Chapter 12 of 26
DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty
“Mun yi waya da Aminiyar ai, ku shigar da kayan nata wancan ɗakin a can zata zauna.”
Mimi ta faɗa, sannan ta mai da kallonta ga Dade ta ce.
“Dade Husna zata zauna damu anan na wani lokaci, zan yi miki ƙarin bayani da safe, a kan dai wannan mutumin ne da ya bada jini.”
“To to, wannan marasa mutuncin kenan? To ai babu matsala, sannu kinji takwarata ki zauna anan kinji, sai ma ki dinga taimakamin da karatuna, Asharaf kam yana shigowa zai faɗa min dalilinsa na matse ki, kuma sai kin rama.”
“Tam Dade.” Husna ta faɗa tana kwantar da kanta kan cinyar Dade, tun da ta shigo bata ma kalli wata Jamila ba, farko ma bata kula da ita ba sai daga baya taga tana faman harare harare, ita bata san ma ba a kanta take ba, wanda ya ajiye mata ba a kanta yake bare ita.
Su Yaya walid basu jima ba suka tafi, sai da suka yi wa Husna faɗa a kan kar su ji kar su gani, sannan ta dinga kiran Abba a wayar Mimi tana gaida shi, kafin Allah Ya sa ya sauko ta dawo. Sai da Husna ta yi kuka wai yau ita ce tabar gidansu tabar ‘yan uwanta tazo nan, ba aure ba, ba rashin lafiya ba, ba tafiya ba.
Haka ta dawo falon jikinta duk ya yi sanyi ta zauna a gafe, Mimi tana kallonta ta gane yanayin da take ciki, cike da tausayawa ta ce.
“Sannu Husna, ki saki jikinki nan ma kamar gidan ai kin sani.”
Dade ta ce.
“Bilki ai uwarki ce, ni kuma kakakrki ce.” Sai kuma ta yi shiru kamar zata yi kuka ta ce.
“Ina ma cikin jikokina ne na tara mahaddata Al Qur’ani, nasan dai su Halima sun yi sauka har sau biyu Alhamdulillah, shi kuma wannan da ya yi haddar gatanan baya aiki da ita, ya haɗu da mata jinin yahudawa sai saɓon Allah suke yi, wai ba su shirya haihuwa ba, kai oh ni jama'a, Allah mun tuba mun kuma tuba.”
Harara Jamila ta watsawa Dade, kar ta sake haɗata da yarinyar nan wallahi, wace ma yarinyar nan da zata haɗa su.
Suna zaune zaman jigun jigun Ashraf ya yi sallama ya shigo, yana shigowa idonsa ya faɗa kan Husna da ke zaune kamar mai zaman makoki, ko zaman me take oho? Tun da ya ji tafiyar su Walid kuma ya san tare suke dole su zasu mayar da ita. Dan a tarihin rayuwarsa bai taɓa ganin yarinyar tazo gidan ta kwana ba, shi ya sa ma wannan tunani bai zo ransa ba.
Jamila ce kawai ta amsa sallamarsa, haka ya shigo ɗakin yana kallon Mimi da Dade da ke ta banka mai harara.
“Lafiya Mimi?”
Ya faɗa ciki ciki, Dade ta yi caraf ta ce.
“Iya nata kallon banza kawai kagani kenan, baka kula dani da idanuna ke shirin zubowa ƙasa ba?”
Murmushi ya ɗan saki wanda ya yi matuƙar ƙarawa fuskarsa kyau, shi ba ma abocin murmushi ba ne, kamar yanda ba ma abocin ɓacin rai ba ne, yana nan kullum fuskarsa daidai, baya ƙawata ta ds murmushi, ba kuma ya rage mata kyau da ɓacin rai a hankali ya ce.
“Dade ke ai rigimarki ba mai ƙarewa ba ce.”
“Ai ba zata ƙare ba, zo nan.”
Ta yi maganar kamar ba ita ba, ba musu ya matso kusa da ita yana durƙusawa, ai kuwa ta riƙe masa kunne ta murɗa, ta ranƙwasar mai kai da dukkan ƙarfinta, sannan ta ce.
“Husna, murɗe masa hannu irin yanda ya yi miki.”
Girgiza kai Husna ta yi, kamar wata ta Allah ta ce.
“Dade kirama min da kan ki, kar wata rana ya dakeni.”
“Hakane kuma dan ba shi da ɗigon Imani ko kaɗan.”
Sai dai Dade ta gama da shi Mimi ta ce.
“Me Husna ta yi maka da zaka matse ta mata hannu har ka ranƙwasheta.”
“Ranƙwashi kuma Mimi?”
Ya maimaita yana kallon Husna da ta turɓune fuskar, ya girgiza kai sannan ya ce.
“Bige ni ta yi, kuma ta gaza bani haƙuri.”
“To bakaga ƙanwarka ba ce, ko baka ga halin da take ciki ba, gaskiyya ka dinga tausayin mutane na faɗa ma.”
“Tam in sha Allah Mimi.”
Ya faɗa sabida yana son tsayar da zancen haka, sannan ya mayar da kallonsa ga Jamila da ta cika ta batse ya ce.
“Ta so mu tafi.”
Miƙewa ta yi kamar kububuwa ta fice, Husna ta taɓe baki a ranta ta ce.
“Iska na wahala da mai kayan kara, ke a kan wannan muguwar hallitar kike wannan abun? Sannunki.”
“Ita ba za ta yi mana sallama na kenan? Kai wannan matar Allah ya canja ma ita.” Dade ta faɗa tana miƙewa tsaye, shi dai bai ce komai ba, amma ya san dai wannan addu'ar ta Dade ba zata taɓa amsuwa ba, ina shi ina wani auren, wannan ma da ya yake lallaɓawa, ita ka ɗai yake ji a zuciyarta ita ma ba wai yana sonta ya aureta ba, kawai yanayin soyyar da kulawarta ya sa ya fara jinta a zuciyarsa, amma wani lokacin kam har mantawa yake da ita a ransa.
Lokacin da ya fita ma ta yi nisa har ta kai wajen da ya ajiye motarsa, a hankali ya taka zuwa wajen tafiyarsa kamar ko yaushe cikin nutsuwa, yana ƙarasawa ya buɗe mata motar ta shiga ta yi kicin kicin, shi dai ya san bai yi mata komai ba dan haka ba abin da zai sa shi ya lallaɓata idan ta so ta kwana tana yi, shi dai ya san bai mata komai ba, har suka yi nisa a tafiyar bai ce mata uffan ba, sanin ba zai ce ɗin ba ya sa ta cewa.
“Me ya sa ka taɓa hannun yarinyar nan dan Allah?”
“Wace yarinya?”
Ya faɗa hankalinsa yana kan abin da yake yi, dan bai ji ma zai bata amsar da take buƙata ba jin yanda ta yi masa tambayar kamar wata wacce ta haife shi.
“Husna take kowa?”
Ta faɗa tana taɓe baki, ya girgiza kai wanda girgiza kan yana cikin ɗabi’arsa Idan baya son magana, a hankali ya ce.
“Idan kin tabbatar da sunanta sai ki yi maganar.”
Kuka ta fashe da shi, sabida zafin da take ji a ranta, wai anya Ashraf yana sonta kuwa? Wane irin mutum ne shi haka, yana zaune da ita amma bai taɓa mai da hankali a kanta ko nuna damuwa a kan ta, har kasuwanci ma yafe masa a kan ta. Bai hanata ba har suka isa makeken gidansu da ke Tudun yola C, sabuwar unguwa da ta tara matasan masu kuɗi a ciki, maka makan gidaje ne na gani na faɗa a cikin unguwar.
Suna shiga cikin falon ya sami kujera ya zauna, gaba ɗaya kansa ya ɗau zafi, bai taɓa tunanin Daddy zai yi masa wannan maganar ba, a kan kawai yana buƙatar ya ba shi contract da kamfanin sa shine ya zuba masa waɗan nan sharaɗun da ya san ba zai iya ɗauka ba, to da tsurar kuɗi ma ya ce ya bashi abun sai yafi haka kenan?
“Honey.”
Muryar Jamila ta katse mai tunanin da yake yi, a hankali ya buɗe idanunsa da suka yi ja ya kalleta, tana tsaye a kan sa fuskarta duk ta yi ja alamar da gaske kuka ta yi, nuna mata kusa da shi ya yi, ya ce.
“Come.”
Matsowa ta yi ta zauna, ya kalleta sosai sannan ya ce.
“What?”
“Honey dan Allah kana sona kuwa?”
Kallonta ya yi sosai, me ya kawo wannan maganar kuma, ita tunaninta baya sonta zai zauna da ita ne har waɗannan shekarun?
“Eyh Honey? Gaba ɗaya na kasa yarda kana sona, babu wata shaida guda ɗaya da kake nuna min soyayya da ita, damuwa ta bata dameka ba, haka kawai ka zauna ka yi hira dani ban isa ba.”
“Jamsy, bana hira da ke?"
Ya yi maganar a hankali, ta girgiza kai alamar a'a sai kuma ta ce.
“Hira irinta soyayya, hira da sa kai bata taba wuce minti goma zaka ja baki yi ka yi shiru.”
Kallon mamaki ya yi mata, ashe bata yaba da wannan minti goman ba, bata san yana ƙoƙari sosai ba a hakan, to kawai sai ya zauna ya yi ta surutu marar amfani har sama da minti goma? Ba a yi wannan macen da zai zauna yana wannan surutun da ita ba, ba kuma za ayi ba har abada.
“Rana ɗaya baka taɓa yi dariya a gabana ba, sai murmushi. Murmushin da kake yi wa kowa irinsa, bani da wani bambanci da kowa kenan? Nifa matarka ka ce, haka kawai baka taɓa kama hannuna ka riƙe ba, amma yau ma kamana waccan yarinyar da ta yi maka rashin kunya.”
“Jamsy, laifi ne dan na matse hannunta na yi mata hukunci?”
“laifi ne babba, matarka ka ce ita da zaka haɗa jiki da ita? Ni kaina nan matarka lokaci da dama haka zan so na yi ta ƙoƙarin shiga jikinka amma ka ƙi, ina da nake halal ɗinka ma.”
“jamila.”
Ya kira sunanta da dukkan nutsuwarsa, ta ɗaga kai ta kalleshi, ya ce.
“Da ace bana son ki ba zan taɓa iya aurenki ba, har na zauna da ke tsahon wannan shekarun, kafin ke mata nawa ke nuna shaawarsu gareni, amma ban taɓa jin zan iya aurensu ba har na rayu da su na wannan lokacin, ban taɓa jin zan iya gudanar da mu'amala aure da wata macen ba sai ke. Dan haka ki cire tunanin bana sonki a ranki.”
Kwantawa ta yi a kan jikinsa, magana ka ɗan yake yi da ita ta ji ta sami mutuwa a ranta, bata san wani irin so take yi wa Ashraf ba, tun ranar da ta fara ganinsa ta kamu da matsanancin son sa, a lokacin da aminiyarta Amrah ta ce mata yana burgeta sai ta ji gaba ɗaya ta tsani Amrah ɗin, Amrah da take ƙawarta tun yarinta amma a kan Ashraf taji ta tsaneta, sai kuma aka yi sa'a Amrah ta ce ita ba son sa take ba. Jamila ta sha matuƙar wahala kafin Ashraf ya dubeta da idanun soyayya, ta sha fama. Sai dai kuma lokaci ɗaya ya ce yana son zuwa gidansu, a lokacin Jamila ji ta yi kamar ta yi hauka da dan daɗi, lokacin da ya zo gidansu mahaifnta ya tambaye shi game da shi ya sanar da shi asalinsa sai ta sake jin son sa ya ƙara kamata, babban su babban ɗan siyasa ne da ya yi suna a cikin garin, ita ce babbar ‘yarsa daga ita sai ƙanninta namiji sai kuma ƙaramar ƙanwarta su uku ne a wajen mahaifinsu gaba ɗaya, kasancewarta babbar ‘yar sa yasa take da izzah da isa da jin kai, a kullum ji take ita wata ce, ko ƙawaye bata kula kowa sai wadda ta kai, haka samari ma. Saurayi idan bai kai matakin masters bama ai ba isa ya tunkareta ba duk kuɗinsa kuwa, ‘ya'yan manyan masu kuɗi masu ilimi sune samarinta, mafi akasarin samarinta daga abroad ta haɗu da su, har da ƙawayenta dan ko ita Amrah ɗin ma babbansu mai kuɗi ne sai da ba taje abroad ba amma pravite university ta yi a abuja har masters dinta.
A lokacin da ta fara ganin Ashraf ta ji fargabar kar ya kasance shi ba ɗan wani babban mai kuɗi ba ne, sai dai soyayyarsa ta danne mata duk wata izzah da jin kanta, to a lokacin da ya sanar da mahaifinta shi ɗan wajen babban ɗan kasuwa ne Alhaji Musa Ɗankaka, sai ta sake jin lallai ta kai, a rayuwar Jamila akwai raina wanda bai kai ba dan son nuna isa da cewar ita ta kai, mussaman da ta auri Ashraf ga kyau ga ilimi ga kuɗi ga shi daga babban gida, sai ya zama ko cikin ƙawayenta ma ta fara nuna musu isa, tana ganin basu isa su kai inda take ba, ta fara nuna musu ta wuce yanda suke tunanin su hakan ya ja wasu da yawa suka watsar da ita, wasu kuma suke ciki da ita.
Ko ‘yar aiki da ta samu a gidan nata a ƙarshen hulaƙanci take kallonta, bata zuwa gidan sai ƙarfe sha biyu na rana tana zuwa zata gama duk wani aiki da za ta yi ta tafi, ba zata sake zuwa ba sai gobe, basu taɓa ido biyu da mai gidan ba, ƙarshe ma ‘yar aikin ko damar zama a gidan bata samu ba, sabida tana gama aikin da ya kawo ta zata tafi.
Tun da tazo sau ɗaya ta gaida Mimi ta gane bata sami shiga wajen Mimi ba, da ta so ta ɗaga hankalinta sai kuma daga baya ta ce ai ba zaman Mimi za ta yi ba, ita dai tun da Ashraf na son ta kuma zai zauna da ita Mimin ta yi ta ƙinta, ko da aka yi auren ma bata zuwa gidan Mimi sai dai shi ya kai ta taje ta dawo, mahaifiyar Jamila Hajja Aisha macece mai kula da tarbiya, tana iya ƙoƙarinta a kan Jamila amma mahaifinsu shi ya ɗaure musu gindi suke taka wanda suka ga dama.
Kullum Hajja Aisha sai ta yi wa Jamila faɗa a kan ta gyara alaƙar ta da uwar mijinta, amma Jamila ta ce. Ai ba zaman ta take ba, zaman mijinta take yi, Hajja Aisha na ƙoƙarin nuna mata uwar miji ita ce komai amma Jamila ta ce a’a.
Anty Laila ƙanwar Hajja Aisha ce, amma aminiyar Jamila ce sabida shekara ɗaya ne tsakaninsu, halinsu yazo ɗaya shi ya sa suke aminci tare, duk wani sirrin Jamila Anty Laila ta sani, haka duk wani sirrin Anty Laila Jamila ta sani, duk jin kai da isar Jamila a bayan Anty Laila take dan itama haka take ko mu'amala ɗaya bata haɗa ta da dangin mijinta, mussaman mijinta da ya yi kuɗi daga sama ba gada ya yi ba, iyayensa duk talakawa ne, shi ya sa Anty Laila ta ɗibesu ta yi watsi da su a bola, to duk wani iya shege wajenta Jamila ke koya, sai dai ita Anty Laila ta yi imani mijinta na son ta, sabida ga alamu nan duk sun nuna, saɓanin Jamila da ke faman haƙuri.
“Honey.”
Ta kira sunansa.
“Jamsy.”
Shima ya kira sunanta.
“Wallahi ina sonka, ina mugun ƙaunarka, ban san yanda zan yi ba idan na rasa ka a duniya ta, dan Allah ka yi min alƙwarin ko da bana duniya ba zaka auri wata macen ba.”
Legendspen
08129553971
🔥🔥*DA JININSA NAKE RAYUWA*🔥🔥
*-Amanan-Janafty-*
https://www.arewapen.com/chapter?id=6ab26027cb0cfb23739014a5
https://chat.whatsapp.com/DyVX8bRFbq66I04yzM5rLp?s=cl&p=a&mlu=0&ilr=4
(13)
Su Ashraf na fita Mimi ta ce da Dade.
“Dan Allah Dade kinga wannan abun haushin, wai yana gani matarsa ta fita haka ba tare da ta yi wa mahaifiyarsa sallama ba, amma ko a jikinsa.
Wallahi Ashraf bai san ciwo na ba, bai san darajata ba ko kaɗan.”
“To daman ina amfanin auren wadda ta girmeka, ai sai dai ta juya ka ba kai ka juya ta ba.”
Dade ta bawa Mimi amsa, Mimi ta sake cewa.
“Ai sai ya yi tun da abin da ya zaɓa kenan, kuma na faɗa miki bafa girmarsa ta y ba, ya bata a kalla shekara biyar.”
Tana faɗin haka ta miƙe tsaye, sai kuma ta kalli Husna ta ce.
“Idan zaki ci abinci ga kitchen a can, idan kuma kin ƙoshi to ki shiga wancan ɗakin anan zaki zauna, Dade da safe zamu yi maganar ko, yau Alhaji ba lallai ya shigo ba, daman idan yana wajen Hajiya Kubrah bai cika shigowa ba.”
Miƙewa Dade ta yi, sannan ta ce.
“Aiko bai shigo ya yi miki sallama ba, ni matsayina na mahaifiyarsa ya shigo dai ko?”
“Hakane.”
Mimi ta faɗa tare da wucewa hanyar part ɗinta, Dade ma ta yi nata hanyar, Husna na ta miƙe ta nufi nata ɗakin.
Ta shafe sama da minti talatin kwance a kan makeken gadon da ke cikin ɗakin wanda ya yi biyu da rabin nata gida, duk yanda taso ta iya runtsawa ta kasa, kawai gidansu da mutanen gidansu take kewa, ba za ta iya rayuwa anan ba babu mutanen gidansu, duk da nan yafi gidansu komai, amma haka kawai ta ji tafi nutsuwa a nasu gidan, sai wajen ƙarfe sha biyu na dare bacci ya yi gaba da ita, kiran Asabar farko ya tashe ta kasancewar akwai massallaci a gidan, amma ta waje yake.
Bayan kwana biyu.
Husna ta fara sabawa da zaman gidan duk da ba wai ta sake ba ne gaba ɗaya, amma ba a takure take ba. Mimi na kula da ita sosai, tana nuna mata soyayya kamar yadda Mama zata yi mata, yanda Mimi je janta a jiki ma yafi yanda Mama ke mata, kullum sai sun yi waya da su Alhaji da su Yaya Abdul amma Mama ba ta ce mata komai, bare kuma uban gayya Alhaji Abba da bai nemeta ba.
Dade ce ke sa mata daɗn zaman gidan, su zauna tare suna hira tana ta bata Labaran nishaɗi, ita kuma tana yi mata ƙarin Al Qur’ani da wasu littafan, Yaya Leemah kam tana gidan kamar bata gidan, bata da aiki sai harkar kasuwanci ƙarfe goma ta fita ba ta dawo sai wajen shida, idan ta shiga part ɗinta bata fitowa sai wajen tara idan zata ci abincin dare, kullum Mimi da Dade cikin faɗa suke mata, wanda da alama ma shi ya sa ta ƙauracewa zaman falon, da ta fito Dade zata fara cewa.
“Wannan zamani Allah Ya gyara mana, sai ka rasa waye yafi shirme, ‘yar da ta ajiye aure ta tawo kula da duniya ko uban da ya karɓi ‘yar ya bata kula da dukiyar.”
Ita dai yaya leemah ba wanda take tankawa, kullum tunaninta yanda za a samu riba, yanda za'a gujewa faɗuwa, ya za ayi a ƙirƙiro sabon abun da zai kawo riba, shikenan lissafinta.
Asharf bai sake dawowa gidan ba, daman sai bayan kwana biyu yake zuwa. Yau kawai Husna ta tashi da sha’awar zagaye gidan, tun zuwanta ba ta taɓa fita zagaye gidan ba kullum tana cikin part ɗin Mimi bata fita, shi ya sa yau ta