Chapter 6 of 45
ZUCIYAR ALIYU CE Zuciyarsa Tata Ce By YUSRAH MUSA
"A'a".
"Amma kikace bakya bu'katar komai please ki fad'a min abinda kike so na kawo miki bana so ki kwana da yunwa kinji"?.
"To Yaya Sameer kawo min gurasa mai 'kuli kad'ai ta isa".
"Ita kike so"?.
"Eh itan ma tayi".
"Ok bani mintuna ina zuwa" ya fad'a yana fita d'akin Umma ta koma ta d'auko handbag d'inta ta koma nata d'akin ta bud'e wayarta ta fara dubawa kafin ya dawo.
Fitar Sameer kam kai tsaye wajen wani mutum me soya doya da naman kaji a anguwarsu ya nufa ya siyo mata abar da tace tana so ya kawo mata godiya sosai tai masa harya juya zai fita tace "Yaya Sameer dan Allah kar'bi wannan ka siyo min klin da 'yan abubuwa a shago da safe zan kaiwa Hajiya kasan indai taga na dawo ban bata abun sannu da zuwa ba saita fad'a ni kuma ba tafiyar shiri nayi ba" murmushi yayi yana cewa "a'a barshi karki damu idan na tashi shigowa gida zan taho miki dashi saiki bata".
"To na gode Allah ya 'kara arziki" Amin yace yana fita itama ta tashi ta fita d'akin Umma ta shiga ta d'iba mata sannan ta koma taci iya wacce zata iya ci ta sake fitowa ta wanke hannunta ta komai fitilar wayarta ta kunna ta d'orata akan keken d'inkinta ta d'auko tsintsiya tai bismilllah ta share d'akin ta gyara katifarta ta fesa turare ta shimfid'a bedsheet tare da d'aukar wayar ta kashe fitilar ta kwanta.
ZUCIYAR ALIYU CE
@YUSRAH MUSA
PAGE 11
Kusan sha biyu da rabi babansu ya dawo daga gurin sana'ar sa dama already kullum saiya shiga gurin Hajiya sannan zai karasa kofarsa shiyasa yauma dukda dare yayi da harzai wuce sai kuma ya tuna indai baije ba gobe saita masa tas da safe shiga yayi ya tarar batai barci ba suna zaune tare da Haulat da su Balki kusan 'yan mata shida sun aje babbar waya suna kallo da sallama ya shiga ya gaisar da Hajiya ya aje mata tsaraba kamar yadda ya saba kullum yad'an siyo mata abun motsa baki ya mi'ke zai tafi tace.
"Abdullahi tsaya zamuyi magana dakai akan wancan yarinyar taka" jin abinda tace yasa saida gabansa ya fad'i tunda yaji tace haka yasan Zainab take nufi ya rasa me tai mata da jinin su baizo d'aya ba yarinya me cikakken hankali da nutsuwa wacce magana bata dameta ba amma Hajiya gabadaya tabi ta addabi rayuwarta ba dalili...........................
"Abdullahi ka kira Zainaba ka fad'a mata sa'ko lallai in jini ta dawo gida gobe wallahi tallahi na rantse da Allah idan bata dawo a gobe ba saika saki uwarta tabi bayanta ka gane kuma ka jini"? Shiru yai ransa babu dad'i bai iya ce mata komai ba cikin fad'a Hajiya taci gaba "nayi magana kayi banza dani saboda ka zauna da marar tarbiyya ta koya maka tsiya da yadda ake wula'kanta uwa shine zaka nuna min"? Kaiya girgiza a damuwance yace "dan Allah kiyi hakuri Hajiya idan na shiga yanxu zansa ta kirata zata dawo goben" gyara zama Hajiya tai tana mayar da hankalinta kan kallon da suke yi tace "wannan kuma ya rage ruwanka tsabar shashanci na rasa wanne irin so kake musu da baka ganin aibun su kodai asiri sukai maka nasan wannan son da kake musu ba banza ba idan bakai a hankali ba wata rana za'ai bakai dan tuntuni na fahimta wannan talaucin da kake fama dashi sune sila basu da 'kashin arziki kaga fa duk sauran 'yan uwanka kowa aikin gwamnati yake yi kuma kaima kayi karatun nan amma auren dangin tsiya da ba'kin jini ya jawo maka ka 'kare a gaban bencin kayan miya ana mi'ko maka d'ari uku d'ari biyar ka na zubawa a leda kana mi'kawa" sosai ransa ya 6aci ganin yadda Hajiya take masa a gaban 'ya'yansa da 'ya'yan 'yan uwansa bai kamata ba.....................
"Tashi ka bani guri kuma ka tabbata sa'ko na yaje gurin wannan uwar gulmar" yaji muryarta ta katse masa tunani mi'kewa yayi yana d'aukar kayan daya shigo dashi a hannunsa yace "saida safe Hajiya" kamar zatace masa kowa ya kwana lafiya shi yaso sai kuma a she'ke tace "toh" fita yayi ya wuce tasa kofar kai tsaye d'akin Umma ya shiga bai shiga d'akinsa ba saboda ranar a d'akinta yake har lokacin tana zaune a yadda take tayi tagumi hatta gurasar da Zainab ta kawo mata bata ko kalli yadda take ba balle ta samu damar ci sallamar dayai ce tasa ta d'ago tana d'an sakin fuskarta saboda karya fahimci halin da take ciki tace.
"Sannun da dawowa" zama yai yana sauke numfashi ransa na sake 6aci ganin yadda ta jefasu cikin damuwa yace "kinyi magana da Zainab ne yau"? Kaita d'aga tana kallon sa tunda taji ya tambaya tasan daga kofar Hajiya yake shima yaje ta tsiyata shi kenan............................
"Tunda kinyi magana da ita gobe da sassafe idan kinyi sallar asuba ki kirata kice ta taho a goben karta 'kara kwana saboda Hajiya ta fad'a min wata magana da banji dad'in ta ba kuma tayi rantsuwa akai cewa indai bata dawo a gobe ba kema sai kin bita" yana rufe baki Umma tai murmushin da yafi kuka ciwo tana cewa "Zainab ta dawo tana d'akinta tun d'azu ta shigo".
"Au ta dawo"?.
"Eh ta dawo tana nan".
Jin haka yasa ya mi'ke yana fita 'kofar d'akin Zainab yaje yana cewa "Zainab Zainab" daga d'aki tace "na'am Abba" tashi daga kwancen da take tayi tana zuwa bakin kofar ta bud'e tare da fitowa ta dur'kusa a gabansa tana cewa "ina yini ya aiki fatan ka dawo lafiya"?.
"Lafiya kalau Zainab fatan kema kin dawo lafiya ya kika baro su Umman da wajen Alhaji Balaraben duk suna lafiya"? Kaita d'aga tana cewa "eh lafiyarsu kalau".
"Masha Allah dama gaisawa kawai zamuyi naga lafiyarki tashi ki koma ki kwanta saida safe" mi'kewa tai tana cewa "Allah ya tashe mu lafiya Abba" Amin yace yana yin wajen kofar d'akinsa ita kuma ta koma d'aki ta kwanta kamar yadda take d'azu.
✍️YUSRAH MUSA ABUBAKAR
💓ZUCIYAR ALIYU CE💓
@YMA DUTSE
PAGE 12
Washe gari da asuba bayan Abba ya dawo daga masallaci sanin da yayi Zainab ta riga ta dawo shiyasa ya shiga 6angaren Hajiya zai gaida ita cikin 'kwarin gwiwa ba fargabar fad'an Hajiyan za tai masa daidai ya zauna sun gaisa tun bai sauke numfashi ba ya ji tace "Ina sa'kona Abdullahi" da 'yar alamar tambaya yace "wanne sa'ko ne Hajiya"?.
"Au harka manta saboda an shanye ka baka damu da umarni na ba"? Cikin ladabi ya sake du'kawa yana cewa "kiyi hakuri Hajiya sa'kon ne na manta" cikin fad'a tace "ai gara daka manta amma bazaka manta ba daga lokacin dana mi'ko maka biro da takarda nace ka saki wancan matar taka zaka tuna ko"? Jin abinda tace yasa ya sauke ajiyar zuciya yana cewa "kiyi hakuri Hajiya sha'afa nayi Zainab ta dawo tun jiyan anan ta kwana".
"Au ta dawo tun jiyan shine saboda rashin arziki data gada a gurin uwarta shine bata zo ta gaida dani ba har yau zata shigo tazo ta sameni sai naci mutuncin ta"?.
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri bansan bata zo ta gaida ke ba amma zan mata fad'a karta 'kara" tsaki Hajiya tai tana cewa "tama 'kara d'in man ni dama da ita da babu duk uwarsu d'aya yarinya ta'ki aure kun zuba mata ido babu ruwanku ko saita zama tsohuwa a gida ne ko kuma auren ne baza tai ba ko wanda zata aura ne bata dashi fad'a min naji"?.
"A'a tana dashi amma ban sani ba ko basa tare yanzu".
"Waye shi d'an waye a ina yake"?.
"Ina jin kamar dai anan anguwar yake saidai bansan ta wajen wanne 6angaren ba abinda na sani kawai dai tace min malami ne a islamiyyar su".
"Hum yayi kyau Allah ya kawota gurina zata sani ne sai naci mutuncin ta wanda ranta zai 6aci tayi zuciya ta fito da mijin aure inace ga Rafi'atu nan da Ralmat duk sa'annin tane kowacce tayi aure harda yara suke dashi amma ita ta tsaya ruwan ido indai tai za6en tumun dare wallahi a kanka masifa take bani ba kune zaku ri'ka sha'kar ba'kin ciki kuna mata aiken abinci daga Nan kunga babu amfani kenan kun siyar da akuya tazo tana gogar muku katanga" sosai ran Abba ya 6aci baya jin dad'i duk lokacin da Hajiya ta fad'i wani abu akan Zainab saboda shi yasan wace 'yarsa yasan irin hankali da nutsuwarta ya tabbata jinkirin aurenta alkhairi ne saboda kullum yana Mata addu'ar ta samu miji na gari yasan hakan ne yasa lokaci yake 'kara ja addu'ar sa ta kar'bu insha Allah Zainab zatai aure zata bar gidan nan duk daren dad'ewa............
"Na gama magana dakai tashi ka bani gu" yaji muryar Hajiya ta katse masa tunani kaiya girgiza yana mi'kewa zai fita ya aje mata d'ari biyar wanda tun bai gama kai ga ajewar ba tace "me zan gani wacce lalacewar ce wannan"? Ta fad'a tana d'ago da d'ari biyar d'in alamar batai mata ba shiru yayi ya rasa me zaice mata "dakai fa nake ka rasa me zaka bani sai d'ari biyar wadanda ban haifa bama suna min babbar kyauta har dubu goma Allah yayiwa yaron nan Aliyu d'an gidan Alhaji Amadu albarka ranar Samar ya kawo shi dubu goma 'kal-'kal suna walwali a mi'ke ya d'auka ya bani balle kai anya kuwa lafiyarka kalau"?.
"Lafiya kalau nake Hajiya kud'in ne na siyo abun karyawa jiya da dare kuma yanzu zanje na bada kud'in abincin rana dana dare shiyasa kud'in suka 'kare babu wani a gurina iya d'ari biyar d'ince tai saura da nayi lissafi saboda jiya na bayar da kud'in sarin kayan miya bani da komai".
"Fatara a kanka ta 'kare ne kullum da anyi magana sai kace baka da kud'i wannna kiran babun da kake shiyasa baka gaba abun ma ya shafi 'yarka ta'ki auruwa kowa zai wuce yana kallonka a gaban bencin tumatur kana cinikin naira dari biyu d'ari uku ba albashi kake d'auka ba waye dama zaizo yace yana sonta yasan ko kayan d'akin arziki ba samu zaiyi ba balle kayan gara" rufe ido Abba yayi yana girgiza kai zuciyarsa gaba d'aya ta 6aci da sauri ya fita daga gurin Hajiyan ko sallama baiyi mata ba yasan idan da rikicin tsufa a wadannan maganganun nata tofa akwai 'kiyayya ma yana so yasan meyasa bata son Zainab amma har yau ya kasa ya ganewa shi dai yana son kayarsa domin koda duniya ne suka taru suke 'kin Zainab shi kad'ai zai so abarsa domin cikin 'ya'yansa babu wanda ya shiga ransa kamar Zainab saboda ladabi da biyayyarta ga tarbiyya.
Zainab tana d'akin ta bayan datai sallah bata fito ba saida gari yayi haske sannan ta fito ta shiga gurin Umma ta gaida ita saboda gudun laifi yasa tace mata ta tashi taje ta gaisar da Hajiya amma sakamakon ba tafiyar shiri tai ba bata siyo tsarabar komai ba yasa bata jeba ta bari Sameer ya shigo ta tambaye shi idan ya siyo mata idan kuma ya manta saita fita ta siyo da kanta domin da taje gurin Hajiya ba tsaraba gara ta ha'kura da xuwa gaida ita.
Shi kam Sameer bai shigo gidan ba har wajen sha biyu sannan yazo mata da takarda a lokacin tana gurin wanke-wanke tana taya Umma ayyuka ya shigo tsayawa yayi daga wajen kofar shigowa yana cewa "Zainab zo nan" kallon inda yai maganar tai tana mi'kewa da fara'ar ta tace "Yaya Sameer ina kwana''? Kaiya d'aga yana cewa "lafiya na tashi akwai biro a gurin ki ne"?.
"Eh da akwai baka zanyi"? Zama yai a kan wata farar kujerar roba dake kofar d'akin Zainab din yana cewa "uhm kawo min abu zanyi dashi" shiga tayi tana cewa "to bari na duba maka jakar islamiyya ta" yana zaune ta d'auko masa ta bashi zata koma gurin aikin yace "a'a Zainab dawo nan zo ki cike" jin abinda yace yasa da mamaki ta juyo tana kallon sa tare da nuna kanta tace "nice zan cike"?.
"Eh kar6i" ya fad'a yana mi'ka mata 'kure takardar tai da kallo tana cewa "amma Yaya Sameer takardar ta mene zan cike"? Murmushi yai shima yana kallon takardar yace "form ne na makaranta" da sabon mamaki tace "form na makaranta kuma waye ya sai mun makaranta Yaya Sameer"?.
"Ba ruwanki kawai kizo ki cike min" dawowa tai tana kar'ba tare da zama akan wata 'yar 'karamar kujera ta aikin gida ta fara cikewa fitowar Asabe kenan daga d'aki ta tashi daga barcin hutu ganinsa zaune ga Zainab na cike paper yasa ta aje butar data d'auka tana cewa "Sameer me kake anan"? D'agowa yayi yana kallon ta yace "ina kwana Umma"?.
"Lafiya nace me kake anan"?.
"Takarda ce na kawowa Zainab ta cike".
"Takarda ta meye ko aikin polio ka samo mata"?.
"A'a ba polio bane".
"To takardar ta meye"?.
"Form ne na makaranta" zaro ido Asabe tai tana cewa "form na makaranta karatu zata d'ora"? Amsa ya bata da "eh" daidai Zainab ta mi'ko masa takardar tana cewa "gashi Yaya Sameer na gode" ta fad'a tana mi'kewa ta koma gurin aikinta da kallo Asabe ta bita cikin takaici kafin ta dawo da hankalinta kan Sameer da shima ya mi'ke yana shirin fita tace "kenan kaine ka biya mata taci gaba da karatun"?.
"A'a bani bane ni ina naga kud'in dazan biya mata tai karatun jami'a"? jin abinda yace ta sake jefa masa tambaya "ban gane bakai bane to waye ya biya mata"?.
"Wani ne".
"Wani kuma Sameer karka raina min hankali fa bana son munafirci uban wa take dashi wanda zai biya mata kud'i tayi karatu a wannan tsadar rayuwar"? Shiru Sameer yai bai sake magana ba taya zai fad'a mata cewa Aliyu ne ya siyawa Zainab makaranta bayan ita kanta Zainab d'in batasan yana sonta ba kawai zaman lafiya ya samu ya fita karma Asabe ta 'kureshi da tambayoyin har yayi 6arin zance juyawa yai zai fita ta ri'ko rigarsa tana cewa.
"Sameer ka fad'a min gaskiya kona tsine maka waye ya siya mata makaranta kaine"? Kaiya girgiza yana cewa "wallahi Umma bani bane wani ne" a masife tace "to waye wanin inda kana da gaskiya ka fad'a min wanda ya siya mata munafirta ta kake Sameer wato kafi d'aukar Zainab wacce kuke uba d'aya da muhimmanci akan Bilki da kuke uwa d'aya uba d'aya ko".
"Ba haka bane Umma dan Allah ki fahimta wallahi bani na siya mata ba nima d'an sa'ko ne" kallo inda Zainab take zaune Asabe tai tana ta'be baki tace "a iya sanina tunda Zainab ta taso ban ta'ba jin ance ga wani fitaaccen saurayi yazo gurin taba sai wannan fatararran malamin islamiyyar tasu waye sunan nasa"? Murmushin daba shiri Sameer yayi yana d'an girgiza kai yace "a'a bashi bane bansan ma wani Yaa sayyadi yana sonta ba sai yanzu naji a gurinki" yana fad'in haka ya juya ya fita cizon yatsa Asabe tai tana komawa ta d'auki butar da zata shiga band'aki tana cewa "humm zanga wannan munafikin ne ya siya miki makarantar idan tai tsami zamuji basai mun tambaya ba munafikai kawai daga ke har Sameer d'in zai dawo ya same ni ne shashashan yaro" shiru Zainab tai ko tari duk da taji zafin maganar da Asaben ta fad'a saidai ya zatai tunda uwace a gurinta bata da bakin da zata bud'e ta rama damuwarta Allah ya had'ata da alkhairinsa........................
Kwacaff taji 'kara a kusa da ita da sauri ta d'ago a tsorace tana kallon Asabe wacce ke tsaye a kanta tana sake turo mata kwanukan data d'ebo daga d'aki tace "yar aiki ki had'a da nawa kwanukan ki wanke dama hakan ne ya dace dake tunda kin 'ki aure saiki zama baiwar mu ashe ware nawa kwanukan kike saboda baki gaji arziki ba kodan ni ban haife kiba shiyasa kika ware nawa cikin naku kika mayar dasu gefe"? ta tambaye ta tana sake d'ebo su ta watso mata su cike da rashin son zaman lafiya shiru Zainab tai ko d'agowa batai ba balle tace wani abu sai kwanukan data tattara ta saka a kusa da nasu kafin ta gama itama ta wanke mata baki Asabe ta ta'be tana juyawa ta shiga d'aki tana rera wa'ka.
Tas Zainab ta wanke mata kamar yadda ta wanke nasu ta d'auka har kofar d'akinta takai mata kamar dai babu abinda ya faru muryarta a daidai tace "gashi Maman Bilkisu na gama" ta fad'a tana ajewa saidai ko juyawa batai ba Asabe tace "shigo ki kawo min kamar yadda kika kaiwa taki uwar ko itama a kofar d'akin kika aje mata ki kace gashi ta fito ta d'auka"? Kai Zainab ta girgiza tana du'kawa ta d'auki kwandon ta shiga da sallama ta aje mata sannan ta fito ta d'auki nasu takai musu shi kitchen ta shiga d'akin Umma ta share ta share nata sannan ta share tsakar gidan ta wanke band'aki saida ta gama komai sannan ta shiga tai wanka ta shirya tana zaune lokacin tana shirin tashi taje gaida Hajiya tunda har yanzu bata samu ta shiga ba hijab d'inta ta d'auka da kayan tsarabar da tasa Sameer ya siyo mata ta koma d'akin Umma ta sanar mata zata shiga gurin Hajiya.....................
We will meet again🤝.
ZUCIYAR ALIYU CE
@YUSRAH DUTSE
Chat with me.
+234 816 098 3083
PAGE 13
Ta fita daga kofarsu kenan taga Afifah ta fito ita kuma daga 6angaren Hajiya ga Balki da Haulat sun biyota kowacce tana so dole sai Afifah tasan da ita kodan su samu kusancin 'kawance su ri'ka shiga gidansu murmushi Zainab tai wanda ganinta yasa Afifah tahowa da d'an gudu tana rungume ta cikin farin ciki tace "kai Hajiya zee-zee nayi kewarki sosai wallahi matafiya kamar bazaki dawo ba gashi idan na kiraki ko kad'an bana samunki kullum wayarki a rufe meya faru ne"? Har lokacin da murmushi akan fuskar Zainab tace "ayya kiyi hakuri Afifah acan ne kwana biyu da zuwana na cire Sim tsautsayi wallahi shikenan na rasa shi babu inda ban duba ba ya fad'i shiyasa kika jini shiru sai d'ayan sabon Sim d'in da nayi lokacin dana kusa tafiya shi kuma sakamakon babu islamiyya yasa bamu had'u na baki ba" d'an had'e rai Afifah tai tana cewa.
"Kuma wato shine kikai tafiya sama da sati hud'u ko sallama baki min ba ko kamar ni