Chapter 11 of 26
DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty
"Mama ba wannan zaku yi magana ba dan Allah, ku yi magana a kan yanda zata dawo hanyar da ake so."
Alhaji ya faɗa, sabida baya so kalaman Mama su ƙara tunzura Abba da har yanzu bai ce musu ya haƙura ba.
"Ta je ko ina nema, abun ta nema ne ta samu, Allah Ya sani bangaza wajen tarbiyarki ba, a kullum ina yi koƙarina wajen kare duk wani haƙƙinki da 'yan uwanki, Allah Ya gani kuma zai shaideni a ranar gobe, ba zan miki baki ba Husna, amma zan barki da abin da kike so."
Yana kaiwa nan ya fice, tabbatacciyar shaida ta bai haƙura ba, Husna sai ta bar gidan.
"Kinga ni Husna, idan kika kasheni, kika kashe shi sai ki ji daɗin duniyar."
Mama ta faɗa, bata so ta yi kuka, ko ƙwalla bata fatan ta yi wa wani cikin 'ya'yanta, amma Husna ta dage ta tirji, ina za ta sanya ranta ta ji daɗi.
"Yanzu Mama mene abun yi? Yanda Abba ya fita dai yana kan bakansa."
Kallon Walid da ya yi magana Mama ta yi, bayan ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Mene abun yi, ita gwanar baka ga ko a jikinta ba, ba taƙi yanzu mu bata hanya ta fita ba."
Kallonsu suka mayar ga Husna da take kallon su ido ƙir, kaman ba a kanta ma ake magana ba. Cike da fushi da ɓacin rai, Mama ta ce.
“Abin da kika yi kin ji daɗi? Yanzu sai ki tashi ki tafi inda kika yi niyar zuwa ɗin, wallahi Husna ki sani duk abin da ya sami mahaifinki ko ni ko ‘yan uwanki, Allah ba zai barki ba.”
Tana kai wa nan ta shige ɗaki, ranta na yi mata soya, ya za ta yi da ranta? Shima Alhaji namene zai ce wai Husna ta bar masa gida? Idan ta bar gidan ta tafi ina?
Walid ne ya shigo ɗakin yana faɗin.
“Mama ya zaki taho nan? Ya kike so mu yi? Idan Abba ya zare hannunsa kema zarewa zaki yi?”
“Walid kenan, to me zan yi? Kana ganin yarinyar ba ta fasa abin da ta yi niya ba, yanzu ana bata dama ma sake ficewa za ta yi.”
“Wallahi Mama ba zan fita ba, Mama na yi danasani, wallahi na tuba na yi danasani, ban taɓa tunanin Abba zai yi min haka ha, Mama ku yi min afuwa, wallahi na daina son sa, Mama ba zan iya rayuwa babu ku ba wallahi, dan Allah ku ba shi haƙuri.”
Husna ta faɗa tana kuka, kuka daga can ƙasan zuciyarta, sabida abun da Abba ya yi mata ya taɓa zuciyarta, a take ta ji son da take yi wa Uncle Dee ya bar zuciyarta, a lokacin ta gane abin da ta aikata, ta gane girman laifinsa, ko a lokacin da Mama ta ce kamar ba ta da ita ake magana ba, suman zaune ta yi. Dan tun da Abba ya ce ba a gidansa ba ta ji ta ɗauke gaba ɗaya kamar ba ta raye ma.
“Wallahi Husna ƙarya kike, wannan maganar da kika yi iya bakinki kika yi ta.”
“Na rantse da girman Allah Mama har zuciyata na yi ta, dan girman Allah Mama ku yi min afuwa, ko yafe min, na yi kuskure na, na rufe idona na yi watsi da tarbiyar da kuka yi min, wallahi Mama ba zan sake ba.”
Husna ta ƙarasa maganar kuka yana cin ƙarfinta, ta kifa kan ta a ƙasa ta shiga raira kuka mai zafi tana yi tana tari, kukan da yake fita daga ainahin zuciyarta, yake goge duk wani mugun abu daga zuciyarta, a yanzu nadamar sanin Uncle Dee ma take yi, ko kuma nadamar biyewa zuciyarta da ta yi, wadda har ta kai ta ga wannnan baƙar ranar da ta santa iyayenta zubar da hawaye a kan ta, dan ido cikin ido taga ƙwalla a idon Alhaji, ga ‘yan uwan da suka so ta suka ƙauna ce ta kowa na kuka a kan ta, ita Husna ina zata kai wannan girman zunubin?
Ƙara fashewa ta yi da kuka, wanda ya sa Alhaji matsowa kusa da ita ya ɗago ta, ya kwantar da ita a kan cinyarsa ya shiga rarrashinta, cikin kuka ta ce.
“Yaya Abdul, Yaya Walid, Alhaji, Ashir dan Allah ku yafe min, na kasance butulu da bata san hallaci ba, na saka muku soyayyar da kuka yi min da saku ɓacin rai, dan girman Allah ku yafe min, Mama dan Allah karki ji haushina, kar ki sake zubar min fa hawaye, ku roƙi Alhaji Ya yafe min, ni kam zan roƙi Allah Ya ɗauki rayuwata, ko zaku hutu da saku maganar da na ke yi.
Tabbas Husna ta yi tuban gaske, tuban da ake so kowanne ɗan Adam ya yi, dukkansu a cikin ransu suka gamsu da haka, Yaya Abdul ya ce.
“Ki daina addu’ar Allah Ya ɗauki ranki, ki yi addu’a Allah Ya baki tsahon rai mai amfani, ya baki damar da zaki goge duk wani ɓacin rai ko damuwar da kika haifarwa da iyayenki, mu baki yi mana komai ba, ko kin yi ma mun yafe Husna.”
“Na gode Yaya.”
Yaya Walid ma ya ce.
“Duk mun yafe idan kin yi mana, yanzu Abba ne zaki nemi yafiyarsa, kuma kin san yanda Abba ya fusata a yanzu gidan nan ma ba lallai ya dawo shi yau ko gobe ba.”
Mama ce ta ce.
“Ai indai ba tabbatarwa ya yi tabar gidan ba, ba lallai ma ya dawo. Ni a rayuwa ta ban taɓa ganin mutum mai zuciya irin Alhaji ba, abin da nake gujewa Husna kenan, kar ta tayar masa da zuciyarsa da aka samu lafiya a kai, to yau ta tayar.”
“Mama yanzu mene abun yi?”
Alhaji ya tambaya, Mama ta ce.
“Ki shirya kayanki gaba ɗaya, ku je ku kaita gidan Aminiya, yanzu zan kirata na sanar da ita, nasan zata zauna a can zuwa shi kuma ya sauko.”
Dukkansu sun yi naam da zancin Mama, Alhaji da Ashir ne suka taya Husna kwashe kayanta, suka haɗa mata a jaka. Suna cikin haɗawa Mama ta shigo ɗakin ta ce dasu.
“Ku ɗiba da yawa fa.”
“Dayawa kuma Mama?”
Alhaji ya faɗa, Mama ta ce.
“Zata daɗe a can, har sai ya sauko.”
Shiru Husna ta yi, wai yau ita ce ke haɗa kayanta zata bar gidan mahaifinta na wani lokacin, haka suka haɗa kayan suka fito, har suka fita Mama ba ta ce da Husna komai ba, haka Husna ta fito tana kuka. Kukan da da ace ɗan Adam ya san ƙaddararsa da Husna kwantawa za ta yi a ƙasa ta yi burgima ba iya kuka da hawaye ba.
Haka ta yi ta kallon gidan nasu, kamar ta san kallon ban kwana take yi wa gidan ta tsaya tana kallonsa sosai, haka kawai ta ji zuciyarta ta yi rauni.
Sai bayan su Husna sun fita Mama ta kira Hajiya Bilki, bugu ɗaya ta ɗauka tare da faɗin.
“Aminya yanzu nake zancen ki a raina? Lafiya dai ko?”
Ajiyar zuciya Mama ta sauke, sannan ta ce.
“Ina fa lafiya? Ga su Husna nan zuwa gidanki, zata kwana biyu.”
“Me ya faru? Wai bata fasa abin da take yi ba ne?”
“Ina fa, Aminiya Alhaji ya hau kan dokin zuciyarsa, a yanzu ya ce ta bar masa gidan, ya yake so na yi da raina dan Allah?”
“Ya salam, Allahuma ajirni fi musibati, Ya Allah ka sauƙaƙa mana.”
Mimi ta faɗa tana runtse idonta, sai kuma ta ce.
“Bai kyauta ba ko kaɗan, amma ki yi haƙuri ki bashi lokaci, ta zauna anan ko zuwa yaushe ne, idan ya gama zuciyar sai ta dawo kawai.”
“To shikenan Aminiya na gode, yanzu zasu ƙaraso.”
“Tam sai sun zo.”
Mimi ta faɗa tare da kashe wayar, Mimi na kashe wayar ta lafta tagumi, a fili ta ce.
“Allah ka sauƙawa wannan yarinyar, Ya Allah ka cire mata wannan taurin kan na masifa.”
Allah ya sani tana son Husna, kaf cikin ‘ya’yan Aminiyarta tafi son Husna, haka take jinta kamar ‘yar cikinta, kuma bayan haka Aminiya ma tana son ‘ya’yanta kamar na ta.
“Ke kuwa Bilki lafiya kika rafka tagumi haka? Ko dan Asharaf ya ce zai zo da wannan gantalalliyar matarta sa ne?”
Dade da ta fito daga cikin ɗakin ta ta faɗa, sauke tagumin Mimi ta yi sannan ta ce.
“Ina fa Dade, ni mene alaƙa na da zuwan sa da ita, kawai wani abu na tuna.”
“To Allah Ya yi mana maganin abin da zai damemu alfamar Annabi da Al Qur’ani.”
Dade ta faɗa tana zama, tare da miƙawa Mimi arba’una Hadis.
“Ni kam Bilki ki ci gaba da yi min ƙarin hadisin nan mana, kinga tun a hadisi na ɗaya bamu ƙara yi ba.”
Karɓa Mimi ta yi, tasan sababin Dade yanzu ba ta isa ta ce mata a’a ba, zata hau sababi, Dade irin tsofaffin nan ne masu son addini, ba ta samu wani karatun ba, shi ya sa yanzu bata jin kunya ko nauyin neman karatu a wajen kowa, duk cikin matan da ɗan ta yake da su, tafi son Mimi da ‘ya’yanta, a cewarta ko ba komai Mimi da ‘ya’yanta sun san Allah kuma suna karatun addini, saɓanin sauran matan da ko izu guda ba lallai suka kawo maka ba.
Buɗe Hadisin Mimi ta yi zata fara karanta ma Dade, sai ga Ashraf ya yi sallama cikin muryarsa mai kama da raɗa.
“Bilki ba ni, tun da wannan yazo ma yi karatun bayan sun tafi.”
Dade ta faɗa tare da amsar kayanta, daidai lokacin kuma ya shigo, bayansa kuma matarsa Jamila ce, fuskarta a haɗe kana ganinta kamar wadda aka yi wa dole sai ta zo gidan, sai wani harare harare take, bata son gidan kamar yanda ta san masu gidan basa sonta, kuma ita ko a jikinta ɗansu ne dai ta aura ko zasu mutu ba zata rabu da shi ba.
Legendspen
08129553971
🔥🔥*DA JININSA NAKE RAYUWA*🔥🔥
*_Amanan-Janafty_*
https://www.arewapen.com/book?id=6a933361f3eaa6dc8f5ff715
Comment section
https://chat.whatsapp.com/DyVX8bRFbq66I04yzM5rLp?s=cl&p=a&mlu=0&ilr=4
(12)
Sai da ya sake yin sallamar sannan suka amsa, itama Jamila ta yi tata ciki ciki, Mimi ce ta amsa ita kam Dade ta bawa banzan ajiyarta.
“Dade barka da dare, Mimi barka da dare.”
Ashraf ya faɗa kansa a ƙasa, dan a rayuwarsa bai cika iya haɗa ido da mutane ba, mussaman iyayensa ko waɗanda suka girmeshi, duk da fitinarsa shima.
“Mimi ina yini, Dade ina yini.”
Jamila ta faɗa ganin yanda mijinta ya yi, sai a lokacin Dade ta ce.
“Daman da ke aka zo ai ban ji sallamar ki ba.”
Murmushin yaƙi Jamila ta yi a cikin ranta ta ce.
“Wannan tsohuwa dai anyi kininibabiya.” A fili kuma ta ce.
“Tare muke Dade, na yi baki jini ba ne.”
“To ke ɗin ce kina magana ciki ciki kamar bakya so, hala yanzu uwar mijin naki ma ba ta ji kin gaishe ta ba.”
“A'a Dade na ji mana har na amsa ma, ke ce dai baki ji ba.”
Mimi ta faɗa dan ita bata son sababin Dade, sannan ta sake cewa da Jamila.
“ku zauna mana ko tafiya zaku yi?”
“A’a ba yanzu ba, ai zan ga Daddy ma.”
Ashraf ya faɗa, Jamila ta taɓe baki ita ba ta son zuwa wanna gidan nasu.
“Ni kuwa Jamila haihuwa har yanzu shiru, aure yana neman shekara biyar.”
Dade ta faɗa, dan dama ita zancen ta kenan. Ashraf ne ya ce.
“Mu fa Dade ba haihuwa muka rasa ba, kawai ba yanzu muka shirya ba ne.”
“Allahuma salli ala, taɓɗijam. Wannan zamani Allah ka yi mana magani.”
Dade ta faɗa tana riƙe haɓa, sai kuma ta sake cewa.
“Uwarka ga tanan kamar ta yi bakwaini sabida saurin haihuwa, tsakanin Halima da Nusaiba ko shekara biyu bai rufa, kaine ma ka zama kalen hanji, shine zaka zo mana da kinibibi da sanabe, duk yayyanka maza kai ne ka ɗai ka samu dama ka yi aure shine zaka zo da wannan ɗabi’ar Yahudawan? Ke kuma kika biye masa ko?”
Dade ta ƙare maganar tana kallon Jamila, wadda take watsa mata harara ƙasa ƙasa.
“Ki harareni da kyau shi ya ja min, zan yi addu'a Allah Ya kawo masa matar da zata haihu, wadda ɗabi'ar Yahudawa bata ratsa su ba.”
Wani ƙululun abu Jamila ta ji ya tsaya mata a rai, wai kishiya ita akwai wadda ta isa ta yi ganganci shiga gidan ta a matsayin kishiya?
Mijinta ma da ba iya magana da mata yake ba wace zata iya da shi? Ai sai ita ɗin.
Ashraf ne ya tashi ya fita ba tare da ya ce da su komai ba, Daddy ne ya yi masa message ya sami shi a part ɗinsa, da sauri sauri yake tafiyar amma a nutse yake yinta cike da izzar da ta zame masa jiki, wadda shi bai ma san yanayi ba.
Hankalinsa yana kan wayarsa kawai ya ji an bangaje shi za a wuce, ko gezau bai yi ba sai ma wanda ya bugeshin da ya yi baya, kamar an ce ya ɗaga ido ya yi ido biyu da ita sai faman harare harare take tana hura hanci, wani irin kallo ya yi mata yana mamakin yanda yarinyar nan ta riƙa a rashin kunya, ta buge shi amma ta tsaya tana hararshi tana jiran shi ya bata haƙuri, kallonsa ta ci gaba da yi shima yana kallonta, cikin kaushin murya ya ce.
“Baki da hankali ne? Ko bakya gani?”
“Eyh.”
Ta faɗa tare da zagaye shi zata wuce, cike da fushi ya sa hannu ya kama tsintsiyar hannunta ya riƙe da ƙarfi, ba wai duka ƙarfinsa ba kawai ya yi riƙewar da ba zata iya ƙwacewa ba.
Husna ji ta yi kaman ankwa ya sa ya matse mata hannunta sabida wani irin damƙa da ta ji, ƙoƙarin motsa hannu ta fara amma taji kamar ya shiga inda yafi dacewa da shi sabida kwata kwata yaƙi motsawa.
A hankali ya janyota baya kamar yana jan akwati, sai da ya dawo da ita inda ta tsaya da farko sannan ya sake maimaita abin da ya faɗa ɗazu, kamar mai irga kalmomin da yake faɗa, ya ce.
“Baki da hankali ne? Ko ba kya gani?”
Taso ta sake maimaita abin da ta faɗa ɗazu, amma riƙon da ya yi mata ya shige ta sosai, sai da ta tura baki gaba sannan ta ce.
“To ai kaine ka taho kana danna waya, na matsa ma amma baka kula ba.”
Kallonta ya yi, yana son yin magana amma kuma bakinsa nauyi yake masa, a hankali yaja siririn tsaki sannan ya cika ta ya wuce.
Juyawa baya Husna ta yi ta maka masa harara, daidai lokacin kuma su Ya Walid suka nufa wajen suna riƙe da jakar kayanta, gaba ta yi ta shiga part ɗin da saurin ta, tana gab da shiga ta ji muryar Dade na faɗin.
“Duk lalacwar zamani Allah ka bar mu a naka.”
Taɓe baki Husna ta yi tare da fashewa da kuka haɗi da tura ƙofar da zata sada ta da fallon, kukan ta ya karaɗe ɗakin tun kafin ta ƙarasa shigowa, miƙewa Mimi ta yi tana faɗin.
“Husna ke dawa kike kuka haka? Ko tun daga gidan ne baki yi shiru ba.”
Rungume Mimi Husna ta yi ta ci gaba da kukan, hankali a tashe Mimi ke tambayarta lafiya har da Dade ma, amma ta ƙi ce musu komai sai faman kuka take, abin da ya yi matuƙar ɓata ran Jamila, daman mugun haushin yarinyar take ji sabida bata da kunya ko kaɗan, gashi haka kawai take jin wani ƙarin haushin nata ba tare da ta yi mata komai ba, ga yan da Mimi da Dade suke ta faman lallaɓata suna tambayarta amma ta yi banza da su.
“Husna ki yi shiru ki faɗa min abin da ya faru, Abban naku ne?”
Girgiza kai Husna ta yi, cikin kukan ta ce.
“Ashraf ne.”
Wani irin bugu ƙirjin Jamila ya yi jin Husna ta ambaci sunan mijinta, me ya haɗata da shi? Mijinta dai da ko kallon mata ba ya yi? Wani kallo ta watsawa Husna da ke ci gaba da kukan, Dade ta ce.
“Shi Asharaf ɗin me ya yi miki, daga zuwanki?”
Cikin Kuka Husna ta ce.
“Matse min hannu ya yi, ya kuma ranƙwashe ni.”
Ta faɗa tana nuna tsintsiyar hannunta da ya damƙe.
“Kai wannan yaro anyi mugu, zai aikata abin da yafi haka indai wannan yaron ne, yana abu simi simi.”
Dade ta faɗa, Jamila kam wani irin yanayi taji ya ziyarce ta, me ya haɗa Mijinta da wannan mara kunyar yarinyar har da zai kama mata hannu, wai hannu. Ji ta yi zuciyarta na neman fara hayaƙi sabida zallan kishi, ga ƙarin tsanar Husna da ya sake girma a cikin zuciyarta.
“Kinga yanda wajen ya yi ja.”
Husna ta nunawa Mimi, girgiza kai kawai Mimi ta yi, sabida ga shatun matsar nan ya fito ƙiriri ƙiriri a hannun Husna, ta san dai dole wani abu ne ya haɗasu, sabida kowa ta san halinsa, amma ko mene ya haɗa su ina shi ina matse mata hannu har haka ya yi shata.
“Ki ƙyale ni da shi kawai, ga shatar hannun nan wallahi.”
Mimi ta faɗa tana ƙara kallon hannun Husna, jin abin da Mimi ta ce ya sake ɓata ran Jamila, kenan da gaske Honey ya taɓa Husna, wannan shegiyar yarinyar da bata da kunya ko kaɗan, wallahi zai zo sai ya yi mata bayanin me ya kai shi.
“Wai har sai dai shata ya fito?”
Maganar Dade ta katsewa Jamila zancen zucin da take yi, Mimi ta ce.
“Gashinan, ya fito ƙarara.”
“Mu gani.”
Dade ta faɗa, Husna ta matsa kusa da Dade ta nuna mata hannu, a take Dade ta ɗau salati tana faɗin.
“Jijiyar hannun ya so ya tsinke miki.”
Ba ta kai ga magana ba, Su Yaya Walid da Alhaji suka yi sallama suka shigo, hannayen su riƙe da jakukunan kayan Husna, sallama suka yi sannan suka shigo, har ƙasa suka fara gaida Dade ta amsa fuskarta a sake, tana son su Walid mussaman idan ta tuna mahaddatan Al Qur’ani ne shi ya sa take basu girma.
“Ai sai dai mu mu gaida ku, mahaddata ai malamai ne.”
Dade ta faɗa tana washe baki, suka ƙara gaidata sannan suka gaida Mimi ita ma ta amsa fuskarta a sake, Alhaji ne ya gaida Jamila sabida shi zata iya girma, Yaya Walid ma zata girme shi amma sabida yana da girman jiki sai