Back to novel

Chapter 5 of 6

MAI DAKI Ilimi Da Talauci BOOK 1 BY Nana Haleema | Hausa Novel

tana ganina ta fara salati. ""Ba ki"

"da lafiya ne Hauwa'u? Na ce, ""Eh Momi."

"Hindu nake nema."" Ta ce, ""To je ki gida"

"gata nan."""

"Hindu ce ta gyara mun gida ko ina,"

sannan na sa ta tayi mun faten tsaki don

abinda zan iya ci kenan.

99

Na kuma yi matukar sa'a na samu na

sha sosai nayi wanka na dan samu karfi a

jikina.

"Ita ce kuma ta taya ni nayi girki sosai,"

tuwon semovita miyar kubewa danya da

taji tantakwashi da naman rago na' hada

komai na ajiye wa Ishak a wurin cin

abincinshi na shige daki na kwanta.

Duk da dan (Paracetamol) din da na

"samu na sha jikina bai yi sauki ba, sai"

dada tsananta yake yi.

Da sassafe na lallabo na shiga dakin

Ishak yana zaune yana duba wasu takardu

rabon da na saka shi a idona kwana hudu

kenan yau.

Yanayin da ya ganni a ciki bai hana shi

yamutsa fuska ba. Wane irin abu ne haka

ke wai wacce irin yarinya ce? Kin ga

yadda ki ka yi wujiga-wujiga kuwa?

Don Allah can wuce ki gyara jikinki

kafin ki zo mun nan muryata tana rawa ta

"ce, ""Ba ni da lafiya ne."

100

To idan ba ki da lafiya sai ki zo mun

haka? Mits! Fita don Allah kije kiyi wanka

"wawiyar yarinya kawai."""

Dawowa daki nayi na zauna sai da

nasha kukana ya ishe ni sannan na mike na

lallaba nayi wanka na saka doguwar riga

mai gyale na zauna na hada tea din da zan

sha.

"Ruwan lipton ko birebi ban iya ci ba, na"

koma na sake kwanciya don ko

Paracetamol din da zan sha ba ni da shi ya

kare.

Ishak bai fito ba sai wajen sha daya

kasancewarta Asabar. Sanye yake da Jeans

blue a shirt long sleeve wuce muje.

Hijabi na dauko muka fita zuwa asibiti.

Muna zaune a gaban Likita bayan ya

"tabbatar mana ciki ne da ni karami, ya"

kuma rubuta mana prescription na

magunguna wadanda muka karba a

chemist din asibiti muka kamo hanyar

komawa gida.

101

Tsananin zazzabin da ke damuna vasa

ban ma lura na gane hanyar da Ishak yab

ba sai da ya ce mun fita ki shiga ina

jiranki.

"Na duba naga a kofar gidanmu muke,"

cikin sauri na bude kofar motar na shiga.

"A kicin na samu Umma taji sauki sosai, na"

durkusa a gefen kicin din tana kallona.

"""Hala kema ba ki da lafiyar ne ko naga"

"kin zama haka?"" ban bata amsa ba sai"

kuka da na fara yi mata.

"""To menene kuma na kuka ai hakuri za"

"ki yi ba a yiwa ciwo kuka Hauwa'u, ki"

zama jaruma. Ban daina kukan da nake yi

"ba har ta gaji ta.ce ""Ko dai kina da wata"

"matsala ne?"""

"Ban san me zan cewa Umma ba, ta gaji"

"da tambayata ta ce ""Uhm, hakuri fa ake yi"

"da komai ma da ki ka gani na duniyar nan,"

ballantana zaman aure.

Kada ki sa wa kanki wata damuwa

game da lamarin mijinki tunda dai bai

102

gaza miki da komai ba. Bai zama lallai sai

ka samu yadda ka ke so a kowanne lokaci

"ba, kin gane.?"""

Na tashi na yi wa Umma sallama na fito

muka dawo gida da Ishak. Wanda tsawon

watanni goma sha daya da nayi da shi a

matsayin matarshi ta aure bai sa shi ya yi

tunanin rana daya yaje ya gaisa da iyayena

da suka ba shi aurena ba.

Har kuma da rashin lafiyar da Ummana tayi.

Ciwo sosai nayi na wajen wata kusan

"guda ina kwance ko aikin gida bana iyawa,"

sai Hindu ta shigo tayi mun.

Ban samu saukin laulayin da naketyi ba

"sai ana gab da sallah, ba ta fi sati biyu ba."

A cikin akwatina na dauki atamfa daya

da shadda mai laushi na bayar aka kaiwa

Umma don ta dinka atamfar ta bayar da

"shaddar don a dinka wa su Tasi'u, tunda"

bani da kudin da zan saya musu.

103

Ni kam Ishak yayi mun har kala biyu

"masu kyau sosai, ban ma san da su ba sai"

da ya karbo su daga wurin Tela.

Daga ni har shi din shirin sallar muke yi

ba kadan ba. Ta bangare na dai wannan ita

ce sallar da zan yi ta farko a dakin aurena.

Shi kuma yayi sayayya na abinci ba

"kadan ba. Nayi cincin, cake, sannan nayi"

miya mai dadin gaske da taji naman

Saniya.

Sannan na soya naman kajina gaba

daya. Ga kunun zakin da nayi wanda ya ji

kayan yaji sosai da busasshen dankali.

Hindu ce ta shigo da sassafe tun kafin a

tafi sallar Idi ta rinka mika mun abincin

gidajen makwabta saboda sammakon da

nayi na gamawa.

Tayi sallama a bakin kofä saboda sahin

"da tayi Ishak na nan, na amsa mata na fito"

"ina tambayarta akwai,sauran gidan da ba a"

baiwa ba ne?

104

"Ta ce, ""A'a."" Na ce, ""To don Allah idan"

kin yi wanka sai ki kai mun na gidanmu

"Ta ce, ""To."""

Na shiga daki da shiri na shiga wanka.

Ke zo nan. Ishak ne ya kira ni.

Kwanakin baya ba na hana yarinyar

nan shigowa gidan nan ba? Ba na ce bana

so ba? Gidannan wai shin ba gidana ba ne?

Idan na ce bana son abu menene dalilin

"da yasa ba za a bari ba, ki kiyaye ni fa! Me"

take zuwa ku ke yi? Gulma ko ba ki

munanan shawarwari da koya miki

"dabi'un banza? To ya ishe ni haka."""

Karo na farko da al'amarin Ishak ya

gundure ni na zuba mishi ido ina kallonshi.

Yana dandanna wasu lambobi ne a

"waya, alamar zai yi kira. Kamar na ba shi"

amsar maganganunshi sai naga ba zan iya

ba.

Yayi mun kwarjini da yawa sai kai na

wuce shi na shiga bandaki nayi wankana

na fito.

105

Lokacin nan kuwahar ya gama

shirinshi. Jamfa ce a jikinshi dogswa ta

yadin shadda geitzner ja. Tayi mishi wani

irin kyau.

Ban taba ganin ya saka babbar riga ga

wata kila don baya ra'ayinta. Yana rike da

hularshi yana kokarin karyata haka kawai

na ga kalanta bai yi mun ba.

Na mika hannu na dauko watamai

ruwan ja da brown da wani ratsin nace ko

za ka ajiye wannan ne ka saka wannan

zuba mun ido ya yi yana kallona.

A hankali na ce mishi na gane kamar

tafi shiga da kayan. Ya mika hannu ya

karba bayan ya ajiye ta hannun nashi.

Ya karyata ya saka a kannan shi sannan

ya feshe jikinshi da turare. Yayi mun kyau

a idona. Ina matukar son yin mu'amalla

mai kyau da Ishak irin wacce nake ji ana

"bada labari,"

106

Don na san rayuwa ce da take faruwa a

"zahiri. Ya juyo da kallonshi gare ni, nima"

shi nake kallo.

"""Zan tafi hawan Idi, ana saukowa zan"

"dawo, don zan yi baki daga office dinmu."

Ayi mun shiri na abubuwan ci sosai don

"suna da yawa."""

"Na ce,To Allah ya bada sa'a."" Ya"

"kuma amsa mana lbadunmu. "" Ya ce,"

"""Amin.Ya fita."

Zama nayi na yi kwalliya ta burgewa ba

"kadan ba, na dauko yadin material wanda"

Ishak ya karbo mun daga gun Tela na saka

ya kuma karbi jikina ba kadan ba.

Gashi kuma na fara yin kibar ciki ga

fatata da ta yi haske tayi laushi zan iya

cewa ban taba yin kyau irin hakan ba.

Hindu ta shigo ita ma tayi kwaliya sosai

"ta shadda da ta sha ado. Ta ce, ""Kai Aunty"

"Hauwa, kin gan ki kuwa? Kin ga irin kyan"

da ki ka yi?

107

"Nayi murmushi na ce, Haba Hindu,"

"har na kai ki? Ta ce, ""Haba wane ni, keta"

dubi kalari kin san yadda ado yake yi wa

"farin mutum kyau kuwa?"""

"Na ce,""Ke kuma ga ki doguwa kin san"

kyau yana ga dogon mutum. 99 Gaba daya

muka yi dariya. Na ce mataTo barka da

"sallah, Allah ya maimaita mana."""

"Ta ce,""Amin."" Ta kwashe manyan food"

flask guda biyu da na cika da abincin

"gidanmu, daya dai miya ce da taji nama"

don kuwa raba miyar nayi biyu na juye

rabi.

Dayan food flask din kuwa soyayyen

naman kaji ne da cincin da kek. Na saka

mata a nan ne don kaninta ne zai rike

gudun bari.

Ban zuba shinkafa ba don nasan Umma

zata dafa. Na shiga shiryawa Ishak abincin

bakinshi komai na tanadan mishi.

Karfe goma daidai ya shigo gidan. Nayi

mishi barka da sallah ina kallon shi ga

108

zatona zai yaba kwalliyata tunda ko da ba

dabi'arshi ba ce yin hakan.

Ai kuma yau sallah. Bai ce mun komai

ba har na gama shirya mishi abincin shi.

"Ya ce ""Da kin bari sai sun zo muci tare."""

"Na ce, Ai ba ka da tabbacin lokacin"

zuwan nasu tunda yanzu ne ma aka sauko

"daga Idi, kaci ko babu yawa zai rage maka"

"yunwa."" Sai dai na daure ne kawai nayi"

mishi wadannan bayanan.

Don tuni zuciyata ta fara hankoron

fushi. Na shiga daki na zauna a bakin gado

naga abin bai yi mun ba.

Na gaji da abubuwan ko in kula da

Ishak yake yi mun ko ma meye zai faru

kawai ya faru a yau dinnan.

B Ban san lokacin da na ganni zaune kan

kujerar da ke gabanshi ba.

Na kare mishi kallo yana cin abincin shi

cikin nutsuwa kana kallon shi ka san ba shi

da matsala.

109

Ya dago ya kalle ni Yaya lafiya?

kullum salon tambayarshi kenan. Ban ce

mishi komai ba ban kuma daina kallon

nashi ba.

Kina da matsala ne? ko wani abu yana

miki ciwo. Wani tunani yazo mun cikin

raina da kuma yasa na fasa yi mishi

magana na mike da nufin komawa daki.

Hauwa'u na juyo tare da amsawa. A tun

farkon zamana da Ishak zan iya kirga

adadin lokutan da ya kira sunana.

Zo ki kwashe wadannan kwanukan na

"gama."" Na zo ina kwashewa., Dan"

sassaucin da na samu na mu'amalla ni

kaina nasan don juna biyun da nake dauke

da shi ne wani lokaci ya kan tambaye ni

akwai matsala ne ko kuma wani abu yana

yi miki ciwo?

Haka nan ya rage yawan dadewa a waje

karkari ya kai karfe goma shi kenan.

Na gama kwashewa da karin gyaran

wurin na dawo dakina na kwanta don

110

dan samu na huta ayyukan da na kwana

biyu ina yi.

Ya shigo dakin sanye da farar singilet

da wandon kayan da ya cire ya miko mun

kudi bandir din Naira dari sababbi fil da

su.

Na mika hannu na karba ina jira yayi

"mun bayanin abinda za a yi. Ya ce, ""Ki"

ajiye barka da sallanki ne. in tsaya cewa

kudin nan sun yi mun dadi ma bata baki ne.

Sai dai kan nayi mishi godiya aka fara

buga sallama. Ya juya ya shiga dakinshi

don dauko rigar shi da ya tu6e.

Ni kuma na jawo gyalena mahadin

material din jikina na yafa na fito har ya

ba su izinin shigowa. Lallai kam bakin

Ishak da yawa.

A can gefe na zauna müka gaisa da su.

Ban tsaya kallonsu ba amma nasan sun

kusa goma. Ban iya komawa ba lokacin daa

111

na shiga kicin tunanin yadda zan yi na kat

musu sa'a shima ya fito ya zo kicin din.

Bani abincin kawai ba sai kin shiga ba

tunda kun gaisa.Ya fara kwasa yana

shigarwa sannan na hada Plate-Plate da

kofuna na sake mika mishi ya shiga.

An dai kai kamar mintina talatin na

"motsin plate da cokula kawai nake jiwowa,"

yayin da nake zaune a single dakin dake

tsakar gidan.

Kafin daga baya hira ta barke. Ina

sauraronsu kowa da abinda yake fada

game da abincin yayin da ake sakawa

wasu waigi.

Hira sosai _uka shiga yi daga baya da ta

kunshi wajen aiki da kuma wasu al'amura.

Koda nake kwance a kan gadon dakinnan

na kasa barci duk kuwa da irin gajiyar da

"nayi saboda muryar Ishak da nake jiyowa,"

Da yadda yake dariya da wasu

"abubuwa. Mamaki ya kama ni, dama yana"

112

hira da mutane da ni ne.bai yi ko kuwa ya ya?

Ba su tashi tafiya ba sai wajen azahar

"suka fita gaba daya don yin sallah, bayan"

sun nemi nazo muyi sallama ya ce musu

nayi barci.

Na dawo dakin na sake gyara shi tsaf

"kamar ba a yi komai a ciki ba, sannan nayi"

sallah na hau gadona na sake kwanciya.

Ishak bai dawo ba sai wajen hudu da

rabi. Na mike na bishi dakinshi baya ciki

alamar yana wanka na zauna a bakin

gadon ina jiran fitowar shi.

Tunda ya fito nake bin shi da kallo har

"ya sanya short da jallabiya fara sol, sannan"

ya sake kallona.

Ga wannan suka ce na baki goron

sallah. Yana miko mun kudi na kalli

"kudin a hannunshi da yake miko min,"

sannan na kalle shi shima ni yake kallo.

113

"""Ya ya dai akwai matsala ne?"" Na ce,"

"""Eh akwai, wannan ma da ka bani da safe"

"gasu nan na dawo maka da su bana so."""

"Ba karamun kada shi maganata tayi ba,"

don tsawon zamana da Ishak ban taba

amsa mishi magana ba ballantana nayi

jayayya da shi.

Kuka na fara yi a daidai lokacin da na

"fara magana. ""Ni ba zan iya irin wannan"

rayuwar ba. Dama abinda yasa nake ta

"hakuri na dauka haka ka ke, haka"

dabi'arka da halayyarka suke. To ashe ni

kadai ka ke yi ma.

"Ya ce, ""Wacce irin banzar magana ce"

"wannan, ke lafiyarki kuwa?"" Na ce,"

"""Lafiya kalau, na dai gaji ne. Ban taba"

saka kaya a gidan nan ka ce yayi kyau ba.

Ban taba yin girki kaci ka ce yayi dadi

"ko bai yi ba, ban taba yin wani abu da"

nufin na burge ka ka yaba mun abinda nayi

ba.

114

Ni a kullum a wajen ka a kushe nake.

Bana gwaninta a wajenka sai kuskure. Ni

kulluma wajen ka mai laifi ce ni.

Ba ka ganin nawa da mutunci saboda

"ni, babu wani mutum da zai shigo cikin"

gidan nan da sunan wurina yazo ba tare da

ka wulakantashi ni kuma ka bata min

"ba..."""

"""Ke dakata! cikin tsawa ya dakatar da"

"ni. ""Ita ce ta turo ki ki zo ki titsiye ni?"

Kina nufin kin isa ki sa ni nayi abinda ban

yi niyya ba?

Wannan abin da ki ka zo ki ke yi ba zai

sa na canza daga dokata ta kada wani ya

shigo mun gida ba ko wanene ba tare da

yardata ba.

Kuma tunda yanzu na kara gane aibun

hakan nasan abinda zan yi kenan har kin

fara bin shawarwarinsu ne kina titsiye ni

"akan abin da bana so. To babu laifi."""

"""Ba titsiyeka nayi ba, kuma ni babu"

wani wanda yasan abinda muke yi

115

ballantana har ya bani shawara a kan

abinda zan yi.

Amma wacce irin rayuwa ce wannan?

Za ka iya zama da abokai kuyi hira kuyi

dariya tare amma ni matarka ta aure ba ka

da lokacina?

Idan gari ya waye ka fita ba zan sake

saka ka a idona ba sai wani wayewar

garin? Amma ni kana saka mun takunkumi

"na yin mu'amalla har da 'yan uwana, to..."

kafin na karasa tuni ya dauke ni da

marin da na kife a kasa.

"""Ki rinka fahimtar lokacin da mutum yá"

"gundura da abu."" Ya watsar mun da kudin"

a wajen ya dauki mukullin motarshi yayi

waje.

A hankali na mike na goge hancina da

"naji alamar ruwa-ruwa yana biyowa, jini"

ne. Ban ci gaba da kukan da nake yi ba sai

dai duk da gargadin da zuciyata take yi

mun kan abinda nayi nufin yin ban fasa ba.

116

Wannan karon shi ne karo na uku da

"Ishak yake dukana, Jakata na dauko har na"

fito na nufe ko'ina sai na tuna ko kudin

mota ba ni da shi.

Dawowa nayi na bude dakin Ishak har

yanzu kudin suna watse a kasa na sunkuya

na dauki gudan dubu guda uku a kudin da

bakin shi suka ce ya bani na sake shig

dakina na dauko kaya set daya na sake fita

a gidan bayan na rurrufe ko ina na tafi

gida.

"Ba karamin mamak1n ganina suka yi ba,"

don kuwa ban gaya musu zuwana ba.

Babana muma yake yi daga ganinshi

"kuma na san ya dan samu canji, don kuwa"

yayi fes da shi. Umma atamfar da nayi

"mata ce a jikint, haka nan su Ta_i'u."

"Umma ta zubo mun abinci ta ce ""Ga shi"

"nan duk da dai daga gidanki yake."" Na dan"

"yi murmushi na ce ""Umma ba ni, naki"

"mana na ci,"""

117

"Ta ce, ""Fuwo ne miyar taushe."" Na ce,"

Eh bani kawai. Cin abincin nay1 sosai

"sannan na sha kunun zaki. Ta ce, ""Amma"

ai ba yau muka yi da ke za ki zo ba ko?

"Lafiya dai ko?"""

Na dan yi shiru ban ce wa Umma koai

"ba. ""Idan akwai wani abu kiyi magana"

"mana, naga kamar ranki a bace yake."""

Na rasa ta inda zan fara yin maganar

"nan take kuma na kama kuka, sosai da"

sosai. Sai dai na kasa cewa Umma ga

matsalata.

"Ta ce, ""To ko nayi, iki magana da"

"Babanku ne? Na girgiza kai na ce, ""A'a."""

"Ta ce ""To ki share hawayenki kiyi hakuri"

"kowacce mata da ki ka gani, da irin"

matsalarta.

"Shi aure haka yake, kina hango na wani"

ne wani kuma yana hango naki. Ki daure

ki zamo mai sirTi a tsakaninki da mijinki.

Babu mai ganinki ya ce kina da matsala

"kwata-kwata, tunda mijinki ba gaza miki"

118

"ba, bai kuma yi tsari ba a ce tun yanzun"

kin koyi kai kararshi ba ki iya warware wa

kanki matsalarki ba tare da wani ko wata

ya fahimta ba.

Ki tashi ki koma kada ki dade kuma ya

"zama matsala, tunda dai da'alama ma ba ki"

"sanar da shi zuwan ki ba."""

Sai da Umma tayi wannan maganar ne

naji gabana ya yi matukar faduwa. Na

koma gida idan Ishak ya dawo kuma muyi

ya ya kenan?

Ban bari Umma ta fahimci halin da

"nake ciki ba, dauko kudin dake Jakata nayi"

na bata biyu na baiwa su Tasi'u canjin

kudin mota ta dari takwas na rage kudin

da za su mayar da ni gida.

Fitowar da zan yi kenan na hango motar

"Ishak ta karyo kwanar unguwarmu, cikin"

sauri na koma gida.

"Umma ta ce ""Lafiya?"" Na ce, ""Gashi"

"nan zuwa shima."". Ta ce, ""To, to Allah"

119

yasa kalau. Umma ce da kanta tayi mishi

shimfida suka gaisa.

Sannan aka kira Babana da ke tare da

wasu daga cikin makwabtanshi suna

tattaunawa. Gaisuwa sosai suka yi sannan

ya kawo goron sallah ya baiwa su Tasi'u.

An dan jima kafin ya nemi na fito mu tafi.

"Bai ce mun komai ba har muka iso gida,"

daidai an fara kiran sallar Magriba. Bayaan

gida na wuce nayi alwala na fito don bada

farali.

Shima a dakin shi yayi sallah. Ban fito

ba don kuwa na riga na kudurawa rainaa

zan zauna ne da lshak irin zaman da yake

"so muyi da shi, tunda dai haka ya zaba."

Lekowa yayi dakina ya kira ni na shiga

"yana tsaye. ""Kwashe mun kudin nan. Na"

sunkuya na kwashe su gaba daya..

"Ya ce, ""To zauna."" Na nemi wuri a kasa"

na zauna. Tashi ki zauna a bakin gado.

Nayi kamar yadda ya ce shima yazo bakin

gadon kusa da ni ya zauna.

120

"""Na dauka kina da tarbiyya hakan ne"

yasa ban taba yin zaton za ki yi abin da ki

ke yi a yau ba. Sake gaya mun abubuwan

da ki ka ce ba kya so wadanda nake yi

miki sai na kula nan gaba na daina.

"Amma abinda ba zan lamunta ba shi ne,"

ki kara zuwa mun cikin fusata irin na yau

ki ce za ki gaggaya mun bakaken

maganganu kin gane ko? Ba ke ce za ki

koya mun yadda zan rinka mu'amallata da

wasu ba.

Ina so ki san ke din ba za ki taba zama

"mai sa ni ko mai hana ni ba, koyi samuna"

cikin nutsuwa kina yi mun magana ta

yadda zan gane har kullum cewa ni ne

mijinki ba ke ce mijina ba kin gane ko?

Dokata ba za ta sauka ba na cewar ban

son shigowar waccan yarinyar cikin

gidana ba don a zahiri ga abinda ki ka yi

mun a yau wanda a da ba ki taba yi mun

"ba, gabanin fara mu'amallarki da ita."

121

"Na dago ido ina kallonshi ""Zan kuma"

dauki mataki da kaina ba sai kin shiga

matsala tunanin fuskantarta ba. Ba zan

lamunci masu son shiga lamarin aurena ba.

Na kuma yafe miki fita da ki ka yi ki ka

je gida a yau ba tare da kin nemi izinina ba

sai dai ina so ki san kin fitan ne a madadin

"wunin da za.ki je na gaisuwar sallah."""

Na mike da nufin fita a dakin. Ya ce

"""Dawo ki zauna. Na dawo na hau gadon"

na kwanta sai dai kuka na kama yi saboda

tukukin da zuciyata take yi mun.

Washegari da safe kamnar ba zan