Chapter 10 of 26
DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty
"Haka kuma Allah ya sake jaddadawa a wata ayar ya ce. Idan kuka san su muminai ne, to kada ku mayar da su zuwa ga kafirai. Su (matan) ba halal ba ne gare su, su ma (mazan) ba halal ba ne gare su...' Suratul Mumtahanah aya ta 10.”
Abba ya mayar da kallonsa ga Husna ya ce.
“Husna, kin ji da kunnenki abin da Ubangijin da ya halicce ki ya faɗa? Aure ba tsantsar soyayya ba ne kawai, bautar Allah ne. Ta yaya za ki gina ibada a kan abin da aka rushe tun farko?”
Shiru Husna ta yi, maganar Abba ta soma taɓa ta, amma ai akwai zaɓi ko? Zai iya musulunta me ya sa Abba bai kawo wannan ba? Abba ya maida kallonsa ga Uncle Dee, bayan ya zuba masa idonu ya ce.
"Iliya, a tsarin Musulunci, mijin shi ne shugaban gida kamar yanda Allah ya ce. Ar-Rijalu qawwamuna 'alan-nisa. Addinin Musulunci ya amince namiji Musulmi ya auri macen da take Ahlul Kitab saboda Musulunci ya tilasta masa girmama Annabi Isa (AS) da Littafin Injila.
Amma addininka bai yi imani da Annabi Muhammad (SAW) ba ko Al-Qur'ani. Ta yaya za a danƙa mace Musulma a ƙarƙashin shugabancin namijin da bai yi imani da abin da ta yi imani da shi ba? Wannan zai shafi addininta, da makomar 'ya'yan da za a haifa, sannan ke Husna.”
Abba Ya mai da kallonsa ga Husna da ke kuka ƙasa ƙasa, ya ce.
“A tsarin addininsa akwai abincin da yake halal ne a gare shi, kamar naman alade, giya, ko naman dabban da ba a yanka ta da sunan Allah ba. Idan kuka zauna a gida ɗaya a matsayin mata da miji, a matsayinsa na shugaba a gida kina ƙarƙashin ikonsa, zai iya buƙatar ki dafa masa waɗannan abincin. A Musulunci kuwa, mutumin da ya dafa giya, ya matsa ta, ko ya taimaka wajen sarrafa abin da Allah ya haramta, la'anar Allah da ta Manzonsa tana kansa.
Ta yaya za mu gina rayuwar 'yarmu a gidan da kowace rana za ta iya aikata abin da zai janyo mata la'ana?
Bama wannan kaɗai ba, Idan safiya ta yi, Husna kina buƙatar tashi ki yi Sallah, ki sa hijabi ki fuskanci Alƙibla. Shi kuma mijinki yana shirin tafiya Coci ko gudanar da ibadar da ta saɓa wa kaɗaituwar Allah. Idan 'ya'ya suka taso a wannan gidan, wane ne za su bi? Mahaifinsu da ke tafiya Coci ko mahaifiyarsu da ke gudanar da Sallah? Wannan shi ne babban gurɓataccen yanayin da zai watsa imaninsu baki ɗaya.
Sannan Idan aka samu saɓani na aure wanda ya kai ga saki ko rabuwa, matakin da na san bakya so azo, to dole sai na faɗa miki. A Shari'ar Musulunci kina da haƙƙin Idda, da samun haƙƙin ki ta hanyar Hukuncin Alƙali. Amma muddin mijinki ba Musulmi ba ne, babu Shari'ar Musulunci da za ta haɗa ku ko ta tilasta masa ba ki haƙƙinki. Ba zai amince da hukuncin Alƙalin Musulunci ba, sakamakon haka haƙƙin ki na mace Musulma zai murƙushe kuma ki zama babu kariya.
Idan baku rabu ba har rai ya yi halinsa, a Shari'ar Musulunci, rabon gado dokar Ubangiji ce ta gindayayya. Manzon Allah (SAW) ya faɗa cewa 'Musulmi ba ya gadon kafiri, shi ma kafiri ba ya gadon Musulmi.' Idan ɗaya daga cikinku ya rasu, babu haƙƙin gado a tsakaninku ta fuskar addini.
Husna ba za ki gaje shi ba, shi ma ba zai gaje ki ba, kuma 'ya'yan da kuka haifa za su shiga tsakani na rashin samun gado. To duk a kan me zaki tura rayuwar ki a wannan wahalal? Idan kika yi duba da waɗannan hujjojin, ina sake tabbatar muku cewa auren mace Musulma da namijin da ba Musulmi ba kuskure ne guda ɗaya mai gina jerin saɓa wa dokokin Ubangiji. Saboda haka, wannan al'amari ya ƙare a nan! Babu aure tsakaninku har abada."
Abba ya miƙe tsaye, ya dubi Uncle Dee cikin girmamawa duk da ya rufe fuskarsa bai bar wata kafa ta tausayawa ba, hakan ya sanya masa kwarjini sosai da sosai, ya ce.
"Iliya, muna godiya ta musamman gare ka da halaccin jinin da ka bayar wajen ceto rayuwar Husna, da kuma nuna kulawa da ka yi. Muna maka fatan alheri a rayuwarka. Amma dangantakarmu da kai ta tsaya ne a kan wannan alherin kawai, babu wata alaƙa ta aure da za ta haɗa mu.”
Iliya ya ji duk abin da aka ce, amma shi dai bai gane ko abu ɗaya ba, ji dai ya ji amma fahimta babu abin da ya fahimta, jikinsa ya yi wani irin sanyi, a hankali ya miƙe kamar mai koyan tafiya ya fita.
Bayan Uncle Dee ya fita Abba ya kalli Husna da ke durƙushe tana kuka, muryarsa a kausashe ya ce.
"Husna! Ki saurare ni da kyau! Na rantsa da Allah wanda ya halicci ni ba za ki taɓa auren Iliya ba! Ko da shi kaɗai ne namijin da ya rage a doron ƙasa, wannan auren ba zai yiwu ba!
Daga yau, na haramta miki ambaton sunansa, na haramta miki sake sanya ƙafarki a makarantarsu, kuma babu ke ba sake magana da shi! Idan na samu labarin kina ƙoƙarin nemansa a ɓoye, wallahi kashinki ya bushe! Daga yau kowanne motsinki yana ƙarƙashin idon 'yan uwanki!”
Husna ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi, jikinta ya shiga ɓari saboda tsananin kukan da take, numfashinta ya fara sama sama, sai kuma ya tsaya cak, ta zube ƙasa sumammiya.
Hankali a tashe Mama ta yi kanta tana kiran sunanta, su Yaya Abdul ma suka hau kiran sunanta amma bata numfashi ko kaɗan.
Basu kai ga miƙata asibiti ba, aka gane suma ta yi, bayan an yayyafa mata ruwa ta farfaɗo, kallo ɗaya ta yi musu ta fashe da kuka, tana kuka tana faɗin.
“Wallahi ni sai na aure shi, shi nake so shi zan aura. Da jininsa fa nake rayuwa haba sai ka ce ban san hallaci ba.”
Bazan suka yi da ita suka barta tana ta faman kuka, babu wanda ya ce mata sannu har dare, bacci ma ɓarawo ne ya ɗauketa ranar sabida kukan da take yi bata da niyar kwanciya.
Washe gari da safe wayar Mama da take yi da Mimi ce ta tashi Husna, a ranta ta ce. ‘Ita Mama komai sai ta sanar da Mimi.’ haka kawai take jin ma ta tsani kowa a gidan nasu, ko breakfast a ranar Husna ƙinyi ta yi, tun suna banza da ita har suka fara mata magana, amma ta ce ita ba za ta yi ba.
Sai da Abba ya zaunar da ita ya yi mata nasiha mai ratsa jiki fiye da wadda ya yi mata jiya, sannan ya sanar da ita babu ita babu auren Uncle Dee ko da kowa ya musulunta, sabida idan har ya musulunta sabida yana so ya aureta, to musuluncinsa yana gareta ne kawai ba shi da wani lada wajen Allah, sabida ba dan Allah Ya musulunta ba, bare kuma shi da har a wannan matakin ma bai yi zancen musulunta ba, hakan ya nuna cewar yana nan a kan bakansa na addininsa.
Tun da Abba ya sa ƙafa ya fita Husna take ta rusa kuka, tun Mama tana banza da ita har ta yi mata magana.
“Ke wai wace irin banzar yarinya ce da ba ta san ciwon kanta ba, Husna?!"
*Cigaban labari*
Kukan ta ci gaba da yi, maganar Alhaji na dawo cikin kunnenta, mussaman da ya ce zai roƙi Allah Ya ɗauki ransa kafin lokacin da zata auri Uncle Dee, cikin kuka take faɗin.
“Wai ni shikenan dole sai na haƙura da wanda nake so? Da wane ido zan kalli rayuwa idan babu wanda nake so? Wallahi ba zan taɓa son wani ba sai Uncle Dee.”
Haka ta yi ta surutai cikin kukan nata, har aka yi magariba aka yi isha tana kwance, Mama ce ta shigo ɗakin daga bakin ƙofa ta ce.
“Husna ba zaki tashi ki yi sallah ba? Ko kin bi addinin nasa ne?”
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, kanta ne yake wanin irin sarawa kamar da gatari ake sara mata ƙwaƙwalwa, a hankali ta miƙe tsaye tana dafa bango ta fito ta nufi toilet, tsaki Mama taja a fili ta ce.
“Kina zaune a kan soyayya zaki halaka rayuwarki, wai Husna ma nawa take da har za ta yi wannan nisan a kan soyayya?”
Tsaki ta sake ja ta koma ɗaki ta ci gaba da lazimin da take yi, Husna kam ko a cikin banɗaki ta kwashe kusan mintuna 20 sannan ta kammala alwalar ta fito, adaddafe ta yi sallar magariba da isha’a tana idarwa ta kwanta a kan kafet ɗin, lokacin Mama ta shiga haɗawa Abba abinci sabida ya kusa shigowa, kuma indai ta tashi yanzu zata ɗauki kusan minti 30 kafin ta gama tun da har sai ya ci abincin zata dawo falon.
Wayarta da ke kan kujera Husna ta ɗauka, tana fargaba take rubuta lambar wayar Uncle Dee da ta haddace ta a kan ta, tashi ta yi ta shige ɗakinta tana shiga ta danna kira, sai dai har wayar ta tsinke ba a ɗauka ba, ƙara danna kiran ta yi shima har ya ƙare ba a ɗauka ba, tana shirin danna na ukun sai ta ji ƙarar shigowa saƙo, da sauri ta shiga wajen saƙon taga daga lambarsa aka turo.
“Ki yi haƙuri Husna, kalaman Abba sun shiga zuciyata fiye da yadda kike tunani, ina tunanin wannan soyayyar kawai mu barta hakan nan.”
Legendspen
08129553971
🔥🔥*DA JININSA NAKE RAYUWA*🔥🔥
-Amanan-Janafty-
(11)
Sai dai Husna ta sake maimaita saƙon kusan sau biyar, wannan ma ai ba zata saɓu ba, mutumin da take jin za ta iya rasa komai sabida son da take masa shine zai ce wai yana ganin su haƙura? Hannunta na rawa ta shiga rubuta masa reply.
“A'a Uncle Dee kullum kaine ke ce min kar na sare, idan muka tsaya a kan matsayar mu zasu haƙura su bar mu. Har yanzu ban ji anzo gaɓar da mu iya barin zuciyoyinmu a tarwatse ba, munsha wahala a soyayya to mu bari mu sha daɗin.”
Tana rubutawa ta tura mai, bayan ta tura ta ci gaba da kiransa ko zai ɗauka, sai dai kwata kwata yaƙi ɗaga kiran, sai da aka ɗauki wasu mintunan sannan ya ce.
“Mafita ɗaya ce Husna, tana da tsauri amma ita ce kawai mafitar mu.”
“Wace mafita ce.”
Ta tura mai tun da ta fuskanci baya son magana da ita ne, cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo mata da amsa.
“Mu gudu.”
Bata gama karantawa ba, wani ya sake shigowa.
“Mu gudu, muje can mu yi aurenmu, idan mu ka yi auren sai mu dawo, nasan zasu karɓe mu, babu yanda zasu yi dole su haƙura su samana albarka.”
Sai da Husna ta karanta saƙon kusan sau goma, tana jaddada kalmar guduwa, su gudu su yi aure. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, shin za ta iya ma wai? Guduwa ta bar iyayenta. Amma kuma ya ce ai aure kawai zasu yi sai su dawo, da sauri ta rubuta masa.
“Yaushe zamu dawo?”
“Ko yau muka tafi, gobe zamu ɗaura aurenmu, kuma a ranar zamu dawo tun da mun zama miji da mata. Idan kin amince ki fito mu haɗu a ƙofar nasarawa yanzu.”
“Yanzu!”
Ta mayar masa da amsa cike da mamaki, ya sake cewa.
“Eyh yanzu, Husna idan ba haka muka yi ba iyayenmu ba zasu yarda ba, kin san ina sonki sama da kowa a duniyar nan. Idan na rasa ki ban san inda zan sanya rayuwata ba.”
“Nima haka.”
Ta tura mai reply, tana tura masa ta miƙe daman sanye take da Hijab, jakar da ta fita da ita ranar nan ta duba akwai kuɗi a ciki ta ɗauka, daidai lokacin wani saƙon ya shigo.
“Kin taho?”
“Yanzu zan taho.”
Ta yi masa reply, cikin sanɗa ta fito ta ajiye wayar Mama a falo, ta fara tafiya kamar ɓarauniya, cikin sa’a ta buɗe ƙofar gidan ta fice, tana fita ta kwasa da gudu ba ta tsaya ko ina ba sai bikin titi, napep ta fara tsarewa tana faɗin.
“Ƙofar nasarawa.”
Ba ta ƙarasa faɗa ba taji an kama mata hannu da ƙarfi, waigowar da za ta yi taga Alhaji ne ya riƙe ta, ta fara ƙoƙarin ƙwace hannun ya ɗauke ta da wani zazzafan mari wanda ya haifar mata da ganin taurari suna zagaye a sama, da dukkan ƙarfinsa ya shiga jan hannunta, yana janta tana turjewa, haka ya kawota har ƙofar gida, suna ƙoƙarin shiga Abba ya dakatar da su.
“Alhaji, ai angama cika ta kawai.”
*Uncle Dee*
Tun barinsa gidan su Husna ya shiga wani hali, da ƙyar ya iya ƙarasawa gida. Kasancewar iyayensa basu san ya dawo daga tsarkake addinin da ya tafi ba ya sa shi nufar ɗakin Moses, tun da daman a can ya sauka.
Moses yana zaune cikin ɗakin yana haɗa shisha Uncle Dee ya shigo yana dafa bango.
“Dee? Me ya sa meka, me suka yi maka?”
Uncle Dee bai ba shi amsa ba ya kwanta a kan katifar ɗakin yana sauke wata irin ajiyar zuciya, sai da ya yi kusan minti biyar a haka sannan ya fashe da wani irin kuka, a cikin jinin jikinsa yake jin ya rasa Husna, kalaman Abba sun sanyaya masa jiki, ya ji kuma zai iya haƙura ya bar musu ‘yar su, sai dai ya san tabbas ba zai yi tsahon rai ba, in dai babu Husna kwanakinsa ƙayadaddo ne.
“Come on Man, kukan me kake? Na faɗa maka musulmin mutum bai san hallaci ba, bai san godiya ba, shi ya sa tun farko na hanaka ba su jini amma kaƙi, yanzu sun nuna ma halinsu.”
Banza Uncle Dee ya yi da shi, ya fuskanci babu wanda zai gane halin da zuciyarsa ke ciki, babu wanda zai fahimci son da yake yi wa Husna.
A daren ranar bacci ɓarawo ne ya yi gaba da Uncle Dee, washe gari ya tashi da jinya, zazzafan zazzaɓi ya rufe shi baka jin komai sai nishin da yake yi, duk ya sake ramewa a iya yinin ranar.
Moses kam duk kusan minti ɗaya sai ya tsine ma Husna da ‘yan uwanta, shi yana mamakin ma banzan hali irin na Uncle Dee yarinya tana binka har haka, tun da kaga bazaka sami abin da kake so ba ai zaka iya amfani da ita ka wuce wajen, amma sabida sokwanci irin na Uncle Dee ya tsaya wai true love.
Har dare Uncle Dee bai moru ba, yana ta faman jinya sai dai ya ɗan samu sauƙi ba kamar wayewar gari ba. Moses na zaune lokacin Uncle Dee na bacci kira ya shigo wayar Uncle Dee, har ya yi banza da wayar ya saki jin kira ya shigo, yana ɗaukan wayar ya ga anyi saving da heart, hakan ya sa ya tabbatar Husna ce, ganin irin wahalal da Uncle Dee yake sha ya yanke shawarar kawai ya ce mata su haƙura da juna kamar hakan zaifi sauƙi, tun da ya sanar da shi abin da Abbanta ya ce da shi.
Sai dai amsar da ta dawo masa da ita ta sa muguwar zuciyarsa ta motsa. Ya shirya mata ne tazo nan ya haɗata da Uncle Dee, duk masifa sai ya yi dis virgin ɗinta, idan ya so bayan ya yi ko iyayenta su amince ya aureta ko kar su amince sune suke da asara.
Abin da ya shiryawa Husna kenan, tana cewa yanzu zata fito shima ya miƙe ya yi waje, can ƙofar nasarawar yaje ya yi ta jiranta amma ba ta zo ba, rai a ɓace ya dawo yana bawa Uncle Dee labari, duk halin jinyar da Uncle Dee ke ciki sai da yaji ba daɗi kuma ya nunawa Moses ɓacin rai sosai abin da ya sa shima ya yi niyar komawa can tsarkake addini, dan shi ba zai bar addinisa ba a kan Husna, duk runtsi duk wuya sai dai ya aure ta yana addininsa, yanda ba zai hanata na ta addinin ba itama ba zata hana shi nasa addinin ba.
*Husna*
Dukkansu suna tsaye kowa ya yi carko carko, fuskarsu duk ta nuna ɓacin ran da suke ciki, cikin wata irin muryar da ba su taɓa ji ba, Abba ya ce.
"To wallahi ba a gidana ba, Asma'u. Tun da har kin fara wannan tunanin, to komai yazo ƙarshe, fito nan”
Ba kalmar ba a gidana ba ce, ta ƙara tsorata su ba sunan Asma'u da Abba ya ambata shi yafi basu mamaki, ba su ba kowa ya san Abba ba ya kiran Husna sai dai ya ce Nanata, idan yana son yi mata faɗa ne ma zai ce. Nana Husna, to amma yau ainahin sunan ma ya kira.
Husna da ke cikin ɗaki a zaune, dan a lokacin da Alhaji ya riƙo ta bai a jiye ta ko ina ba sai cikin ɗaki. hantar cikinta na faman kaɗawa ta tashi ta fito tsakar gidan, kanta a ƙasa ta durƙusa.
"Tun da abin da kika zaɓa kenan, daga rana mai kamar ta yau na yafeki cikin 'ya'yana, na haƙura da ke har duniya ta naɗe, soyayyar da nake miki Allah Ya bani wata 'yar da zata so ni ana gaba, dan haka ina son ki haɗa duk wani abu naki ki tafi ko ina ma zaki, abin da kika zaɓa kin Samu."
"Dan girman Allah Alhaji, dan soyayyar da kake wa Annabi Muhammadu a'a."
Mama ta faɗa tana zubewa a gaban Alhaji, Yaya Abdul ma ya zo kusa da ita ya zube, a take Walid da Alhaji ma suka zo suka zube har da Ashir, suka kama ƙafar Abba, Yaya Walid ya ce.
"Abba kar ka hukunta tata a haka, Abba wannan hukuncin dukanmu ka yi wa har da kai ma, kar ka je fa rayuwarta a wani hali na daban, Abba dan Allah kar ka watsar da tarbiya da ka shafe shekaru kana yi mata, Abba dan girma Allah ka yi haƙuri."
Kuka ya ciyo shi har ya kasa ƙarasa maganar da yake yi, Mama ta sake cewa.
"Idan ka ce Husna ta tafi ina zata? Mun bata dama kenan ta yi duk wani abu da take so, Husna