Chapter 8 of 45

ZUCIYAR ALIYU CE Zuciyarsa Tata Ce By YUSRAH MUSA

zai zo ya sameni zaki bar gidan nan kwanan nan" mi'kewa Umma tai bayan fitar Hajiya zata shiga d'aki Asabe tai wuff ta fito waje tana dariya ta kalleta tana sakin gud'a "ahayye ayuririiiiiiiii gaskiya naji dad'in wannan al'amarin dama ashe abinda kike 'kullawa kenan asirin ki ya tonu gara da Hajiya ta gane yanzu kowa yasan halinki ashe D'an Yanan da take zuwa da sunan hutu duk 'karya ce asiri kike aikata tayo miki dan ki mallake miji ke kad'ai humm wallahi baki isa ba ni nan da kika ganni ina daidai dake" kallonta Umma tai cike da damuwa tace "bazan biye kiba Allah ya fitar da mai gaskiya a cikin mu nasan tsakani da Allah nake rayuwata a gidan nan ban ta'ba nufar wani da sharri ba ina ro'kon ubangiji ya saka min zargin da kuke min bazan ta'ba yafewa duk wanda ya jefani cikin 'kunci ba Allah ya isa" tana fad'in haka ta shige d'aki zazzafar gud'a Asabe ta sake saki tana cewa "yau ake nanaye a gidan nan ji min munafikar mace kamar ta Allah karki yafe d'in man dama kinji nace miki ina neman yafiyar kine kedai kije ki da borin kunyarki ganin asirin ki ya tonu duk kin bi kin rud'e to wallahi idan ma dani kike nikam nafi 'karfin ki saidai ba'kin ciki ya kashe ki na zame miki ciwon ido na zama 'kashin cikin turmi maganin wadan kare nan gani nan bari d'umamen mayya".

Umman na jinta bata sake tanka mata ba sai Zainab data kifa kanta tana ta rusa kuka kallonta Umma tai itama idonta ya cika fal da hawaye tace "Zainab kiyi hakuri dan Allah karki d'orawa kanki hawan jini kisaka a ranki kamar babu abinda ya faru komai yai zafi maganinsa Allah babu wanda yake samun wata d'aukaka face an jarraba shi na sani baka samun farin ciki saika shiga 'kunci duk wanda kika ga ya samu wata rayuwa mai inganci idan kika bincika zakiga yasha matu'kar wahala kamar dai mu shiyasa nake sake fad'a miki kiyi hakuri insha Allahu akwai nasara ga duk wanda ya kasance mai ha'kuri ne kuma duk inda kika samu farin ciki dole yana tare da ba'kin ciki sannan idan kinga kin shiga wani 'kuncin rayuwa akwai sau'ki da jin dad'i a gaba kiyi hakuri ki daina kukan ki goge hawayen ki kinsan wannan kad'an ne daga aikin Hajiya zatai wanda yafi haka to tunda kin sani meyasa zaki 6ata lokacin ki kina kuka"? Kai Zainab ta girgiza tare da d'agowa ta goge hawayen fuskarta muryarta na rawar kuka tace.

"Dole na damu Umma dole nayi ba'kin ciki duk gidan nan babu wanda Hajiya takewa haka saike sannan a jikanu ma nice abar zaginta bansan me nayi mata ba ta tsane ni koda ace ni agola ce kika zo gidan nan dani ya kamata ta bani daraja sannan ta d'auke ni matsayin jikarta balle a gidan nan kika haife ni anan na taso kawai dai idan mutum baiyi maka ba shikenan saika tsane shi me nayi mata idan laifi nayi mata ta fad'a min na bata ha'kuri na gyara man amma wadannan matsalolin sunyi min yawa".

"Babu abinda ki kai mata sannan ba tsanar ki tai ba kamar yadda kike tunani ni nasan dalili laifi nane ya shafe ki sannan tana ganin kamar nice na hana kiyi aure saboda taga Hadiza Maryam da kuma Rafi'atu Aisha duk sunyi bayan sune sha'anin ki a gidan shiyasa ta d'auki abun da zafi batasan aure nufi ne na ubangiji ba sannan lokaci sai yazo da ayi ina fatan indai hakan zai gyara komai Allah ya kawo miki miji na gari kema kiyi auren nan kowa ya huta" numfashi Zainab ta sau'ke daidai anyi sallama suka amsa wasu 'yan mata biyu ne suka shigo gaida Umma sukai bayan ta amsa Zainab ta mi'ke domin tasan gurin ta suka zo kar6ar d'inki tace "muje ku kar6a Umma bari na dawo" to Umma tace su kuma suka fita d'akinta ta shiga ta d'auko musu tana cewa "saidai ban samu na goge ba sakamakon bana gari jiya na dawo ko zaku bari zuwa jimawa idan sun kawo nefa na goge muku ko zuwa yamma sai kuzo ku kar'ba"? Kai d'aya ta girgiza tana cewa "a'a wallahi barshi kawai zamu goge d'inkin yayi kyau sosai kawai saka mana a leda mu tafi" saka musu tai ta mi'ko musu suka bata sauran kud'in d'inkin ta sukai mata godiya bayan fitarsu ta aje kud'in tana komawa d'akin Umma ganin bata nan yasa ta fahimci maybe tayi kitchen shiyasa ta zauna jiran dawowar ta..................

ZUCIYAR ALIYU CE


@YMA DUTSE
PAGE 15
Fitowar Shareef kenan yaga Mami a dinning murmushi yayi yana karasawa ta bayan ya sunkuya yayi mata kiss a kumatu yana cewa "good morning mah fatan kin tashi lafiya"? Murmushi Mami tai tana girgiza kai daidai ya mi'ke ya zagayo ta gabanta ya samu kujera kusa da ita ya zauna kallonsa tai tana cewa "lafiya kalou na tashi Shareef yaushe zaka girma ne"? Jinjina kai yayi yana cewa "anya kuwa Mami zan girma"? Baki Mami ta bud'e tana dariya tace "tofa ban gane ba me kake nufi bazaka girman ba kenan" cire Bluetooth din kunnensa yayi yana cewa "gaskiya dai da alama domin koda ace yara na tara har lokacin ban girma ba tunda kuna nan nima ina da parents sannan kune kuka haife ni koda ace gemu na yana jan 'kasa a gurin ku ni yaro ne kallon da zakuyi min kenan koba haka ba"? Kai Mami ta d'aga tana cewa "tabbas maganarka nakan hanya domin har yanzun nan da muke magana nikam dama ban ta'ba ganinka a babba ba ko daidai da rana d'aya".

"Yauwa kin gani Mami alamu dai sun nuna ni yaron ne da kuma har nake shirin d'auko miki suruka" zaro ido Mami tai tana kallon sa tace "da gaske Shareef"? "Kwarai Mami da gasken gaske saidai ban fad'a mata ba so nake saina gama wani abu tukuna".

"Baka tsoro wani ya riga ka"?.
"A'a babu wanda zai riga ni Mami saboda a jikina ina jin cewa wannan yarinyar mata ta ce" kaiii dariya Mami tai tana cewa "to Allah ya tabbatar mana da alkhairi me kake so nayi serving d'inka"? Ta tambaya tana d'agowa ta kalleshi amsa ya bata yana mayar da Bluetooth d'in kunnensa yace "abinda zaki ci Mami shi nake so" "to aini faten wake da bushashshen kifi nasa akai min kai kuma baka so".

"Eh yau zanci saka min".
Plate ta d'auka ta saka masa ta d'auko spoon ta aje masa daidai kiran Baby ya shigo wayarsa kallon wayar yayi yana d'auke kai dama yasan za'ai haka bazata ta'ba iya fushi dashi ba amma fa shi kam a nasa 6angaren yayi fushi da ita sosai tunda batasan darajar d'an adam zai nuna mata kuskuren ta koda gaba bazata sake makamancin irin haka ba koda ace baya gurin.................

"Shareef kiran ka fa ake a waya baka gani bane"? Mami ta tambaye shi tana sake kallon wayar da akai kira karo na uku kai ya jinjina yana katse kiran yace "na gani Mami bana amsa waya idan Ina cin abinci su bari na gama" ok kawai Mami tace itama tana ci gaba da cin abincinta amma dai tsabar naci ba'a daina kiransa ba gudun kar Mami ta sake cewa wani abu yasa ya saka wayar a silent yana jan 'karamin tsaki saboda karta zargi wani abu ji yayi tace.

"Na gani fa Shareef kiranka ake amma ka share kodai kiran ba mai muhimmanci bane"? Kaiya d'aga yana kallon sabon kiran daya sake shigowa yace "eh" murmushi Mami tai tana d'agowa ta kalleshi ganin yadda ya had'e rai tasan akwai matsala tsakanin sa da mai kiran shiyasa tace "amma ba mai muhimmanci bane aka dame ka da kira kai da kake da patient ai bai kamata ka ri'ka sharewa ba gashi naga number gurin aikinka ce ba family number ba please ka d'aga dan Allah kaji ko ba lafiya ba" numfashi ya sauke a hankali yana jinjina kai yace.

"Mami ki yarda dani lafiya kalou kiran ba mai muhimmanci bane" kad'a kai Mami tai tana cewa "Ok shikenan na yarda" Mami ta fad'a tana d'auke hankalinta daga saitin sa amma tana hankalce jira take a sake kira ta fake shi ta d'auke wayar taji waye yake kiran ko gama shawara batai ba taga hasken secreen d'in wayar tasa tunda ya kashe ringtone d'in wuf tai ta d'auke yana shirin kashewa ta d'aga ji tayi cikin azama ance "hello Shareef Shareef dan Allah ka saurare ni karka kashe mun waya" d'agowa tai tana kallon Shareef wanda yai mugun had'e rai shima ya d'ago yana kallonta ganin irin kallon da take masa yasa yace "karki kiyi zargin komai Mami ba wani abu bane ki rabu da wannan".

"Na rabu da ita alama ya nuna baka da gaskiya Shareef tunda gashi tun kafin nayi magana har ka harka ankara"?.
"Ba ankara nayi ba Mami na fad'a miki gaskiya ta ne".

"Oh na gane" Mami ta fad'a tana sake kallon secreen d'in wayar da akai sabon kira zatai magana yace "ki rabu da ita Mami wannan yarinyar bata da hankali" "na rabu da ita kuma Shareef wace Baby a ina take me zakai mata take ro'kon ka"?

"Ki yarda dani Mami babu komai karki kiyi zargin komai tsakani na da ita bani da had'i da ita".
"Dama kaji nace ina zargin kane kawai tsarguwa kayi" ta karasa maganar tana mi'ka masa wayar 'kin kar'ba yayi kawai yaci gaba da breakfast d'insa "amshi man" yaji Mami ta fad'a had'e fuska yai yana kar'ba zai aje tace "no kiranta zakai a gabana naji wace ita".

"Oh my God Mami karki damu a kanta dan Allah" tsare shi da ido Mami tai tana cewa "saboda me baka so nayi maka tambaya a kanta"? "Saboda bana so kisan wace ita balle a gaba tayi tunanin zuwa gidan nan gurin ki nasan zata iya idan ta samu fuska".

"Anya Shareef maganar nan taka akwai 'kamshin gaskiya kuwa"? "Akwai Mami ki yarda dani bata da wani dalili da zaisa ta kirani da safiyar nan"

"Meyasa ka yanke hukunci bayan bakasan gaibu ba"?.

"Saboda bata da wani dalilin da zaisa ta kirani ne kawai ba komai ba tunda yau ba ranar aiki bace" d'agowa Mami tai tana kallon sa daga baya tai murmushi tana cewa "baka da gaskiya Shareef akwai abinda kake 6oye min haka ne"?.

"Babu abinda nake 6oyewa Mami ki yarda dani wallahi kawai 'yar gurin aikin muce ba komai ba had'uwar asibiti rabuwar can ba had'in biri da gada" kai Mami ta jinjina tana cewa "to meyasa take baka hakuri tayi maka wani abu ne"?.

"A'a".

"Ban yarda ba".

"Da gaske nake Mami amma shikenan zan fad'a miki wace ita amma ba yanzu ba saina samu nutsuwa" murmushi Mami tai mai kama da dariya tana girgiza kai tace "zargi na ya tabbata kenan magana ta tana kan hanya ba komai ka samu nutsuwa sosai yadda ya kamata ina jiran ka" ta fad'a tana mayar da hankalinta kan abincin da take ci yayin da Shareef ya mi'ke yana shiga part dinsa yaje toilet yai brush ya fito yana sake fesa turare a jikinsa tare da tsayawa a gaban mirror yana dad'a gyara kansa a ransa yana tunanin meyasa Mami take zarginsa akan Baby kodai ta d'auka budurwarsa ce humm aiko zai sakewa Baby warning kar kuskure yasa ta sake kiransa a waya indai ranar weekend ne bazai yuwu ta jawo masa aiki ba a ri'ka tunanin ya fara soyayya alhalin ba haka bane yasan wuya Mami ta fad'awa Abban sa cewa yana da budurwa yanzun nan zaice yayi aure tunda dama yakai kusan wata biyar da kiransa ya tambaye shi yaushe ne zaiyi aure yace masa ko budurwa baida ita a lokacin Abba yace lallai-lallai ya samo wacce tayi masa yaji yana sonta ya aureta domin zama haka sam bai kamace shiba tunda babu abinda ya nema ya rasa.....................

Ringtone d'in wayarsa ne ya katse masa tunanin da yake kallon secreen d'in yayi yaga still Baby ce yanzu ma take kira bai d'aga ba saida ta katse sannan yabi bayan nata kiran tana d'agawa tace "hello Shareef dan Allah ka............

"Baby" taji ya fad'a cikin tsawa wanda ba shiri ta d'auke wayar daga kunnenta tana kallon secreen d'in taga tabbas Shareef ta kira ba wani ba amma shine yake mata irin wannan tsawar d'an tsaki taja tana kallon wayar tata data kawo haske alamar ya katse kiran numfashi ta sauke tare da mi'kewa ta tafi jikin window ta d'aga labulen d'akin tana kallon compound d'in gidan ranta a 'bace yanzu ya zatai tasan kota sake kiransa bazai d'aga ba gashi yau weekend ne mahaifin ta yana gida bazai bari ta fita taje ko'ina ba taya zata had'u da Shareef gaskiya tana so suyi magana ta fahimta yadda ya kamata kar zuciyarta ta kamu da ciwo bayan baisan tana son shi ba gara ta fad'a masa a wuce gurin addu'ar ta dai Allah yasa kar yace a'a domin idan ya'ki amincewa tofa Abban ta yana son aura mata d'an gidan abokinsa ne wanda bata fatan faruwar hakan gashi yau kwanan biyar da dawowa Nigeria duk da tasan bai kammala karatun sa ba amma idan ya samu hutu yana zuwa gida yaga mahaifansa ya koma huuuuhhhhhh ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tare da sakin labulen ta dawo cikin bedroom d'in cikin rashin makamar abinda ya kamata tayi zama tai a gefen gadon ta tana tagumi can take mi'ke ta soma zaga d'akin zuciyarta cike da tunanuka iri-iri wanda ko kad'an bata da masaniyar ta yadda zata iya 6ullowa lamarin.

💓ZUCIYAR ALIYU CE💓

@YUSRAH MUSA ABUBAKAR
PAGE 16
A 6angaren Shareef kam bayan ya daka mata tsawar bai sake ce mata komai ba saboda yadda yaji 6acin rai yana mamaye zuciyarshi ya tsani mutum mai masifae naci balle Baby da tun ranar data mari Nihal a gabansa yaji ta fice masa a rayuwarsa dan ya tsani yaga ana wulakanta mutum a take ransa zai 6ace shi mutum ne wanda yasan darajar mutane.

A 6angaren Zainab kam alhamdulillah kamar yadda Sameer ya saka ta cike form d'in makarantar ta haka ta fara karatun ta cikin nasara da fatan alkhairi saidai ta 6angaren Hajiya taci ba'ka'ken maganganu da wulakanci daga ita harsu Umma saida sukai kuka tsabar irin ba'kin tozarcin da Hajiya tayi musu.
Fitowar Bilki kenan daga d'aki ganin kwanukan Umma a kusa da nasu a gurin wanke-wanke yasa taja tsaki tana kallon kofar d'akin Zainab ganin takalman ta yasa tasan tana nan bata tafi school ba bakin kofar d'akin taje tare da cewa.

"Zainab Zainab"

A lokacin Zainab tana cikin karatu taji Bilki na kiranta dakatawa tayi tana mi'kewa ta karaso ta d'aga labule ganin tazo har kofar d'aki yasa tasan akwai abinda ya kawo ta kallonta tai sosai yadda ta had'e rai take girgiza cikin nutsuwa tace "meya faru"? Buntsura baki Bilki tai tana turo d'aurin kwali gaban goshi tace "kalli wancan kwanuka na tsohuwarki daga yau na saukewa kaina bazan sake mata wanke-wanke ba domin niba baiwar kowacce 'katuwar bace" jin abinda tace yasa Zainab tai murmushi tasan fitina take nema so take ta kula ta, ta zage ta shiyasa tace "idan dan wannan ne karki damu zan wanke mata idan kika gama naku" baki Bilki ta ta'be tana cewa "da dai yafi miki alkhairi sannan magana ta gaba shara ma daga yau bazan sake share dukkan kofar nan ba saboda ni ba jaka bace zan share iya kofar d'akin uwata idan kinga dama kema ki share naku idan baki ga dama ba ki barshi da datti" tana fad'in haka ta juya ta nufi gurin wanke-wanke da kallo Zainab ta bita tana d'an girgiza kai kafin ta saki labulen ta koma cikin d'akinta karasa kai surar da take yi sannan ta rufe al-qur'anin tayi addu'a tare da mi'kewa ta cire hijab d'in jikinta ta fita samun Bilki tayi a gurin tana wanke kwanukan su bata ce mata komai ba itama ta d'auki kujera ta had'a ruwan klin dana d'auraya ta fara wanke nasu ta gama ta d'auka takai kitchen sannan tazo ta saka ruwa ta wanke gurin ta share kofar tasu tas ta wanke ta tasaka tsumma ta goge tayis d'in daidai Umma ta fito ta kalleta cikin jin dad'i tace.

"Sannu Zainab Allah ya miki albarka" murmushi Zainab tai daidai ta wanke 'kafarta da hannunta tace "amin Umma nagode" kai Umma ta d'aga tana wucewa ta shiga kitchen domin ranar aikinta ne bin bayanta Zainab tai tana cewa "wanne aikin zan kama miki"? Doya Umma ta nuna mata tana cewa "ki d'auki wu'ka saiki fita waje ki fere mana ita yau da ita za'a karya jiya baban ku ya shigo da ita da dare" kallon doyar kitchen d'in tai da d'an yawanta tasan zatakai kusan dubu goma ko tafi maybe 'yar ribar daya samu ce yayo musu cefane saboda suji dad'i suma tunda taga d'aurin kayan miya kuma ga d'anyan kifi ma a gefe numfashi ta d'auko tana d'auko babbar roba da wu'ka Umma ta d'iba mata iya wacce zasuyi amfani da ita waje ta fita ta zauna akan kujera a kusa da kitchen ta soma aikin fere ta domin yau sai karfe d'aya zataje lecture harta gama tana shirin mi'kewa Umma ta sake mi'ko mata guda d'aya tace a dad'a saboda saura kofafin ma akai musu abinda ka bayar shine rabonka tana cikin gyaran wacce ta mi'ko mata Sameer ya shigo da sallama hangota dayai yasa ya taho inda take yana zuwa ya tsuguna a kusa da ita yana cewa.

"Yau kuma doya zamu ci kenan kece zaki dafa yau ba school ne"? Murmushi tai tana girgiza kai tace "a'a akwai amma ba yanzu zan tafi ba sai 'karfe d'aya".
"Ok Allah ya kaimu wannan doyar wanne kalar samfurin dafi za'ai mata ne"?.

"Nima ban sani ba saidai na tambayi Umma".
"A'a basai kin tambaye ta ba kawai ni ban cika son faten doya bane gara sakwara yanzu abinda za'ai tunda sai karfe d'aya kike da school bari kawai na siyo 'kwai kiyi min yamballs" ya fad'a yana mi'kewa ya fita daidai Asabe kuma ta shigo kofar tun daga nesa take zaro ido tana kallon Zainab harta karaso ganin abinda take yasa tace "tofa wannan wanne irin kalar munafirci