Chapter 11 of 45

ZUCIYAR ALIYU CE Zuciyarsa Tata Ce By YUSRAH MUSA

gurin masu saida abinci ya siya miki" kai Zainab ta d'aga tana cewa "eh inaga hakan ne amma da sauran abinci fa a ciki" bud'ewa Umma tai taga had'add'an girki na gidan masu akwai zubawa abincin ido tai can ta d'ago ta kalli Zainab tana cewa "anya wannan a gurin masu saida abinci ya siya gaskiya bana jin hakan saidai idan a restaurant ko kuma hotel yaje ya siya baiyi kama da abincin shago ko gurin masu saidawa ba" murmushi Umma tai tana d'agowa ta kalle ta tana cewa.

"Ikon Allah kenan soyayya gamon jini gashi tsakanin ki da Sameer kamar uwa d'aya ce ta haife ku wasu 'yan uban kuwa basu da buri sai ganin ka fito rana ka tozarta amma banda irin su Sameer" jin abinda tace yasa itama Zainab d'in tayi murmushi batare da tayi magana ba ta sake gyara zamanta tana kallon fuskar wayarta da message ya shiga bud'ewa tayi domin ta duba tare da mi'kewa ta fita ta koma nata d'akin.

Sakamakon yau Monday da wuri Shareef ya shirya dan ya fita hospital gudun makara a lokacin daya fito daga part d'insa ko Mami bata fito ba sai iya masu aiki su biyu suna gyare-gyare a parlor wucewa yayi ya fita zuwa harabar gidan ya bud'e motarsa ya zuba takardun daya fito dasu a hannunsa kafin ya rufe ya sake komawa gidan daidai Mami ta fito ya shiga 'kare masa kallo tayi taga ya shirya tsaf yasha farar rigar likitoci kallon agogon parlon tayi tana sake kallonsa murmushi yayi yana cewa "good morning Mami na" kaita d'aga da alamar tambaya tace "amma dai ba hospital zaka tafi tun daga yanzu ba"? "Eh saboda gudun makara yasa na fita da wuri".
"Ok abinci fa haka zaka tafi ba kayi breakfast ba"?.

"Eh Mami zanyi acan".

"Acan gurin wa"? Had'e hannuwansa yai yana cewa "please Mami ina da gaskiya" baki ta bud'e da mamaki tana cewa "tofa Shareef ban gane kana da gaskiya ba dama kaji nace 'karya kake kawai nace a gurin wa zakai break d'in ne"?.

"Ina da abokai da yawa a hospital d'in".

"Indai haka ne ka bari yanzun nan ko 'karamin abu ne mara nauyi na dafa maka kaci kafin ka tafi".

"A'a Mami kawai ki barshi saina dawo".

"Meyasa to bazaka tafi dashi ba"? "Babu komai dalili na mai 'karfi ne bana son 6acin rai a wancan ranar da kika had'a min basket na tafi dashi matsala ya zame min shiyasa yau bazan je dashi ba".

"Matsalar me ya zame maka"?.
"Humm kawai basai na fad'a ba na tafi saina dawo" ya fad'a yana shirin juyawa ya fita ri'ko hannunsa Mami tai tana girgiza kai tace "Shareef tsaya min ina zuwa" sakin hannun nasa tayi tana wucewa ta nufi kofar da zai kaita kitchen ta shiga kallon matar da take aikin tayi tana cewa "Laraba kin had'a wani abu ne"? Cikin girmamawa ta d'an risina tana cewa "ina kwana"?.

"Lafiya kalou me kika dafa"?.
"Yanzu na fara aiki Irish kad'ai na soya da 'kwai sai yanzu zan fara aikin" wata 'karamar cooler Mami ta d'auko tana cewa "ok sakawa Shareef anan zai fita hospital" kar6a Laraba tayi tana zubawa kamar rabin cooler tasa murfin ta rufe tare da mi'ko mata amsa Mami tai ta fita samun Shareef tayi zaune akan kujera a cikin parlon ya d'ora 'kafa d'aya kan d'aya mi'ka masa tai tana cewa "Allah ya tsare saika dawo" mi'kewa yai yana bud'e hannu ya rungumeta yana d'an lumshe ido fuskarsa da murmushi uwa kenan mahaifiya tafi 'karfin komai ba abun wasa bace duk yadda yaso ta barshi ya tafi ta'ki saboda bata so ya zauna da yunwa alhali ya mallaki hankalin kansa d'agowa yayi har lokacin fuskarsa da murmushin ya kalleta yana d'ago hannunta ya bata kiss yana cewa.

"Na gode Mami babu kamar ki duk duniyar nan kinfi kowa ina son ki Mami na" ya karasa maganar yana sake rungume ta kansa Mami ta shafa tana cewa "karka damu Shareef kai d'ana ne nagari wanda za'ai alfahari dashi jeka tafi Allah ya tsare min kai" "Amin Mami" ya fad'a yana kar6ar cooler ya juya ya fita ya nufi motarsa ya bud'e kawai ya shiga yana aje cooler a d'ayar kujerar ta kusa da driver kafin ya kunna motar ya nufi gate mai gadi ya bud'e masa ya fita daga gidan.

A shirye Afifah ta sau'ko daga stairs tana waya ta karaso gurin su Momy dake dinning suna breakfast zama tayi tana cigaba da wayarta harta gama bayan ta aje ta d'auko karamin kofi ta had'a tea ta fara sha tana dariya kai Afif ya girgiza yana cewa "wasu lokutan ina jin mamaki idan naga ke kad'ai kina dariya meyasa"? Kallonsa Afifah tai har lokacin bata daina dariyar ba tace "wallahi Amirah ce ta ban dariyar ba kowa ba wai akan ta tambaye Aliyu fa nace mata ai ya koma bakaji wani uban ihu data sakar min a kunne ba kamar zata fasa min kai haka ta hau salati wai kuma bayan ta dawo daidai tace min kodai da wasa nake mata nace mata a'a da gaske nake ya tafi shine kawai naji ta kama kuka wai ta rasa me yake damunsa yanzu tsakanin su ba amana tunda har zai iya komawa bai sanar da ita ba kuma ko a waya bai kirata ya fad'a mata ba tuna hakan yasa nake dariya ba komai ba" baki Fati ta ta'be batai magana ba Elham ma dai batace komai ba balle Asma'u da babu ruwanta idan suna magana.

"Da kyau ya kyauta irin wadannan 'yan matan da basu san komai ba saidai su saka maka headache meye amfanin dan zakai tafiya saika fad'a musu amfanin me hakan zaiyi mata"? Afif ya fad'a yana d'aukar tissue ya goge bakinsa tare da mi'kewa yana d'aukar key d'in motarsa da glass d'insa dake aje akan dinning d'in yana shirin fita Afifah ta mi'ke tana cewa "please bro dan Allah muje kayi drooping d'ina a school saika wuce company kaga banyi breakfast ba a hanya saika siya min wani abu mai d'an dad'i-dad'i kaji" jin abinda tace yasa ya kalleta yana cewa "sannu uwar zilamammu waye zai siya min abun dad'in amma dai ba dani kike ba"? Kai ta d'aga tana cewa "dakai nake man waye nake dashi bayan kai"? Juyawa yayi zai fita yace "gara ma ki tsaya kiyi breakfast d'inki a gida kisa driver ya kaiki school nikam ba zanyi miki abinda kike so ba idan kika biyoni zakiyi wunin yunwa" ganin zai fice ya bud'e kofar parlor yasa Afifah d'aukar handbag d'inta tana bin bayansa tace "a'a da wasa kake yasin saika kaini kuma saika siya min abunda zan karya" tana fita Momy ta kalli su Elham tana cewa.

"Ku baza ku bishi yayi dropping d'in naku ba in yaso lokacin tashi driver ya d'auko ku"? Kai Fati ta girgiza tana cewa "a'a gara mubi a huce driver ya kaimu hankalin mu kwance haka kawai zamuje muce ya kaimu shima Yaya Afif halin Yaya boss ne dashi abu kad'an yace anyi masa laifi ku karasa kawai mu tashi muje a kaimu" jinjina kai Elham tayi tana cewa "gaskiya ne Fati wannan haka yake mun riga munsan halin bosawan namu kinga gara mu kama kanmu tun kafin su kama mana ko"?

"Haka ne wallahi tashi mu tafi kar lokaci ya fita" mi'kewa sukai a tare Asma'u da yake ita primary take yi Momy ta had'a mata basket d'inta na abinci ta tafi dashi a mota d'aya ake kaisu idan anyi dropping d'in Husnah sai a wuce a kaisu.

HOSPITAL
wata mace ce ta fito da sauri tana kokarin shiga wani d'aki a cikin asibitin Baby dake tsaye tana hangen ta inda zata ga Shareef amma shiru d'an tsaki taja tana kallon agogon hannunta tasan dai yanxu duk tsiya ya baro gida to a ina ya tsaya? Ya tambayi zuciyarta tare da cizon yatsa daidai wannan matar tazo zata wuce ganin inda zata shiga yasa Baby cewa.

"Baki ji ba" dakatawa tayi tana juyowa tace "na'am dani kike"?.

"Eh dake nake amma dai ba wannan d'akin zaki shiga ba ko"? Kaita d'aga tana nuna mata ruwan faron dake hannunta tace "nan zan shiga yarinya tace ba lafiya kuma tana ta kiran zata sha ruwa shine zan shiga na kai mata" yatsa Baby ta d'aga mata tana girgizawa tace "ba yanzu ba koma inda kika fito yau manyan likitoci suna zagaya patients ne" kallonta matar tai cike da tashin hankali tace.

"Bakinta a bud'e yake kuma ya bushe saboda ta bakin take numfashi dan Allah ki barni ina bata zan fito" wani d'an iskan kallo Baby tai tana cewa "baki ji abinda nace miki bane ki koma inda kika fito nan da awa d'aya idan sun gama saiki dawo" tsananin mamaki ne ya kama matar har batasan lokacin da tace "anya kina da imani kuwa"? Wani irin zaro ido Baby tai tana nuna kanta tace "ni kike kira mara imani saboda na hanaki shiga? Shiru matar tai ta zuba mata ido kaita jinjina tana sake ri'ke murfin kofar tace.

"Bazaki shiga ba saiki bari mai imani idan yazo ya barki ki shiga amma badai niba" jin abinda tace kuma ga halin da yarinyar tata take yasa ta sake kwantar da murya tace "dan Allah 'yata ki barni nakai mata wallahi rashin bata ruwa yana da babbar matsala kuma doctor ne ya fad'a min haka".

"Wallahi bazaki shiga b.................

Bata 'karasa ba taji anja kofar an bud'e 'kiiiiiii wanda ita da take jiki a jingine tai baya luuuu zata fad'i da sauri matar ta ri'ko hannunta tana dawo da ita ta tsayar ta numfashi Baby ta sauke yayin da doctor daya bud'e kofar ya fito ko inda Babyn take bai kalla ba ya wuce a abun sa sosai ran baby ya 6aci musamman da taga Ammar ne abokin Shareef tasan za'ai haka gabadaya hospital d'in nan su biyun nan sune 'yan jin kai wanda baka isa su tsaya su saurare ka ba 'kak'karfan tsaki taja tana d'aukar handbag d'inta data fad'i gefe matar dake tsaye a gabanta ta kalleta tana cewa.

"Kin gani ko shiyasa a rayuwa ake so ka kyautata bakasan wanda kaima zai taimake ka ba gashi ina tsaye ina ta neman alfarma a wajenki kin 'ki yi min amma gashi wani yazo yayi silar fad'uwarki ni kuma na taimaka miki ko ta haka ya kamata ki d'auki darasi ki daina wula'kanci d'an Adam ba abun wula'kantawa bane kinji"? Maimakon Baby ta d'auki maganar da matar ta fad'a mata sai wani banzan kallo data watsa mata tana cewa.

"Dama nace ki taimake nine mai yasa baki barni na fad'in ba taimakon ki bai 'kareni da komai ba sai takaici kar kisa a ranki naji dad'i balle kiyi tunanin zan gode miki mtwwwe taja mata tsaki" wuce tabar gurin tana masifa ji take kamar ta rufe matar da duka da kallo matar ta bita tana jinjina kai lallai ta dad'e bata ta'ba ganin mara tarbiyya irin Baby ba koda ace gidansu ba manya bai kamata ta aikata abinda ta aikata mata ba itama wucewa tai ta shiga ta baiwar 'yar tata ruwa duk da barci ya d'auke tama tun tana kiran ruwan shiyasa ta tasheta ta bata.

Batun baby kam tana barin gurin kanta tsaye office d'in Shareef ta wuce harta rike handle d'in zata murd'a sai kuma ta tuna yayi mata warning kwanan baya cewa karta kuskura ta sake shiga masa office tsayawa tayi tana juya bayanta can take hango shi sun gitta su uku tare da wannan abokin nasa dayai silar ta kusa fad'uwa yanzu da kuma wata bururwa mai glass da takarda a hannunta da sauri tabi bayansu harda d'an gudunta amma bata gansu ba tsaye tayi tana kallon gabas da yamma ko zata hangon su saidai babu alamarsu kaita jinjina tana juyawa ta koma kofar office d'in nasa ta tsaya tasan duk tsiya nan da a tashi ai zai dawo tana so ta bashi ha'kuri ne akan abinda ya faru kwanan baya gashi shi kuma sai yawo yake mata da hankali.

Haka ta wuni batai aikin daya kawota asibitin ba har aka tashi sai a lokacin taga Shareef ya rufo office d'insa ya fito numfashi ta sauke da sauri ta karasa tana cewa "Shareef dan Allah ka tsaya muyi magana" ko kulata baiyi ba har yaje gurin da motarsa take ya bud'e ya shiga ganin datai yana shirin rufewa ta ri'ke murfin motar tana girgiza masa kai tace "haba dan Allah Shareef ya kamata ka saurare ni man" kamar bazai magana sai kuma yace "kina da abinda zaki fad'a min"?.

"Sosai ma nice nake da abun fad'a dan Allah Shareef kayi ha'kuri abinda ya faru kwanaki ka yafe ni nasan na aikata kuskure amma nayi maka alkawari insha Allahu bazan sake makamancin irin haka ba har abada fatan zaka yafe min"? Shiru yayi yana ri'ke da sityarin motar kusan mintuna biyu ya d'auka har ta fitar da rai akan zaice wani abu sai kuma taji yace.

"Ok" yana fad'in haka yaja murfin motar ya rufe ya tada yabar gurin kamar Baby ta d'ora hannu aka tayi ta rusa kuka haka taji wani irin ba'kin ciki ya rufe ta me yake nufi da cewa ok anya Shareef ba so yake yaga gawarta ba ta sani tana matu'kar son sa tana so ta aureshi amma ya kasa tsaya ya fahimci irin halin da zuciyarta ta samu kanta a ciki saboda shi kawai akan 'karamin abu ya d'auke mata wuta data san haka abinda taiwa Nihal zai zama to da ta rabu da ita a wancan ranar ko kallonta bazata yi ba amma ba wanda yasan mezai faru a gaba zata zauna tayi nasari akan yadda zata shawo kansa tunda tana sonsa haka zata yi ha'kuri da duk abinda yayi mata kodan ta samu damar shiga jikinsa ta nuna masa manufarta a kansa huci mai zafi ta fitar tana kallon zanen tayun motarsa kafin ta juya ita ma ta nufi tata motar ta shiga tabar asibitin amma ta saka a ranta saita binciko gidan su gara tasan komai nasa idan ya'ki ha'kuri ya yafe mata saita koma 6angaren mahaifiyar sa duk tsiya idan yaga tana kyautata mata tun kafin ya aureta zai kamu da sonta.mm........................
YUSRAH MUSA ABUBAKAR

ZUCIYAR ALIYU CE.............

@DUTSE JIGAWA
PAGE 21
Karfe takwas da rabi Zainab tana d'akinta tana d'inki Bilki ta banko kofa ta shigo ba sallama tana zuwa ta ri'ke kan keken tana cewa "gaskiya bazai yuwu ba haba wacce irin masifa ce wannan da safe baki barmu munji dad'i ba da rana baki barmu munji dad'i ba da daren ma muna so muyi barci dan jaraba bazaki barmu mu huta ba kamar a kanki aka fara neman kud'i to gaskiya bazai ta'ba sa6uwa ba wallahi dole kisan yadda zakiyi" ta karasa maganar tana sake ri'ke kan keken sosai harda jijjiga kallonta sosai Zainab keyi cike da mamakin ta tace.

"Bilkisu sake min kan keke" a masife Bilki ta sake ri'kewa tana cewa "bazan sake ba wallahi bazan sake ba tun karfe bakwai nake so nayi barci amma dan mugunta 'karar wannan tsinannan keken ya hana ni yanzu kuma nayi magana harda wani na sake miki ban saki d'in ba ki 'kwace daga hannuna" jin abinda tace yasa Zainab mi'kewa ranta a 6ace ta kama hannun Bilki ta 6an6are daga kan keken nata sannan ta tattarata ta had'ata waje ta tura kofar d'akin tasa sakata ta ciki ta koma taci gaba da d'inkin ta.

Bilki kam ganin abinda tai mata yasa bayan ta mi'ke daga fad'uwar datai ta kad'e jikinta komawa kofar d'akin tayi tana dannawa jin ta saka masa sakata ta ciki yasa tace "idan kin cika ke isashshiya ce kuma kin haifu a cikin uwarki ki bud'e min kofar nan na shigo wallahi saina 6a66alla keken nan" jin abinda tace yasa Zainab mi'kewa ta bud'e kofar tana kallon ta tace.

"Na isa harna wuce inda kike zato na dan Allah Bilki indai kin haifu 'yar halak ce ki ta'ba min keken nan yau saidai ki kwana da kumburarran jiki wallahi saina miki d'an iskan duka a gurin nan" baki Bilki ta ta'be tana cewa "wallahi saina ta'ba ki dake ni ki daki masifa duk yadda kike jin rashin mutunci nawa ya dame naki ya shanye ba'ayi budurwar da nake tsoro ba kaf gidan nan ba babu 'yar iskan data isa na raga mata wallahi" murmushi Zainab tai tana jinjina kai tace.

"Ai shiyasa nace ga keken nan idan kin isa ki ta'ba tunda bakya tsoron kowa yau zan nuna miki kalata" tsaki Bilki taja tana juyawa ta fita daga d'akin tana cewa "a tari gaba gamon mu dake bazai Miki kyau ba yau dai kinci sa'a barci🤣 nake ji amma badan haka ba wallahi saina nuna miki niba kanwar lasa bace" d'an karamin tsaki Zainab tayi tana komawa kan kekenta taci gaba da d'inki harta had'a rigar ta d'auko skirt d'in shima ta fara had'awa Sameer yayi sallama yana tsayawa daga kofar d'akinta yace.

"Taso ki kar'ba Zainab zan wuce d'aki nane" mi'kewa tai tana zuwa kofar d'akin inda yake tace "barka da dare Yaya Sameer" kaiya d'aga yana d'auko kayan dake wata babbar leda ya mi'ka mata sannan ya d'auko kwalin indomie itama ya bata da mamaki tabi kayan da kallo kafin ta d'ago ta kalleshi tana cewa.

"Yaya Sameer wannan fa"?.

"Sa'kon kine" da sabon mamaki tace "sa'ko na kuma"?.

"Eh".

"To amma waye ya bani"?.

"A'a kiyi godiya kawai Zainab amma karki nemi sanin wanda ya baki yanzu saboda tsaro ri'ke wannan" kallon hannun nasa tayi taga kud'i yakai wajen dubu ashirin haka ko talati bata kar6a ba ta girgiza kai tana cewa "Yaya Sameer kar kasa na kasa barci man wadannan abubuwan daga ina"? Murmushi yayi yana mayar da kud'in cikin aljihunsa yace .

"Ok tom bari na aje miki kud'in a gurin na idan kin tashi bu'kata saiki fad'a min na baki wadannan kayan da kike gani wani bawan Allah ne ya umarce ni dana siya na kawo miki kyauta" cikin sabon rud'u Zainab tace "wani bawan Allah amma meye sunan sa"? Ta tambaya tana 'kure Sameer da kallo duk tunanin ta ko Yaa sayyadi ne ya bayar a bata amma kuma zuciyarta bata amince shi d'in bane..............

Ji tayi Sameer yace "karki damu ki kwantar da