Follow us on social media

Showing 6001 words to 9000 words out of 28581 words

Chapter 3 - DAN MILLIONAIRE COMPLETE Alkawarin Zuciya by Mrs Al'ameen

kece kikai ra'ayi" .


"Allah ni umma bana son yar aiki tana shiga daki na tana kallon asiri na".


"Yayi masu asiri karki sake cewa ta gyara miki gado bansan shashanci".


Cikin jin haushi Zainab ta mike tana 'ku'kuni tabar palon hajiya Binta data bita da kallo tace humm Zainab kenan indai Afeeyah ce tana daidai dake".


Kwana Al'ameen yai a sume baisan inda kansa yake ba sosai daddy ya shiga damuwa mami kam suman Al'ameen bai d'ara taba saima wani irin farin cikin data tsinci kanta aciki na muutuwar Abni din ji take kamar ta taka rawa🙊🙄.



Wanda dole sai a asibitin suka baro shi domin bai dawo hayyacin saba Abni kuwa tun jiyan akai mata sutura😢.


Abuh da 'kawayen ta suna zaune a dandali suna musu akan samarin 'kauyen suka hango Fatima tsaye a 'karkashin wata bishiya tana dariya".


Rabi tace lah Abu ga hegiyar gidan ku can tana dariya ita kadai kamar me aljannu".


Abu data kalli gurin tace barni da yar iska tunda bata da samari dan ta fini kyau a banza".


"Ahayye ji tsinannun munafikai wato kun zauna kuna gulmar 'kawata ko inji uban waye ya fada muku bata da saurayi ita data fi kowa sa'a ma tunda Sa'adu ne yake sonta dan gidan me gari".


Juyawa sukai inda ake maganar suka ga Asabe tsaye da itace a kanta alamar gida zataje daga gonar baban su take".


'Duuuu sukai kanta zasu rufe ta da duka ta sauke icen tana zaro guda daya tace naga hegiyar da zata taba ni saina fasa mata kai".


Duk tsayawa sukai cikin huci Abu tace idan kin isa ki aje itacen mana wallahi saina fasa miki baki".


Aje itacen Asabe tai tare da shakar wuyan Abu wacce batai zato ba tana cewa" na aje da kina nufin dan kina tare dasu yasira bazan iya dukan kiba zanji tsoronki".


Idon Abu sun fitfito sakamakon Asabe jibgegiya ce dakyar ta samu su Balki suka babbare hannun Asabe daga wuyanta".

Tari ta kama yi babu kakkautawa kamar zata shide Asabe data dau kayanta tace nan gaba ki sake kawo min raini saina kusa kahe ki shashasha".


Saida Asabe ta tafi sannan rahma ta samu bakin magana kiyi hakuri Abu bamusan zata shake kiba amma nan gaba zamu shigar miki😹😀".


Tsaki Abu taja ke dalla matsa gefe matsoraciyar banza duk yawan ku mutum daya ta gagare ku".


Ihu suka sa mata suna wakarsu ta dandali suka ce dama waye ya tsokane ta tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa ke duka.


Mikewa Abu tai a fusace tana kallonsu tace kada hegiyar data sake kula ni a cikin ku tsinannu kawai".

Dariya suka kwashe da ita suna tafawa to sai me dan mu daina kula ki wata uwar kike bamu.


Daukar fantekar abincin ta Abu tai tana barin gurin dama a wuya take domin tayi kwashe ilya baizo ya sayi abincin ba".



Mrs Al'ameen Ahmad ce


Page 13 to 14.
Satin Al'ameen guda aka bashi sallama ya dawo gidan su Abni nan sabon ciwon sonta ya bude babi ganin da daddy yai ba warkewa Al'ameen zaiyi su dawo Nigeria ba yasa yace wa su mom kawai zasu koma gida".


Anan daddyn Abni yace mr Mustapha mezai hana ka amince a bashi 'kanwarta Saira".

Al'ameen dake gefe tun kafin daddy yai magana yace a'a daddy na hakura bazan yi aure ba a rayuwa ta".


"Me yasa my son? da Abni da Saira daya ne"?.


Kai Al'ameen ya girgiza yana cewa" daddy bazan iya auren Saira ba badan bana son hada jini daku ba dan Allah ka fahimce ni aure ya fita a raina".


"Shikenan son ba komai na fahimce ka" alhaji Mustapha ya kalla cikin fara'a yace babu komai ai muna tare mun zama dangin juna Allah ya tsare hanya yasa kuje gida lafiya".

.

Anan mami ta gane cewa da gaske Al'ameen yake ashe gidan su Abni musulmai ne amma itafa duk da haka gara da Abni din nan ta mutu hankalin ta ya kwanta yanzu d'anta zai dawo daidai.



Sosai alhaji Mustapha ya tausaya musu kuma ya sake yi musu ta'aziyyah da godiya akan abinda sukai musu "gaskiya kuna da karamci mun gode sosai Jonah mu zamu tafi".


Har airport sukai musu rakiya sannan suka sake yin ban kwana da juna. Wanda Al'ameen baisan lokacin daya rungume Jonah ba hawaye na zuba a idonsa".


Mami taji haushin rungumar dayai masa Allah-Allah take su tafi kamar tana kan 'kaya dakyar Al'ameen ya saki Jonah suka shiga jirgi domin dawowa Nigeria.



Mutuwar Abni hatta Sadiq da yazo gidan washe garin da suka dawo mutuwar ta taba shi wani irin mugun tausayin dan uwan nasa ne ya kama shi".


Yace" Al'ameen kayi hakuri dan Allah kada kasa damuwa aranka ka zama musulmi me daukar kaddara da cinye jarrabawarka Allah ya canza maka da mafi alkhairin Abni a rayuwar ka".


"Amin" kawai shine abinda Al'ameen yace dan bai cika magana sosai ba Afeeyah tayi kuka sosai domin ya taba bata wayarsa sunyi vidio call da Abni kuma sun saba da ita sosai".


Tana kwance akan kujera tai ruf da ciki idonta a rufe kamar me bacci saidai zurfi kawai tai cikin tunani mami dake tsaye a kanta tana kiran sunan ta .


Ganin bata amsa ba yasa afusace ta sakar mata duka wanda a razane ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya me karfi tace " mami lafiya".


Tsaki mami tai tana cewa wato kema ashe sakarya ce ban sani ba ko dan ubanki wannan yarinyar dangin kice zaki dorawa kanki masifa kullum kina cikin tunani wanda kila koni na mutu bazaki damu haka ba".


Hade rai Afeeyah tai tana kau da kanta gefe cikin takaici tace mami ko makiyin kane ya mutu jikinka yana sanyi balle Abni me ta tare miki wanda tabar duniyar baki daina ambaton taba".


"Kwarai Afeeyah zage ni zamani ne yaya su zagi iyayen su kwalliyace duniya tazo karshe dan jakin ubanki har tambaya ta kike me tai min ta kusa kashe min yaro ta mutu ma ban huta ba kema da baki je ba gashi nan ta hada da kurwarsa da taki ta tafi dasu lahira meye na bata lokacin ki wajen tunanin ta kome zakuyi ba dawo wa zatai ba".


Kai Afeeyah ta girgiza batare data sake magana ba Zainab ce tai sallama da dumemen akwatin ta bayan ta driven gidan sune daya kawo ta dauke da wani akwatin.


Cikin mamaki Afeeyah ke kallonta yayin da mami ta washe baki cikin murna tace tun shekaran jiya da Binta ta kira ni tace zaki zo kimin kwana biyu nake zuba ido saiyau sannu da zuwa".


"Yauwa mami ina kwana Zainab tace tana zama kujeran dake facing din Afeeyah a fakaice ta nuna Afeeyah da yatsa tana maganar kurame".


Tsaki Afeeyah taja cikin tsanarta ta mike zata bar gurin mami tace ke Afeeyah ja akwatunan nan ki kai mata su part din ki acan zata zauna cikin daya daga bedroom din part din".


Matukar takaici ne ya kama afeeyah har bata san sanda hawaye ya zubo afuskarta ba amma ta goge tana rike hannun akwatin ta wuce kamar yadda mami ta umarce ta".


Zaunar da Zainab mami tai tana cewa kinsan me yasa nace ki dawo gidan nan da zama "?.


Kai Zainab ta girgiza mami taci gaba babu komai zan fada miki ba yanzu ba wani aiki zaki min".


Daidai Afeeyah ta dawo tadau dayan akwatin Zainab tace hay madam kidan hada min ruwan wanka no hot no cool".


Cikin bacin rai Afeeyah ta juyo muryarta da fushi tace ko kinfi uwarki kokari baza ki samu abinda kike so ba ni ba sa'arki bace nafi karfin yi dake jaka kawai".


Zanci uban ki fa Afeeyah jimin shashashar yarinya".


Mami ta fada tare da kallon Zainab tace rabu da ita dama fushi take bari zansa a hada miki yanzu".


Afeeyah na shiga bedroom dinta ta fada kan gado tana fashewa da kuka tace" ya Allah kaine ka fimu son Abni ka karbi kayar ka kayi mana canji da mafi alkhairin ta ka tausayawa dan uwana ka bashi mace ta gari me share hawayen mijinta".


Hayaniya ce sosai ke tashi da shewar mata a gidan su Abu domin anzo nemawa ilya aurenta.


Lami makwafciyar su dake duba kayan da komai kala bibiyu ne ta rafka gud'a kamar zata cire hancinta tace.


"Kai masha Allahu Allah yasa Jamila ta tayi 'kashin arziki kamar Abun ki Saude ni ina Salamatu ne".


Saude dake rausaya kai irin uwar 'yar nan tace wai ta tafi gidan su tun safe munafika".


Aliya ta amshe da cewa ba wani bakin ciki take saboda 'yarta zatai kwantai tunda dame Abun ta fita yan watanni ne".


Gadoji tace humm aiko bakin ciki zai kashe ta don tunda nake ban taba ji ance ga wani yana san fatin taba inaga bakin jinin daga sune".


Mukam biki zamusha mu gwangwaje matsalle me kalangu zamu gayyato yazo ya buga mana gangar cahiya😂🙉.


Laraba tace ni kuma hankalina be kwanta da fitar Salamatun nan kar muje munna nan mun bude baki da hanci tana can tana gunbudowa Abuwa asiri".


Zaro ido Saude tai tana dafe kirji tace Allah ko 'kawata har kinsa naji nima nawa hankalin ya tashi".

Tsomo baki tabawa tai to meye muma sai mu tashi tsaye ko taki ko taso aure sai Abu nada 'ya'ya Fatima bata samu mashinshini ba ehe🙄.


"Kunga mubar wannan maganar bari na duba mana jalaf din shinkafar kota nuna muci" cewar Saude tana mikewa.


Lami na ganin Saude ta wuce kitchen ta rike baki cikin munafirci tace" jama'a yau nake ganin wani ikon Allah mutuwar zuciya ta 'kare a dangin su ilyasu kalli wai komai biyu".


Tabawa na kallon kofar kitchen tace hum abinda yake cin raina kenan yar uwa kika riga ni furtawa mutum da hankalinsa bazai kai yarsa wannan gidan ba".

Gadoji tace nima sheda ce ina marsida yar gidan Bala sai daga gida ake kai mata abinci mijin ya kasa riketa kuma ai kinsan mijin nata Sado (Sa'idu) dakin su daya da ilyan".


Laraba tace mukam ai taushe zamu zo mu kwasa ina ruwan mu dama irin su abuh ai sai ana basu tantirai kuma nasan zataci ubanta a gurin Halima domin ita bata zama lafiya da surukai".


Aliyah tace yo matar da ko naman miya ne sai a gaban ta ake rabawaa dan kar a cuceta duk cefanen da yayanta zasuyowa matan su saita burkice kowacce leda idan kaje kasuwa baka biyo ta dakin taba kuna zaune zata fado muku daki ba sallama🙊".


Lami dake dariya tace kice Saude abar hankata baki Abuh karamar bazawara za ai sakin uwar miji ba sakin wawa ba".


Duk gurin dariya suka kaure daidai Saude ta fito da katon tire fal da abinci ta ajiye tana cewa dariyar me kuke"?..


Lami tace dariyar farin ciki kawata sai aurar da yaran mu muke asirin mu a rufe tuna hakan ne ya samu dariya".


"Wallahi kuwa lami ai abin da dadi zuma da madara muci kartai sanyi dan nasa mana kitse a ciki .


Hummm ayya Saude kin 'baro🙄😖😠😕.



💰'DAN MILLIONAIRE💰


Page 15 to 16
Zaune suke a palor misalin karfe tara na dare daddy dake rike da wani photo ya mikawa Al'ameen yana cewa.


"Aminullahi wannan 'yar gidan abokina ce Mudansur sunan ta Afnan ban sanii ba ko tayi maka saika aure ta".


Da sauri mami ta amshi photon daga hannunn Al'ameen tana cewa me laifin wannan yarinyar ta hadu kawai ka nema masa ita".


Hade rai Afeeyah tai tana kallon daddy tace nidai a shawara ta abar min dan uwana ya huta ya nutsu daga baya zai samu wacce yake so da kansa".


"To uwar iyayi wa ya sako dake" mami ta fada tana harararta.


Murmushi daddy yai yayi kyau Afeeyah kin fadi gaskiya amma bari naji ta bakinsa Al'ameen kana son ta"?.


" a'a daddy" shine kawai abinda yace .


"Ji banza " mami ta fada cikin haushi".


Dariya Afeeyah tai tana kallon mami tace gaskiya ne yaya Afnan bata dace dakai ba kalleta fa fiyu da ita kamar an zana d'aya .


Duka mami ta kawo mata tana cewa jakin uban ki Afeeyah".


"A'a daina zagin ta mana karki debe mata albarka tabi 'ya'yan kaji🐣🐤🐥.


Amma tsakani da Allah alhaji meye abin kushe a wannan yarinyar".


"Babu amma tunda baa kece zaki zauna masa da ita ba shi kuma yace baya yi shikenan abar maganar".

Mikewa mami tai irin tayi zuciyar nan tace saida safe".

Har hada baki daddy da Afeeyah suke wajen cewa Allah ya tashe mu lafiya".


"Zan kama kine Afeeyah zaki min bayani".



Bayan wata daya Abuh ce ta shigo gida da kukan ta Saude dake kan tabarma tace lafiya kukan me kike ko keda ilyasun ne yaron nan ya fara bani haushi ba wata uwar ya bamu ba tun kafin a kaiki gidan sai wulakanta ki yake zaici kwal ubansa😜😂".


Kai Abu ta girgiza a'a ba shi bane Sa'adu ne dan gidan me gari".


Ba shiri Saude ta mike na shiga uku meya hada ku zaki yayo min masifa😁".



"Abu na kuka tace wai Fati yake so😱".

"Wacece Fati kuma ina ruwanki koma wa yake so tunda kina da naki".


"Kefa Fatin nan gidan yake so".

A zabure Saude tace me karya ne akan hakan kike kuka".


"Wallahi ba karya bane yanzu na wuce su suna waje akan dakali suna hira".


"Kan bala'i wato Salamatu dan me gari kika yiwa asiri ko aiko sai kowa yaji a garin nan kina zuwa gidan boka bari gari ya waye tabdijan wallahi da sake dan kinga bikin shekara ya kusa kada yarki tasha kunya agaban dunbin jama'a na gari da gari".


Tari dabai kama Salamatu ba bataiwa Saude ba ta tura mata aniyarta domin batasan ma wani Sa'adu nason Fati ba".


Kasa nutswa Saude tai saida ta sayar da akuyarta ta dangana gurin boka akan ya karkatar da hankalin Sa'adu kan Abu ".


Yaji ya tsani Fati haka ta juyewa boka dukkan kudin sisi bai bari ta dawo dashi gida ba amma fa ya mata aiki domin tun a ranar labari ya sauya akala".


Da dare sai akace Abuh tace inji Sa'adu wata irin faduwa gaban Salamatu yai cikin tashin hankali ta kalli fati dake kallon Abu".


Dariya Saude keyi tana juyi da habaice habaice tace dadi na da gobe saurin zuwa maza Abuh shirya kije kada ki bata masa lokaci tsuntsun soyayyar🕊 ya dawo kanki ahayye ayyuriri nanaye nisa tazo kusa".


Kallon Fati Salamatu tai cikin tausayawa tace kada ki damu Allah yasa haka ne mafi allhairi kinji babu komai kai Fati ta daga cikin damuwa sosai amma batace komai ba"'.


Tashin hankali ne karara ya bayyana da kiyayyar 'kauye🏕 a fuskar mami lokacin da daddy yace mata ta shirya yana son zai gano danginsa".


Cikin cika da batsewa tace amma alhaji mezai hana kaje kai kadai".

"Saboda me" ya tambaye ta cikin mamaki.


Kai tsaye tace" dole sai munyi gayya me zamu ciyo"?.


A garin daya tare dukkan zuriya ta kike cewa me zaki ciyo Aisha tun ba yau ba na fahimci bakya kaunar zuwa dangi na saboda a kauye suke amma ki sani sune komai nawa idan kika 'kisu nine kika 'ki fito fili kice mustapha bana sonka basai kinbi ta bayan gida ba".


Zaro ido mami tai ni da yaushe nace bana sonka"?.


"Yanzun nan kika fada tunda bakya bukatar asalina kinga son karya kike min yaudara ta kikeyi".


Kuka mami ta kama yanzu alhaji shedar da zakai min kenan"?.


Mikewa daddy yai ransa a hade yace na fada miki ki shirya idan kuma baki canza halayen kiba zan dau mataki a kanki".

Yana fita tace na shiga uku ni Aisha wannan tsinannan 'kauyen kuma zanje daga wannan masifar takau sai wannan😢.



Humm mami manya 'kauye🏘 tushe da asalin kowa😘 duk wanda bashi da 'kauye to bashi da asali😠 tsintaccen kan hanya ne🙄.


Washe gari motoci biyu suka dauka yayin da Zainab tace baza ta bisu kauye ba ta wuce gidan su kafin su dawo".


Da matukar murna Muntari ya tari yayan nasa nan aka hau yi musu hidima da bajinta duk wani abu dazai burge su na gargajiya".


Afeeya dake shan fura ganin mami tayi gurum yasa tace wai mami bazaki ci komai ba to kisha wannan akwai dadi".


Cikin bacin rai mami tace zanci 'kaniyarki fa Afeeyah ni abokiyar wasan kice"?.

"Yi hakuri mami " daga haka bata sake magana ba".

Sadiq kam dama ya shiga gari idan yazo baya zama guri daya kamar kifi🐟".


Al'ameen da yake suna tare da daddy a dakin muntari yace dad nifa yunwa nake ji".


"Kuma Aminullahi ga abinci iri daban daban sai wanda kake so".

"No daddy ba irin wannan nake so ba".


"Uhmm wato sai kwai ko wannan abincin yafi wanda kake ci a birni sa lafiya da gina jiki".



"Nidai daddy mubar maganar samo min mafita Allah ina jin yunwa sosai".

Daddy dake kallon shi yace to Aminullahi hanya mafi sauki ga yaji da mai nan a kusa dakai dauki ka cinye ni amma ka fara ta 'kafofi na saboda kar na gudu😂😝".


Dariya wacce babu shiri Al'ameen yai yana kallon daddy yace haba dad idan na cinye ka babu wanda ya kaini asara".


Muntari dake gefe yace to yanzu me kake so a dafa maka".


"Am small dad in son samu ne dan wake".

"Shikenan karka damu bari yanzu zansa ayi maka" mikewa yai yana fita".


Al'ameen dake kallon photon Abni dake screen wayarsa yace daddy bari naje gurin grand-mah".


"Ok yayi ka gaishe ta"

Al'ameen na fita daidai Fati ta shigo da bokitin ruwa a kanta tana cewa wash Allah umma ki sauke ni".


Da sauri Salamatu ta fito daga daki tana cewa meyasa kika ciko".


"Umma bana son na koma ne".


Zama Salamatu tai tana hada kayan wanke wanke Fati tace barshi zanyi umma ki huta".


To Allah ya miki albarka".


"Ameen umma motar waye guda biyu a kofar gidan nan masu kyau".


"Ayya Fatima yan uwan kine suka zo daga birni da yayan babanki Mustapha yana dakin baban ku kije ki gaishe shi".


"To umma " fati tace tare daa mikewa kusa gwaruwa tai da al'ameen da sauri taja baya tana cewa yi hakura dan Allah ban ganka ba sannu da zuwa ".


"Thank" yace daga haka bai sake magana ba yai hanyar waje cikin mamaki ya tuna yarinyar nan kamar ba ita yake dauka a hannu ya sayo mata chocolate ba shakka babu amma girmanta ya gani sai yaga ta cika masa ido.



Yana zuwa gidan ya tarar da Sadiq acan da ido ya masa magana cikin tsokana Sadiq yace .



"Lah hajiya kinsan me Al'ameen yace wai ya yaga kin kara tsufa sosai kin ragargaje kiji fa hajiya kamar wata kwarya".


"Rabu dashi Saddiqu lokaci ne shima wata rana zai taka wannan matsayin".


"Matsala ta dake hajiya bata suna meye zakice Saddiqu just kice Sadiq".


"Bazan ce jas Saddiq dinba karka dameni😂😜".


Al'ameen ta kalla tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login