Follow us on social media
Showing 21001 words to 24000 words out of 28581 words
Chapter 8 - DAN MILLIONAIRE COMPLETE Alkawarin Zuciya by Mrs Al'ameen
burkitaccen kiss me dumi wanda yasa ta dauke numfashi yace.
"son wa kuwa Zarah ki gode wa Allah domin kin maye min gurbin Abni a zuciya ta ina sonki".
Rungume shi Fati tai tana kuka tace" Allah ya mata rahma amma kafi karfin yin soyayya dani".
"Waye ya fada miki kece kika dace dani duk duniya bani da tamkar ki kina da babban matsayi a zuciya ta tun kafin na fahimci cewa sonki nake".
"But do u luv me".
Kara kankame shi tai cikin farin ciki har yana jin sautin murmushinta akan idonsa beauty point din ya lotsa tace.
"Nima ina sonka son gaske bana hada ka da kowa kaike da mukullin zuciya ta fatana mu kasance tare har abada".
"Zamu kasance tare Zarah kece numfashi".
Dagowa tai tana kallonsa ranta fari tas zuciyarta cike dajin dadi fuskarta da annuri.
Zatai magana ya katseta da cewa" muje ina son mu gana๐".
Fuska ta shagwabe tana komawa kalar tausayi tace" Allah nina gaji kafa na ciwo take".
"Wanda kake so baka gajiya dashi Zarah dan haka muje na cewa mami zan koma mata da tsaraba kinga dole na dage".
Yana fadin haka ya dauketa yana barin palon cikin rad'a ya mata magana a kunne wacce tasa da sauri ta kifa fuskarta a kirjinshi tana dariya kasa kasa.
๐ Mrs Al'ameen Ahmad ce.
๐ผ๐น๐ผ๐น๐ผ๐น๐ผ๐น๐ผ๐น๐ผ๐น
Page 32 to 32.
Kamar yadda Al'ameen yace wa mami saida suka shafe tsawon wata takwas harda sati biyu a bangkok saidai sunje london ziyara gurin iyayen Abni".
Wanda suka samu kyakkyawar tarba kamar su maida su ciki haka suke nuna musu kauna da basu kulawa har ranar da zasu dawo Nigeria.
A ranar da suka dawo mami ta sako Zainab gaba da akwatinta ta rakota tayi sa'a ta samu Al'ameen a gida haka ta balbale shi da masifa kamar zata rufeshi da duka.
Sannan ta juya kan Fati dake gefe tai mata zagi na tsamar nama harda kakannu saida suka samu rabonsu.
Fati tayi kuka tayi bakin ciki batasan me taiwa mami ba da bata kaunarta sam".
Kwanan su goma da dawowa Fati tana part dinta a kwance bata da lafiya Zainab dake palor zaune tana jiran yar aiki ta gama gyara dinning tabar gurin.
Da sauri ta mike tana waige-waige ta nufi dinnig din tare da bude cooler ta fara zuba wani abu.
Al'ameen na tsaye a bakin kofar palon yana kallonta saida ta juya zata tafi ta ganshi cikin razana da rashin gaskiya tace.
"Harka dawo sannu muje kai wanka ga abinci na jiranka da kaina na shiga kitchen na shirya maka shi".
Karasowa yai har inda take yana rike hannunta ya mayar da ita gurin dinning din yace.
"Me kika zuba a ciki".
muryarta na rawa tace mezan zuba kawai gyara murfin coolan nai saboda karta huce.
Bude wa yai tare dasa mata spoon a cikin abincin ransa a hade sosai yace.
"Eat".
Zaro ido tai jikin na kakkarwa ta soma jada baya ganin tana shirin guduwa yasa ya cafko ta yana matseta sosai a jikinsa ya debo abincin ya danna mata da karfe dole saida ta hadiye.
Ihu ta kurma domin tasan guba ta zuba a ciki bai damu ba ya sake deba ya cusa mata saida ya bata spoon biyar sannan ya ture ta daga jikinsa yana mikewa ya barta a gurin.
Da sauri ta mike tana shiga part dinta ta wuce toilet ta fara amai cikin galabaita ta fito dakyar ta iya lalibo number mami ta kirata tana kuka".
Mami na dagawa Zainab tace mami please karna mutu kizo ki kaini asibiti yanz...........
Bata karasa tari ya rufe ta sakin wayar tai tana durkusawa a gurin.
Mami dake cewa hello zainab kina jina meke damunki ina Al'ameen din"?.
Jin shiru ba amsa yasa mami kallon wayar ganin ta katse a firgice ta sa'bi mayafi tana fita taiwa driver magana cikin gaggawa ta shiga mota suka tafi.
Lokacin da mami ta samu Zainab cikin mugun hali kwance farin abu na fita a bakinta.
Salati mami keyi ta dagota da sauri amma tai luuu ta koma ihu mami tai tana kuka ta ciccibe ta suka fita".
Saka ta a mota tai suka wuce asibitin Sadiq domin ya dubata Sadiq yayi mamaki abinda ya gani tattare da Zainab din.
Wanda bayan ya fito daga dakin da aka kwantar da ita ya koma office dinshi inda mami ke zaune tana jiransa.
Ganin ya shigo da sauri ta mike tana tambayarsa "Abbakar yaya jikin nata meke damubta"?.
Zama yai cikin nazari yasan Fati bazata zuba mata guba ba balle Al'ameen shine abinda yake bashi mamaki toshi yanzu mezai cewa Mami na damun Zainab?.
Katse masa tunanin da yake mami tai da fadin "Sadiq ka bani amsa mana, ko wani abune ya sameta"?.
Kai Sadiq ya girgiza yana cewa "a'a ki kwantar da hankalinki na mata aiki zata samu lafiya da yardar Allah saidai ban gama binciken abinda ke damunta ba".
"To amma Sadiq wannan farin abun dake fita a bakinta fa".
"Eh mami harda shi zan bincika idan na tattara bayanan zan fada miki".
"Shikenan to Allah ya bata lafiya".
Afeeyah kam najin batun tasan akwai wata a kasa gashi Al'ameen yace ta dawo gidansa gurin Fati domin har lokacin bata gama warwarewa ba.
Sadiq suna zaune tare da Al'ameen yake tambayarsa "kai Al'ameen ya akai Zainab taci guba a cikin abinci ko taje wani gurin ne"?.
Kallon Sadiq Al'ameen yai "no ko daya a gidan taci".
Zaro ido Sadiq yai to waye yasa mata kenan"?.
"Babu kowa ita ta zubawa kanta".
"Kamar ya bayan tasan abin cutar da ita zaiyi zata ci please Al'ameen dan Allah ka fada min gaskiya kodai kaine ka zuba mata"?.
"Haba Sadiq akan me zan bata guba taci dan kawai bana sonta kka yarda itace tasa abarta da kanta".
Sadiq yace taya kenan wanne tabbaci kake dashi ko ka ganta lokacin data zuba din"?.
"Kwarai ina tsaye a kofar falo ta zuba data juyo ta ganni kasan me tace min"?.
Kai Sadiq ya girgiza.
Al'ameen yaci gaba "wai sai tace ga abinci ta gama shirya min dama danni ta shiga kitchen da kanta ta dafa shI saboda ni".
"dana tambayeta me ta saka a cikin abincin sai tace babu da tana da gaskiya da nace taci sai taci amma jikinta yana rawa taso guduwa".
"Ni kuma na riketa na dura mata spoon biyar kaga nine take shirin kashewa dan haka bazan mata uziri ba"'.
Kai Sadiq ya jinjina lallai tayi kuskure amma kasan mami baza ta yarda ba "?.
"Na sani".
Sadiq yace to kaje ka dubata kafin ka wuce".
Mikewa Al'ameen yai yanaa kallon Sadiq yace "Bana bukatar ganinta Sadiq ni dama gurinka nazo muyi sallama dan haka na tafi".
Mikewa shima Sadiq din yai yana cewa to Fatin kuma fa bakace batajin dadi ba"?.
"Eh Afeeyah tana gurinta".
"Ok muje na maka rakiya Allah ya kiyaye saika dawo".
"Amin Sadiq dan Allah lokaci zuwa lokaci ka rika zuwa kana duba Zarah".
"Ok ba damuwa daddyn baby za'ai yadda kace" fita sukai ya masa rakiya sannan ya dawo".
Mami data koma gida haka takai karar Al'ameen gurin daddy domin ita batasan ma baya gari ba.
"Yanzu alhaji tsakani da allah abinda Al'ameen yake ya kyauta kenan ka duba yarinyar Zainab ba ta da lafiya kullum ina asibitin amma bai taba lekowa ya duba jikin taba".
Wani kallo Alhaji Mustapha ya mata domin yasan komai tun ranar da abun ya faru Al'ameen ya kirashi ya sanar dashi.
Ganin irin kallon da yake mata kuma bai tanka zancenta ba taji gaba.
"Gaskiya alhaji kanada abin mamaki nace maka ga abinda ya aikata amma saikai burus dani, kana min wannan kallon kamar zaka dake ni saboda na tabo dan lelenka kodan bakason a fadi laifinsa tunda lu'u lu'un zuciyar kane"?..
"Aisha to me kikeso nace meye nawa a ciki kece silar gurbacewar komai kuma laifin kine tunda ke kika 'kulla komai ni babu ruwana a cikin wannan al'amarin".
"Abinda zaka ce kenan alhaji a tunani na zakai masa fada ka nuna fushinka ai Zainab dince ta dace dashi shiyasa na dage ya aureta domin auren 'kwarya tabi 'kwarya na musu".
Kai daddy ya jinjina yace" to dakyau ai kinyi musu ga sakamako nan na biyo baya kiyi addu'a abin ya tsaya iya haka".
Mikewa yai zaibar gurin da gudu mami tasha gabansa tana huci tace" wallahi alhaji nagaji bazan yarda ba domin yanzu kam na gane kaine ke shiga tsakaninsu ka hana su zaman lafiya duk wata kitimurmura da fitina kaine kake shiryata".
Cikin tsananun mamaki daddy ke kallon tsaurin idon mami dake fada masa duk abinda yazo bakinta".
Ganin tana shirin sake magana ya daka mata tsawa wanda a firgice ta matsa daga gabansa domin iya tsahon rayuwarta dashi bai taba mata tsawa ba saiyau".
Cikin bacin rai ya nunata da yatsa yana cewa" babu shakka Aisha yau kin sake tabbatar min da baki da tunani kuma kinsamu gushewar hankali kamar ki ace har yar bakida hankali kinyi asara bari kiji bazan dau wannan shashancin naki ba ina mai baki shawara ki gyara bar ganin mun dau shekaru tare ga zuri'a hakan bazai hana idan kinyi ba daidai ba nadau mataki a kanki".
Mami datai tsalle ta koma gefe guda tun sanda ya mata tsawa jin abinda yake cewa yasa ta dafe kirji tana kallon wani irin bacin rai a fuskarsa wanda bata taba gani ba tace.
A
"Wayyo Allah ni Aisha wannan wacce irin kaddara ce ta sameni alhaji da muna zaune lafiya tun daga lokacin da Al'ameen yazo da bidi'ar sa ya nuna yana son auren baturiyar nan alhaji ka fara juya min baya".
"Amma banyi dace ba haihuwar Al'ameen batai min rana ba nayi asarar haihuw...'.....
Katse ta daddy yai jin tana neman dorawa Al'ameen alkaba'i yace "Aisha idan kika karasa yau saina baki mamaki dan zanyi abinda bakya zato".
Kuka mami keyi na bakin ciki da kuma rudewar abinda daddyn yace tana zama tace" na shiga uku na lalace".
Jinjina mata kai dady yai alamar batai karya ba ta fadi gaskiya yace" zadai ki shiga ukun ki lalace din kamar yadda kika fada idan har baki gyara halin kiba" bar mata palon yai ya shiga part dinsa.
Page 33 to 34.
Sati uku da faruwar haka aka sallamo Zainab daga asibiti mami taci gaba da kula da ita a gida har ta karasa warwarewa".
Suna zaune a falo mami ta tasa gaba da tambaya" wai Zainab meke damunki ne kwanan baya Sadiq yaki fada min komai yace tunda kin warke shikenan"?.
Kuka Zainab keyi tana kallon mami tace" mami Allah neyai ba gawata zakije ki tarar ba da sauran kwana na a gaba".
"Eh meya faru"?.
Cigaba Zainab tai "mami wannan shegiyar yarinyar yar kauyen nan wai ta shigo birni ta waye itace ta zuba min guba a abinci naci bansani ba".
Zaro ido mami tai "guba ta baki wato kashe ki take sonyi ta zauna ita kadai a gidan ko aiko bata isa ba koda uwar ta take yawo tashi muje yau saita gane kuren ta".
Mikewa Zainab tai tana dauko mayafi suka fita ko driver daya zo mami tace bata bukata da kanta tai tukin zuwa gidan.
Suna shiga ganin bata palor yasa mami shiga part dinta dama tana wuya da ita akan dawowa gidan da Afeeyah tai gashi alhaji yace bazata koma ba sai Al'ameen ya dawo.
Afeeyah bata nan ta tafi makaranta ita kadaice tana gado a kwance sakamakon kanta dake mata ciwo.
Mami ta banka kofar da karfi ta shiga ganinta kwance tana bacci yasa ta yaye bargon tana sakar mata wani zazzafan duka tace.
"Tashi matsiyaciya kin samu guri wato kura ta mutu ko"? To baki isa ba gata ta dawo".
A firgice Fati ta farka cikin magagin bacci ganin wacce ke tsaye a kanta yasa ta wartsake a zabure tace.
"Mami kece"? Sannu da zuwa".
Cikin tsawa mami tace sannu da zuwan ubanki munafika annamimiya mai hana zaman lafiya yau sai naci uwarki a gidan nan".
Mamaki ne ya kama Fati muryarta na rawa tace" mami meya faru wani abu na miki"?.
'Dauketa da mari mami tai a fusace ta fincikota ta soma janta tana cewa "uban maye baki ba ni kike tambaya me kika min zaki gane kurenki yau saikin gwammace mutuwa da rayuwa".
Tana zuwa palor da ita ta kifa ta tana kallon Zainab tace "me kike jira fara abinda ya kawo mu ki lakada mata dukan mutuwa".
Kanta Zainab tai tana tirmishe ta da dukkan karfinta ta rufe ta da duka ta ko'ina mami na tsaye tana kallo.
Dakyar Fati ta samu ta fisge da gudu ta fita daga palon yayin da suka rufa mata baya "
Daidai me gadi ya budewa Al'ameen kofa ya shigo Zainab ta shake wuyan Fati'.
Ko kashe motar baiyi ba ya fito Afeeyah ma dawowarta kenan taga abinda ke faruwa cikin sauri ta kira daddy da kukanta ta sanar dashi".
Hankali tashe Al'ameen ya nufi inda suke yana zuwa wani gigitaccen mari ya sakarwa Zainab wanda azaba tasa da sauri ta saki wuyan Fati tana dafe kunci ta zunduma ihu.
Cikin bacin rai yake kallon mami wacce ke aika masa da sakon harara yace".
"Mami me kenan kika aikata haka kina kallo a gabanki wannan jakar yarinyar zatai kisa".
Wani razanannan kallon 'kiyayya mami kebin Fati dashi tace" ga babbar jaka nan a gabanka mara tarbiyya ita da yake goyon bayanta kake datai nufin kasheta ta zuba mata guba cikin abinci ai baka kula ba".
"Itance ta zubawa Zainab guba cikin abinci"?.
"Eh ita din karya akai mata"?.
Kallon Zainab yai cikin bacin rai yace" ke kuma kinyi sanadin aurenki na sake ki" sannan ya juya gurin mami datai mutuwar tsaye yace.
"Kenan mami shine dalilin da yasa kika sakota a gaba tazo tadau fansa bayan bakisan komai game da hakan ba bata da lafiya yanzu da kikasa take dukanta idan ta kashe mata d'a a ciki fa"?.=
" 'Da kuma kana nufin ciki ne da ita kome"? mami ta fada tana dafe kirji idonta kamar zasu fito waje
Bai tanka ba sai hannu daya rikewa Fati zaibar gurin da ita kukan kura mami tai tana fisgo ta tace.
"Wallahi karya ne baki isa ki haifa min jika ba yau saina 'barar da cikin nan".
Duka ta sakar mata a ciki harda naushi wanda Fati ta saki 'kara tana faduwa kasa.
Daidai shigowar daddy a rude Al'ameen ya durkusa yana dagota kuka Fati keyi sosai ta rike cikin ta.
Al'ameen na ganin daddy ya mike da sauri ya rungume shi cikin kunar rai da radadin abinda mamin ta aikata yace.
"Daddy mami ta kashe min d'ana ina son baby na amma ta raba ni dashi".
Cikin nutsuwa daddy yace" Al'ameen ka saurar.....
Shiru yai jin Al'ameen ya tafi luuuu zai fadi yasa yai saurin tare shi yana dago fuskarsa ganin suma yai ya cewa Afeeyah maza ta dauko masa ruwa.
Da gudu Afeeyah ta shiga cikin gidan Kasa magana daddy yai tsabar tsananin fushi sai kallo me ma'anoni da yakewa mami wacce ke tsaye gefe duk ta rikice.
Ruwan Afeeyah ta kawo masa ya shashshafa masa sannan ya kira Sadiq cewa ya turo motar asibiti guda daya.
Harda Sadiq din aka zo ganin haka harda mami a gidan ga Zainab tana kuka yasan ba kalau ba.
Sa Al'ameen sukai a mota Afeeyah kuma da Fati suka shiga motar daddy suna fita daga gidan aka bar iya mami da Zainab tsaye'.
Dora hannu Zainab tai aka tana rusa kuka tace "na shiga uku shikenan mami Al'ameen ya sakeni wallahi ina sonsa".
Tabe baki mami tai ke kada ki wani damu tunda kindau fansa ga kuma na kashe shege ko shegiyar yarinyar dake cikinta ai komai yayi duk wani mataki da zasu dauka aikin banza ne burina ya cika bazan ma koma gida ba yau saboda alhaji yadau fushi bansan mezai faru ba muje gurin Binta" mota suka shiga suma suka bar gidan.
Sosai Sadiq ya duba Fati duk abinda ya dace ya mata kuma Alhamdulillahi babu abinda ya samu babyn.
Sosai daddy da Afeeyah sukai murnar jin haka kuma suka godewa Allah.
Kwanan mami uku a gidansu Zainab bata koma ba saboda tsoron haduwarta da daddy saiyau ta shirya taje asibiti gano Al'ameen.
Tana shiga dakin ta ganshi a zaune fati na gefenshi wata uwar harara ta wurga mata tana cewa.
"To sarkin kinibibi mahaifiyarsa tazo saiki fita ki bamu guri zanyi magana dashi kinzo kin gurbata mana zama kin zama ba'kar ashana fita nace me idanun mayu kosai kin lashe min tawa kuruwar nima kamar yadda kika lashe tasa mayya kawai". ?
Mikewa Fati tai cikin takaicin maganganun da mami ke fada mata ta fita waje tana share hawaye haduwa sukai da Sadiq ganin tana kuka yace.
"Zarah lafiya ina zakije ko wani abune ya samu Al'ameen din"?.
Kaita girgiza" babu komai gida zan tafi".
"Amma Zarah meyasa? ki bari sai dare mana".
"Mami tazo itace zata wuni a wajensa".
Kallon tsaf Sadiq ya mata haba shiyasa take kuka yasan da dalili.
"Ok muje na kaiki to"fita sukai domin ya mayar da ita yana kuma sake bata hakuri.
Page 35 to 36.
Fati na palor a zaune bayan Sadiq ya ajiyeta ita kadai tai shiru ta nutsa cikin tunani da mamakin wacce irin 'kiyayya mami ke mata abin ya wuce ma hankalinta.
Jin karar bude kofa yasa ta dago mami ta gani ta shigo jikinta ne ya soma rawa kamar taga hallaka.
Zama mami tai tana kallonta fuska babu wasa tace" ba wata tsiyar ta kawo niba na baki minti biyu ki shiga ki tattaro kayan daud'ar ki kibar gidann nan yadda kikai silar fitar Zainab to kema ya zama haramiyarki saidai ya auro wata yasa".
Hawaye suka gangarowa Fati da sauri ta goge tana juyawa ta shiga part dinta bata dade ba ta fito mami na zaune tana kad'a kafa ganin ta fito yasa ta mike tana sakata gaba da, tsinuwa suka fita harabar gidan.
Karbe key din gidan tai a hannun Fati sannan taiwa driver umarni cewa.
"Ga wannan bagidajiyar ta nuna maka hanyar kauyensu ka mayar da ita yau sai kwanan tabarma cikin 'kunci da zafi ba a.c sai ai ta fama da mafici daula kinyi bankwana da, ita".
Tana gama fadin haka ta shige motarta ta fice daga gidan Fati na kuka ta shiga mota bangare guda tana farin cikin barin masifar mami datai.
A ranar Al'ameen yabar asibitin Sadiq ne ya kaishi har gida sannan daya huta ya tafi nasa gidan.
Karfe goma daidai Al'ameen yace zai tafi gidansa tari mami batai masa ba balle ta nuna masa cewa ta koreta.
Tana kallonsa ya fice daga palon dariya tai tana cewa "hummm yaro man kaza ai kaida wannan shegiyar yarinyar har abada je ka dawo ina daidai dakai saika saketa".
Kamar an jefo Al'ameen haka mami ta ganshi murmushi tai tana dauke kanta daga saitinsa tace "a'a me kuma ya dawo dakai"?.