Follow us on social media

Showing 3001 words to 6000 words out of 28581 words

Chapter 2 - DAN MILLIONAIRE COMPLETE Alkawarin Zuciya by Mrs Al'ameen

zuciyar ka bai dawo daidai yadda yake ba ka fada min matsalarka".


Sauke ajiyar zuciya Al'ameen yai domin maganar dazai fada ba lallai daddyn nasu ya amince ba yace.


"Dan girman Allah daddy ka dube ni da idanun rahma ka tausayawa zuciya ta ka fahimcr cewa danka ya fada cikin jarabtar soyayya kamin maganin damuwa ta".


"Me kenan zanyi maka Al'ameen ka fada min kada kaji shakka niba mami bane babu abinda zai gagara".


"Daddy na roke ka ka duba Allah ka amince min na auri Abni yarinyar nan ta sadaukar da rayuwar ta saboda na samu farin ciki ta kula dani lokacin da bansan kowa ba a London.



Ta musulunta saboda ni ta yarda zata aure ni ta zauna dani sannan mahaifanta basu nuna min kiyayya kamar yadda mami ta tsane taba.


Da tazo gidan nan ta rako mahaifin ta mami ta zage ta ta aibata ta ta kafurta ta sannan ta mare ta amma batai zuciya dani ba saboda tana sona".


Cikin mamaki daddy yace ita Aishan ce ta mare ta ".


"Eh daddy wai tazo har gida zata cinye ni".


Murmushi daddy yai kuma an fada mata mayun 'kiri da 'kiri suke kama mutum su cinye shi yanzu dai me za'ai".


"Daddy abin da za'ai shine zan aure ta ina sonta da ita zan zauna dan Allah daddy ka fahimce ni itace komai nawa banajin zan samu madadin ta".


"Ok yanzu kana so aje nemar maka auren tane "?.


Eh daddy wannan shine damuwa ta ka taimaka min".


Hannunsa daddy ya rike karka damu zan yi kokari akan hakan zamuje london cikin satin nan domin kudi ba sune kwanciyar hankali ba".


Tashi zaune Al'ameen yai ba shiri yana cewa a satin nan na gode daddy Allah ya kara daukaka".


"Amin daddy yace yana kallon yadda lokaci guda fuskar Al'ameen din ta washe da farin ciki".



Lokacin da mami taji wannan maganar kuka ta fashe dashi na bakin ciki tana cewa yanzu alhaji tsakani da Allah aura masa arniya zakai karya fa take bata sallah".


"Shine damuwar ki"?.


Shiru mami tai tana goge idanunta da sukai jawur saboda kiyayyar Abni.

Ganin taki magana daddy yaci gaba inda rashin sallah shine matsalar me sauki ne zata musulunta tunda tana sonshi kuma ba haramun bane danya aure ta".

"Dan haka ranar monday jibi kenan ki shiri za muje london nema masa auren ta kiyi fatan itace alkairi a rayuwarsa".


Hannu mami ta dora akai tana sake zunduma wani ihun cikin burgima tace wallahi bada yawu naba kuma ko kofar gate bazanje ba balle naje wata london gurin shegun arna naje su bawa gunki jini, na".


"Bazai auro min wata baturiya ba saidai ya mutu baiyi aure ba".


"Aishaa" daddy ya fada a tsawace tare da nuna ta da yatsa yace.


"Idan ke bakya sonsa ni ina sonsa kuma na amince ya auri wannan baturiyar tunda itace zabun ransa kece zaki zauna masa da yan mata da kike kawo masa"?.


"Shashancin banza kin girma amma kina shiga daji bakisan kaddara ba na biye miki kina neman kashe min yaro kamar ba kece kika haife shi".


"Saiya aureta idan har matarsa ce saiki dau mataki kuma umarni nake baki ki shirya tafiya ranar monday nan da kwana hudu na gama yanke magana".


Yana fita ta mike da gudu tana shiga part din Al'ameen yana zaune ruwan ya kusa karewa tana zuwa cikin karaji da ihu da yage yage kamar me ciwon hauka ta fisge ledar ruwan tana wurgi da ita sannan ta fadi kasan carpet tana shure shure.



"Tace Al'ameen ka cuce ni nayi asarar haihuwa Sadiq bai taba sani nayi bakin ciki ba balle kuka haka kanwarka Afeeyah daka girmeta da shekaru sosai bata bani wahala ba.


"Amma ka sani kuka na zubar da hawaye saboda kai idan har kana so na yafe maka kaje ka samu daddyn ku kace ka fasa auren wannan banzar yarinyar".


Al'ameen dake mata kallon mamaki ganin yadda take kuka kamar yarinya ya mike tare da dago ta yace mami lafiya wani abu ne ya sake faruwa".


Fisgewa tai tana cewa ban sani ba wallahi Al'ameen nayi asarar haihuwa amma ba lallai kai dana bane ne tunda haihuwar asibiti nai kila an canza min kai dan da na haifa bazai rika wahalar dani haka ba ".


Zaiyi magana ta daga masa hannu babu abinda zakace min baka da wani abu da zaka fada min kaje ka karata" tana fadin haka ta fice a bedroom din.


Typing📲


💰'DAN MILLIONAIRE💰


YUSRAH MUSA ABUBAKAR


Page 07 to 08
Iya tsananin damuwa Al'ameen ya shiga domin bai taba tunanin kiyayyar mami zata sa tace kila anyi mata canjinsa a asibiti lallai dole ya samu daddy koda son Abni zai kashe shi ya hakura".


Fita yai daga part din nasa yana shiga bangaren daddy cikin sallama zaune ya same shi a palor yana duba takardu masu yawa zama yai a kasan carpet yana kallon daddy cikin dauriya dason ganin ya jure yace.


"Daddy na fasa auren Abni na hakura basai kunje ba Allah zai musanya min da mafi alkhairin ta dama ba komai mutum keso ya samu ba".


Batare da alhaji Mustapha ya dago daga kan aikin da yake ba yace " me kake cewa banji sosai ba hankali na ya kasu gida biyu".


Sauke numfashi Al'ameen yai yana cewa daddy na hakura da auren Abni na fasa".


Murmushi daddy yai yana dan kallonsa yace saboda Aisha ko "?.


Shiru yai domin gaskiya badan mami ba babu abinda zai hana shi auren zabin ransa".


Dawowa daga tunani yai jin daddyn na cewa" nace saboda mamin ku. Ka hakura ko"?'


"Eh daddy domin mahaifiya ta tafi min komai mahimmanci tace duk cikin yaran ta nine batai sa'ar haihuwa ba ina wahalar da ita ni kuma banason saba mata na fasa auren amma bazan auri kowacce yarinya ba".


"Ni kuma ban fasa ba Aminu ina nan akan bakana saina baka abinda kake so aure meye baya samarwa dan tana yar wata kasar saiya haramta ka aure ta ka kwantar da hankalinka idan yarinyar nan matar kace saika aure ta ba gida daya zaka zauna da mamin kaba balle kace kana can gurin ka daban".



"Daddy na sani cewa tai idan na aure ta bata yafe min ba".


"Zata yafe maka idan taga abinda auren ya kawo mata kaga bar bata wa kanka lokaci wajen tunani da damuwa ranar monday zamuje London babu fashi".


Sauke ajiyar zuciya Al'ameen yai cikin tunanin ya zai kare da mami baya son hayaniya ko kadan.


Washe gari suna zaune a palor mami ta fito daga part dinta tana waya ganin su a zaune yasa bayan ta gama tace.


"Al'ameen kadau mota yanzu kaje airport ka taho da Zainab munyi waya da hajiya Binta tace min driven ta ba lafiya".



Tun kafin Al'ameen yai magana Sadiq yace amma mami ga direbobi da yawa anan mezai hana daya yaje ya dauko ta yarme iyayi ta fito ta tari motar haya man a kaita gida".


Cikin harararsa mami tace to uban yan shishshigi banyi dakai ba kaiba asibiti zakaje ba meye ya biyo dakai tanan gidan".


"Mami nida gidan mahaifina kice meya kawo ni dan kawai aure yasa nabar gidan".


Bata bashi amsa ba ta kalli Al'ameen tana cewa kaji dai na fada maka ko tana can tana jiranka"?.


"Jiwai tana jiran ka kamar wani driven ta wato wannan yar iskar yarinyar hajiya Bintan ce ta dawo".


Cikin yanayin tambaya Al'ameen yace wace ne yarinyar wai yar gidan umma kanwar mami dai ina take da yar dahar take fita waje".


Daidai sun mike Sadiq yace kai amma Zainab wata yarinya me shegen tsiwa kodan ba a hannun hajiya Bintan ta girma ba tana dangin babanta amma kai da yar uwar ka".


Shiru Al'ameen yai suna tafiya yana tunani amma gaskiya ya manta yarinyar saidai yanzu idan ya ganta.


Tana tsaye tadau wankan riga da wando wanda sunyi bala'in matseta gashi tasa wani dan mayafi wanda dashi gara babu tana sanye da glass .


Sadiq da yake shike driving yace kalli to gata can wani irin kallo Al'ameen ya bita dashi ganin shigar datai arniya sak ba wanda zaiyi tunanin yar musulmai ce.


Tsaki yaja yana fita a motar daidai ta karaso ta zare glass din idonta tana kallon su sai kuma tadan murmusa cikin yanga tace Sadeeq ashe zan iya gane ka tsawon lokaci bamu hadu ba".


"Eh shigo muje" abinda yace kenan domin shima shigar datai ta bashi haushi".


Juyawa tai saitin da Al'ameen yake tsaye tace driver samin kaya a bayan mota kayi sauri nan, da minti biyar na ganni a gida".


Zaro ido Sadiq yai ke driver fa kika ce ya miki kama da driver"?.


Yatsina fuska Zainab tai mezai hana direbobin aiba kamace dasu ba".

Kai Sadiq ya jinjina bai sake magana yace Al'ameen shigo mu wuce".


Katseshi Zainab tai wai dan Allah Sadiq nice zansa kayan cikin mota shi meye amfanin sa".


Banza Sadiq ya mata jin motar ta tashi tsoron karsu tafi su barta yasa dole tasa kayan da kanta sannan ta shiga motar".


Sun danyi tafiya kadan tace gaskiya ne haka nake son driver babu sanya amma Sadiq ina wannan 'kanin naka mejin kannan naji umma na tace yanzu ya zama soja ko"?.


Lallai yarinyar nan ba karamar yar iska bace Sadiq ya. Fada a ransa yana kallonta tta mudubin mota yace.


"Ga miciji ai ba a neman ja ki tambaye shi da kanki".


"Oh shine wannan sorry nace maka driver ya kake".


Babu wanda ya kula ta zuwa wani lokaci tace yauwa na tuna shakka babu sunan ka Aminu na manda'ko😂.


"Dariya ce ta kama sadiq lalli Zainab taci kai amma bari ya kyale ta Al'ameen na daidai da ita".


Cigaba tai ko shekarun baya na tuna ya tsani zuwa kauyen mahaifin ku wata rana zakuje ya fadi a kasa yana burgima shi bazai jeba daddyn ku ya ciro bulala a garden ya zane sh...........'


Wani irin taka burki Al'ameen yai wanda saida ta gwaru da kujera a fusace yace "fita a motar nan".


Zaro ido tai baka karaso ba ga gidan can dan kawai na fadi gaskiiya na tuna maka da baya"?.


Cikin tsawa yace "get lost".

Kallon Sadiq tai ko zai magana taga yayi banza ya dauke kansa daga saitin su dole ta fita daga cikin motar tana daukar kayan ta"".


Wata irinn 'kura ya buleta da ita yaba bawa motar key tari ta kamayi sosai har saida idonta yai ja".

Dakyar ta samu ta daaina barin kayan tai a gurin da sauri ta shiga gidan su tana zuwa ganin ummanta a palor yasa ta fada kanta tana kuka".


Cikin tashin hankali hajiya Binta tace lafiya dota daga dawowa ina murnar ganin ki sai naga kina kuka meya faru ina su Al'ameen din kosun tafi".


Cikin shagwaba tace ba shinee ya ajiye ni a wajen gidan alhaji Faruq ba kuma ya tule ni da ''kura a gaban mutane dan kawai nace masa ya karaso dani gida kayan nawa ma suna can".


Cikin bacin rai hajiya Binta tace kan uba amma wallahi yaron nan baida mutunnci wato ya tule miin ke da 'kura bari zan kira auty Aishan na fada mata".


Kayan hajiya. Binta tasa ma'aikatan gidan suka dauko mata sai bala'i take. Ita kadai.


💃 🎶 By mrs Al'ameen Ahmad ce.


Page 09 to 10
Kamar yadda alhaji Mustapha ya fada haka ce ta faru ranar Monday sukai shiri suka wuce london Afeeya kuma tace gidan Sadiq zata zauna gurin matarshi kafin su dawo sai kuma ta fasa ta tafi gidan kanwar mami hajiya Binta idanuwan mami a kumbure sakamakon kwanan datai tana kuka kamar ranta zai fita.


Da yake Al'ameen yasan gidan kuma saboda kada a samu matsala yasa bai sanar dasu ba Saira kanwar Abni na zaune a tafkeken palon su sai ganin mutane tai cikin mamaki ta mike tana cewa bros kaine sannu da zuwa".


Dan murmushi Al'ameen yai tuna rayuwar da sukai lokacin yana nan cikin yan mintuna tasa aka hada musu kayayyakin ci dana sha na alfarma".


Fafur mami taki shan koda ruwa ne zama ma dan ba yadda zatai ne amma yadda take jin tsanar mutanen nan da wuta zata kone gidan sai tafi kowa farin ciki".


Tambayar Saira yai ina mom domin yasan Abni da daddyn suna gurin aiki.


Sauyawa fuskar Saira tai daga yar walwalar da take zuwa damuwa tace" mom na asibiti bata zama a gida".


Waye baida lafiya "? Ya tambaye ta cikin faduwar gaba.


Kuka ne ya kwace mata tana girgiza kai tace" Abni ce ".


Wata ba'kar hajijiya ce yaji ta kwashe shi lokaci guda idonsa ya rufe luuuu ya tafi zai fadi da sauri Saira zata tare shi mami ta ture ta tana cewa.


"Karki taba shi arniyar banz......


"AISHA" daddy ya fada da karfi cikin fushi yace wato kinzo gidan su ma saikin nuna rashin arziki ko kinga ki kiyaye ni ".


Jijjiga mami keyi tana huci yayin da Saira taja baya daga gareta Sosai cikin jin tsoro".


Da murya a nutse daddy yace" kinga Saira karki damu muje ki kaimu asibitin".


Kai ta jinjina tana shiga ta shiryo tare da dauko key din motarta ta fito suka wuce".


Dukda su mom suna cikin damuwar rashin lafiyar Abni din hakan bai hana su nuna matukar farin cikin su da ganin familyn Al'ameen din ba kuma sun karbe su hannu biyu".


Tambayar inda take Al'ameen yai cikin damuwa mom tace " son Abni tana ICU".


"Mom muje na ganta".


Kai mom ta girgiza babu dama muma basa bari mu shiga balle mu ganta saidai ta na'ura".


Tabe baki mami tai tana dauke kai daga kallon su domin ko ganin su bata son yi".


Haka suka zauna har dare a asibtin ganin lokaci zai kure yasa mom tace Saira kuje gida ki basu masauki gobe sa dawo".


"Ok mom" Saira tace sannan ta dauko su a mota suka dawo gida a ranar Al'ameen bai runtsa ba ko kadan kwana yai akan Sallaya har asuba yana rokon Allah".


Kwanansu uku da zuwa iya gajiya da bacin rai mami tayi bata da buri kamar taga ta dawo gida gashi basa zance tahowa".


Samun alhaji Mustapha tai ranta a hade tace waini sai yaushe zamu koma gida ne kawai munzo garin mutane mun zauna".


Ko karasa kallonta alhaji Mustapha baiyi ba yace sai ranar data warke idan bazaki iya jira ba ga hanya nan".


"Gaskiya bazan jira saita warke ba kamar wasu dangina tafiya zanyi saikun taho".


"Ki gaida gida Allah ya kiyaye amma ki sani bada kudina zaki koma ba ki biya da naki".


Zaro ido mami tai dan akwaita dason kudi kamar me tace" haba alhaji da kudi na kuma dama nice na kawo kaina".


"Oh da wa ya kawo ki gurin nemawa d'anki aure kika zo".


"Nidai wallahi ba ason raina nazo ba gaskiya ka biya min kudin jirgi na tafi gida".


"Aisha idann kinga na biya miki kudin jurgi munyi abinda ya kawo mu muddin baza ki jira muba saidai ki biya kudin jirgi da kanki".



Bakin ciki ne sosai ya mamaye mami ga koshi ga kwanan yunwa dole ta hakura dan bazata zare wadannan mmakudan kudin ta bbiya jirgi ba".


Satin su guda babu wani labari don haka mom da daddyn Abni suka roki alfarma a bari su shiga su ganta ko minti biyu ne".



Tare da Al'ameen suka shiga Abni na kwance akan gado ganin Al'ameen yasa tadan juyo saitin sa muryar ta can kasa tace" Al'ameen kaga halin dana tsinci kaina a ciki saboda rashin ka ko na sani ba tashi zanyi ba inai maka fatan alkairi ka kasance cikin farin ciki Allah ya baka madadi na".


Kai Al'ameen ya girgiza" a'a ki daina cewa haka kece nake so Abni zaki warke muyi rayuwa tare bana fatan na raasa ki tare da mahaifa na nazo domin su karba min auren ki please Abni ki tashi muyi rayuwa me kyau".


Dan lumshe ido tai tare da budewa tana kallonshi ta riko hannunshi muryarta kamar bata me jinya ba tace.



"kada ka damu zaka kasance cikin farin ciki koda babu ni bazan taba rabuwa dakai ba muna tare bazan taba barin ka ba".


Tari ne ya kama ta harda jini ke fita a bakin ta da sauri su mom suka yo kanta kallon su tai bata ce komai ba".


Al'ameen wanda tashin hankali da rashin nutsuwa sun mamaye shi ya sake rike hannunta wani zobe ne a yatsan ta tacire shi tana baiwa Al'ameen .


Ganin tai shiru yasa da karfi Al'ameen ya kira sunan ta bude ido tai tana murmushi a hankali ta furta" I LOVE YOU AL'AMEEN".


Daga haka bata sake cewa komai ba sai kallon da yaga ta koma yi masa wanda bai gamsu dashi ba jin ta sake hannunsa yasa yace Abni Abni Abniiiiiiii da mugun karfi yaja sunan.


Ji yai daga bayansa mom ta fashe da kuka domin shakka babu Abni ta rasu".


Ganin dayai daddyn ta ya matso ya lullube ta yasa hannu zai bude rike masa hannu daddyn yai yana girgiza kai".


Wanda hakan ya tabbatar masa da mutuwa tai a take ya fadi a gurin ya suma😢😭 .


[23/09/05 12:44pm] Typing📲


ANNURI W ASSOCIATION
Home of hospitality and harmony


YUSRAHMS CE😜😍.

Page 11 to 12
Fitowar Afeeya kenan zata tafi makaranta Zainab tasha gabanta tana cewa ke dan rainin hankali wato ke isashshiya ko maza ki koma saikin gyara bedroom din idan ba haka ba ki hakura da zuwa makarantar".



Wani kallo Afeeyah ta mata. cikin rainin hankali tace Allah ko mami da gaske kike"? To bazan gyara ba makaranta zanje ba irin kice me zaman kashe wando a gida ba zan fita idan kin isa ki dakatar dani ko kidau mataki".


Da kallo Zainab ta bita lallai yarinyar nan zaki ci ubanki bin bayan ta tai da sauri daidai Afeeyah ta tashi mota tasha gaban motar.


Afeeyah bata fasa ba tayo kanta zata bigeta da gudu Zainab tai tsalle tana fadawa cikin fulawoyi😂🌻🌷🍁 ".


Dariya Afeeyah tai tana lekowa ta glass din motar tace au dama zaki gudu dakin tsaya saina maida ke gurguwa nakasashshiya nasa ki zama mabaraciya a cikin gari amma a juri zuwa rafi mu zuba nida ke dan halas ka fasa".


Tana gama fadin haka tai kofar gate tsaki Zainab tai tana mikewa ganin yadda ta taba farar rigarta domin ba a dade da yiwa flowers din bayi ba".


Tana komawa ciki hajiya binta na fitowa ganin kayanta a bace yasa tace daga ina meye ya bata miki riga"?.


Cikin takaici Zainab tace waye zaimin haka idan ba wannan shegiyar yarinyar Afeeyah ba".

Toke meye damuwar ki da ita kuna yan uwa amma jinin ku bai hadu ba".


"Yo umma dan ubanta waye jakin ta da zata kwanta da safe bazata gyara gado ba".


"Ok akan haka ne amma dai aiba wani ne ya hana kiba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login