaba na basu man" kai Haulat ta jinjina tana zama ta mi'kawa Hajiya ledar kifin tare da zuba mata ido saida taga ta fara ci tace.

"Hajiya kinsan me nake tunani akan Aliyu"? Kai Hajiya ta girgiza tana cin kifi ko bakin magana bata samu ba murmushi Haulat tai tana cigaba tace "nima ina son Aliyu sosai kuma shima yana sona kullum muna waya dashi ban fad'a a gidan nan bane saboda kinsan akwai 'yan bakin ciki gashi yace aure na zaiyi Hajiya ki taya ni da addu'a idan nasamu ya aure ni kema kin warke domin bazan bari kici gaba da zama anan ba zan d'auke ki ki koma gurina muyi kyakkyawar rayuwa mai dad'i a gidansa komai kina zaune za'a akawo miki kici kisha kyauta ki kwanta a gado na alfarma Hajiya ke bakya son irin wannan daular ne"? Kai Hajiya ta d'aga tana cewa "ina so man wa ya'ki dad'i ne".

"Tom kin gani Hajiya abinda nake son nuna miki kenan kuma ya fad'a min nan ba da dad'ewa ba mahaifan sa zasu yi magana amma yace bazai amince ya aure ni ba saina zama 'yar gayu irin sa".

"Ban gane me kike nufi ba gayu kamar ya"? Cikin wayo Haulat tace "yace na samu kud'i na na sayo mayukan bleaching wanda zanyi fari sol kamarsa sannan na sayo kayan sakawa masu tsada na ri'ka cin kwalliya yadda baza'a kushe niba kuma iyayen sa zasu amince ya aure ni idan ya kaini gidan kinga Hajiya bai kamata nayi sake ba saboda nasan ko nawa zan kashe dana aure shi shikenan zan mayar da kud'i na harda riba zan samu" kai Hajiya ta d'aga tana cewa "tabbas haka yake to yanxu ya za'ai a ina xaki samu kud'in domin nima ina so naga d'aya daga cikin ku ta aure shi".

"Abinda za'ai kawai yanzu wannan sauran dubu shidan zaki bani naje na sayo kayan kwalliya zan tambayi abban mu idan ya dawo ya bani kud'i na sayo atamfofi nakai shago ayi min manyan d'inkuna na alfarma watakil yadda nake da kyawun nan da yaga na koma haka kwanan nan ya aure ni na d'auke ki kikoma gurina da zama sai abinda kike so zaki ci" Haulat na rufe baki Hajiya ta saki dariyar farin ciki tana zura hannunta cikin fulon ta d'auko sauran dubu shidan ta mi'ka mata tana cewa "gashi nan kiyi sauri ki tashi kije kawai ki sayo komai gara kiyi auren nan mu bar gidan dama ba wanda yake so na sai ke duk 'yan 'kwal ubane babu tsiyar da suke bani tashi maza ki tafi shagon sannan wadannan 'yan iskan yaran kici ubansu idan kin had'u dasu kice su dawo min da dubu hud'u na" mi'kewa Haulat tai kamar zatai dariya ta danne da'kyar tana rufe baki saboda kar dariyar ta fito fili tace "to shikenan Hajiya karki damu zanyi miki maganin shegu dani suke zancen zasu san sun ta'bo min ke ki rabu dasu ina daidai dasu zan kar'bo miki kud'in ki bari naje na dawo" haka Haulat ta fita tabar Hajiya sai sambatun murna take tana hasko yadda zata ri'ka yiwa komai cin hauka tasan zata kwashi dad'i indai akai dace Haulat ta auri Aliyu tunda taga tana bata komai idan ta samo.

Fitar su Balki daga gurin dariya suna dariya Rasheedat tace "wallahi dama yau haka na tashi ko sisi banda shi amma yanzu ga dubu biyu ziyau ta shigo mana ba aiki fari balle na ba'ki haka ake so muje muyi wanka muzo muci uwar dubu hudun nan kafin sauran 'yan matan gidan su dawo su saka mana ido" wucewa sukai kowa ta shiga 6angaren su.

Daga gurin Hajiya dasu Sameer suka fito waje sukai ganin da Aliyu yayi Sameer bai nuna masa abinda ya tambaye shi ba yasa kalle shi yana cewa "kai Sameer wannan wanne irin wulakanci ne ka nuna min"? Kamar baisan akan me yake magana ba yace "da nayi maka me"?.

"Da kai min ban sani ba cewa fa nayi muje ka nuna min ajiyar dana baka amma har muka fito banji kace komai ba"? Murmushi Sameer yai yana cewa "oh sorry buddy kayi ha'kuri zan nuna maka ba yau ba" wani kallo Aliyu yai masa yana cewa.

"Ba yau ba sai yaushe"? Cikin tsokana Sameer yace "tommorow morning"? Jin abinda yace yasa ya had'ee rai yana cewa "tommorow morning kuma"? Shiru Samir yai bai bashi amsa ba kallon sa Aliyu yai ganin dariya yake masa yasa yadan daki kafad'arsa yana cewa "you're not so kind mutumi na kana bani ciwon kai wallahi meyasa kake min haka ne"?.

"Babu komai Marshall insha Allah gobe da safe zan baka magani zaka warke daga ciwon kan daya same ka".
"Meyasa baza ka nuna min yanzu ba sai gobe bayan kasan irin damuwar da nayi da abun"?.

"Nasan ka damu gaskiya ne amma maganar Allah zan fad'a maka ajiyarka bata nan ta tafi D'an Yana tana gidan su mahaifiyar ta Amma jiya munyi waya da ita tace min nan da kwana biyu maybe zata dawo" numfashi Aliyu ya sauke jin abinda yace ya jinjina kai yana cewa "ok shikenan muje" wucewa sukai zuwa babbar rumfar kofar gidan su Aliyun domin su samu zama ayi hirar yaushe gamo da aka dad'e ba'ai ba.

Ameerah na jin labarin cewa Aliyu ya dawo ta ciko trolley da kaya ta taho gidan cikin farin ciki da nuna za'kuwa ga soyayyar da take masa 'karara baya boyewa wace Amira? 'ya ce a gurin professor Bashir da hajiya Adama ala'kar abota ce tsakanin Daddy da mahaifinta kuma Abban Aliyu akwai shakuwa mai karfi yarda da amince wanda suka zama tamkar 'yan uwan jini wannan dalili yasa Amira ta taso da ciwon son Aliyu a zuciyar ta hakan yasa kullum tana zarya a gidan tun tana karama take burin aikin soja saboda Aliyu saidai dole ta hakura da aikin sakamakon cutar asma da take damunta bazata iya aikin ba saita sauya karatun zuwa bangare irin na babanta tayi zama da Aliyu a kasashe daban daban shine yake kula da karatun ta saida bayan ta kammala ya dawo da ita gida cikin aminci kamar yadda aka bashi amanar ta tun bayan rabuwar su basu sake haduwa ba shekara uku da rabi sai yanzu 'kawarta khulsum dake aiki a airport tai kiranta a waya ta sanar mata cewa taga Aliyu ya dawo shiyasa ta tattaro kayanta kamar yadda ta saba ta taho gidan wannan shine ala'kar ta dashi.

Afifah tana zaune a bedroom taga an bud'o kofa zubawa kofar ido tai cike da fargaba farko ta d'auka Aliyu ne sai kuma taga Amira ta shigo bakinta ko rufuwa bayayi tsabar farin ciki jikin ta na mazari ga trolley sha'ke da kaya da mamaki Afifah tace "Amira yaushe rabon da na ganki kusan shekara uku fa tun lokacin da yaya discipline ya dawo dake gida sai yau anya kece kuwa nake gani ko mai sifar kice"? Murmushin Amira tana karsowa tace "yau kuma sai gani bayan wadannan shekarun naji labarin Aliyu ya dawo shiyasa kika gan ni yanzun ma nazo" kai Afifah ta jinjina dama tasan sai hakan saidai idan labari ne yakai mata anga dawowar Aliyun to wanne munafikin ne? Numfashi ta sauke tana 'kara 'karewa Amira kallo tace.

"Waye ya fad'a miki"?.
Zama Amira tai tana zuge zip din jakarta ta dauko phone d'inta zata kira Aliyu tace "ina da 'kawa a airport d'in daya sauka sunanta Ummu-Khulsum itace taga saukarsa shine ta kira ni tayi min albishiri a take data kira ni ta fad'a min nayi mata kyautar dubu hamsim sannan nayi wanka ko Daddy ban fad'awa ba na taho tsabar zumud'i sai daga baya zan kirashi na fad'a masa dukda nasan Aliyun zai je gidan ya gaisar dashi".

Murmushi Afifah tai tana cewa "gaskiya ne yayi fa to sannu da zuwa kun had'u da Yaya discipline d'in kenan"? Kaita girgiza batare data d'ago daga kallon wayar tata ba tace "a'a ban ganshi ba maybe ya tafi wani guri bari na kira shi domin na matsu mu had'u" cikin tsokana Afifah tace "gaskiya ne ya kamata ku gaisa musamman yadda kuka dad'e kuna tare sannan tare kukai karatu tsawon shekaru sha'kuwa iya sha'kuwa dole ki matsu ku had'u amma yaushe zamu sha bikin ki ne"? Murmushin Amira tai har lokacin bata d'ago ba tace "taya zaku sha biki bayan baku shirya ba" da mamaki Afifah tace.

"Ban gane ba kamar ya bamu shirya ba meye namu a ciki bayan anko ko a dangin mu angon yake"? Ta tambaye ta tana kallon ta rolling eyeballs dinta Amira tai tana kad'a kai tace "to da ina kike kaini a dangin ku yake man" da sabon mamaki Afifah tace "waye kenan"?.

"A'a bazan fad'a ba zaki sani ba yanzu ba sai nan gaba fatana zaki taimake ni wajen cika buri na"? Nuna kanta Afifah tai tana cewa "ni kuma na taimake kifa kika ce"?.
"Kwarai ki taimake ni man ko bazaki taimaka min d'in ba"?.

"a'a mezai hana dan taimako kawai ba wani abu ba babu abinda zai gagara karki damu" cikin jin dad'i Amira tace "yauwa Afifah na gode har kinsa naji kamar komai ya faru ya 'kare please dan Allah Afifah kisa a kawo min abin sha mai sanyi man yanzu kinji"? Mi'kewa Afifah tai daidai zata fita tace "ok zansa a kawo miki" fita tai tabar Amira wacce ta kwanta tana kallon secreen din wayarta ganin kiran na shiga amma ba'ai picking ba karshe idan ta tura kira ma sai ai reject aje wayar tai tana jan tsaki wato Aliyu har yanzu yana nan kamar da bai canza ba lallai da 'kura a gabanta da alama zata sha fama dashi kafin ta shawo kansa.........

💓ZUCIYAR ALIYU CE💓

@YUSRAH MUSA
PAGE 03
Har dare sosai Amira batai barci ba tana jiran dawowar sa bai shigo ba harta gaji ta tafi ta kwanta ko barci arziki bataiba tsanar damuwa washe gari da wuri tai wanka bayan tayi sallar asuba taci ado sosai tasa lace mai tsada ta kashe d'auri ita da kanta ta tsaya a gaban mirror tana kallon kanta ganin wani irin kyau datai tasan matu'kar sukai four eyes da Aliyu tofa bazai san lokacin dazai bita da kallo ba domin ta fahimci dole saida siyasa zata samu zuciyarsa da'kyar ta bari gari yai haske lokacin masu aiki sun gama aikin kayan breakfast har wasu sun karya amma banda ita saboda bata fita da wuri ba sai data daidaici kamar zata sameshi a parlon sannan ta fito.
Tana zaune Afifah ta fito itama saboda tana part d'in Momy ganinta a zaune ita kad'ai ga yanayi mara kyau a fuskarta yasa ta karaso tana zama itama tace "yadai Amira ya haka"? D'agowa Amira tai cikin damuwa da rashin walwala tace.

"Ya me"? Kallon ta sosai Afifah keyi tana nazarin ta da abinda yake damunta kafin tace "naga kinyi tagumi kuma da alama kamar baki breakfast ba meyasa baki ba ko akwai matsala ne"? Kai Amira ta jinjina tana sau'ke hannunta daga tagumin datai tana fitar da huci ranta a 6ace tace "eh Afifah banyi breakfast ba taya zan iya cin abinci a wannan yanayin bayan na shiga matsala".

"Matsalar me wani abu ne ya faru"?.
"Meye ma bai faru ba Afifah ni Aliyu zai wula'kanta har kamar ni na masa kira yakai ashirin daga jiya zuwa yau amma bai picking ko d'aya ba karshe har rejecting yake min ne yake nufi da hakan yaushe ya canza ki fad'a min Afifah lallai kuwa Aliyu ya d'auko damin da bazai sauke ba ya d'auko ya'ki zaisan yayi dani saina nuna masa fushi na Allah ya fito dashi lafiya ina nan ina jiransa nan da gobe wallahi sai nayi masa mugun rashin mutunci".

Wani kallo Afifah tai mata jin abinda tace ta jinjina kai tana cewa "tabd'ijan babbar magana Amira shawarar dazan baki karki soma Yaya discipline ya canza ba wanda kika sani da bane shawara ce nake baki ki fita hanyarsa" a masife Amira tace "wallahi bazan rabu dashi ba Afifah saina idar masa da 6acin ran daya d'ora min" gyara zama Afifah tai tana cewa "to shikenan Allah ya taimaka nidai gaskiya ce kuma na fad'a miki amma naga da alama kafin ki tafi gidan ku so kike ya 6alla ki dan Yaya discipline ba irin wanda kika d'auka bane baya son raini ba'ai masa wargi humm Yaya discipline sha'anin sa sai sh...........

Shiru Afifah tai tana rufe baki ganin Aliyu ya sauko daga stairs kuma ya kalleta yasa tad'an kau da kai kamar bata ga irin kallon daya aiko mata ba wucewa yai yana zama a dinning ya d'auki karamin kofi zai hada tea mi'kewa Afifah tai tana karasawa inda yake batare daya dago ba yace.
"Meya faru kina neman wani abu ne"? Jada baya Afifah tai tana cewa "a'a Yaya dama kai zanyi serving".

"I don't want bar nan kafin ke na 'balla miki 'kafar da kike magana akai" juyawa Afifah tai da sauri tabar gurin ta koma parlor tana zama a inda ta tashi d'aram Amira ta mike tana zuwa inda yake cikin shiahshigi tad'au plate tai serving d'insa Irish wanda yaji 'kwai tana direwa a gaban sa ta kama kujera ta zauna itama tana serving kanta tunda dama damuwa bata barta ta samu damar karyawar ba sai yanzu data ganshi ganin abinda take yasa fuska ba wargi yace.

"Ke meye haka"? Bata bashi amsa ba saida takai loma bakinta sannan ta dago tana kallonsa cikin yanga ta sauya murya tace