Chapter 10 of 45

ZUCIYAR ALIYU CE Zuciyarsa Tata Ce By YUSRAH MUSA

har nice zan fad'i magana ka mayar min ina daidai dakai" juyawa 6angaren Zainab tai tana cewa "ke zo'kal'kalar banza mai had'a husuma masharranciya baki nasara ba saiki sauya tasha banza kawai" kan Umma ta koma tana nunata da yatsa tace "kema na dawo kanki kiwa 'yarki gargad'i karta kuskura ta sake min sharri idan kina bu'katar zaman lafiya a cikin gidan nan mtwwww" taja tsaki tana komawa d'aki.

Hawaye ne shar shar suke zuba a fuskar Zainab irin maganganun da Asabe ta fad'a mata suna mata ciwo bata son ace abu yana had'ata da ita amma ina ko bata takale taba ita kuma zata ta6o ta.................

Muryar Umma taji ta katse ta "Zainab ke d'in meya had'a ku nifa ban gane komai da take cewa ba a ina kika ganta ta d'auki kud'in"? Kaita girgiza tana goge hawayen fuskarta muryarta a hankali tace "d'azu ne da Yaya Sameer yace nayi masa yamballs ya kawo min 'kwai saiya manta ya tafi anguwa bai siyo farin man dazan soya masa ba shine na kirashi a waya na fad'a masa ni bansan ya tafi wani guri ba a lokacin ne yace na shiga d'akinsa na bud'e littafi akwai kud'i na d'auka na siyo na shiga na d'auko dubu d'aya Umma Asabe ta shigo ta ganni shine tace sata zanyi masa nace a'a kud'i yasa na d'auka zan siyo mai ne a lokacin ma ta zazzage ni daga haka nidai bansan komai ba hijab na d'auka na tafi na siyo man amma lokacin dana gama yamballs d'in na shiga d'akin zan aje masa naga an wargaje d'akin komai dabam shine na fasa aje yamballs d'in a d'akin nakai nawa d'akin na tafi makaranta yanzu kuma saiya kirani yake tambaya ya akai nace masa lafiya 'kalau nabar d'akin amma Umma Asabe ta shigo ta ganni daga haka bance masa komai ba bansan meya faru ba sai ji nayi tana zagina yanzu" numfashi Umma ta sauke tana girgiza kai tace.

"Allah ya rufa asiri koma d'aki ai shi Sameer d'in yana da hankali yasan bazaki ta'ba yi masa haka ba karma ki d'orawa kanki damuwa ki 'kyale" Umma tai maganar tana komawa d'aki itama Zainab d'in nata d'akin ta koma shikam Sameer saida gyara d'akinsa tas ya mayar da komai daidai sannan ya fita daga gidan.

Duk abinda akai Abban su Zainab bai sani ba daya dawo gida ma Umma bata nuna masa komai ba saboda bazai yuwu ya wuni yana fafutukar nema musu abinda zasu ci ba ya dawo gida dan ya huta kuma ta tada masa hankali ba amma me yana fara cin abinci kenan suna hira da Umma Zainab ta shigo ta gaida shi ta fita sai ganin Asabe sukai ta bamko muku kofa ta shigo ba sallama tana huci da mamaki Umma ta kalleta cike da fargabar Allah yasa ba abun d'azu zata fad'a ba karta taso masa da 6acin rai shi mutum mai sau'kin hali amma idan ka ta'bo shi zakaga tsantsan abinda ake kira da 6acin rai........

"Gaskiya na gaji da wannan na gaji da rashin adalcin da ake min a cikin gidan nan" sukaji ta fad'a da mamaki baba da baisan komai ba yace "akan me kike magana Asabe wanne irin rashin adalci akai miki kuma waye yayi miki"?.

"Waye kuwa banda kai tunda kaji na ambaci adalci a gurin wa aka sanshi idan ba mai gida ba".
"Ina jinki meya faru"?.

"Meye ma bai faru ba taya za'ai jiya kayo cefane baka sanar dashi ba alhali nice uwar gida wannan ba adalci bane" kai baba ya jinjina yana cewa "ba rashin adalci bane Asabe ba abinda kike tunani bane a kitchen na saka kayan nan ba'a d'akin Hauwa ba kowa ranar girkinta ta d'auki abinda ya kamata ta dafa sannan naga jiyan ba girkin ki bane nata ne ke gobe zaki kar'ba shiyasa ban sanar dake ba amma idan kin d'auki hakan a rashin adalci kiyi ha'kuri" ya fad'a yana kokarin mayar da hankalinsa kan cin abincin sa ya sake ji tace.

"Gaskiya baka kyautawa ha'kurin me zanyi bayan an gama dani komai baza'ai min na Allah ba ranar girki na saika bani abu mai wahala nayi ta faman shan wuya amma ranar girkin Hauwa da yake ta asirce ka kafi sonta sai abinda tace shi kake yi shiyasa ka siyo doya da kifi da kayan miya da su maggi da komai amma baka fad'a min ba saida na shiga kitchen d'in na gani kai gaskiya ana munafirci a gidan nan" ta fad'a tana dan'karawa Umma harara wacce fuskarta ta nuna alamun 6acin rai musamman ganin datai Abba yayi shiru tasan maybe ya gama 'kulewa ne numfashi ta sauke tana cewa.

"Nidai Asabe tsakani da Allah nake zaune dake da zuciya d'aya ban ta'ba ji a raina daidai da rana d'aya na cutar dake kona nufeki da sharri ba sa6anin ke meyasa bazaki zauna kiyi nazari ki fahimce ni ba" hannu Asabe ta d'aga mata tana cewa "ke kinga bazan yi d'in ba badake nake ba ki rufe min baki adalci nazo ayi mun dan haka baza kisa mana baki a ciki ba indai kina da gaskiya saiki 'kyale ni" jin abinda tace yasa Umma jan bakinta tai shiru ya zama suyi maganar ita da Baban.

"Magana nake yi ina so zan tafi" Asabe ta fad'a tana mayar da hankalinta kan Baba saboda kar tace da gaske baya yi musu adalci bayan ba haka bane ya d'aure duk da ta 6ata masa rai amma matsayin sa na mai gida kuma xaman lafiya da fahimtar juna yake bu'kata shiyasa ya danne duk abinda yake ji muryarsa a daidai yace "yanzu me kike so ayi miki ki fahimce ni kuma ki fahimci abokiyar zamanki me zakice"? Had'e rai Asabe tai ganin Umma ta d'ago ta kalleta kafin tace "ni bani da abun cewa saidai nace Allah ya isa Allah ya saka min cutar dani da Hauwa take yi domin yanzu ma wannan tambayar da kai min bakaga wata ba'kar harara data sakar min ba kawai na ha'kura da komai na barta da Allah idan munje can ayi masa sakamako a 'kwatar mun hakki na" tana fad'in haka ta juya da sauri ta fita saboda kar Baba yace ta dawo shiru d'akin ya d'auka daga baya Umma ta sauke ajiyar zuciya tana cewa.

"Dan Allah kayi ha'kuri" kaiya girgiza batare da yayi wata magana ba ya d'ora cin abincin sa Umma taji dad'in hakan domin yadda ransa ya 6aci ta d'auka bazai ci abincin ba sai kuma taga ya d'ora daga inda ya fara shiyasa taja bakin ta tai shiru tana fatan Allah yasa kar idan ya gama ya sake kiran Asaben kawai a wuce gurin babban farin cikin ta ma shine jin ba tashin hankalin d'azu Asabe ta fad'a ba domin sai yafi 6ata ran Baba idan yaji sharrin da Asaben taiwa Zainab cewa ta shiga d'akin Sameer ta d'auka masa kud'i dubu ashirin.

ZUCIYAR ALIYU CE..............

J.W.A

@YMÄ YUSRÄH ÇË
PAGE 19
Washe gari karfe bakwai Zainab ta gama shirinta zata tafi school bayan ta gaisa da babanta da Umma a lokacin Sameer baya gidan iya tea ta kar'ba a gurin Umma tasha a tsaitsaye ta fita 6angaren Hajiya ta shiga a lokacin ita kad'ai ce ta gaisar da ita duk da bata samu amsuwar arziki ba amma tunda ta saba wannan ba wani abu bane tana fita kofar gate d'in gidansu ta hango Sameer acan nesa wajen gidan su Afifah yana tsaye tare da wani mutum suna magana tsayawa tayi daga inda take bata cigaba da tafiyar ba addu'a take me napep yazo ta shiga kawai basai sun had'u ba amma dai shiru ba wulgu d'an napep saboda lokacin gari ya waye ba sosai suka fito ba har Sameer ya gama magana da mutumi ya taho bata samu ba karasowa inda take yayi yana kallon ta yace.

"Yau da wuri zaki tafi makarantar"? Kaita d'aga ta kasa d'agowa ta kalleshi saboda abinda ya faru jiya murya a 'kasa tace "Ina kwana"? "Lafiya kalou nace yau kuna da lecture ta safe ne"? Kaita d'aga tana cewa "eh yanzu bakwai da rabi karfe takwas da rabi zamu shiga lecture d'in".

"Ok abinci fa kin karya ne zaki tafi"?.

"Eh nasha tea a gurin Umma yanzu".
"Tea kuma Zainab aiba abinci bane mezai tare miki"? Shiru tai har lokacin bata d'ago ta kalleshi ba juyawa yayi yana kallon ko'ina ba mutane sosai yaci gaba "gashi masu abun saidawa basu fito ba balle na sai miki wani abu" jin abinda yace yasa ta girgiza kai tana cewa "a'a Yaya Sameer ba komai zan iya bari saina dawo naci abincin ko kuma naje cafeteria" "ok tom ba damuwa amshi wannan" ya fad'a yana mi'ka mata dubu d'aya kamar yadda ya saba kullum tsabar rud'ewa batasan lokacin data d'ago ta kalle shi ba duk da fuskarta da nikaf da sauri ta girgiza masa kai hawaye yana nema taruwa mata a ido tace.

"A'a Yaya Sameer bazan kar6a ba jiya kayi asarar kud'i dubu ashirin ta dalili na ka barshi zanje da 'kafa babu nisa idan na fara tafiya kafin takwas da rabin na karasa school d'in" murmushi yayi yana kallon ta yace "karki damu kedai ki kar'ba kawai ai nine na baki kud'in jiya da aka d'auke ba nawa bane" zaro ido tai tana sake kallonsa tace "ba naka bane na waye kenan saika biya shi"? Kaiya jinjina yana cewa "tabbas ajiya aka bani Kinga kuwa ai ban isa naje nace ya 'karo wani kud'in ba wancan an sace" muryarta da alamar kuka tace "kuma kana da dubu ashirin d'in da zaka biya shine ko a cikin kud'in chemist d'inka zaka biya"?.

"A'a ki kar'ba yanzu ki tafi karki latti" ya fad'a yana dad'a mi'ka mata dubu d'ayan kai ta girgiza tana cewa "ni bazan kar'ba ba kawai ka barshi" zata wuce yace "Zainab nayi miki tambaya"? Ji tayi gabanta ya fad'i wani yawu ta had'iye da'kyar tace "eh" numfashi Sameer ya fitar yana cewa "yanzu misali ace nine matsayin baban mu dan kud'i na ya 6ata idan na d'auka na baki baza ki kar'ba ba me ya sa? Kodan saboda bani da wadatar dazan baki ko kuma yaya"? Kaita girgiza tana cewa "Yaya Sameer dan Allah ka fahimce ni.........

Katse ta yayi "na fahimce ki sosai fiye da yadda kike tunani amma saikin kar'bi wannan kud'in bana so idan na baki abu mu tsaya kina ja in ja sakamakon yanzu da wani ya fito daga gidan ya gani sai aje a fad'awa Umman mu ina shiga ta hauni da fad'a haka kike so"? Kaita girgiza masa "idan kina so na yarda amshi ki tafi" ya fad'a yana mi'ka mata hannu biyu ta saka ta kar'ba ba don ranta yaso ba tace "na gode" "ba matsala jeki sai kin dawo" wucewa tayi a sanyaye taci gaba da tafiya yana tsaye yana kallonta ta wuce kofar gidan su Aliyu kenan ya fito amma duk da haka saida ya ganeta a tafiyarta yasan school zata tafi hango Sameer yayi yana tsaye a inda sukai magana yanzu shima Sameer d'in ya ganoshi shiyasa ya dawo su gaisa.

"Sameer ina Zainab zata tafi yanzu yau lecture safe take dashi"?.

"Eh tace takwas da rabi zasu shiga" kallon agogon dake d'aure a hannunsa Aliyu yayi yaga takwas d'in ta cika harda mintuna kafin ya kallo inda Zainab d'in tabi yace "kafin taje school fa lokaci ya fita bari na tura driver ya kaita" ya fad'a yana juyawa cikin taku da sauri yaje yayi umarni a kaita yayiwa driver kwatancen irin kayan da ta kasa.
Zainab tana cikin tafiya taga mota ta parking a kusa da ita kamar zata buge ta da sauri ta matsa gefe kad'an tana fad'in "Subhanallahi" sauke glass driver yayi yana cewa "ranki ya dad'e ki shigo na kaiki school d'in" wani irin zaro ido waje Zainab tai tana kallon sa da mamaki tace "na shigo ka kaini school waye kai"?.

"Ranki ya dad'e babu bu'katar hakan wanda ya aiko ni yace karna fad'i sunan sa" jin abinda yace yasa Zainab sake 'kare masa kallo tana cewa "na gode ina da kud'in dazan hau napep" tana fad'in haka ta wuce taci gaba da tafiya da sauri driver ya fito da d'an gudu yabi bayanta daidai ta tsayar da d'an adaidaita yace "ranki ya dad'e dan Allah kizo na kaiki karki jawo min fushin uban gidana" kamar bazatai magana ba sai kuma tace "na gode" daga haka ta shiga napep mai napep yana shirin tayarwa cikin azama driver yace "malam d'an tsaya kinga Hajiya dan Allah ki fito daga napep d'in nan muje ga mota can na kaiki" kai Zainab ta girgiza gabadaya lamarin driver ya d'aga mata hankali domin harta fara zargi a ranta kodai wani ne ya aiko shi ayi kidnapping d'inta....................

"Hajiya ki fito muje" taji saukar muryar driver ya katse mata tunani a firgice tacewa mai napep "dan Allah rabu dashi mu tafi bansan shiba" jin haka yasa mai napep kallon driver da damuwa da bayyana 'karara a fuskarsa kamar zaiyi magana sai kuma yaga ba abinda ya shafe shi bane karya jawowa kansa bala'i tunda baisan waye shi ba sannan da ganin motar da yazo da ita kaima kasan ba motar 'kananun mutane bace fuuuu yaja napep d'insa sukai gaba yayin da driver yayi tsaye a gurin kamar ya fasa ihu karshe ganin ba yadda ya iya saboda ya nemawa kansa mafita saiya koma mota yad'an jinkirta kamar misalin yaje ya dawo sannan ya tada motar ya bar gurin kuma koda ya koma bai fad'awa Aliyu cewa ba shine ya kaita ba.

Zainab kam da taje school ma kasa nutsuwa tayi ta kalli nan ta kalli can da'kyar ta tsaya tayi karatu yadda ya kamata lokacin da akai break kiran Sameer ya shigo wayarta tana d'agawa yace ta fito wajen aje motocin school d'insu yazo jin haka yasa ta mi'ke ta tafi wajen a tsaye ta same shi ri'ke da cooler a hannunsa da mamaki tace "Yaya Sameer amma dai ba abinci ka kawo min ba"? Murmushi yayi yana kallon ta yace "abinci ne mana kin fita gida baki karya ba ai dole na kawo miki indai ba so nake ki kamu da ulcer ba kar'bi ki koma cikin school ni tafiya zanyi" ya mi'ko mata kar'ba tayi cikin jin dad'in nuna kulawarsa gareta tace "na gode sosai Allah ya saka da alkhairi" "Amin karki damu kin fi 'karfin komai yaushe za ku tashi"?.

"Nan da awa hud'u ne".
"Ok ba damuwa jeki sai kin dawo"

"To Yaya Sameer na gode" ta fad'a tana juyawa saida yaga 'kulewar ta sannan shima ya koma cikin motar da suka zo duk abinda suke Aliyu yana zaune a cikin mota yana kallon su wata iriyar nutsuwa da farin ciki yana yawo a zuciyarshi ya rasa wanne irin so ne yake yiwa Zainab wani lokaci idan abun ya juyo masa ji yake kamar ya mutu a kanta kamar zaiyi hauka ya matsu yaga ta zama mallakin sa..................

"Aliyu muje ko" Sameer ya fad'a bayan ya shigo motar sauke numfashi Aliyu yayi yana kallon Sameer yace "Sameer dan Allah ka fad'a min wace Zainab"? Da alamar tambaya Sameer yace "kamar ya"? Sabon numfashi Aliyu ya sake fitarwa yana tada mota suka fita daga school d'in a hanya yace "ina nufin wace ita gani nake kamar tafi kowa ita d'in tamkar wani babban ginshi'kin abu ce wacce idan babu ita wannan abun bazai amfanu ba" ya fad'a ya juyowa ya kalli 6angaren da Sameer yake ya zuba masa ido ajiyar zuciya ya sauke yana ci gaba "Sameer Zainab zuciya tace Zainab rayuwa tace Zainab farin ciki nace Zainab abar nema nace sonta ya riga ya zama sinadarin dake sarrafa rayuwa ta dukkan zuciyata tata ce bazan iya saka kowacce mace a raina ba idan ba ita ba ina sonta da dukkan zuciyata ina tsoron rasa ta dan girman Allah Sameer ka taimake ni karka bari wani ya shiga rayuwar Zainab idan hakan ta faru zai zama sanadiyar rayuwa ta ina fatan zakai min wannan alfarmar"? Murmushi Sameer yayi yana jinjina kai ransa fari tas yace "insha Allahu Aliyu kamar yadda kake dakon 'kaunar Zainab kake sonta wata rana itama zata tsinci kanta kamar yadda kake ji nima ina tayaka da addu'ar ta zama abokiyar rayuwarka bazan ta'ba bari wani ya shiga cikin rayuwarta ba saidai idan ban sani ba ka kwantar da hankalinka".

"Shikenan Sameer na gode zuwa karfe biyar na yamma zan koma gurin aiki shiyasa na sake tunatar dakai ka kula min da ita".

"Insha Allahu Aliyu zanyi hakan zanyi iya bakin kokari na" ya fad'a daidai sun karasa kofar gate d'in gidansu Aliyu yai horn masu tsaron kofar suka bud'e ya shiga parking space ya tsaida motar tare suka fito shi da Sameer ta wata kofa ya bud'e suka shiga part d'insa tare domin ya sake bashi amanar kula da Zainab d'in.

ZUCIYAR ALIYU CE

YUSRAH MUSA
08160983083

@YMA DUTSE JIGAWA
PAGE 20
Sai wajen karfe biyar Zainab ta dawo gida da yake dama ranar ba islamiyya tana aje jakarta ta fita ta d'ebi ruwa tayi wanka bayan ta fito ta shirya ta d'auki cooler ta shiga d'akin Umma a lokacin tana zaune tana waya da babarta Kaka A'i kar'bar wayar Zainab tayi suka gaisa bayan sun gama wayar ta mi'kawa Umma itama suka karasa sannan ta aje wayar a gefe tana kallonta tace "har kinyi wanka kin dad'e da dawowa ne"? Gyara zama Zainab tai tana cewa "a'a yanzu na shigo kawai dai zafi nake ji shiyasa na fara yin wankan".

"Ya karatun fatan kina lura ko"?.

"Sosai Umma ai bana wasa"
"Masha Allah naji dad'i kije kitchen ki d'auko plate ga abinci a cikin cooler nan kizo kici dama yau abincin da kike so ne shinkafa da wake" girgiza kai Zainab tai tana mi'ko mata cooler data dawo da ita daga school tace "na 'koshi saidai zuwa dare kinga abincin da Yaya Sameer yakai min ma ban gama cinye shi ba" da mamaki Umma tace "Sameer yakai miki abinci to wannan cooler ta waye"?.

"Oh ba ta nan gidan bace"? Zainab ta tambaya tana 'karewa cooler kallo amsa Umma ta bata "eh ba tanan bace kalli ki gani man ina muke da kuloli masu tsada irin wadannan saidai a wanke masa idan ya shigo a bashi watakil a