Chapter 15 of 26
DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty
“Zauna.”
Cikin sanyin muryarshi kamar ko yaushe, Husna ta maƙe faɗa alamar a’a, ya sake cewa.
“Ki zauna na ce miki.”
“Kana ji fa aka yi min gori, shine zaka ce na zauna sabida bansan darajar kaina ba ko me?”
“Ni kike faɗawa wannan maganar, zaki zauna ko sai na kwashe ki da ƙafa.”
Zama Husna ta yi, tana zama ta fashe da kuka, wanda ya sake ɓata ran Jamila taji kamar ta yi wurgi da Husna ƙasa ta hau kanta ta yi ta jibga, yarinyar yar ficika na shrin yi mata bariki a gida, ko da yake ita taja, da ba ta yi abin da ta yi ba ai da ba zai je har inda take ba.
“Zaki yi shiru ko sai na dake kin?”
Shiru ta yi tana turo baki, shima ya zauna tare da fara zuba suger a cikin cup din da zai sha tea ɗin, Zama Jamila ta yi ranta duk ya yi baƙi ta rasa inda zata sa ranta da Husna, ita dai dole duk masifa da balai sai yarinyar nan tabar mata gida shine kawai dan wallahi ba zata iya ba.
Shi ya miƙawa Husna kofi irin wanda yake using tare da plate, Jamila kamar ta mutu duk ta yi danasanin abin da ta yi sabida gashinan duk a zamansu bai taɓa miƙa mata plate ba sai gashi yau ya miƙawa wannan yarinyar, Allah Ya isa.
Husna kam ko a jikinta, ita kanta zaman gidan ma ya fita a ranta, wallahi Mimi tayi ta dawo dan ba zata iya zama ba, daga mijin har matar babu na arziƙi.
Idan Husna ta ce jamila bata iya girki ba tabbas ta yi ƙarya ta kuma yaudarin kanta, tun lomar farko da ta kai bakinta ta ji ɗanɗanon da bata yi tsamanni ba, abinci ya yi daɗi ya kuma daɗi. Ba abin da ya dami Husna tasa abincin a gaba ta cinye tas, ita gaba ɗaya ma ta manta da su a ɗakin duk abin da suke bata gani ba.
Tana gamawa ta miƙe ta yi cikin ɗaki ba tare da ta kalli inda suke ba, abun ya ɓatawa Jamila rai wato ta mai da su ‘yan iska kenan, ko plate ɗin da ta ci ba zata ɗauke ba kenan? Ashraf bai san tana yi ba dan shima ya manta da wata Husna a cikin gidan, yana gama ci ya fice ya bar gidan, shi damuwarsa har yanzu tana kan yanda Daddy zai basi contract ɗin da yake nema a wajensa.
Jamila kam ko rakiyar da ta saba masa bai samu ba, ita dai gaba ɗaya an cuceta wannan yarinyar da aka kawo, wayarta ce ta soma ringing, rai a a ɓace ta kai hannu ta ɗaga ba tare da ta duba mai kiran ba.
“Hello Anty.”
Aka faɗa bayan an ɗaga wayar, murmushi ta yi sannan ta ce.
“Auta, yaushe kika dawo?”
“Yanzu Anty, ya gida.”
“Lafiya ƙalau Auta, yaushe zaki zo, ko zaki iya zuwa yau?”
“Yau kuma Anty?”
“Eyh, akwai maganar da zamu yi.”
“Tam zan faɗa ma Hajja.”
“Okay, nima zan faɗa mata.”
Jamila ta faɗa tare da kashe wayar, abin da ya sa ta ce ƙanwarta tazo ko banza idan itama tana nan zata rage jim haushin ganin Mijinta da yarinyar nan mara kunya, sannan ƙanwarta ta itama daidai take da Husnan tun da boading school take, yau suka yi hutu ta dawo, to idan suka haɗu Husna ta yi mata itama zata yi mata.
A ɓangaren Husna kam tana shiga ɗaki ta kwanta, ita dai zaman gidan gaba ɗaya bai mata ba, sai take jin kamar ba za ta iya kwana biyar ɗin nan ba, yau kwana ɗaya ma an hau sama an sauka bare kuma kwana huɗu nan gaba.
Bacci ne ya ɗauketa wanda bata farka ba sai kiran sallar azahar, anan ɗakin ta yi salla ta sake kwantawa sabida bata jin yunwa, kuma idaan ta fita ma babu abin da za ta yi, tana dai son zagaye gidan, amma ta bari sai zuwa yamma haka, sake kwantawa ta yi baccin ya sake ɗaukanta, amma wannan lokacin bata yi wani dogo ba wajen ƙarfe uku ta tashi, sai da ta sake wanke fuskarta sannan ta fito, a lokacin babu kowa a falon kai tsaye ta yi kitchen ta sami abinci a plast, bata ɓata lokaci ba ta ɗeba ta yi cikin ɗakinta ta zauna ta ci, tana cikin ci ta fara jin magana alamar baƙi aka yi suna ta hira cikin raha, sai da ta gama cin abincinta tsaf sanan ta fito hannunta riƙe da plate ɗin, muryar da ta ji na magana ya sa ta ɗaga kai ta kalli cikin falon, wa za ta gani inda ba Aisha Sharif Tafida ba, Aisha da suka yi faɗa a kan Uncle Dee, a take abin da Said Kibiya ta faɗa mata lokacin da ta koma makaranta ɗauko kayanta ya dawo kanta, wai Aisha Sharif Tafida tana cewa ta mutu, tabi kowa tana faɗa masa wai ciwon zuciya ne ya kamata ta ce tana son Uncle Dee ya ce ita yake so shine zuciyarta ta buga ta mutu.
Tun a lokacin Husna taso su Ali Kaita su barta taje su bugata da Aisha Sharif ɗin amma suka bata haƙuri, aikuwa yanzu Husna na ganinta abun ya dawo mata sabo a ranta, ta ƙurawa Aisha Sharif ido ko mene haɗinta da Jamila oho? Aisha sharif ɗin ma tun fitowar Husna ta ƙura mata ido, tana mamakin mai ya kawo Husna gidan yayarta, wata uwar harara Husna ta watsawa Aisha Sharif, sannan ta ce.
“Allah ya haɗani da ke anan domin na gurje bakinki a dandaryar ƙasa, sai dai kuma yanzu bazan kulaki ba sabida wanda kike haushi a kan sa ni na gama da shi, Uncle Dee ba. Har abada na gama da shi, kije ki ci gaba da tura kanki a inda ba ayi da ke.”
Harara Aisha Sharif ta mayarwa da Husna, sannan ta ce.
“Eyh naji ɗin, a kin gama da shi ƙawayenki suka zo suna neman lambarsa ruwa a jallo.”
“Wallahi Aisha Sharif yanzu zan haɗa kanki da bango, kinsan ba yau na fara ba.”
“Allah Ya baki sa’a wallahi, da sai kin yi nadama.”
Jamila ta faɗa, sannna ta juya ga Aisha Sharif ta ce.
“Ke auta aina kika san wannan mara kunyar yarinyar?”
“Anty a ajinmu take a FGGC, tana jin haushi nane sabida form master ɗin mu y ce yana sona.”
“Allah Ya tsare wallahi, Uncle Dee ni Husna na gama da shafinsa dan da yanzu sai dai kuji munyi aure, to da yake nasan tarbiya iyayena bazasu iya ɗaukan aurena su bawa wanda ba musulmi ba. Ke kuwa da kike daga gidan ‘ya’yan Yahudu da nasara sai kije ki yi ta aurensa.”
Husna na kaiwa nan ta saki faranti a wajen ya faɗi ƙasa ta juya ta yi cikin ɗaki, Jamila ta kalli Aisha ta ce.
“Auta daman makaranta ɗaya kuke yi, ai na ɗauka ta yi candy ne?”
“A’a Anty ko sakandiri bata gama ba, ajin mu ɗaya kuma wallahi daƙiƙiya ce. Amma me take yi anan?”
“ƙanwar Honey ce.”
“Ƙanwarsa kuma, na zata su wannan Nusaiba ne ‘yan uwansa, kuma ai bai da ƙanwa.”
“Cousin sister I mean.”
Jamila ta faɗa tare da zama, sannan ta sake cewa.
“Wallahi bana son yarinyar nan ko kaɗan, bata sa kunya.”
“Nima Aunty ko a school bana kula ta, ban yi tunanin ma suna da kuɗi ba, ma ɗauka she is from poor family.”
“Yeah, ai su ba masu kuɗi ba ne, shi ya sa ma aka kawo ta gidansu, so yanzu maman shi ce bata nan aka kawo ta nan.”
Taɓe baki ta yi, sannan ta ce.
“Anty ita ce fa ta rabani da Uncle Dee da nake faɗa miki, wallahi ina son sa amma gaba ɗaya baya bani attention ɗinsa, yanzu ma ya bar school ɗin, tare ma suka bar school shi da ita.”
Harara Jamila ta watsawa Aisha,sannan ta ce.
“Kinsan Allah babu wanda zai barki ki auri wani school teacher, waye malamin makaranta, me yake da shi?”
Tura baki Aisha ta yi, ita dai tana son sa kuma ai Abbanta zai iya ba shi wani aikin daban. Husna dai tun da ta shiga ɗaki ta zauna tana faman tunani, kenan Aisha Sharif ƙanwar wannan matar ce kenan, shi ya sa haka kawai taji ta tsanai Jamila ashe kishin da take yi da Aisha ne ya shafe ta, to wallahi ko anan ɗin ma ba raga mata zata yi ba, idan ta ce zata mata uban duka zata ci, babu ruwanta da wata Jamila bare kuma mijin jamila.
Tun wannan lokacin Husna bata sake fitowa ba sai wajen ƙarfe biyar da rabi, lokacin da ta fito duk basa falon, ita daman zagaye gidan zata je ta yi, dan a rayuwarta tana ƙaunar fita zagaye waje idan tazo.
Haka ta fita ta zagaye gidan tsaf, ba wani girma ba ne da shi amma ya tsaru sosai. Gidan bene ne amma taga kamar basu cika amfani da benen ba ma, gaba ɗaya rayuwarsu a ƙasan suke, ko da yake me zasu yi a saman, su biyu ransu ko ƙasan ɗakuna ban da wanda aka bata sun kai biyar, ga shi kowanne da toilet ɗinsa, kitchen ɗaya ne a ƙasa amma kuma yana da girma sosai da sosai, dan ya kusa girman falonsu na gidansu.
Kuma da alamu yanda ƙasan yake haka saman yake shima, ɗan gefen da mai gadi yake zama ta samu ta zauna, tana kallon ‘yan ƙananan bishiyoyin da ke harabar gidan daga ɓari ɗaya. Ita ka ɗai ke zancenta kamar da wani a kusa da ita.
“Ni wallahi na raina ma ji da kai irin na Jamila, wannan gidan kamar zuciyar talaka chaɓ, mu dai Allah ka yi wa ‘yan uwana arziƙi su gina mana irin na Mimi, shima mijin nata yana wani izzah da gadara a ɗan wannan gidan, Mitchewwww.’ Taja dogon tsaki, dan har cikin zuciyarta ta raina gidan wallahi, ai idan ɗa ya taso gidan da yafi na iyayensa yake ginawa amma shi ya gina wannan ɗan tsirut ɗin gidan, ko dayake gida irin na Alhaji Musa Ɗankaka gina shi sai an shirya, sabida yana da matuƙar girma, ya tsaru fiye da duk yanda mutum zai iya hasasowa.
Kiraye kirayen sallar magariba ya sa ta tashi ta koma ciki, a lokacin kuma ta tarar da Aisha Sharif a falon tana zaune tana kallo, harara Husna ta watsa mata ta wuce, itama ta bi Husna da harara.
Husna na idar da sallah ta dawo falon sabida itama tana son ta yi kallon ko zata rage wannan kaɗaicin da ya isheta, zuciyarta a nutse ba tare da hayaniya ko neman masifa ta zauna daga gefe ta zubawa TV ɗin ido, MBC bollywood Aisha ɗin ke kallo hakan yasa Husna ma kalla ba wai dan tana jindaɗin kallon ba, kawai sabida ta gaji da zama haka shirun. Har aka sake kiran sallah Husna ta miƙe taje ta yi ta sake dawowa ta tarar da Aisha a zaune, ita dai bata tanka mata ba tun da ba magana suke ba.
Suna nan zaune Jamila ta fito cikin kwalliyar dare da ta saba yi domin mijinta, wani kallon banza ta watsawa Husna, sannna ta zauna.
“Me kike kallo haka a mbc bollywood ɗin?”
Ta tambayi Aisha, Aisha ta ce.
“Nama gama kallon, tashi zanyi na yi sallah.”
“To kashe min Tv.”
Jamila ta faɗa, Aisha ta kashe ta tashi, ita dai Husna bata ce musu komai ba, falo ne dai duk masifa ba zata tashi ba, dan ba tsoron su take ba.
“Anty, amma idan yarinyar nan ta tafi zaki kai kujerunki car wash ko?”
Aisha ta faɗa tana zama, kallonta Husna ta yi wa har ta yi sallar ta gama a ƙasa da minti biyar, Allah mai iko.
“Ke nifa wallahi koma mene sai yarinya tabar gidan nan shine kawai.”
Jamila ta faɗa, sabida duk lokacin da ta kalli Husna wani irin abu take ji tokare mata a ƙirji, Husna na son yi musu magana, sai kuma ta ƙyale su tun da dai basu kama sunanta ba, bata da hujjar yi musu magana.
“Uhm, ni banga ma masifa ba a dinga liƙewa mutane dan suna da kuɗi.”
Aisha ta faɗa, Husna a rayuwarata babu abin da ta tsana kamar ta ji ance sun yi abu sabida basu da kuɗi, ba shiri ta miƙe ta cafke wuyan Aisha, bata tsaya wata wata ba ta hau gaura mata mari, Aisha ta miƙe ta cakumi wuyan Husna sai faɗa ya kaure a tsakani, daman sun saba a makaranta, ita Aishan ma ta manta Husna ne ko kuma dan tana gani kamar a gidan yayarta ne shi ya sa za ta yi mata abin da ta ga dama.
“Wallahi ki cika ta ko na yi miki ɗan bazan duka, kuma wallahi bari Honey ɗin yazo, Allah sai kin bar gidan nan, kije ko ina zaki ma.”
“Kinga ban shiga sabgarki ba, bazan kula ki ba sabida baki kai na kulaki ba, ita kuwa mun saba gwabzuwa da ita, tasan na jaki take sha a wajena.”
“Na jaki dai muke sha a wajen juna.”
Aisha Sharif ta katse Husna, ai bata gama magana ba Husna ta gwara kanta da bango,ta fara dukanta. Husna na dukan Aisha, Jamila na dukan Husna ta baya daidai lokacin Ashraf ya shigo, ya yi sallama har yagaji ba a amsa ba, daman ciki ciki yake magana, to ya shigo ana ta dambe babu wanda zai ji sallamarta tasa.
Sai dai ya tsaya ya ƙare musu kallo, ya fahimci yanda faɗan nasu yake, Husna Aisha take faɗan da ita, ita kuma Jamila Husnan Aisha take shigewa faɗan. Wani duka da Jamila ta kaiwa Husna wanda ta ji shigarsa ya sa ta juya da dukkan ƙarfinta ta hankaɗa Jamila ta yi baya, cike da zafin nama ya tare ta ta faɗa jikinsa, wata ajiyar zuciya Jamila ta sauke a take ta sauya yanayin fuskarta kamar ita ake cuta a faɗan, Aisha ma ta kula da shi ya sa ta dakata Husna kam ta rufe ido sai dukan Aisha take babu ji babu gani.
A Tsawace ya ce.
“Enough.”
Husna ta yi ƙirmijiji kamar ba ta ji ba, ya sake cewa.
“Ba zaki dakata ba.”
Wani haushine ya takoreta, duk abin da aka yi mata bai gani ba sai matarsa da ƙanwarta, to wallahi a shirye take daidai da shi, ba zata ɗauki raini ba tun da taga abun na sa shima ba mutunci, ko dayke daman ina mutunci a tare da shi.
“Ke wai ba magana nake miki ba, idan nazo nan sai na dake ki fa.”
“To ka dake ni ɗin mana, mu shikenan daga zuwa cin arziƙi sai abu ya zama tsiya, nima ai ba a son raina nazo ba kuma in Allah Ya yarda gidan nan yau zan bar shi.”
Wani irin kallon mamaki yake mata yanda ta rufe ido tana ta zuba ruwan bala'i, bai san jujin nata yakai har haka ba, shi iya abin da ya sani gunguni da zunɓuro baki, amma yau dai gashi tana neman fige mai gashi, lallai wanda ya kwashi yarinyar nan ya kwashi buhun masifa. Ganin ba za ta yi shiru ba ya sa shi zuwa kusa da ita ya fusgota, a fusace ta juyo tana watsa mai harara, ya ɗaga hannu zai tsinka mata mari, itama ta dunƙule hannu ta ɗaga shi, tana harare harare, jira kawai take ya sauke mata marin itama ta kai mai nata dukan.
Legendspen-Sayyid
08129553971
🔥🔥*DA JININSA NAKE RAYUWA*🔥🔥
*-Amanan-Janafty-*
(16)
Wani irin mamaki ne ya ziyarci ƙwaƙwalwarsa wanda ya haifar masa da mutuwar tsaye, wai ta dunƙule hannu kenan dukansa za ta yi? Bai san lokacin da wani murmushi ya suɓuce masa ba, lallai yarinyar nan da sauran ta.
Jamila da Aisha kam suma mutuwar tsaye suka yi, Jamila a ranta tana ayyana dole kuwa yarinyar nan tabar gidan nan yau, tun da har rashin kunyarta ya kai wannan matakin. Ita kam Aisha ta san Husna zata yi abin da yafi wannna ma, amma bata yi tunanin zata iya yiwa mutum kamar Yaya Ashraf ba, mutum mai girman har haka, cikkaken mutum mai kwarjini, duk irin girman Anty Jamila idan suka jera gani ake ya kereta, amma wai Husna ta ɗaga hannu haka zata dake shi.
Murmushin da Jamila ta ga ya yi ya ɓata mata rai, cikin salon yaudara ta ce.
“Rashin arziƙin da kika yi min bai ishe ki ba kenan ko? Sai kin haɗa da shi kenan. Kuma da kika ce yau zaki bar gidan dama wa ya riƙe ki, ɗazu da kika ce zaki tafi wani ya hanaki.”
Kallon Jamila Husna ta yi, ita bata san me ya sa ba amma haka kawai sai taji bata son biyewa Jamila, mussaman data fuskanci neman rigimata take da ita, ita Husna irin mutanen nan da indai kana son rigima da su a lokacin to baka isa ka yi ba, sai lokacin da ka manta zasu zo maka da nasu jujin kuma duk ƙin da mutum yake wa faɗan to sai fa anyi, shi ya sa bata cika son kula jamila ba.
Cika ta yi ya sauke hannunsa, itama ta saki nata hannun ta yi cikin ɗaki ko kallonsu bata yi ba, tana shiga ɗaki ta sauko da jakarta daman kaya ɗaya ta sa tun da tazo, daman bata jera sauran a ko ina ba, sai brush da ta ajiye a banɗaki, shima shiga ta yi ta ɗauko.
Suna tsaye a falo Husna ta fito, Jamila sai sharri take karantawa Ashraf Husna bata ko kallesu ba ta nufi ƙofa za ta fita, Hunsa na fita Jamila ta sauke wata ajiyar zuciya, wani irin sanyi ya ratsa ta kamar ta sauke wani ƙaton dutse da aka ɗaura mata a kanta, sai dai bata gama sauke ajiyar zuciyarba Husna ta sake shigowa.
“Azo a buɗe min ƙofa.”
Husna ta faɗa tana turo baki, da yake idan ka fito daga falon wata ƙaramar baranda ce akwai wata ƙofa da ke kusa da ƙofar falon ya zama suna kallon juna, sai kuma ƙofar da zata sadaka da waje, to wannan ƙofar ce a rufe, abin da bata sani ba ƙofar na amfani da remote ne kuma Asharf ya kulle suna tsaye ko Jamila bata kula da lokacin da ya danna remote ɗin ba.
Kamar ta