Back to novel

Chapter 3 of 6

MAI DAKI Ilimi Da Talauci BOOK 1 BY Nana Haleema | Hausa Novel

ranar ba shi da

bukata ta to zai yi juyawar shi ne ya kalli

bango nima nayi tawa kwanciyar ban

kuma taba daukan hakan a matsayin wata

matsala ba.

Idan kuma ranar sati ne to kuwa haka

"zai wuni yana kallon Jaridar shi ta sati,"

53

idan kuma yamma tayi to zai fita ba zal

dawo ba sai sha daya ko da rabi idan ya yi

dare kuwa har sha biyun dare.

To zan iya cewa wannan ita ce babbar

matsalata da shi amma nauyinshi ya hana

ni yi mishi magana.

Sai dai maganar Makaranta ta ce a yau

nayi nufin yi mishi magana saboda tafiyar

lokaci.

Saida ya gama cin abincin shi na

kwashe kwanukan sannan na dawo na

zauna can gefe na ce mishi cikin ladabi.

"""Don Allah ina so ne nayi maka wata"

"magana idan ba za ka damu ba."" Ya dan"

kawar da Jaridarshi daga kan fuskarshi ya

"ce, ""Uhum ina jin ki."""

"Na ce, Dama maganar Makaranta ta"

nake so nayi maka don yanzu na kai wata

shida bana zuwa kada lokaci ya yi ta

"tafiya."""

Yayi shiru zuwa wani lokaci da har na

fara gundura da shirun nashi sai da ya

54

daga Jaidar ya ci gaba da dubawa sannan

"ne ya ce ""Ba yanzu ba."""

"Na ce, Na'am!"" saboda yanayin da"

amsar tashi tazo mun. Na ce miki ba

"yanzu ko da matsala ne?"""

"A hankali na ce, ""A'a babu."" Ya ce,"

"To madallah."" Sannan ya ci gaba da"

kallon Jaridarshi. Daki na shiga na kwanta

sai dai na kasa hana kaina kukan da yazo

mun.

Ba yanzu ba sai yaushe? Sai dai ba zai

yiwu nayi mishi irin wannan tambayar ba.

To waye zai tambayan mun shi? Ai sai

daini din don kuwa ni ce nake zaune tare

da shi. Hakan ne yasa ni mikewa daga kan

gadon na fito falon na sake neman wani

wuri na zauna.

Na ce To yaushe ka ke ganin ya dace

kenan na koma Makarantar? Ya janye

Jaridar daga fuskarshi ya zuba mun ido

yana kallona.

55

"""Ke! Tashi ki bani wuri, ke kuma"

wacece da za ki yi mun titsiye? Shashashar

yarinya kawai.

Wadanda ya zamarwa dole ma ba su

"tsaya sun ga kin yi karatun ba ballantana ni."""

Mikewa na sake yi na hau gado na

kwanta. Har aka kira assalatu ban runtsa

"ba, kuka kawai nake yi kukan sharbe."

Wane irin abu ne kuma haka meke

faruwa ne? Shin me Ishak yake nufi? Na

mike daga kan gadon na nufi bayan gida

nayi wanka sannan na dauro alwala.

Har yanzu barcin shi yake yi cikin

kwanciyar hankali. Nayi sallolina na nafila

raka'a biyu sau uku sannan na zauna na

dan yi karatun Kur'ani.kafin aka fara kiran

sallah.

Lokacinne ya tashi ya shiga bayan gida

yayin da ni kuma na tada sallar nafila ta

"raka'atul fijri, sannan nayi sallar asubahi."

56

Na durkusa na gaishe shi kamar yadda

na saba sannan na shiga kicin don kokarin

yin abin karyawa kada ya makara.

Ba tun yauba na sha yin tunanin shiga

gidajen makwabta da muke unguwa daya

da su saboda mu'amalla da Jama'a.

Ban kuma samu damar yin hakan baa

duk kuwa da cewar su sun shigo ba sau

daya ba ba sau biyu ba. Haka nan ma

yayan su.

Baran ma dai Hindu wacce nasan ko

bata gime mun ba to zamu yi sa'a da ita

don a yanzu a SS 2 take kenan da muna

tare a Makaranta.

Don haka ko a yau da nayi nufin na sha

kunun gyada da safe sai na tashi domin na

leka sudaga nan kuma na samu wanda zai

siya mun gyada da kamu.

Ba a yi hanzarin tambayar Ishak ba

amma a a raina sai na kuduri aniyar idan ya

dawo daga wurin aiki sai na sanar da shi.

57

sNa fito na rufe ko'ina na cikin gidan

sannan na nufi gian su Hindu wanda yake

kallon namu gidan nayi kyakkyawan

sallama a tsakar gidan wanda hakan yasa

Momy mahaifiyarsu ta leko.

"""A'a'a Amarya ce yau a gidan namu?"

"To shigo daga ciki mana."" Na bita muka"

"shiga falon na zauna a kasa ta ce ""A'a"

"zauna a kan kujera mana."""

Na mike na gyara zam a kan kujerar

sannan na gaisheta cikin girmamawa ta

amsa tare da yin yar hira kadan wacce

mafi yawancinta kan al'amuran gida ne.

"Na ce, Hindu bata nan ko? Ta ce, ""Eh"

"ba su dawo daga Makaranta ba, saboda"

"tana tsayawa lesson."""

Ban. wani tsaya bata lokaci ba na mike

don dawowa gida har kofar gida ta rako ni

da yar leda a hannunta ta miko mun nayi

godiya na nufi gida ina tunanin inda zan

samu abin da na fito nema.

58

Wanda ba zai yiwu kuma na kara yin

gaba ba. Wani abin mamaki shi ne ban

lura na hangi motar Ishak ba sai da nazo

shiga gida.

Wani irin mummunan faduwar gaba ne

ya same ni sai dai kawai sai naga to ai ba

nisa nayi ba sai nayi mishi bayani.

"Na shiga dakin cikin murmushi na ce,"

"Lah ban yi zaton zaka dawo yanzu ba, shi"

"yasa... "" kan na gama maganata ya ce"

"""Dama idan na fita yawon ki ki ke tafiya?"

lye? Inà ki ka je? Na ce miki daga ina ki

"ke, kaga mun shegiya 'yar matsiyata."

"Raina yayi mummunan baci na ce ""A'a"

"ni kada ka sake zagina ka hada da iyayena,"

"me nayi da zafi haka?"""

"Ya ce, ""An zage su matsiyata me za ki"

yi iye na ce me za ki yi idan an zage su su

"din banza su din wofi."""

Wannan shi ne na farko kuma na karshe

na gaya miki idan ki ka kuskura ki ka sake

59

ita na dawo gidan nan ba kya nan sai nayi

"miki abinda ba ki yi zato ba."""

Ya juya ya fita ina jin shi ya sakala

kwado ya rufe gidan ta baya. Na zauna a

wurin nayi kuka irin wanda ban taba yi ba

a rayuwata.

Dama haka auren yake? Na san iyayena

talakawa ne wadanda ba su da komai

amma ba haka yana nufin Ishak ya zage su

ba ne tamkar sun dauke ni sun ba shi ni

auren da ko wata biyar bai yi ba.

"Tausayin Babana ya sake kama ni,"

mutum mai kokari da bai taba zuwa kofar

"gidan wani neman taimako ba, ya dogara"

ga Allah ne da kuma dan abinda yáke

samu a wurin aikinsa.

Hakanne yasa mutanen unguwarmu har

da ma su kudin suke matukar girmama shi.

Na lallaba na mike da nufin shiga kicin

nayi girkin abincin dare. Na kuwa samu ya

kawo wani cefanen abinda a yau ya daina

birge ni.

60

"Na dauko na fara rarrabawa, ina ajiye"

"komai a wurinshi, na zaro ledar da naji"

"danshi, kifi ne manya masu kyan gaske"

guda uku.

Na bude frizer na ajiye guda biyu na

fara gyaran dayan da alama shi yake son ci

da daddare.

Farfesun kifi nayi mishi wanda bai yi

"romo mai yawa ba, sai nayi coconut fried"

ice na ajiye a food flask ganin har na

gama bai dawo ba duk kuwa da daren da

nayi sabodamakarar da nayi wajen

farawa.

Har nayi sallar Isha'i shiru bai dawo ba.

Bai saba yin dare a waje ba idan ba

kwanakin sati ba ne wato Asabar da

Lahadi.

Tun ina sa ran dawowan shi har na

hakura na hau gado na kwanta. Can cikin

dare na ji motsin shi.

Na mike na same shi tsaye yana cire

riga da niyyar canzawa don kwanciya.

61

Na fito falo na dauko abincinshi na

"kawo mishi, bayan nayi mishi sannun da"

ko kallona bai yi ba.

Na ajiye abincin da farfesun na koma

gefe na zauna yadda na saba yi. Ya gama

shirin shi ina tunanin zai zauna yaci

abincin ne sai kawai naga ya hau gado ya

kwanta.

Na dan daure na ce ba za ka ci abincin

ba ne? Bai ce mun komai ba duk kuwa da

nasan idonshi biyu saboda haka sai na

tattara na kai kicin na zuba cikin wani abin

na saka a fridge don gudun kada ya lalace.

Na dawo dakin na gyara na sake

kwanciya sai dai a yanzu kam ban samu

yin barcin ba.

Kan kace meye wannan sai na fara jin

saukar numfashin Ishak yau ma haka na

kwana ban yi barci ba.

Sai dai duk tsawon lokacin tunani nake

yi na ya kamata naje gida naga iyayena

62

haka nan na sanar musu da abinda yake

faruwa.

Hakanne yasa da na gama gaishe shi da

safe na roki ya bani izinin zuwa gida bai

bani amsa ba haka nan bai tsaya karyawa

ba yayi ficewarshi.

Da wani bacin ran na wuni wanda yau

duk da dadin da gyaran gidan nan yake yi

mun yau haka ya zauna sai da naga

La'asar tayi sannan na mike don shirin

abincin dare.

"Shaf, na mance da abincin jiya da Ishak"

"bar ci ba, don haka na nufi kofar gida don"

na samu yaran da zan baiwa abincin.

Sai dai a kulle na ganshi ta baya. Sai

kawai na dawo na kama aiyukana. Kamar

yadda jiya bai dawo ba sai tsakar dare

haka nan yau ma.

Sannan bai ci abincin ba ya sake

kwanciya. Gari ya waye na sake yi mishi

maganar zuwa gida yau ma bai ce mun

"komai ba, ya fita ba tare da ya karya ba."

63

Na dai lura idan nace zan zauna ina

"kunci da bakin ciki to zan nakasa kaina,"

sai kawai na nemi samun saukin

damuwata ta wata hanyar.

"Ni ba ma'abociyar kallon fim ba ce,"

amma yau sai na shiga laluben drawer da

ke jikin TV stand din don neman kaset din

kallo.

s1Na yi dace da wani mai suna Why did I

get married too?' sunan shi ne ya dauki

hankalina da na saka kuma sai na samu

kaina da nutsuwa don yin kallon.

Kawaye ne guda uku sai dai kowacce

da irin matsalar aurenta. Na dan ji dadin

yin kallon don ya rage mun damuwa.

Ban ki yin abinci ba don ganin ba ya ci

kuma ina ta tara shi a fridge. Tuwo nayi

miyar kubewa bushasshiya na ajiye kamar

yadda na saba.

Ban kwanta ba zama nayi na jira

dawowarshi. Shima yau bai vi dare sosai

"ba, don kuwa sha daya da kwata ya dawo."

64

Babu irin tunanin da ban vi ba amma ina

kasa sanin abin vi a kan matsalar. Zaman

auren da nayi ba mai yawa bane

ballantana har nayi wayon zama da miji.

Amma sai na kudure a raina a yau idan

ya dawo zan san abin yi akai shi ne kuma

na ba shi hakuri.

Ganina da yayi zaune a falon bai tsaya

ba wucewa yayi zuwa cikin daki yadda ya

saba.

"Na bishi na sake yi mi1shi sannu, sannan"

na tsugunna a gefe na ce Don Allah idan

nayi maka laiti ne ka yafe mun abinda nayi

maka. Ba kuma zan sake ba da ikon

"Allah."""

Wannan magiyar da nayi mishi ita ce

tasa shi ajiye rigar barcin da ya dauko zai

saka ya kalle ni.

To kenan har kin isa na zage ki ki

rama. Iye! Ke kuma wacece a cikin mata?

Duk da bacin ran da maganar tashi ta sa

ni wacce a take kuma na kasa danne

65

hawayen da suka fara zuba a idona

hakurin na ke ba shi kafin daga baya ya ce

"ya wuce amma kadá ki sake ko da wasa."""

"Hakan bai sa yaci abincin ba, amma bai"

dame ni ba. Na hau gado na kwanta.

Washegari na lura ba shi da niyyar buga

sammak0 irin na sauran kwanakin.

Don haka na shirya mishi abin karyawa.

Ya fara ci kenan ya kalle ni Na baki

mintina goma kI shirya na sauke ki a

"gida."""

"Ban san sanda na fara godiya ba, duk da"

cewar mintina goman ba 1sa na za su y ba.

Na riga nayi wanka don haka atamfata

na dauko Exclusive na daura da gyalenta

"da set din takalmi da Jaka 'yan taly, sai"

yan canji na da ba su fi Naira dubu daya

ba.

Da wasu yan abin kwalam da nake

ajiyewa idan ya kawo sun ban sha'awa na

karewa dakin kallo na rasa abinda zan

kaiwa Umma.

66

Don haka na bude akwatin aurena da

zannuwa suke ciki na dauko mai kyau na

fara nadewa ban san ya shigo ba ya ce

"""Me za ki yi da ita? """

"Na rasa abinda zan ce, ya ce To"

mayar. Na sake budewa na mayar

gwiwata a sanyaye.

A kofar gida ya ajiye ni na shiga rabona

da gidanmu watanni biyar. Haka na Umma

da Babana. Gani na rinka yi kamar ba ni ba.

Haka nan Umma ta rinka ina ta ka saka

da ni. Ta zuba mun ido ko kyaftawa bata

yi. Ni kuwa kunya duk tà kama ni.

Farin ciki mai yawa Umma ta nuna na

ganina. Ita ma na ganta tayi kyan gani ba

kadan ba.

Na bude Jakata na ciro ma su Tasi'u

Bueno cakulet da biskit kwali biyu na

"mika musu suna ta murna, wanda iyakacin"

kuma abinda na riko nusu kenan.

67

Ni ce na tashi yau ma nayi mana girkin

rana muna ta yar hirar mu da Umma.

Wacce ganin irin murnar da take yi ne

yasa ni kasa gaya mata mnaganar da ke cina

a cikin raina.

Wato maganar Makarantata. Ba zai

yiwu na dakushe mata wannan farin cikin

da take ciki na ganina ba.

Karfe hudu da rabi daidai sai ga

sallamar dan aika wai na fito na dauko

gyalena na zo inda Ishak ke hakimce a

"cikin mota na dan risina ta gefe na ce ""Ai"

na dauka zaka shigo ku gaisa da Umma ne

ko da ba za ka bar ni na jira dawowan

"Babana ba."""

"Ya ce, A'a ba zan shiga ba, fito"

"kawai. Na ce, ""To."" Na koma na ciro ""yar"

Naira dari taran da nake ta nuku-nuku na

"kasa bai wa Umma, na mikawa su Tasi'u"

nayi wa Umma sallama na fito zuciyata

kamar ta fashe.

68

"Muka iso gida ya ajiye ni ya juya, ni"

kuma na shiga kicin da nufin dorà abincin

dare.

Tunani nake yi na yadda zan rinka

"taimakon iyayena, don kuwa ba zai yiwu."

na zauna a haka ba. Ishak ba ya bani ko

sisi zan iya cewa tun bayan aurena a shi

sile biyar bata shiga tsakanina da shi ba.

Haka nan duk wani abu na amfanin gida

shi ke kawowa bani da wata hanya da zan

bi na samu kudi da zan iya yi musu wani

abu. Ya zama mun dole nasan abin yin.

Tun daga ranar da na samu matsala da

Ishak kan zuwana gidan su Hindu ban

"sake ba, sai dai da yake ya daina kulle ni"

"bayan na roki yayi mun hakan, to ita takan"

shigo.

Mafita daya ce shi ne na dan rinka

taimaka musu da dan abinda za su ci

"wanda shi kam ina da shi, don haka da"

Hindu ta shigo na roke ta ta gayawa

Mominsu ina son aikanta gidanmu.

69

Na debi shinkafa mudu biyar da su

"Taliya da cous-cous, man gyadan (Turkey)"

da soyayyen nama da sauran abubuwan

amfani na hada mata rigijif ta kai ta dawo.

ow Zuciyata tayi mun dadi naji sanyi na

dan yi wani abu. Sai dai babban abin

"takaicin shi ne, bayan kwanaki biyu kawai"

da faruwar hakan sai naji wa'azi a Rediyo

ana yi na matar da ta yi wa miji kyauta da

"abinci ba tare da ya sani ba, irin"

hukuncinta.

Sai dai har idan ta tabbatar da shi din

"ma zai yi hakan, to sai tayi da nufin Allah"

ya ba shi ladan.

Nayi shiru a raina ina tunanin to shi zai

yarda da hakan ko kuwa shisshigi nayi? Ba

zai yiwu na gaya mishi ba kada na Ballo

"wa kaina liki, tunda dai an ce haramun ne"

gara kawai na nemi hanya da zan nemi

"nawa ita ce ta hanyar dinki tunda na iva,"

kuma ina da keken yin dinkin.

70

Sannan unguwarmu sabuwar unguwa

"ce, da alama za a samu alheri idan mutum"

ya ce zai yi wata sana'a.

Washegari asabar don haka Ishak yana

gida da rana. Sai da na gama aikace-

aikacena na gida sannan nazo falon da

yake na zauna na fara yi mishi magana kan

tunanin da nayi na dinki tunda na iya.

"Amsar da ya bayar a gajarce ce, ita ce"

idan ina gidanshi to ba zan yi dinki ba. Ba

zai lamunci irin wadannan abubuwan na

nuna karanta ba.

"Ba ni da abin fada, don haka naja"

bakina nayi shiru. Kamar yadda shima ya

yi. Bani da wani abu da nake yi da ya

wuce aikin gida da girki.

Wannan a yanzu nake rayuwa akai babu

abinda yafi damuna irin tsayawar karatuna.

Ba zan ce Ishak ya yaudareni da

"1yayena ba, don kuwa matsayj shi ya"

wuce hakan mijina ne.

71

Sannan babu wanda zai kalle ni ya ce

Ina da matsala don kuwa a bayyane yake

na samu canji. Kana kàllona ka san ina

"cikin wadata,"

Sai dai to iyavena fa? Wannan shi ne

babbar matsalata.

Yau ma zama nayi da nufin jiran

dawowar Ishak na nemi i2inin zuwa gida a

washegari don kada ya ce ban fada mishi

da wuri ba.

Ina matukar kewar Babana saboda zan

iya cewa tun da aka yi aurena rabona da

"shi, a yanzu kuma wata na bakwai nake"

ciki.

Na jira shi har na gaji na hau kan

doguwar kujerar dake dakin na kwanta.

Bai shigo ba sai karfe goma sha biyu

daidai.

Na mike zaune saboda jin motsin da

nayi na kuma yi mishi sannu' ya amsa: Ban

tsaya zancen kawo mishi abinci ba don

72

kuwa ma a yanzu idan ya dawo ba yaci ko

"na kawo mishi,"

Ban yi mishi maganar ba sai da ya

kammala shirin kwanciya sannan na fara

kokarin yi mishi maganar.

Bai bar ni ba saboda dago mun hannu

da yayi alamar dakatawa.

Wai ke ba ki da wata magana ne sai ta

gidanku? Mits! Yayi tsaki ya yi

kwanciyarshi.

Sai mutum ya wuni aiki amma idan ya

dawo gida a maimakon a barshi ya huta

wai sai a tasa shi a gaba da surutan banza.

Ya ja abin ruhuwarshi ya kwanta.

"Na riga na saba da dabi'un Ishak, don"

haka a yanzu ba su cika damuna ba.

Washegari har na gama mishi shirinshi na

karyawa da sauran abubuwan shi na tafiya

aiki a raina ina tunanin zai yi mun

maganar zuwana gida da nayi mishi bai ce

komai ba ya tafi.

73

A duk 1ökacin da ya tafi aiki na kan

"dauki wayata na kira Hindu ta taya ni hira,"

hakan ne yasa muka yi wata irin shakuwa

ba kadan ba.

Hindu wayayyiyar yarinya ce ba kadan

"ba, haka nan yanayin irin gidajen da muka"

tashi ma ba daya ba ne.

"Don kuwa kamar yadda nake ""yar talaka"

ita kuwa ya ce ga babban Ma'aikacin

"Gwamnati, Mominsu ma wayayyiyar mace ce."

Wunin da nake yi da ita a cikin gida

yayi matukar taimaka mun kwarai da

gaske kan al'amurana. Ban taba zama na

"fada mata wani abu game da mijina ba,"

amma sai ta gane hakan.

"Wanda yasa ta yi mun magana, ban"

saurari abin ba don ganin da nake yi mata

na cewa ita din ko da muke kusan sa'o'in

juna ita ba macen aure ba ce.

74

Haka nan kullum Umma tana gaya mun

na rike sirrina. Don haka ko da ta yi mun

magana murmushi kawai nayi.

An dan dade kafin na samu Ishak ya

bani izinin zuwa gida. na zaune cikin

motar daidai ya tsaya a kofar gidanmü na

"ce mishi ""Ko za ka bar ni ne zuwa dare"

"don na gaisa da Babana?"""

"Bai ce komai ba, nima kuma ban sake"

yin magana ba. Hira sosai muka yi da

Umma ina mata korafin ba a taba kawo

min su Tasi'u ba

"Tayi murmushi ta ce, ""To sai ki gayawa"

"Babanku tukunna. Na ce, ""To."" Babana"

ba karamin jin dadin ganina ya yi ba.

"Yayi ta murmushi ba iyaka, yana ta dan"

yi mun tambayoyi ina ba shi amsa tare da

jaddada tambaya daya da yake yi min.

Babu matsala dai ko Hauwa'u? Na

"ce, ""A'a babu."" Ya ce, ""To ki yi ta hakuri"

"kin ji, shi zaman tare hakuri ake yi."""

75

"Na ce, ""To Baba."" Kamar na danne"

abinda ke damuna sai dai na kasa. Na ce

"""Baba sai dai maganar Makarantata ne har"

yanzu shiru.

Nayi mishi bayanin yadda muka yi da

"Ishak ya dan yi shiru zuwa can ya ce, ""Too"

babban al'amari a wurin mu ai shi ne ki

zauna lafiya a dakin aurenki.

Kuma ga dukkan alamu kina da

kwanciyar hankali. Ita maganar karatu tana

zuwa ne daga baya.

Amma tunda dama can yasan da

maganar ina ganin bari ni da kaina nayi

"mishi tuni muji abin da zai ce."""

Tun kan Ishak yazo daukana nayi wa

Babana magana akan ina bukatar su Tasi'u

"su zo min kwana biyu, ya ce ""To."""

Ba a wani dade ba rannan kawai da rana

sai ga