Chapter 8 of 26

DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty

ganin sa, aina zata sake jin motsinsa, muryarsa komai nasa. Ranar haka ta yi bacci tana faman tunani, gaba ɗaya cikin baccinta Uncle Dee ne, haka ta dinga ganinsa da duk wasu abubuwa da suka yi tare.

Washe gari da safe ma haka ta tashi jikinta sanyi ƙalau, gaba ɗaya babu wani karsashi a tare da ita, wata matsananciyar kewar Uncle Dee take yi, so kawai take ta yi ido biyu da shi ko zata daina jin yanayin kewa da ya dabaibaiyeta.

Bayan sati uku.


Gaba ɗaya zaman da Husna ta yi a gida ta sauya, babu wani kuzari ko magana ba ta cika yi ba, haka ‘yan uwanta zasu zo su yi ta jan ta hira amma sai dai ta bisu da idanu bata ko iya tanka musu ba ta yi, haka Ashir zai zo ya yi ta mata wasa amma bata kula shi, su kansu duk jikinsu ya yi sanyi a kan sauyin Husna, sai dai su yanke shawarar cewa babu abin da zasu bari ya sake haɗata da Iliya har abada.

Ganin zaman ya yi yawa har ta kai wata guda da dawowa daga asibiti kuma a jikinta tasan ta warke, kawai kewa da soyayyar Uncle Dee ce ke ɗawainiya da rayuwarta sai kuma ɗumbin tunanin me ya sa bai nemata ba har wannan lokacin, ko dai gidansu sun yi masa shamaki da ita? To me ya sa zai yi mata haka, sai kuma ta tuna kalaman ƙarfafa gwiwa da yake mata, hakan ya tabbatar mata cewar Iliya ba zai watsar da ita ba dole da wata a ƙasa, ko ya koma makaranta ne? Dole ma ta je Munjibir anan ne zata san komai.

Tashi ta yi zuwa falo ta sami Mama zaune a falo tana tsintar waken da za ta yi girki rana, zama Husna ta yi daga can gefe cikin sanyi murya ta ce.

“Mama.”

Mama ta amsa da Na’am, tana ci gaba da abin da take yi, cikin sanyi muryar dai ta ci gaba da magana.

“Mama, ya zancen makaranta na? Munjibir ɗin zan koma? Ko jeka ka dawo ɗin da kika faɗa, na gaji da zaman gidan nan.”

Sai da Husna ta gama magana, sannan mata ta ɗaga kai ta kalleta, cike da kulawa ta ce.

“A gaskiyya bana buƙatar ki koma wannan makarantar, zanfi so ki dawo nan kina zuwa jeka ka dawo zaifi, kuma shima mahaifinki haka ya ce.”

Shiru Husna ta yi, ita a yanzu so take kawai ta je Munjibir tasan anan zata sami labarin inda Uncle Dee yake, dan har lambar wayarsa zata karɓa wajen sauran malamai, cikin sanyin muryar ta ce.

“To Mama Allah Ya sa hakane yafi alheri, yanzu yaushe zamu je can na kwaso kayana na yi sallama da ƙawayena su Said Kibiya.”

“Hakane idan Alhajin ya dawo sai kizo ki sanar da shi kamar yanda kika yi min, nasan zai sanya ko Abdul ko Walid ko shi kansa ya kai ki tun da sai an amso takardar transfer.”

“Tam Mama.”

Ta faɗa tare da tashi, tana zaune a ɗaki bata sake fita ba har sai da Abba ya dawo, kamar yanda ta sanar da Mama haka ta sanar da shi, kuma ya gamsu da hakan, ya ce gobe ta shirya zasu je da shi da Walid su gama komai. Sai da ta yi masa godiya sannan ta tashi ta shige ɗaki.


Washe gari da safe Husna ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, bayan ta sanya ta ɗauki wata baƙar doguwar riga ta ɗaura akai, ta yafa baƙin mayafi na baƙar doguwar riga, tasa baƙin plat shoe da baƙar jaka, ta yi kyau sosau. Yanda Husna ke ɗaukan wanka sai ka ranste wata buduruwa ce ʼyar 20 ko fi, tana da tarin suttura mussaman atamfofi da yake kasuwancin mahaifinta da ʼyan uwanta kenan. Tana zaune zasu haɗo atamfofi kusan tirmi goma su kawo mata, idan ta dawo hutu sai ta tarar anyi mata ɗinki ya kusa Seat 20, haka da salllah har sai ta gaji da wankan sallah, shi ya sa tasan yanda zata sanya kaya, kuma Husna irin matan nan ne masu diri, kowanne kaya tasa ɗas suke karɓar jikinta su zauna. Ba dai kaga Husna ta sa kaya sunqi amsar ta sai dai ita taqi amsar kayan da son ranta.


Tana fitowa daga ɗaki Mama ta bita da addu’ar kariya, suka shiga motar Abba suka huce ita da Abba da Yaya Walid, su biyu ne a gaba ita kuma tana baya tana kallon hanya, a ranta tana ayyana shikenan wannan hanyar ta yi mata wucewar ƙarshe kenan. Allah Sarki su Said Kibiya koya suke rayuwa tasan dai sun yi kewarta kamar yanda itama ta yi nasu, ta yi alƙwarin ko basu haddace lambar gidansu ba ita zata rubuta musu lambar Mama idan sun koma hutu su kirata, tun da yanzu ma kwalfain xasu yi, hutun gaba ɗaya bai wuce sati uku ba gaba ɗaya.

Tana wannan tunanin suka shiga cikin makarantar, ofis ɗin Pc suka nufa Abba ya sanar da ita komai a kan hukuncin da suka yanke, malamai suka zo suna ta faman yi mata ya jiki, daga nan pc ta bata umarnin taje ta haɗa komai nata ta tawo da shi, ta yi sallama da ƙawayenta da malamanta.

Jikin Husna har ɓari yake ta shiga cikin makaranta, bayan an haɗa ta da headcaptain da zata jagorance ta shiga cikin makarantar. Ɗalibai duk wanda ya ga Husna cikin shigarsa sai ta burgeshi, suna ta mamakin haka Abubakar Sheshe ta iya ɗaukan wanka, daman duk uniform ne yake rage musu kyau kenan.
A bakin Hostel ɗin head captain ɗin ta tsaya sabida suk an san juna ba wai tsayawa zata yi a kan ta ba, Husna na shiga cikin ʼyan Hostel ɗin suka yo kanta suna mata sannu, sai murmushi take musu tana amsawa, ba ta ƙara sa shiga Said Kibiya ta shigo ciki da gudu tana famfo aka ce mata Abubakar Sheshe tazo, tana zuwa ra rungumeta sai suka fara kuka, har da Ali Kaita ma har suka ƙarasawa bakin gadonsu, sai da suka yi mai isarsu sannan Husna ta ce.

“Kayana fa nazo kwashewa Mama ta ce ba zan dawo ba.”

Aikuwa suka ƙara fashewa da kuka, shikenan zasu rabu da aminiyarsu, sun yi matuƙar kewarta gashi ashe rabuwar dindindin ce, suna cikin kukan Husna ta ce.

“Ina Unclee Dee?”
Said Kibiya ce ta ce.
“Shima fa yazo ya kwashe kayansa, ya bar makarantar gaba ɗaya, amma ya bada takarda a ajiye miki ko?”

Ta ƙarasa maganar tana kallon Ali Kaita da wasiƙar ke wajenta, Husna ta ce.

“Tana ina? Kun san me ya faru kuwa?”

Duk suka zuba mata ido, daman sun san zasu ji komai a bakinta idan ta dawo.

“Uncle Dee sai da yaban jini leda biyar, har jinya ya yi shima, kuma ya ce yana son amma kun san mene matsalal?”

“A’a.”

Said Kibiya ta faɗa, Husna taja dogon numfashi ta sauke, ta ce.

“Ashe ba musulmi ba ne.”

“Kai! Waya faɗa miki?”

Ali Kaita ta faɗa, sabida abun ya yi matuƙar girgizata, Husna ta ce.

“Shi, gashi iyayensa ma sun zo har asibitin sun yi mana kaca kaca, kuma har matar aure an bashi, gashi a lokacin ya ce mu ɓoye gaskiyya har zuwa lokacin da zamu sami mafita.”

“Chaɓ, daman ni ban taɓa ganinsa a massallaci ba.”

Said Kibiya ta faɗa, Husna ta basu labarin abin da ya faru gaba ɗaya, har da soyayar da suka ƙulla, da kuma abin da ta yanke, Ali Kaita ta ce.

“Tun da yana son ki kam tsaf zai musulunta, Allah Ya sa yana da rabo.”

“Amin amin.”

Suka amsa, sai Husna ta ce.

“Allah Ya sa akwai lambarsa anan, dan ni ita nazo nema, wallahi ba zan iya rayuwa babu shi ba, da jininsa nake rayuwa.”
“Buɗe to.”
Said Kibiya ta faɗa, Husna ta buɗe takardar ta fara karantawa.
Daga sama cikakken sunansa ne, daga gefe kuma sunan Husna ne, sai kuma bayani kaman haka.
Dear Husna,
Ina rubuta miki wannan wasiƙar ne da idanu masu ɗauke da hawaye marasa adadi. Zuciyata tana ƙuna, ɗauke da zallan soyayyar da ko mutuwa ba ta isa ta goge ta ba. Ina son ki sani ina son ki, Husna. Zan ci gaba da sonki ba wai iya yau ba, har zuwa ranar da numfashina na ƙarshe zai fita a wannan duniya.
Mahaifana sun gaza fahimtar abin da yake cikin ƙirjina, kamar yadda naki iyayen suka kasa fahimtar cewa jinina da naki sun riga sun zama ɗaya. A kullum sai na kira Yayanki a waya, ina roƙo da magiya ko zan samu daƙiƙa guda kawai na ji muryarki... amma sun ƙi, sun rufe duk wata ƙofa da zata haɗani da ke. Yanzu haka kiran ma baya shiga, alamar sun toshe layina baki ɗaya.
Husna, ban san gidanku ba. Da na sani, da zan tako ƙafafuna na zo ko da kuwa 'yan uwanki za su yanka ni zan sadaukar da raina muddin zan sa idanuna a kanki kafin na mace.
A yanzu na bar aiki a wannan makarantar, babana ya sama min wani aikin daban. Ina nan zaune a Hotoro T-Shima, gida ya zame min tamkar kurkuku, zuciyata kuma tana saƙa ranar da ƙaddara za ta sake haɗa idanunmu.
Ina roƙonki alfarma guda ɗaya tak! Kar ki sare, kar ki daina sona. Ni ma ba zan taɓa daina sonki ba, ko da duniya za ta juyo mana baya. Ina fatan wata rana wannan wasiƙar ta isa hannunki, kuma ki neme ni a duk inda nake.
Naki har abada,
Iliya.
Kuka Husna ta fashe da shi, ta san daman Uncle Dee bazai taɓa ƙin nemanta ba na wannan lokacin, ashe ga abin da ya faru nan. Su Said Kibiya ne suka shiga rarrashinta har ta yi shiru, Ali Kaita ta ce.
“Ki haɗa kayan muje wajen Malamai ki yi musu sallama, sai mu fake dan nan mu karɓi lambarsa, kin ga komai zai zo da sauƙi.”
Haka suka yi kuwa, duk suka haɗa kayanta, banda kayan abinci dan babu abin da za ta yi da su, sai kuma rigar sanyi Ali Kaita da ta karɓa da Abun Hannu Said Kibiya, sai da ta karɓi duka lambar wayar ‘yan gidansu, ta maman Said Kibiya da ta Abban Ali Kaita daman wayar Yaya Abdul na jakarta, har ta bawa su ma suka ɗauke su hoto, ta ce zata tura musu ta whatsapp tana komawa gida, idan sun dawo hutu sai su buɗe group su dinga magana a can. Har lambar wasu ‘yan ajinsu ta karɓa. Daga nan suka wajen malamai, sai dai duk wanda suka buƙaci lambar Uncle Dee sai ya ce bai da ita, wajen Uncle Sulaiman za a samu kuma baya nan.
Gashi Abba sai kiran Husna yake a waya akan ta tawo ta shanya su, Said Kibiya ce ta ce.
“Husna zamu duba miki lambar kinga muma saura sati uku mu dawo hutu, sannan zan sanar da Mamana zan zo cikin gari gidan ƙanwarta na yi hutuna a can kinga sai mu hadu ko ba a sami lambar ba sai muje hotoron mu duba shi.”
Da wannan shawarar Husna ta dawo gida, bayan sun sha kukan rabuwa da su Ali Kaita, haka ta dawo gida tana lissafin kwanakin da suka rage ayi hutu. Aikuwa ranar jumaar da aka yi hutu ta kira lambar Mamansu Said Kibiya, bayan sun gaisa ta ce anje ɗauko ta ba a dawo ba.
Da yamma kam Mama na zaune a falo Husna na haddar karatun da Abba ya yi mata da safe wayar Mama ta fara ringing, Mama na dubawa ta miƙawa Husna tana faɗin.
“Said Kibiya aka saka.”
Da sauri Husna ta rufe Al Qur'anin ta karɓi wayar tare da tashi ta shiga ɗaki, Mama na jiyota ta ma faɗin.
“Sai yanzu kuka dawo? Tun safe na kira Mama ta ce anje ɗauko ki ba a dawo ba.”
Daga can ɓarin Said Kibiya ta ce.
“Tun azahar muka dawo, bacci na yi sai yanzu na tashi.”
“Manya, to yanzu ya ake ciki an samu?”
Husna ta tambayeta, Said Kibiya ta ce.
“Uncle Sulaiman dai ya hana wallahi, bayan da Ali Kaita ba ta yi ba, amma ya ce ba zai iya wannan kasadar ba.”
“Ai shikenan.”
Husna ta faɗa jiki a sanyaye, Said Kibiya ta ce.
“Amma kinsam Aisha Sharif tana da ita, amma wallahi ba yanda ba mu yi ba ta hana.”
“Ke na tsani Aisha Sharif ɗin nan, uban me take da lambarsa?”
“Ita ta sani, wai ashe an naɗa babbanta minista shine take wani iyayi a school anan ne ma muka ji tana da lambarsa.”
“Can su yanka.”
Husna ta faɗa, sai kuma ta ce.
“Yaushe zaki shigo?”
“Ina ga ranar Litinin idan Allah Ya yarda.”
Said Kibiya ta amsa ta, dan har sunyi magana da Antin tata, ta ce zata aiko a zo a dauketa, kuma a kwanar ganduje take basu da nisa da su Husna, sai da suka ɗan taɓa hira sannan Husna ta kashe wayar ta dawo falo, anan take sanar da Mama zuwan Said Kibiya, ta ci gaba da karatunta. Karatun take amma hankali da nutsuwarta basa tare da ita, kome take yi hankalinta na kan Uncle Dee, haka zata shiga ɗaki ta yi ta kuka kawai fuskarsa take son gani, ta rasa me yake mata daɗi.
Batasan ta iya zane ba sai yanzu da takama, dan duk littafanta ta cika su da zanen fuskar uncle Dee, zanen ya yi kama da shi, amma rashin nutsuwa yayin yin zanen da rashin kayan aiki ya sa zanen yaƙi yin kyau, amma kallo ɗaya zaka yi wa zanen kasan me zanen tana da baiwar zane, ita kanta har mamaki take idan ta tuna a makaranta Ali Kaita ke kwaɓa musu zane idan an ce su yi a biology amma wai yau ita ke zane haka.
Haka ta gama karatunta ta rufe Al Qur'anin ta ajiye ta koma ɗaki ta kwanta, rayuwarsu a asibitin Malam Aminu Kano ta shiga dawo mata a kan ta. Lokacin da Uncle Dee ya riƙe hannunta bata ji komai ba sai a yanzu taji tsigar jikinta na ta shi, ji take kamar hannunsa ne a cikin nata, ta lumshe idonta tana hango kyakywar baƙar fuskarsa, a fili ta furta.
‘Ni mai zan so a namiji fari dan Allah? Wane kyau ne da yafi naka Uncle Dee?’
Hawaye ta ji sun fara zuba a saman fuskarta, Allah Ya gani ta yi matuƙar kewarsa, babu abin da take so da muradi sai ganin fuskarsa da sauraron sassanyar muryarsa.
Sai da ta yi kukanta ta gama bacci ya ɗauketa, bata tashi ba sai dare a lokacin Abba ya dawo ta sanar da shi zuwan ƙawarta sannan ta sanar da shi zasu je gidan ƙawayensu na makaranta da ke nan cikin gari. Husna ba ta iya ƙarya ba, amma tun da aka zo kan lamarin Uncle Dee ta fara ɓoyewa iyayenta gaskiyar lamari, duk abin da ya shafe sa bata faɗa musu ainahin gaskiya, kuma bata ganin hakan a matsayin laifi tun da sune suka nuna basa son abin da take so.

Ranar asabar Said Kibiya tazo gidan antynta, a yammacin ranar tazo gidansu Husna ita da Hafsa ‘yar gidan ƙanwar Antynta wadda take sakuwarta, sun taɓa hira sosai sun kuma sanar da Hafsa duk abin da zasu yi, itama da ke ‘yar zamani ce ta biye musu, sannan suka yanke zasu je ranar litinin. A daren ranar suka tafi Husna ta so binsu ta kwana amma Mama ta hanata a kan cewa ba yanzu ba, Walid ne ya mayar da su gida a motar Alhaji, tare da Husna suka je gidan har ta shiga ta gaisa da Antyn Said Kibiya.
Ranar Monday kafin ƙarfe goma na safe Husna ta shirya cikin doguwar riga ta wani Green ɗin yadi mai santsi, tasa jaka da takalmi da mayafi baƙaƙe. Ba su Said Kibiya suka zo ba sai ƙarfe sha biyu na rana, Husna ta yi masifar ta gaji, ta kira su a waya ya kai sau goma sai da suka zo Said Kibiya ta ce mata wai yau Sunday tasan su Uncle Dee suna church shi ya sa suka zauna. Ita dai Husna bata bari sun gama gaisawa da Mama ba tafi to waje.
“Wai ke Abubakar Sheshe saurin uban me kike haka? Tun dai gamu mun fito zamuje ai dai shikenan ko? Yanzu wace area zamu nufa a hotoron?”
“T-Shama mana, ai nan ya ce mana.”
Husna ta faɗa tana yin gaba, Hafsa ce ta ce.
“To ai idan munje T-Shama wane ɓangare zamu yi?”
“Me zaku yi a T-Shima?”
Muryar Yaya walid ta shiga kunnen Husna, wanda ya haifar mata da matsanancin bugun zuciya.


Legendspen-Sayyid
08129553971
🔥🔥*DA JININSA NAKE RAYUWA*🔥🔥

*-Amanar-Janafty-*


(09)


“Me zaku yi a T-Shima, ina tambayarki kin bini da idanu.”

Yaya Walid ya sake faɗa, ransa a haɗe.

“Mun faɗawa Mama zamuje gidansu ‘yan ajinmu, ta gidansu Aisha Sharif zamu fara sune a T-Shima tun da yafi nisa.”

Husna ta sami kanta da shirga lafiyayyar ƙaryar da bata san ta ƙware a kai ba sai yanzu.

“Shine ina miki magana kin yi min banza? To duk inda zaku ki tabbatar la'asar ta yi muki a gida, sannan wannan kayan da yake jikin ki kar na sake ganin kin fita da shi.”

“Tam, in sha Allah.”

Ta faɗa bakinta har rawa yake, zuciyarta na wani irin bugu da ƙarfi ƙarfi, ya sa hannu a aljihu ya zaro kuɗi ya miƙa mata.

“Ku hau napep, kuma drop zaku ɗauka. Sannan idan baku san waje ba ku jaddadawa mai napep ɗin ku ce daidai waje kaza zai ajiye ku.”

“Tam Yaya, mun gode.”

Ta faɗa tare da amsar kuɗin, su Said Kibiya ma suka yi masa godiya suka tafi, Hafsat ce ta ce.

“Yayanki ne wannan?”

Husna ta gyaɗa mata kai, dan ita har yanzu zuciyarta ba ta daina bugawa da ƙarfi ba.

“Amma dai yana da kyau.”

Tsaki Said Kibiya ta yi, sannan ta ce.

“Kuma duk gidansu yafi kowa zafi ba.”

“Wallahi fa.” Husna ta faɗa suna ƙarasawa bakin titi, napep ɗin farko da suka tsayar ya ɗaga suka ce masa T-Shima zai kai su drop, ya ce dubu biyu, suka ce zasu bashi.

Tun da suka shiga cikin napep ɗin Husna ta ƙurawa titi ido, kawai fargaba take ji da kuma zaƙuwar haɗuwa da Uncle Dee, dafa kafaɗarta aka yi ta juyo ta kalli Said Kibiya, a hankali Said Kibiya ta ce.

“Husna Abubakar Sheshe, kisani duk wani abu