Chapter 4 of 6

MAI DAKI Ilimi Da Talauci BOOK 1 BY Nana Haleema | Hausa Novel

Yaya Auwalu da su Tasi'u da dan

kayansu a kullin leda.

76

"Murnata bata boyuwa, na rasa inda zan"

ajiye su. Nan da nan na shiga kicin na fara

ajiye musu dan abinda nake dashi.

Muka yi hira da Yaya Auwalu sosai

daga ni kuma ya yaba da inda nake don

kuwa bai taba zuwa ba shima sai yau.

Ya jima sosai kafin yayi mun sallama

"ya tafi, ya bar mun Tasi'u da Sadisu akan"

za su y1 mun sati guda.

Muka wuni muna harkokinmu ba kadan

ba cikin raha da jin dadi. Hindu kuma tazo

ta debe su ta kai wa Mominsu suka gaisaa

suka dawo tare da kaninta Abubakar.

Da daddare kuwa hira muka sha ba

"kadan ba, nayi dariyar abubuwan da suke"

bani labari har na gaji.

Rabon da naji dadi irin a yau har na

manta. Ba su yi barci da wuri ba saboda

kallon da suke yi sai wajen karfe goma na

dare kafin nan kuwa ni kaina na gaji.

Nayi wanka na gyara na hau gadona na

"kwanta, kan ka ce meye har nayi barci"

77

abinda ya hana ni jin dawowar Ishak don

kuwa ban farka daga barci ba sai da naji

"kiran sallar Asubahi,"

Da sassafe Ishak ya fita wanda shi ne

dalilin da ya sa ban tuna gaya mishi zuwaan

su Tasiu ba sai bayan tafiyarshi.

A yau mna wuni muka yi muna

harkokinmu. Nayi mana abinci mai dadi

dafadukar taliya da taji hanta ga kuma

"farfesun kayan ciki, don kuwa nasan babu"

abinda suke so irin taliyar.

Yau ma sai da muka yi hirarmu wajen

karfe goma sannan na shinfide su a dayan

dakin na gyara musu komai na fito na hau

gadona ina tunani a raina irin kewar da zan

ji ranar da su Tasi'u za su koma gida.

Idan da da hali da na roki Umma ko

Babanmu su bar mun su Tasi'u.

Kwanciyar nayi da nufin na yiwa Ishak

"maganar idan ya amince to, tunda muna da"

wadatar waje.

78

Yau ma ban san sanda ya dawo ba

saboda barci mai nauyi da ya dauke ni.

Can cikin barcina naji kamar ana kirana.

Na bude ido cikin sauri saboda gane ba

mafarki nake yi ba. Sadisu ne. Sai dai ba

ni kadai ce na tashi ba har da Ishak.

"""Menene ya faru Sadisu? Ya ce,"

"""Aunty zan yi fitsari ne."" Na mike cikin"

sanyin jiki saboda irin kallon da Ishak

"yake yi mun, na dawo dakin da suke nasa"

shi a bayan gida yay.

Na sake shimfide shi ina kara jaddada

musu in sun ji wata bukata ba sai sun tashe

ni ba su shiga bandaki kawai su yi.

Na kuma gaya musu hakan tun kafin su

kwanta amma kuma sha'ani irin na yaro.

"Na shigo dakin, Ishak yana zaune a kan"

bakin gadon nayi nufin wucewa naje na

"kwanta, duk kuwa da sanin da nayi na"

cewa ni yake jira.

79

"Sai, dai yanayin shi da ke sani cikin"

"faduwar gaba. ""Zo nan. Abinda yace mun"

kenan.

Na nemi wuri a kasa na zauna. Me

wadannan yaran suke yi mun a gida?

Lafazin da yayi amfani da shi yasa na rasa

"abunda zan ce, ko kuma ta inda zan fara."

"Cikin daga murya ya ce, ""Ba ki ji"

"abinda na ce ba ne ko ya ya? Na ce, ""Eh"

"naji, ba ka gane su ba ne? Su Tasi'une fa"

da Sadisu kannena.

"""Hala kin ga alamar makanta ne a tare"

"da ni ko? Nayi maza na ce ""A'a ba haka"

"ba ne."""

Idan na ce zan tsaya fadin irin tashin

hankalin da na gani ranar a tare da lshak to

nayi karya. Duk kuwa da irin bayanan da

nayi mishi wanda ko saurarona bai yi ba.

Maganar kuwa da muka wayi gari da ita

"ita ce, ta bai yarda su sake kwana mishi a"

"gida ba, maza-maza na sa a mayar da su"

kwana biyun da suka yi ya isa haka.

80

Bai ci komai ba ya fita. Bai bani kudin

"motar mayar da su ba, duk kuwa da yasan"

banida ko asi.

Nayi iyakacin kokarina wajen juriya

kada 'yan yaran nan su fahimci wani abu.

"Tasi'u bai fi shekara shida ba, shi kuwa"

Sadi yafi uku amma bai cika hudu ba.

Yan kannena da nake da su amma wai

Ishak ba zai iya mu'amalla da su ba.

To sai da wa? Ko da yake ni din ma da

ya aura ga irin yadda yake tafiyar da ni.

Sanin hakan da nayi bai hana ni bakin ciki

mai yawa ba. Biye mishi zan yi?

Ko kuwa dai zan nemi mafita ne? Na

gama ayyukana nayi lullubi tare da rufe

gidan na shiga gidan su Hindu.

Mominsu tana daki nayi sallama na

"shiga, na bar su Tasi'u a wajen yara suna"

wasa. Ban boyewa Momi komai ba.

Ta tashi ta shiga daki ta dauko kudi

"masu yawa ta bani ta ce ""Ki koma gida"

81

idan Hindu ta dawo zan turo miki ita sai ki

bata ta mayar da su gida.

"Kiyi hakuri, ki kuma yiwa mijinki"

iyakacin biyayyar da za ki iya idan har

bata sabon Ubangiji ba ce.

Kada ki s damuwa a ranki ko kuma ki

"ce wai za ki yi fushi da shi kin ji ko?"" Na"

"ce ""Eh."""

"Na dawo gida na ci gaba da kwanciya,"

don kuwana rasa kuzari tunani iri-iri a

cikin raina.

To da Ishak ya yi mun haka a kan

kannena shi nashi 'yan uwan baya tunanin

za su iya zuwa ko kuwa idan suka zo ya ya

yake so ayi?

"Na sake yin shiru, to a zaman da nake"

yi ma zan iya cewa bai taba yi mun wata

magana ta game da 'yan uwanshi ba kamar

yadda ban taba ganin wani yazo ya ce shi

abokin shi ne ba.

82

Nayi saurin mikewa na zauna ina wasu

"yan anane-tunane a raina, tambayoyi iri-"

iri da nake bukatar na samu amsarsu...

Sallamar Abubakar kanin Hindu ne ya

katse mun tunanina. Ya miko inun bakar

"leda ya ce ""Ga shi in ji Momi. Na karba"

ina dubawa.

Littattafai ne na Hausa da alama ta bani

ne na samu na karanta ni ba ma'abociyar

"karatun ba ne, amma sai naga bar1 na ajiye"

kada ta ce na gwasaleta.

Na mike don samarwa kaina abinda zan

Ci tunda yamma ta fara yi. Chives kawai

na soya da kwai naci na sha shayi aka:

sannan nayi sailar Magriba.

Ina idar da saliah sai kawa naji

"sallamar shigowar Ishak, mamaki ne yayi"

"Ihatukar kama ni, zan iya cewa tunda, aka"

yi aurenmu ya koma aiki bai taba dawowa

kafin ayi saliar isha'i ba.

Asali na ya dawo karie tara yayi sauri.

Na mike ina nade dardumar sallah tare da

83

"yi mishi sannu da zuwa, bai amsa ba don"

dama nasan hakan ne zai biyo baya.

Saboda zai yi mun abu wanda zai sani

bakin ciki amma shi ne kuma mai yin

"fushi idan har ba hakun na bashi ba, kuma"

to ba zai taba saukowa ba.

Sai dai a wannan tunda dai nasan ban yi

"mishi wani laiff ba, to nima ban shirya"

bada hakurin ba.

Na shiga kicin cikin sauri nayi mishi

"abinda zai ci, fried rice da farfesun danyen"

kifi wanda duka aikin bai dauke ni awa

guda ba.

Na kawo na ajiye mishi. Sai dai ban

ganshi a falon ba. Na shiga cikin dakin

kwananmu nan ma hakan. buruntun da

naji a daya dakin ne yasa ni lekawa.

Gyarawa yake yi yana kakkawar da

wasu abubuwa duk da dai har da ba a wani

amfani da daki banabarin shi da datti.

Ine tsaye ina kallon 'irin gyaran da yake

yi na shiga daki na dauko wani zanin

84

gadon na shimfida akan gadon na sa

tsintsiya na share dakin.

Bai ce mun kala ba ya shiga asalin

dakinmu ya fara kwaso kayan shi yana

maida su daya dakin.

Aikin da ya dauke shi har karfe goman

"dare, don kuwa tsinke nashi sai da ya"

"dauke ya kai shi daya dakin, kuma ya"

gyare shi tsaf ina zaune a. falon ina

kallonshi.

Ya shiga bandaki yayi wanka ya bada

tea yasha bai ko kalli abincin da na ajiye

mishi ba ya shiga sabon dakinshi ya

kwanta.

Ba sai na jira an yi mun wani bayani ba

nima da kaina na fahimci abinda hakan

"yake nufi, nima sai na shiga tsohon"

dakinmu ko kuma na ce na asalin na

kwanta.

"Al'amarin Ishak ba na karewa ba ne,"

kuma na lura idan na ce zan zauna ina

85

kwana ido biyu saboda bacin ran da yake

sa ni to zan wahala ba kadan ba.

Kwana da kwanaki muna cikin wannan

hali ya mayar da wancani dakin na shi

nima kuina ga nawa.

Tsakanina da shi gaisuwa ce ta sate ta

dare kuwa bana ma sanin sanda yake

dawowa. Nayi iyakacin addu'o'in da zan

yi a kan hakan ban ga canji ba.

Gyaran daki nake yi lokacin da na sake

cin karo da littattafan Momi. Na bude

daya na fara karantawa. Wunin ranar bata

kare ba sai da na gama shi tas na dauko na

biyun shima haka.

Cikin kankanin lokaci sai na koma

wurin Momi neman kari. Kullum da safe

idan na gama aikina na gida sai na zauna

nayi ta karatuna bana tashi sai sallah ko

cin abinci.

Sai ya zamana na koyi abubuwa in-iri

wadanda wani bai taba zaunar da ni ya

koya mun ba.

86

Abubuwa da suka danganci zama da

"miji, zama da mutane, girki, kuia da kai."

"gyaran jiki, kai abubuwa daban-daban."

"Idan nazo wani wajen naji takaici, wani"

"wajen nayi dariya, wani wajen naji tausay1,"

wani wajen kuwa naji kamar labarina ake

bayarwa da' Ishaf.

Don haka ga abinda zan yi. Damuwata

"tayi matukar raguwa, na kuma y1 niyyar"

yin amfani da shawarwarin da Marubuta

suke bayarwa da suka danganci zama na

aure na kuma Zubar da na banza.

Tsawon sati biyun da muka yi a hakaa

"muka yi ta da Ishak gaisuwar safe, dn uwa"

da daddare kan ya dawo nayi barci.

Amma na kuduri aniyar gyaran aurena

don na fahimci ba haka ake auren ba.

Aure yana yin nasara ne idan har akwai

kyakkyawar alaka ta addini da

"zamantakewa a tsakanin ma'aurata, uwa"

uba: kuma soyayya ta gaskiya da take

haifar da yafiya a kowanne lokaci.

87

Sannan Annabi (S.A.W) ba haka yayi

"Zama da nashi 1yalin ba, don kuwa babu"

wani mutum da zai nunawa matarshi

kwatankwacin irin soyayyar da ya nuna ga

iyalinshi.

"Babu kyamata, babu hantara bare"

tsangwama a cikin al'amarin aure. Miji da

mata (ma'aurata) duka su baiwa junansu

"lokaci na hira, kulawa, da tausayawa"

wacce suke haifar da karin soyayya da

fahimta a tsakani.

Na jawo akwatin kananan kayana na

bude ina dubawa tare da tunanin wacce

zan yi amfani da ita.

Duk da ina jin kunyar yin hakan amma

idan har zai kawo mun gyara ga aurena to

ko meye zan yi idan ba sabon Ubangiji ba

ne.

"Rigar bata wuce mun iya gwiwa ba,"

haka nan shara-shara ce don kuwa kusan

koma: nawa a bayyane yake.

88

Na gyara gashin kaina wanda na wanke

shi da man wanke gashi na (Trichup)na

kuma shafe shi da kayan gyara iri-iri.

Duk da ba wani tsawo ne da gashin

nawa ba ya yi kyau ba kadan ba. Ga jikina

da yayi luwai-luwai saboda jin dadi.

Maganar gaskiya ita ce Ishak ya wadata

ni da abubuwan jin dadi da suka danganci

abinci da na gyara.

Sai dai a yanzu na fahimci ba su ba ne

masu muhimmanci wanda bai bani ba shi

"ne komai, wato soyayyarsa da lokacinsa."

Na kuma kuduri aniyar nema ta hanyar

da ta dace.

Na dawo falo na zauna na ci gaba da

"yan karance-karancena, don kada barei ya"

dauke ni.

Yau sha daya saura kwata ya dawo. A

lokaci na dawowar Ishak kuwa to ya dawo

da wuri. Ya shige dakinshi ban ce mishi

komai ba kamar yadda bai kalle ni ba.

89

"Gabana sai faduwa yake yi, kodai na"

"kyale shi ne kawai? Kai a'a, na dauki"

abincin da na ajiye mishi wanda ni kaina

rabon da nayi girkin gidan da shi har na

manta saboda ba ya ci.

Nayi sallama a daidai. kofar dakin na

shiga ba tare da na jira amsawar shi ba.

"Wanka yake yi, don haka na zaunaa"

bakin gadon ina jiran shi. Ya fito yana

goge kanshi da karamin tawul nayi mishi

sannu na kuma gabatar mishi da abinci.

Bai ce mun komai ba sai da ya zo zai

kwanta.

"Ya ce, ""Ni fa kwanciya zan yi ko za ki"

"je dakinki ne?"" Wani abu ne ya tokare ni a"

"wuya, na mike na dawo dakina na kwanta."

Don takaici sai kawai na fashe da kuka.

Me ke faruwa ne'? Shin fita hanyar Ishak

zan yi ko ya ya? Abu daya ne ya sani na ji

sanyi da naje debe kwanukan abincin da

na kai mishi naga ya dan ci.

90

Yau ma shiri sosai nayi mishi ban damu

"da korata da yayi ba jiya, don kuwa gyara"

nake so.

Kuma na kuduri aniyar yi ta kowacce

hanya in dai ba fin karfina abin ya yi ba.

Ganin da nayi ya dan ci abincin yasa ni

yin niyyar yi mishi wani abincin da nufin

neman burge shi.

Sai dai kash! Ban ma san abincin da

yake so ba. To amma na cire wannan

tunanin a raina kawai nayi abincina mai

kyau kuma na burgewa na dan hada mishi

da kunun zaki.

Yau ma irin kwalliyar jiya nayi. Ban

kuma yi barci ba har ya dawo. Dakin shi

na bishi yana kokarin daure igiyar rigar

barcinshi na ajiye tiren da ke dauke da

food flask da sauran plate da cokula na

Juya na je na dauko Jug din da na ajiye na

kunun zaki na dawo.

"Ina shigowa ya ce, ""Ki kwashe"

kwanukan nan ki fita da su ba zan ci abinci

91

"a wannan daren ba."" Raina bai baci ba, na"

"ce ""To ga kunun zaki mai sanyi ne sosai."""

Na kalli yanayin shi yana daga kwance

hakan ne yasa na jawo kofi na tsiyaya

mishi kunun na mika mishi.

Kamar dai ba zai karba ba sai ya mike

ya zauna ya karba ya kara miko mun kofin

"na kara, mishi na tashi da niyyar fitar da"

kwanukan abincin da ya ce ba zai ci ba.

"Har na juya ya kira ni ""Zo ki zuba mun"

"kadan."" Na ce ""To."" Kadan din na zuba"

mishi na kara mishi kunun zakin sannan

na jira ya gama na kwashe kwanukan na

fitar.

Ban koma dakin ba nawa na shiga nayi

kwanciyata. Da sassafe ban koma barci ba

sammako nayi na yi mishi abin karyawa

cikin sauri na kawo mishi.

Har ya gama shiri lokacin da na shiga.

Kwalliya sosai nayi ya kalle ni ya kalli

"tiren kayan karyawan. Na ce ""Ko za ka"

"karya ne kafin ka fita?"""

92

Bai musa ba zama ya yi na zuba mishi

ya karya har ya mike sai ya kalle ni

"""Unguwa za ki je? Na ce, ""A'a."" Ya ce,"

"""Au to na dauka ko kin fara fita ne ba ki"

"tambaye ni ba."""

"Na ce, ""A'a ba za a yi hakan ba."" Yau"

wuni nayi cikin jin dadi a raina. wajen

karfe uku da rabi yaron da ya saba aikowa

da cefane yayi sallama.

Na zauna ina duba cefanen yadda ya

saba kawowa ne bambanci kawai shi ne

kafar Saniyan da na gani a ciki. Na dauko

"wayata duk da ban taba yin hakan ba, ban"

kuma san ya ya zai dauki hakan ba.

"Tana yin kara ya dauka, ""Lafiya?"

"Tambayar tayi mun wani iri, amma sai na"

"daure na ce ""Dama zan tambaye ka ne,"

kafar Saniyar da na gani za ka ci abincin

"dare a gida ne?"""

"""Da can sauran cefanen da ake kawowa"

"tambaya ki ke yi?"" Na ce, ""Aa."" Ban"

saurari jin karashen maganar ba na kashe

93

wayar saboda abinda naji a cikin zuciyata

na tamkar ina kokarin cusa kaina da yawa

a wajen Ishak.

Na hada kayan kawai na sanya

kowanne a mazauninshi na kuma wanke

kafar da niyyar yin miyar ganda da ita.

Sai da na hada komai sannan na dora

tuwon shinkafa. Na gyara kicin din na

kammala komai a mazauninshi. Na dawo

daki nan ma na kara kikkintsa abubuwan

da suke bukatar kintsi.

Sai da na gama ayyukan abinci sannan

na shiryawa Ishak nashi abincin a inda na

"saba, tare da sauran kunun zakin jiya"

wanda ya kara jika.

Yayi dadi ba kadan ba. Na shiga wanka

na hado da alwala nayi sallar Magriba

sannan na zauna domin nayi shafa.

Yau ana idar da sallar Isha'i kawai sai

ga Ishak shi kanshi ya gane nayi mamakin

"hakan, sai da ya gama shirinshi kafin ya"

fito ya zauna a falon.

94

"""Kawo mun abincin nan wurin"". Na"

shiga dakinshi inda na ajiye abincin nashi

na fito dashi na zuba. Ba karamin abinci

"yaci ba, don kuwa miyar tayi dadi ba"

kadan ba.

Na gama kwashe kwanukan sannan na

dawo ina kallon tashar da ya kamo ta

Aljazeera yana sauraron labarai.

Sai wajen karfe goma sannan na mikKe

don kwanciya. A raina nasan 1dan na ce

zan jira Ishak ban san lokacin da zai

kwanta ba.

Haka nan kwanakin da nayi ina zaman

jiran dawowarshi sun sa barci ya kama ni

da yawa. Na gama shirina na zauna a

bakin gado ina addu'o'ina da na saba yi na

"kullum kafin kwanciya, sai ya shigo."

"""Zo mana."" Na mike na bishi.ba zai"

yiwu na ce Ishak yana neman mata ba don

kuwa ban gani da ido ba bani kuma da

wanda zai fada mun.

95

Amma idan abin shi ya motsa mishi na

fushi ko halin da ya saba yana jimawa ba

tare da ya neme ni ba sat da tun da na

samu na fara shawo kanshi ta wannan

hanyar al'amuran gidana sun dan fara yi

mun sauki.

Na farko dai ya daina zaman karfe sha

"daya ko sha biyu a waje, idan yayi dare to"

"karfe goma, duk kokarin da nayi kuma na"

ganin na gane ko na fahimci abin da yake

yi a wajen na gagara.

Tun da na lura da shi na gane ina janye

"hankalinshi da irin shigar da nake yi mishi,"

kullum da irin wacce nake canzawa.

nKo da ba ya cewa komai kuma ina gani

a aikace. Sai dai abubuwa kullum da irin

wacce take zuwa.

Shirin da nayi musamman don naje gida

"yau amma sam 1shak ya ki yarda, duk"

kuwa da na gaya mishi cewa Umma zanje

gayarwa saboda rashin lafiyar da take yi.

96

Har Hindu da Móminta sun je sun

dubota amma sam shiya ki barina ya

kuma ki |uwa shi ya dubota.

Kullum sai dai na kirata a waya. Na

záuna na buga tagumi duk wani abu da

nake Rokarin ya rage mun Bacin rai ya ki.

Da ya dawo kuwa ban fasa yi mishi

abinda na saba ba. Amma gari na wayewa

"da na kara rokonshi ya ki, ban ce mishi"

komai ba.

Yana fita sai na shirya na dauki gyalena

burina bai wuce naga halin da Umma take

"ciki ba, tunda ni dai zamana da ita ban"

taba jin tayi wata rashin lafiya ba.

Don haka hankalina a tashe yake ba

kadan ba.

"Jikin nata babu dadi sosai, amma duk"

da haka ban zauna ba don kuwa kwata

kwata ban fi awa daya ba na dawo.

Na dawo duk da dai ban ji dadin ganin

"da na yi wa Umma ba, na samu saukin"

97

damuwar rashin Zuwa dubata da.ban yi ba

kwana da kwanaki.

Ban dade da shigowa ba sai ga Ishak ya

shigo ina yi mishi sannu bai tsaya amsawa

ba sannan yanayinshi gaba daya ya canza.

Ina ki ka je? Shi ne tambayar da ya

fara yi mun. Nan da nan na kama inda-

inda kan in san abinda zan ce tuni ya

dauke ni da mari kauu!

"Duka Ishak ya yi mun mai shiga jiki,"

sannan yayi ficewarshi ya komawurin aiki.

Tun daga lokacin wani irin zazzabi yaa

rufe ni wanda yafi kama da na bacin rai da

bakin ciki.

Bai dawo ba sai can cikin dare. Ina

zaune a tsakiyar gadona har a lokacin

kukana bai kare ba.

"Washegari, kuwa ga zazzabi, ga karin"

"tsamin jiki, Don haka ko, tashi nayi abin"

karyawa ban yi ba. Sai da naji yunwa tana

neman nakasa ni ne na tashi na lallaba na

hada tea na sha.

98

Har dare yau ma ban samu nayi abinci

"ba, don kuwa ko sallah da kyar nake iya"

mikewa nayi.

Haka nan yau ma da ya dawo sha dayan

"dare bai leko ni ba, dakinshi ya shige da"

gari ya waye ya yi sammako kamar dai

dabi'arshi ta da.

Nayi kukan takaici har na gaji nayi

"shiru, Ishak wane irin mutum ne wanda ko"

kadan bai san hakkin zaman aure ba?

Amma kuma shi yana so ya sanyawa

mutum dokar rashin adalci kuma yabi.

Lallabawa nayi na shiga gidan su Hindu

duk da sanin da nayi me hakan yake nufi

idan har ya gane.

"Momi