Chapter 6 of 26

DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty

ganin tana takurawa sauran da ke hutu kusa da ita ya sa likitan ya ce a fitar da ita ta yi ta kukan a waje, aikuwa ta sha kuka, yi take babu ƙaƙƙautawa, faɗi take ya za ayi a barshi ya sadaukar da rayuwarsa a kan ta, ita ina za ta sanya ranta idan ba ya duniya. Kamar ma ta manta a gaban iyayenta take duk waɗannan maganganun.

Tun Mama na rarrashinta har ta gaji ta yi banza da ita, a cewarta idan jininta ya hau sai ta ji daɗi, Mama na rufe baki Hajiya Bilki ta yi sallama cikin ɗakin tare da Ashraf, Mama na ganin Ashraf ta washe baki tana faɗin.

“Babban mutum idonka kenan? Tun da ka yi aure ka ɓoye kan ka.”

Ya yi murmushi ya durƙusa kusa da Mama ya gaisheta, har cikin ransa yake son Mama, bai san me ya sa ba sai ya ga kamar ita ɗin tafi fahimtarsa a kan Mimi, ko a kan case ɗin aurensa Mimi ta dage ba zai auri wadda yake so ba, wai ita tarbiyar yarinyar ba ta yi mata ba, ba ta san wahalal da ya sha da zuciyarsa ba kafin ka ya amince zai iya zama da ita, har ya ce zai aure ta. Gaba ɗaya tsakaninsu baifi shekara biyu ba, yana da higher test sosai da sosai, kafin yaga mace ta burgeshi za a daɗe bare kuma ya sanya ta a ransa har ya so ta, amma ita Mimi duk bata fahimci haka ba sai da Mama ta sa baki sannan Mimi ta amince, kuma har yanzu baya ganin soyayyar matarsa a tare da Mimi, dan ma ita ma matar ta sa ba ta damu da Mimin ba rayuwar gabanta take, amma shi ba haka ya so iyalinsa su kasance ba, ya so ya sami matar da take da good understanding da Mimi, domin Mimi ita ce komai nasa a rayuwa, sai ko Dade da yake jin yana ɗan sonta, dan ya tabbatar duk tarin jikokin Dade soyyarshi ta daban ce.

“Babban mutum tunanin me kake haka? Ko mamakin kukan ƙanwar ta ka kake?”

Mama ta faɗa, ganin kamar ya shiga tunani, ya gyaɗa mata kai baya son magana ko kaɗan amma Mama kam tafi ƙarfin duk wannan a wajensa, duk da shi ba me sharing damuwarsa da mutane ba ne amma in dai ya kawowa Mama abin da Mimi ta gaza fahimta to ita yanzu zata fahimta har ta fahimtar da Mimi, a hankali ya ce.

“Ya jikin na ta?”

Murya cikin amo, wanda Husna ke ganinsa a tsabar girman kai da hulaƙanci, idan kuma ya yi maganar nan a rabe har tashin zuciya yake sanya ta, gaba ɗaya tsigogin jikinta su ta shi.

“Da sauƙi ita kam, shi wanda ya bada jinin ne abun sai addu’a kawai, shi ne take kuka.”


Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce.

“Waye ya bada jinin haka?”

“Wani malaminsu ne wallahi.”

“Allah Ya bada lada.”

Ya faɗa ƙasa ƙasa, tare da miƙewa ya fice. Yana fita Husna ta ja wani dogon tsaki a ranta ta ce.

“Kamar yanda girman kai ya halaka fir’una, kaima haka zai halaka ka.”

“Magana kika yi Husna?”

Mama ta faɗa, kamar jira Husna take ta ƙara fashewa da kuka abin da ya fusata Mama ta yi ƙoƙarin kai ma ta hannu, Mimi ta riƙe ta.

“Aminiya me kike yi haka? Kin manta a halin da take.”

“Ina ga yarinyar nan ban taɓa mata mugun duka ba, shi ya sa take wannan iskanci.”

Mama ta faɗa, Hajiya Bilki ta ce.

“Koma mene barta ta yi, wata rana ba zata yi ba.”

Ƙwafa Mama ta yi, sannan ta ce.

“Yarinyar nan da ban haushi take.”

Ai bata rufe baki ba Hajiya Bilki ta ce.

“Ga babban mai ban haushi nan, na rasa uban da ya kawo shi asibitin tun da sannu ma bai iya yi wa mara lafiyan ba.”

“To ita ta iya gaida shi ne? Ai har da shi yaja zan maketa, tana kallonsa ido cikin ido ba za ta iya ce mai ina yini ba. Husna abin da kika zaɓa kenan sai ki yi.”

Kukanta ta ƙarawa ƙarfi, ita Mama ba ta ga kallon hadarin kajin da ya yi mata ba, sai ita dan taƙi kula shi zata yi mata magana, kawai dan suna da kuɗi shine zai nemi ya hulaƙanta mutane to wallahi ita dai Husna tafi ƙarfin hulaƙanci a wajen kowa duk kuɗinsa kuwa.


“Ki yi shiru dan Allah ki ƙyaleta, wallahi dani yake zancen, ni banga abin da ya kawo shi ba ma, lamari idan bana waccan sallamammiyar matar ta shi ba baya shiga, wallahi dani yake zancen.”

Banza Mama ta yi da su, ita dai bata ga abin faɗa ba wallahi, Ashraf ne babba, Husna ce ya kamata ta gaida shi amma taƙi, to mene shi dan ya yi banza da ita? Bari ma shi da magana ba ta tsarin hallitarsa.

Ita dai Mimi haka ta yi ta mita har yamma, bata cikakken minti goma sai ta kushe matar Ashraf. Daman ko a gida abin da take yi kenan, Dade na tayata, a cewar Dade wai ɗauko musu tsuwar guzuma mai ido a tsaye.


Washe gari da daddare sai ga Ashraf da matarsa sun sake dawowa, sabida Mimi ta yi masa jan ido nesa ba kusa ba, tun da har yana iya cewa Mama tafi fahimtarshi a kan ta me ya sa bazai nuna kulawa ba ga ‘yarta da ke kwance ba lafiya.


Sai da ya bata haƙuri sannan ya sanar da ita zai je, amma shi bai san me ya sa yarinya ba ta yi masa ba, ba shi da ɗabi’ar ƙin mutane, amma ita dai yarinyar ya ɗauke ta ya Kaita can ƙarshe, ba zai iya fitowa ya ce ya tsani yarinyar ba amma yana ƙyamarta sosai, musamman daya fuskanci bata da kunya, gaɓa kawai take jira ta saukewa mutum kwandon jidali.

Zai je ne kawai domin Mama, mama tafi ƙarfin komai a wajensa, shi ya sa yana komawa ya sanar da matarsa, a farko ma bata nuna zata ba sai da ya ce mata yarinyar Mama ce, to ba laifi Mama tana sakar mata fuska indai sun haɗu, tana nan nan da ita ba kamar surikarta ba, ita kam babu abin da ya dameta ko me sirikiarta za ta yi. As long as tana zaune da mijinta to ita bata da wara damuwa da kowa dan ba sa gabanta.


Tun da suka shigo ɗakin kallo ɗaya Husna ta yi musu ta watsar, a ranta faɗi take ko mene ya sake dawo da shi Allah masani. Ko wannan ɓulkutar matar ta sa ya kawo, ita dai ta san matar ma ba shiga dangi take ba. A wannan karon Mama ce ta ce.

“Husna dan ubanki ba kya ganin anzo duba ki, kinja waje kin zauna?”


Baki ta turo gaba, sannan ta ce.

“Ina yini?"

Jamila ce kawai ta amsa gaisuwar itama a yatsine, shi kam Ashraf bai ma ko kalli inda Husna take ba, baya son rashin kunya shi ya sa baya shiri da duk wani mara kunya, yana girmama wanda ta cancanta to shima yana son idan ya cancanta a girmama shi.

“Shi yayan naki ba zaki gaida shi ba?”

Mama ta sake faɗa, Husna ta sake tura baki gaba kamar zai faɗo ta ce.

“Ina yini.”

Da yake gidan ta tarar ya yi kamar ma bai ji taba, sai Mama da ya cewa.

“Mama ina su Abdul fa? Mun kwana biyu bamu haɗu ba.”

Mama ta yi murmushi ta ce.

“Kuma dukkansu yanzu nan zasu shigo, ku ɗan jira su.”

Sannan ta mai da hankalinta ga Jamila ta ce.

“Ya gidan?”

Jamila ta yi murmushin yaƙe, sannan ta ce.

“Lafiya ƙalau Mama, kin ƙi zuwa har yanzu.”

Mama ta ce.

“To ai tun da kuna zaune lafiya haka ake so, Allah dai ya ƙara dauwamar muku da zaman lafiya, ya baku zuri’a ta gari.”

Sosai Jamila ta ji daɗin addu’ar Mama, haka shima Ashraf kulawar Mama ga ahalinsa tana ƙara mata girma sosai a idonsa, buɗe ƙofar ɗakin aka yi Ashir ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, suka amsa gaba ɗaya, sai da ya tsugunna har ƙasa ya gaida Ashraf, sannan ya gaida Jamila duk suka amsa fuska asake, Ashraf a ransa sai da ya ce. ‘Ita kuwa wannan fitinammiyar kamar ba Mama ta haifeta ba.’

Husna tun da Ashraf ya watsata ta saki ido da baki tana masa kallon mamaki, ta ƙulu iya ƙuluwa amma ko ba komai Mama taja mata, da ta barta ta yi banza da shi kamar yanda ta saba tun da shi ɗan girman kai ne da yafi.

Muryar Ashir ce ta dawo da ita daga tunanin ɓacin ran da take.

“Yaya, yanzu fa aka fito da Uncle ɗinku, yana ɗakin da ke jikin wannan, su Yaya Abdul da Yaya Walid suna can, har da Abba ma da Yaya Alhaji.”

Wani irin sanyi Husna ta ji ya mayaye rayuwarta, har ya mantar da ita ɓacin ran da Ashraf ya ƙunsa mata, ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon dan dama jikinta ya yi ƙwari sosai.

“A’a ki zauna mana.”

Mama ta faɗa, Husna ta ce.

“A’a Mama zan iya.”

“Ki zauna dan Allah, zan fita da ke.”

Mama ta sake faɗa, Husna dai ba ta ji ba ta ci gaba da ƙoƙarin tafiya.

“Ba magana ake miki ba.”

Ta ji ya yi magana cikin wani irin voice, wanda yake haifar mata da tashin zuciya, sabida har cikin jijiyoyinta take jin maganar idan ya yi, duk tsigar jikinta ta shi.

Kamar ba zata ji ba ta koma ta zauna tana faman gunguni, a ranta tana ji muguwar tsanar shi tana sukuwa a zuciyarta.

“Ina zata ne? Waye ya farka?”

Ya yi maganar yana kallon Mama, Mama ta ce.

“Wanda ya bata jini ne, ya bata da yawa shine har sai da ya yi jinya.”

Sai da yaji jikinsa ya yi sanyi sosai, amma duk da haka bai ci ace za ta fita ba dan ita ma jikinta ba wani ƙwari ya yi ba, ga hannunta nan ɗaure da kanula. Husna dai ta cika ta yi fam ta maste a ƙuryar gadon, so take ma ta buɗe baki ta yi mai rashin kunya, amma zallan tsanar shi da ɓacin rai da take ji ya mamayeta har ta kasa magana.

Sai da aka ɗauki kusan mintuna goma sha biyu sannan su Yaya Abdul suka shigo dukkansu ban da Abba, sosai Ashraf ya sakar musu fuska suka hau musabaha suna gaisawa, har ma hira ta ɗan ɓarke a tsakaninsu abin da ya sake ƙulal da Husna ganin ba wanda ya bi takanta, kamar wadda aka yi wa duka ta buɗe baki ta fashe da kukan da ya jawo hankalinsu, ba shiri duka suka yo kanta suna tambayarta me ya faru har da Ashir ma, ita kuwa ta ɓare baki sai kuka take suna ta faman tambayarta ko an yi mata wani abu ne? Jamila da ke gefe mamaki ya kusa Kaita lahira, wane irin guntun iskanci yarinyar nan take ji da shi haka?

Shi kam Ashraf takaici ne ya maƙure masa wuya ganin duk sun wani baibayeta suna tambayarta me aka yi mata. Alhaji ne ya yi magana dan dama shine bai cika ɗaukan kukanta ba, ya ce.

“Idan baki faɗa mana abin da aka yi miki ba sai na buga kanki da bangon ɗakin nan.”

“To buga."

Ta faɗa tana fashewa da kuka, cikin kukan ta ce.

“Daman Alhaji ko mutuwa na yi ai daɗi zaka ji, ban san katsane ni haka ba? Duk kun san banda lafiya amma kun shigo kunyi banza da ni.”


Haƙuri suka shiga bata kamar uwarsu, takaici ya sa mama daka musu tsawa.

“Dan ubanku ku bar yarinyar nan, ta dauwama tana kukan tun da bata san abin da yakamata ba.”

“Haba Mama bata da lafiya fa.”

Yaya Abdul ya faɗa, abin da ya sake bawa Ashraf Mamaki, har Abdul ma da girman sa ake wannan haukan, lallai dole yarinyar nan ta dinga shirme kala kala. Da ƙyar suka samu Husna ta nutsu ta daina kukan, sai da Walid da Alhaji suka riƙe ta zuwa ɗakin da Uncle Dee yake.

Bayan kwana biyu.


Daga jikin Uncle Dee har na Husna duk sun warke, sai dai babu wanda aka sallama a cikinsu suna sake samun kuluwar likitoci ne, Uncle Dee ya buɗe zuciyarsa yana bawa Husna duk wata kulawar da take buƙata, duk dai bai taɓa ce mata yana sonta ba amma yana nuna mata duk wata kulawa da ƙauna, Husna dai tace tana son sa yafi sau shurin masaƙi, sai dai ya yi murmushi ya ce mata.

“Baby girl.”

Bayan nan Husna ba ta taɓa jin kalmar soyayya daga wajensa ba, ita dai ta yi imani a zuciyarta tana son sa mussaman da ya zama yanzu da jininsa take rayuwa, sai ta ji kamar rayuwarta gaba ɗaya tasa ce ma. Har waya ya kira makaranta ya sa aka bawa Said Kibiya da Ali Kaita sun sha waya sosai har kuka suka yi suna tambayarta zata dawo, ta ce musu babu abin da zai hanata dawowa.

05:30pm

Yammace irin gari ya fara duhu rana ta yi yamma tana shirin faɗuwa, Suna tsaye daga wajen bishiyon asibitin, sun fita matso jikine da likitan ya ce abar su suna yi duk yamma sabida su ji ƙwarin jikinsu. Basu haɗe jiki ba akwai tazara a tsakaninsu, suna taɓa hira sama sama Husna ta ce.

“Banga ‘yan gidanku ba har yanzu.”

Kallonta ya yi fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce.

“Kina son ganinsu ne?”

Tana kallon ƙasa ta ce.

“Basu san kana asibiti ba?”

Ya gyaɗa mata kai, sannan ya ce.

“Na hana Moses faɗa musu, kuma daman sun san ina can makaranta, sai dai ya ce sun yi masa magana banzo weekend ba, to jiya dai mun yi waya da su na ce musu muna shirin yin third term exams ne shi ya sa.”

Husna ta gyaɗa kai alamar gamuswa, sai kuma ta ce.

“Naga yana ta yi mana wani kallo, baya son mu a kusa da kai?”

Sai da ya yi shiru na wasu ‘yan mintuna, sannan ya ce.

“Bai san girman soyayya ba, yana mamakin yanda na bada jinina a kan ki, sannan babban mamakinsa bamu haɗa addini ba, yana ganin kamar haram ne mu yi mu’amala da ku ta addini daban daban.”

Wani irin bugu ƙirjin Husna ya yi, wanda ya sa ta runtse idonta na wasu sakanni kafin ta buɗe su, da wani irin mamaki ta ɗaga kai ta kalleshi, muryarta na sarƙewa ta ce.

“Addini daban daban kuma? Wanne addini daban daban?”

Kallonta ya yi na watsu sakanni, ya ga zallan tsoro da firgici a tare da ita, baya ga mamaki da ya mamaye saman fuskarta. Hannu ya sa a aljihu ya zaro wata sarƙa ta cros ya nuna mata, Husna na kallo taji gabanta ya bada ras.

“Kai…kai ba musulmi ba ne?”

Ta faɗa bakinta na wani irin rawa, ya gyaɗa mata kai, sannan ya ce.

“Ni da ke muna da bambancin addini da al’ada, ke musulma ce ni christian, abun bautar mu ba ɗaya ba, tribe ɗin mu ba ɗaya, akwai tarin bambamce bambamce da zasuyi wa rayuwarmu ƙawanya.”

Wani irin yanayi Husna ta tsinci kanta, ta fara jefawa kanta tambayoyi, yanzu fa sai ace ba zan aure shi ba ko? Yanzu ya haramta a gareni duk da abin da ya yi min, to yanzu haƙura zan yi? Ina wallahi ba zan iya ba, ina sonka ina sonka.

Duk maganganun da take yi a zuciyarta kenan. Sai da ya ɗan matsa gaba da ita, daidai yadda rana zata rage mata ganin fuskarsa, kamar yadda ya yi mata lokacin farko da suka yi doguwar magana da shi, cikin amon muryarsa mai sanyi ya ce.

"Husna, kin kasance mace ta farko da ta shiga rayuwata ta hanani zuciyata sakat, komai na ke yi tunaninki nake, ba zan iya cewa ga adadin son ki da yake cikin zuciyata ba, ke ɗin ta daban ce.
Ina son ki, ina son komai naki, murmushinki ka ɗai abun ya isa ya dauwamar da rayuwata cikin farin ciki, rigimarki abar soyuwa ce a gareni.
Sai dai ƙa'idojin rayuwa sun sanya shamki a tsakaninmu. Ina tsoron kar soyayyarmu ta kai mu matakin da zamu rasa kowa namu."

"In dai ina tare da kai, ban ƙi na rasa kowa ba, kai nake so kuma kai zan so yau, gobe, jibi, har numfashina na ƙarshe."

Husna ta katse shi, sabida ba tason ya zo gaɓar da zai furta mata kalmar rabuwa, ya yi wani irin murmushi mara daɗi, ya ce.

"Ina tsoron kada na karɓi zuciyarki, sannan a tsakiyar tafiya al'ada da addini su sa mu miƙa wuya, mu bar zuciyoyinmu a tarwatse.

Ban koya miki darasin lissafi domin ki kasa yin lissafin makomarki ba."

Sai da ta matso kusa da shi, ta tsaya gab da shi ta zarar ta kasance mara yawa, har tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi, kaman yaddaa tata take. Asibiti ne, amma ita ji take kamar wani fili ne aka ware na masoya, ba ta jin komai ba ta jin motsin kowa sai shi, a hankali ta yi magana cikin wani irin salo mai bayyana zallan abin da ke zuciyarta.


"Ni Husna, in dai ina da rai ina da numfashi, kai zan so. Da jininka nake rayuwa, da sonka zan rayu."

"Husna."

Taji an kira sunanta da ƙarfi.


Legendspen
08129553971

🔥🔥*DA JININSA NAKE RAYUWA*🔥🔥


*-Amanan-Janafty-*
(07)


Waigawa Husna ta yi, idonta ya sauka a kan Alhaji yana ɗaga mata hannu, ta ja wani suririn tsaki dan ya yi matuƙar tsorata ta.

A ɓangaren Uncle Dee ya yi matuƙar jin mamakin kalaman Husna, bai san tana da wannan ƙarfim gwaiwar ba, ya yi tunanin da ta san bambamcin da ke tsakaninsu zata watsar da shi ta ce ba zata iya soyayya da shi ba, a hankali ya kamata hannunta ya sanya shi cikin nata.


“Husna, na rantse miki da ubangiji ina sonki, so mai tsananin girma, so wanda ba zan iya fasalta miki shi ba, so wanda yake yi min nauyi a cikin zuciya, so wanda yake dabaibaye zuciyata ya hanani sakat, ina sonki sama da kowacce mace a rayuwata.”


Wani irin sanyi Husna ta ji ya mayaye duniyarta, itama tana son sa so mai girma da bata san irin sa ba, tun ranar da ta fara ganinsa ta kamu da haukan son sa, tun tana musawa har ta dawo ta aminta tana son sa, yanzu yau gata gashi suna musayar kalman soyayya, bata san irin daɗin da take ji ba, ba zata iya fasalta