Chapter 13 of 26

DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty

ce dole taje taga yanda gidan yake baki ɗaya, a lokacin da ta fita Yaya Lemmah ta fita ofis, Mimi na ɗakinta, Dade kuma na baccin da take yi da safe wanda take cewa wai yana ƙara lafiyar ƙwaƙwalwa.


Ko iya harabar gidan Husna ta kwashe sama da minti goma tana kalla tare da yabawa, a ranta take ayyana mai kuɗi yaji daɗi, ko ita ma zata sami irin wannan? Ko wanda bai kai wannna ba, ko wanda yafi wannan ma, Allah ne kawai ya sani, sai kuma ta tuna da Uncle Dee a fili ta ce.

“Allah Sarki Uncle Dee, Allah Ya kula da kai.”

Tana faɗin haka ta fara tafiya, sabida bata son ma ta yi nisa cikin tunaninsa sabida ta yi wa kanta alƙwarin ta cire shi a ranta har abada, sabida tasan iyaye suna gaba da komai kuma bai ci ta watsar da suka a kan soyayya ba.


Tana tafe tana zagaye gidan hankalinta kwance, duk inda ta gani sai ta yi mai kallon tsananiki har ta fahimci su waye a cikin ɓangren. Daga can nesa da part ɗin Hajiya baba ta hangi wani namiji yana zauna a kan kujerar roba ya juya bayansa, har ta wuce shi ta ji yana mata magana.

Kamar ta wuce sai kuma ta tsaya ba tare da ta waigo ba, a hankali ya taka zuwa inda take, shi bai ma san wace ba kawai da ya san baƙuwa ce, kuma yaga ta nufar sashen Hajiya Babba, shi daman mayen ‘yan matane duk inda ya gani sai ya latsa.

“‘Yan mata adon gari.” ya yi maganar cikin muryar da ya saba yaudarar ‘yan mata da ita, a hankali Husna ta juyo ta kalleshi, fari ne irin mai ɗaukan idon nan, yana da tsayi amma ba sosai ba, kan shi cike da suma sata sha gyara, yana sanye da wata ɗanyar milk ɗin shadda mai matuƙar kyau tsada, ɗinkin ya karɓi jikinsa ya kwanta luf, idonta ta sauke cikin nasa, ta yi masa wani irin kallo ido cikin ido, sai kuma ta sauke idonta, sabida ita ba ta ga wani abu ba a tare da shi ba, ta kalleshi sosai ne ko zata ji irin abin da ta ji a lokacin farko da ta yi ido biyu da Uncle Dee, sai dai ba taji komai ba.

Shi kam a karon farko yaji ya yi ido biyu da macen da ta shiga zuciyarsa, kamar kar ya ɗauke idonsa a kan ta, yaji gaba ɗaya ta tafi da zuciyarsa.

“Lafiya dai ko?”
Husna ta yi maganar, ganin yana binta da kallo.
“Lafiya, ina zaki haka?”
Kallonsa ta sake yi, da alama yana da haɗi da gidan, dan suna shigen ɗibar kama da ‘ya’yan Mimi ma.
“Ina ɗan zagayawa ne.”

“Zagaya ina?”
Jin tambayar ta yi wani iri, wai zagaya ina? Ɗan tura baki ta yi gaba, sannan ta ce.
“Non of your Business.”
Tana faɗin haka ta juya inda ta fito, taji gaba ɗaya zagayen ya fita a kan ta, su ‘yan gidan gaba ɗaya haka suke da hulaƙanci kenan? To su ci kan su.


Husna bata san yana biye da ita ba, sai da ta yi sallama a part ɗin Mimi, bayan Dade ta amsata sai kuma ta ji wata sallamar a bayanta, ita ma Dade ta sake amsawa, zama ta yi a kusa da Dade tana faɗin.
“Dade an ta shi kenan?”

“Gani kuwa kin ganni, daga ina kike haka?”
Sai kuma ta miƙe tsaye.
“Alkasim, kai ne anan me ya shigo da kai? Hala wannan uwar taka bata san ka shigo ba ko?”
Sai a lokacin Husna ta kalli shi, shine kenan ya biyo ta.
“Dade wannan anan take?”
Ya faɗa yana nuna Husna, Dade ta ce.
“Anan take, sai aka yi me?”

“A’a bakomai.”
Ya faɗa tare da juyawa, zama Dade ta yi tana taɓe baki.
“Ka ji da shi dai.”
Husna ce ta ce.
“Dade waye shi?”

“AlKasim ne ɗan gidan Kubrah, kingan shi nan ko shi ya girmi Asharaf, amma sun sa sharholiya a gaba babu abin da suke iya yi sai shashancin a rayuwa.”

“Allah Ya kyauta.”
Husna ta faɗa, idan ma ita ya biyo ya biyo banza dan babu abin da zai haɗa ta da shi, ita a yanzu ai ta haƙura da soyayya, aure kuwa tun da ba wajibi ba ne ta haƙura da shi kuma zata roƙi Allah da ya kashe mata zuciyarta yanda ba zata taɓa son wani namiji ba, ta rasa Uncle Dee, to ta rasa soyayya da kowa.



Bayan wata ɗaya.

A zuwa yanzu Husna ta saba da zaman gidan, ta mayar da gidan kamar gidansu tana rayuwa hankali kwance, Su Yaya Abdul sun zo ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, Mama ma tazo sau ɗaya tun da yanzu ta sauko daga fushin da take, Abba ne dai shiru har yanzu bai sauko ba daga na shi fushin, amma suna sa ran ko yaushe zai iya saukowa, dan ranar da Walid yazo na ƙarshe ma ya ce Abba ya yi zancenta.

Ko da suka ce mata yakamata ta koma makaranta ta ce ita ba za ta koma ba, karatu dai ta gama yin sa kenan, idan ta sami nutsuwa daga baya ta ci gaba, duk yanda Mimi ta so fahimtar da ita muhimmancin komawa ta ƙarasa ko secondry ne Husna taƙi ta ce ba yanzu ba, Yaya Leemah da ba ta cika shiga shaaninsu ba ta yi mata magana a kan makarantar itama Husna ta ce ba zata je ba, Husna da alama dai bazaki daina taurin kai ba, abin da kowa yake faɗa mata, ita dai ta ce ba zata koma ba a ƙyale ta.

Yau Mimi bata nan sun je Unguwa da Mama, Dade kuma ta koma ɓangaren Hajiya babba, daman ta kanje can ta yi sati ɗaya ko biyu sai ta dawo nan, ɓangaren Hajiya Kubrah ne da bata zuwa, Husna basu taɓa haɗuwa da Hajiya Kubrah ba, amma duk wasu munanan halinta ta sani a bakin Dade, Hajiya Babba ce dai sun haɗu har wajen sau biyu, ita ma dai babu yabo babu fallasa a wajen Husna.
Tun da Mimi ta fita ta ce mata ta gyara mata kayanta a ɗaki, sannan ta haɗa mata jaka da kaya zata yi tafiya, na kwana biyu. Husna na zaune cikin ɗakin Mimi tana ware mata kaya ta ji anyi sallama, ɗaga kai ta yi ta ganshi, ita rabonta da shi ai anfi wata dan tun zuwanta sau biyu suka haɗu, dan ita bata son ganinsa ma shi ya sa data fahimci ranaku da lokacin zuwansa bata zama inda zai ganta, dan haka ta daɗe bata gan shi ba.

Shima a ɓangarensa ya ma manta da yarinyar gaba ɗaya, mamaki yake wai har yanzu tana gidan, idan zai iya tunawa wajen wata ɗaya da suka zo shi da Jamila sun tarar da ita, sai kamar ya sake zuwa ya ganta, to tun daga nan bai sake ganinta ba, kuma bai sake tunawa da ita ba sai yau da ya ganta anan, to tambayar da yake yi wa kansa, zaman me take yi anan? Ya san dai kamar tana makarantar kwana ne, haka ya ji lokacin da bata da lafiya, kuma baya tunanin ta gama karatun yanzu, ko gudun makarantar ta yi ta dawo nan?
Kamar ba zai kula ta ba ya ce.
“Ke.”
Ƙasa ƙasa Husna ta ce.
“Ƙara ke kaga me zai baka.”
Yana ganin bakinta ya san rashin kunya ta yi masa, dan ya san bata sa kunya ko kaɗan, cike da ɓacin rai ya ce.
“Ba magana nake miki ba?”
“Ai ba sunana Ke ba, sunana Husna.”
Ta faɗa hankalinta yana kan abin da take yi, mamakinta yake sosai yanda bata da kunya kamar ba ‘yar Mama da Abba ba, kamar ba ƙanwar Abdul da Walid ba, tsiwa kawai ta iya rayuwarta. Rai a haɗe sabida gudun raini ya ce.
“Ina Mimi?”

“Ta fita unguwa.”
Bai tanka ta ba ya fice, ƙwafa Husna ta yi a fili ta ce.
“Sai muguwar zuciya, wallahi idan naganshi zuciyata tashi take yi.”
Tana faɗin haka ga ci gaba da aikin da take yi, ranta duk a ɓace, shi rashin mutunci ya ɗauka a matsayin abun yi to yaje Allah Ya haɗa shi da daidai shi.

Har yanzu tana mamakin me ya sa mutum idan Allah ya yi shi a gidan masu arzikin yake hulaƙanta waɗanda basu da shi, wai duk mene ma a cikin duniyar, kwanakin da kullum raguwa suke, da ɗan adama ya san abin da ke ɓoye da bai yi izzah da gadara ba duk kuwa irin arziƙin da Allah zai yi masa.
Haka ta gama haɗa kayan duk ran ta a ɓace, ita ji take yi kamar ta tashi ta tafi gidansu koma mene Abba ya yi, amma ta gaji da wannan zaman gaba ɗaya wallahi, wayar ƙaramar wayar da Mimi ta bar mata ta ɗauka ta saka lambar wayar Alhaji a ciki, bugu ɗaya ɗauka tare da yin sallama, bata amsa sallamar ba ta ce.
“Ni dai gaskiyya gida zan dawo.”
“Wai Husna ba zaki daina wannan taurin kan naki ba, yaushe Yaya Walid ya ce miki ki ƙara haƙuri?”

“ Ni dai gaskiya sai na dawo Haba, zaman ya yi yawa.”

“To ki yi ta dawowar, idan taurin kai kika zaɓa sai ki yi.”

Yana faɗin haka ya kashe wayar, tsaki taja tare da miƙewa a ranta tana faɗin.
“Wallahi tafiya zanyi haba.”
Ɗakin ta tashiga ta ɗauki mayafinta, har ta saka mayafin sai kuma ta yi ɗan tsaya, wani tunani ya faɗo mata tun da tana da lambar Abba a kan ta kuma bai da wannan lambar to ta kira shi ta ba shi haƙuri ko zai haƙura, duk da su Yaya Abdul sun gargaɗe ta sun ce kar ta gwada kiran Abba, amma ai taga an daɗe magana ake ta kusan wata biyu fa, duk zuciyarsa ai ya ci ace ya sauko yanzu.
Tun da har ita ta manta da Uncle Dee, duk da ba wai ta manta da shi gaba ɗaya ba, amma ya ragu sosai a zuciyarta sai dai addu’a ɗaya ta tsananta yinta Allah ya sa har ta koma gare shi ba zata sake son wani namiji ba a duniya.

Wayar ta ɗauka ta rubuta lambar Abba ta danna kiran, har kiran ya katse Abba bai ɗauka ba, tana shirin ake kira sai ga kiran nasa ya shigo, zuciyarta taji tana wani irin bugawa kamar kar ta ɗauka sai kuma ta ɗauka, daidai lokacin kuma Mimi ta shigo ɗakin tana faɗin.

“Husna kina nan ne?”
Sallamar Abba ce ta karaɗe ɗakin sakamakon wayar a handsfree take, cikin sanyin murya Husna ya ce.

“Abba ina yini?”
Shiru ya ɗanyi, kafin daga baya kuma ya ce.
“Asma’u.”
Ai yanda ya kira sunan ya tabbatarwa da Husna Abba bai wuce da fushin da yake yi a kan ta ba. Cikin muryar kuka ta ce.
“Abba, Abba dan Allah ka yi haƙuri ka yafe min, dan Allah.”
Shiru ya yi bai ce komai ba, ta sake cewa.
“Abba dan Allah.”

“Me kike so?”
Ya yi maganar cikin sanyi muryar da ya yi mata yanayi da na Ashraf.
“Abba ka ce ka yafe min na dawo gida.”

“Asma’u, kina so ki dawo gida?”

“Eyh Abba wallahi ina so.”

“To idan har kina so ki dawo gida, dole sai kin zama mace mai daraja, bakina gidan Alhaji Musa ba?”

“Ina can Abba.”
Ta faɗa kamar zata yi kuka, Abba ya ce.

“To na ba shi wakilcinki! Idan lokacin aurenki ya yi, shi ne zai aurar da ke. Daga yau har zuwa ranar da za ki zama mace mai daraja a gidan mijinta, ba na son sake sanya idanuna a kanki a cikin gidana! Matuƙar ba gidan aure kika shiga ba Husna, to ba na maraba da ke. Ko da Allah ya ɗauki raina, wannan ita ce wasiyyata gare ki ba zan taɓa farin ciki da ke ba har sai ranar da kika zama matar aure.”


Yana faɗin haka ya kashe wayarsa, Husna ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya, Mimi ta matso kusa da ita ta rungumeta tana rarrashinta, Dade ta shigo wajen Husna ta yi mata karatu ta ji kukan Husna a ɗakinta, cikin hanzari ta shigo ɗakin tana faɗin.

“Malamata me ya sa me ki.”
Ganin Mimi na rarrashinta ta ya sa ta ce.
“Bilki me ya faru da ita?”
Cikin sanyin Murya Mimi ta ce.
“Mahaifinta ne ya ce ba ya maraba da ita a gidansa har sai lokacin da ta zama matar aure, ko mutuwa ya yi ba zai yi farin ciki da ita ba sai ya yi aure, sannan baya son sake ganinta a gidansa ssi lokacin.”

“Kai wannan Abubakar yaushe ya zama mai zuciya har haka ne?”
Dade ta faɗa, Mimi ta ce.
“Daman yana da zuciyar kawai dai ta yi sanyi ne, ita Husna ce ta tayar masa da zuciyar.”


“Kai wannan abun bai yi daɗi ba wallahi ko kaɗan, ki yi haƙuri komai zai daidaita.”
Ita dai Husna bama ta jinsu kawai kuka take yi, wai sai ta yi aure. Ita da a kullum addu'arta Allah Ya tsareta daga sake shiga lamarin soyayya ko wani namijin, kenan addu’arta babu inda take zuwa.
Yaka Dade da Mimi suka yi ta rarrashinta, har ta samu nutsuwa, Dade da kanta ta ce mata zata je ta sami Abba ta ba shi haƙuri, shine abin da ya sa Husna ta ɗan saki jiki.
Sai da ta kwana biyu kafin ta saki jiki ta ci gaba da mu'amala kamar da, tun safe Mimi ta ce ta haɗa kayanta kala biyar ko shida, Mimi zata je Abuja ganin likita, Dade kuma na ɓangaren Hajiya Babba, Leemah kuma ta tafi Chaina tun wancan satin, Husna dai bata san inda zata ba, amma dai ta haɗa kayanta wajen kala goma ma dan ita ko ina zata je sai ta ɗan zauna, sabida ta gaji da gidan Mimi gaba ɗaya, tana son shaƙar iskar wani wajen daban.


Bayan magariba suna zaune tana yi wa Dade ƙarin arba’una Hadis, duk da Dade ba wani iya take ba, amma soyayyarta da karatun ya sa take jin daɗinsa. Sallama ya yi kamar ko yaushe cikin sanyi muryarsa, Husna na ganinsa ta haɗe rai, bata so ma ya sake ganinta ba, dan har cikin zuciyarta bata son ganinsa.

Bayan ya gaida su Dade karo na farko kenan ya yi magana a kan wani mutum.
“Mimi yarinyar nan wai zaman me take bata zuwa makaranta ne?”

“Ta dawo nan da zama.”
Mimi ta faɗa a daƙile, shi kam zamanta ba damunsa zai yi ba tun da ba a kan sa take ba, shi yana magana ne a kan rashin karatunta, shi a rayuwarsa baya son mutum yaƙi yin karatu, mussaman mace yarinya da bata da wani nauyi a kan ta.

“Mimi, ba wai zamanta ba, magana nake a kan karatun ta.”
A wannan lokacin Dade ce ta ce.
“Ta ce ta haƙura ba zata ci gaba, ko karatun dole ne? Ai tana da na Muhammadiyya kuma shine dole, wannan na nasaran ta ce ba zata yi ba.”
Kallon Husna ya yi ta wani turu baki gaba, shi yana mamakin yanda suka bar yarinyar nan take abin da ta ga dama, da wajensa take ai da tuni ya daɗe da ɓaɓɓalata, yarinyar sai rashin kunya kawai ta iya, karatu ma ko secondry ba ta gama ba ta ce ba zata ci gaba kuma sun barta, ita kuwa wace irin mace take son zama, wani mahaukacin ne zai kwashi wada bata da ilimi.
“Ashraf ba wannan ya sa na kira ka ba.”
Mimi ta faɗa, sannan ta ce.
“Gobe da safe zanje ganin likita, kwana biyar zanyi ina son Husna zata je gidan ka ta har zuwa na dawo, yanzu zaku tafi da ita.”


Legendspen
08129553971
🔥🔥*DA JININSA NAKE RAYUWA*🔥🔥


*-Amanan-Janafty-*


(14)


Ba iya Ashraf ba har da Husna jin maganar ta yi kamar shigar ƙaya, wai taje gidan Ashraf, ina wannan ma ba zai yu ba, wannan matar ta shi mai kama da sakwara wallahi ba zata saɓo ba chab.

Kallon Mimi Ashraf ya yi, yana so ya yi magana amma bakinsa ya yi masa nauyi, Mimi ta sake cewa. “Kaji ni, ko ba kaji ba?”

“Mimi naji, amma ba zata iya zama anan ba?”

“Eyh ba zata iya ba, na ce taje gidanka ko? Ko tsoro kake ita uwar taka ta gidan ba zata zauna da ita ba? To ka ce mata umarnina ne idan kuma taƙi wallahi zata ga mummunan hukuncin da har kai sai ya shafa.”

“Kin burgeni Bilki, ai Asharaf baya buƙatar lallaɓawa, irin wannan umarnin zaki ba shi.”
Dade ta faɗa tana yi wa Mimi jinjina, sannan ta koma ga Ashraf ta ce.
“Idan ni ban isa da kai ba, ai na isa da ubanka shi kuma ya isa da kai, sai mu gani.”

“Mimi ni dai da ba gidansa ba, kin san dai wannan matar tasa wallahi, kuma ba mutunci take muku ba bare kuma ni, shi kan sa kina ganin yanda yake cin zalina bare kuma an haɗa da wannan matar tasa mai kama da sakwarar legas.” Wani ƙululun takaici ne ya tsayawa Ashraf a maƙogwaro, wai Jamila take cewa mai kama da sakwarar legas, ba gwanda Jamila ba a kan ta shi yanzu ai kallon da yake wa Husna gwanda kowa a kan ta, yarinya ko secondry ta gagara gamawa.
“Babu ruwanki da matarsa ai gidan yayanki ne, kar ki tanka ta duk abin da za ta yi miki.”
Dade ta faɗa, Mimi kuma ta ce.
“Idan kin mutunta ita ma zata mutunta ki, ki tashi ki ɗauko kayan da kika haɗa ku tafi.”

“Ni dai Mimi a'a dan Allah, wallahi ni tsoronsa nake ji, ba iya matarsa ba ce abar tsoro.”

“Ki tashi kije ki ɗauko jakar ki, shi ya isa ya ce zai dake ki ne, me kika yi masa.”
Tashi Husna ta yi, bata son jan zance da Mimi amma suna fita zata lallaɓa shi ya kai ta ko gidan su Hajjo ne cikin gari, wallahi ba zata iya zuwa gidansa ba. Sai bayan ta tashi ya ce.
“Mimi ki faɗa mata ta girmama mata ta, kar ta yi mata rashin kunyar da ta saba.”
Kamar jira Mimi take ta hau sababi.
“Ita matar taka girmama mutane take? Ko ganin mu take yi da mutunci? Idan kakai mata ita a hulaƙance dole ta ɗauke ta hulaƙane, idan a mutunce ka kai ta dole ta mutunta.”
Miƙewa Dade ta yi tana faɗin.
“Bilkisu Allah Ya ƙaddara saduwa, ni kam