Chapter 7 of 26

DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty

shi ba.

Ƙara matse hannunta ya yi kaɗan yanda ba zata ji zafi ba ya ce.

“Tun ranar da na fara ganinki, na ji kamar an sanyawa idona mayen ƙarfe na dinga binki da kallo, har kika kula da ni. Tun daga wannan ranar zuciyata ta kasa sakat Husna, ta kai ta kawo har ajinku nake zuwa ina leƙa ki ta window, duk wani motsinki a makaranta a kan idona yake, ban fargaba da abin da nake yi ba sai da naji zuciyata ta fara rayamin idan bake ba zan iya rayuwa ba.

Na shiga tsananin tashin hankali mussaman da na tuna babban bambamci da ke tsakani na da ke. A lokacin kuma na fara ƙoƙarin yin nesa da ke, amma na gagara kamar ƙara janyo zuciyata ake yi gareki, a lokacin da kuka shiga SS section na ji daɗi mussaman da na zama malamin ajinku.

Duk yanayin yanda nake sonki idan na tuna abin da ke gabanmu sai na ji ina neman sarewa, mussaman da ya zama ni kaɗai ke son ki. A ƙoƙarin nesanta kaina da soyayyarki na fara kula Aisha Sharif ina tunanin ko hakan zai cire min sonki a raina, kema kuma ya cire miki nawa da na fara gani, sai dai kuma abin da kika yi ya tabbatar min da tunani na ba daidai ba ne.
Husna bantaɓa jin son mace a rayuwata ba sai ke.”


Ya durƙusa ya zube kan gwiwoyinsa, duk da Husna ta san wajen babu kowa amma sai da ta kalli gefe da gefe sabida yanda zuciyarta ta buga da ƙarfi, ya sake kama hannunta.

“Ina sonki Husna, dan Allah ki yi min alƙwari ba zaki bar zuciyata a tarwatse ba.”

Itama zubewa ta yi akan gwiwoyinta, hannusa na cikin nasa ta ce.

“Na yi maka alƙwarin, duk runtse duk wuya ina tare da kai ina tare da sonka, babu wani mutum da zai iya raba soyayyar da ke tsakaninmu.”

Daga haka suka tashi suka koma kan wata kujera da ke can gefe, ya shiga bawa Husna asalin tarihinsa. Iyayensa ʼyan Sourthern Kaduna ne, acan aka haifeshi da ʼyan uwansa sun kasance suna al’ada irin ta musulmai sabida suma asalin Hausawa ne, shi ya sa suttura, abinci, da wasu abubuwan nasu suke iri ɗaya da na musulmai. Kakansa babban pastor ne da ake kira Devid Man of God, yana daga cin manyan pastoci da mutanen yakin suka yi imani da su, dubban mutane da yawa suna girmama shi, shi kan sa shine prophet ɗinsa, Husna ta kalleshi, sannan ta ce.

“Prophet fa?”

Sai kuma ta ce.

“Kalmar prophet ai ɗan aiki take nufi ko?”

Ya gyaɗa mata kai, sannan ya ci gaba da cewa.

“Bazan ɓoye miki ba, iyayena da ʼyan uwana da duk na kusa da ni basu ƙaunar ‘yan addininku.

Duk da suna mu’amala da su amma ta ciki na ciki, sai dai hakan bai da matsala da zama na ni da ke, dan ba a kusa da su zamu zauna ba.”

“Aina zamu zauna?”

Husna ta ƙatse shi.

“Zamu zauna kusa da gidanku, wajen da yake da tarin musulmai ba kamar unguwarmu ba da ke da tarin waɗanda ba musulmai ba.”

“Wacce unguwa kenan?”

“Hotoro T Shama. Anan duk gambiza ne bakya tantance musulmai da waɗanda ba musulmai ba sai ranar friday da Sunday.”

Husna ta gyaɗa kai, sai kuma ta ce.

“To ‘ya’yanmu fa?”

“‘Ya’yanmu me?”

Ya tambayeta.

“Wanne addini zasu yi?”

“Wanda suke so.”

Ji ta yi jikinta ya yi sanyi, amma duk da haka ba zata karaya ba, amma dai ita bata yarda da wannan zancen ba, cike da ƙuruciya da wauta ta ce.

“To ba sai mun haihu ba, dan ni bazan iya barin yara na su yi wani addini daban ba.”

“Yanda kike so haka za ayi.”

Ya faɗa da dukkan gaskiyyarsa, dan shi indai Husna zata zama tashi to zai yarda da duk abin da take so, idan ma ta so ta yaran su yi nata addinin, shi dai ita yake so ba yara ba.

Shiru Husna ta yi babban abin da ke damunta yanda zata sanar da su Abba wai ba musulmi ba ne, to zasu yarda ma kuwa? Abu ne babba fa.

“Tunanin me kike yi?”

“Iyayena, ba zasu yarda ba fa.”

“To ya zaayi.”

Ya faɗa kamar zai yi kuka, jikinta ne ya yi sanyi sai kuma shawararta da take fitowa daga gajeren tunaninta ta zo mata.

“Kar ka ce musu kai ba musulmi ba ne, kawai ka bisu a musulmi ne kai, mu cire wannan a ranmu munyi rayuwa kamar addinin mu ɗaya.”

Wani irin murmushi ya yi, ya fuskanci dai ƙuruciya ce kawai ke ɗawainiya da Husna, idan ba haka ba ta ina za ayi aure a haka? Abu sai ka ce wasan yara.

“Ka ji.”

Ta faɗa kaman za ta yi kuka, sai da ya juyo da dukkan hankalinsa kan ta sannan ya ce.

“Aure nake so mu yi na gaskiyya da gaskiyya, da sa albarka daga kowanne ɓangare, zancen sako ƙarya a ciki bai taso ba. Idan har muka dage a kan raayin mu, komai tsanani komai wuya to zasu haƙura su barmu mu yi aure mai cike da albarka, abin da ke gabanmu babba ne.”

Shiru Husna ta yi, ta san tana da taurin kai amma fa duk taurin kanta Abba ya sha gabanta, magana ɗaya yake yi kuma duk tsanani ba ya sauka daga kan wannan maganar, sai dai kuma idan ta tuna soyayya da suke mata, da zarar sun ga zata shiga damuwa dole zasu barta, tabbas aure mai albarka take so su yi.

Ɗan taɓa hannunta ya yi ta dawo daga tunanin da ta faɗa, ya ce.

“Sai mun dage, kin dage na dage idan ba haka ba zasu yi nasara a kan mu, zasu raba mu ta ƙarfin tsiya, amma idan har muka dage muka jajirce zamu yi nasara, bambamcin addini ba bambamcin rayuwa ba ne, muna da ido muna gani muna ji, munsan bambamce bambamcen da ke tsakaninmu, babu wanda zai tsallake na wani.”

Kalamansa sanyayar mata da jiki suke yi, haka kawai sai ta dinga jin rauni a zuciyarta kamar tana buƙatar ta yi kuka, ta rasa me yake damun zuciyarta haka. Gaba ɗaya taƙi yi masa magana sai dai ta yi shiru alamar tunani take yi, abin da yake sanyaya masa jiki.

“Kin qi ki ce komai.”

“Baƙi na yi ba, kawai ina tunanin ta inda zan fara magana da su, wa zan samu? Na san suna sona suna ƙauna ta, kuma baza su juya min baya ba, amma ina jin nauyinsu sosai.”

“Eyh tabbas abin da girma, amma kuma mutanenku basa ƙyamar mu kamar yanda namu mutanen ke yi, kuna da kyakyawar zuciya.”

“Amma ai Allah Ya haramta fa.”

Husna ta faɗa jikinta a sanyaye, wani irin kallo ya yi mata, sannan ya ce.

“Amma ai naga anyi sosai.”

Husna ta girgiza kai, sannan ta ce.

“Namiji musulmi zai iya auren macen da take ba musulmi ba, amma mace musulma ba za ta iya auren namiji ba musulmi ba.”

“Hakane? Amma naga manyan stars na duniya da suke musulmai mata sun aure mazan da ba musulmai ba.”

“To ai waɗan nan ba aladar mu ɗaya da su ba.”

Husna ta faɗa da dukkan gaskiyyarta, ba wai so take tace su fasa auren ba, amma kawai tana faɗa masa ne ya sani.

“To kenan al’ada ce ta hana ba addini ba, tun da shi addini guda ɗaya ne, musulunci na nan da na can ɗaya ne, haka shima addinina na nan da na can duk ɗaya ne.”

Shiru Husna ta yi, al’ada ce kenan ta haramta, ita dai a duk karatun ta haram ta sani, amma ai zai iya musulunta sabida ya aureta, tun da akwai hadisi guda da ya yi magana a kan haka. A take ta datsu daidai wajen ta fara maimaitawa a kanta.

‘Faman kanat hijratuhu liddunya yuseebuha, awimra'atin yankihuha, fahijratuhu ila ma hajara ilaihi.’ Sai kuma ta yi shiru, amma hadisin ai ba a kan haka yake magana ba hadisin yana magana ne a kan Mutumin da ya musulunta ko ya yi hijira kawai saboda ya sami wata mace ya aura ba saboda Allah ba, to musuluncinsa ko hijirarsa ba za ta sami lada a wajen Allah ba iyakacinta duniya da matar da ya aura.

Ji ta yi kanta yana sara mata sosai da sosai, hakan ya sa ta dafa kan nata tare da runtse ido, da sauri ya ce.

“Me yake damunki?”

“Kai na.”

Ta faɗa tana sake runtse idonta.

“Tunani da kika sawa kanki ne, ki yi haƙuri ki nitsu kin ji, zamu je a matakin da kika yi magana bazasu fahimci akwai bambamcin addini ba, har sai mun gama fitar da mafitar da zamu yi amfani da ita okay?”

Ta gyaɗa masa kai alamar ta ji, suka lallaɓa suka koma cikin asibitin, a lokacin da ta shiga ɗakin akwai tarin ‘yan uwan Mama da suka zo da wasu cousin sister ɗinsa, kowa ya hau yi mata sannu aka ci gaba hirar da ake yi ana mata sannu, sai dare suka tafi aka bar Mama da yake yanzu ita kaɗai ce ke kwana da ita tun da ta sami sauƙi, shi kuma Uncle Dee Moses ne ke zuwa, suna zaune Mama ta ce.

“Husna wai shi wannan malamin naku iyayensa basu san halin da yake ciki ba ne?”

“Eyh Mamah, ya ɓoye musu ne, kuma tunaninsu yana makaranta tun da kinga daman malamai ma a can suke kwana.”

“Eyh hakane kuma, amma wannan da yake tare da shi fa ba musulmi ba ne, shi ya rasa waɗanda zai yi mu’amala da su sai waɗanda ba musulmai ba, aiko a hadisi an ce ku yi mu’amala da mutane na gari, sabida ku sami kyakyawar shaida. Kuma hausawa suka ce abokinka kammaninka.

Yanzu Alhaji har da cewa yana tunanin shima ba musulmi ba ne, tun da basu taɓa ganinsa yana sallah ba.”

Sai da Husna ta ji kamar an ratso mata kwalba a tsakiyar kanta, cikin rawar murya ta ce.

“To shi da bai da lafiya, ai zuwa massallaci bai kama shi ba, ni dai ban san ba musulmi ba ne sabida ko a mu’amlal sa, shigarsa da ɗabi’unsa zaki gane akwai musulunci.”

“Abin da na ce musu kenan, amma kin san Walid da jaye jaye magana.”

Shiru Husna ta yi bata sake cewa komai ba, sai Mama ta sake cewa.

“Ni kam Husna bana jin zaki koma wancan makarantar kwanan, kina warkewa za aje a karɓa miki takardar transfer, ki kwaso komai naki ki dawo wanan jeka ka dawo.”

“Me ya sa Mama?”

Husna ta faɗa, Mama ta rausayar da kai ta ce.

“Haka kawai, sai mun fi jin nutsuwa idan kina gida, daman ba saura shekara ɗaya ba, to ki ƙareta a gida kawai.”

Hawaye ne suka fara zubowa daga fuskar Husna, ta ina za a fara cewa wai ba za ta koma Munjibir ba, wannan ma ai ba za ta saɓo ba, haka ta kwanta duk ranta babu daɗi, ya za ayi ta ci gaba da karatu a wata makatantar ba FGGC ba, ya za ta yi da Said Kibiya da Ali Kaita da suka zama ʼyan uwanta? Ta san daman dole zasu rabu, amma a bari lokacin rabuwar ya yi mana.


Washe gari da yamma asibitin yana cike ba baƙi, kamar kullum ʼyan uwa sun zo dan basa gajiya da zuwa, mussaman Hajiya Bilki yau har da su Leemah da Dade ma sirikatar, tun da tazo take basu nishaɗi sai barkwanci take yi, sai da Dade ta gyara zama sannan ta ce.

“Ga Ashraf da nafi so cikin jikokina, ya je ya kwaso mana wata tsohuwar guzama, ina ga wannan zai su yi sakwanni da ita, wai ita ʼyar boko ta zo mana gida da gilashi, na ce missa ƙyanƙyanma ya ci ubansa.”

Duka ɗakin suka kwashe da dariya, sai da suka tsaigata ta ce.

“Gashi taƙi haihuwa sai ci kamar gara, wallahi nauyin kashi ne da ita, sai ta yi minti talatin cikin bayi, ai naje gidan nasu.”

Kamar daga sama suka ji an bugo ƙofar ɗakin ta buɗe mutane suka shigo, su biyar ne maza biyu sai mata uku sai kuma Moses daga bayansu cikon na shida, mazan manya sun fara manyanta, amma duk suna sanye da ƙananan ƙaya, ga ƙatuwar sarƙar me cros saƙale a wuyansu, ɗaya ma har hannunsa, matan ɗaya na sanye da atamfa me adon orange babbar kenan, sai kuma ‘yan matan ɗaya na sanye da mini skirt da t shirt, kanta ya sha gashin doki, sai kuma ɗayar sanye da riga da wando itama kanta ya sha gashin doki, da sarƙar cros a wuyanta, tana matuƙar kam da Uncle Dee kamar an tsaga kara an karya, kuma da alama shekarunsu bazasu wuce kai ɗaya ba, duk yanda aka yi ma twin sister ɗin shi ce, domin kamar ta ɓaci.

“Bisimillahi, tsarin ubangiji muke nema daga ire-irenku, su waye ku zaku shigo mana waje, ko baku iya sallama ba ai kun iya gafara.”

Dade ta faɗa tana ƙare musu kallo, tana turo hancinta gaba, Mama da Hajiya Bilki da sauran duk da ido suke bin su, tare da tambayoyi fal ransu, Husna kam ta riga da tasan ‘yan uwan iliya ne, abin da suke ɓoyewa ne ya fito fili.

“Hey where is our son? Ina ɗan mu?”

Ɗaya daga cikin mazan ya faɗa, Hajiya Bilki ce ta ce.

“Wanne ɗan?”

Daidai lokacin kuma su Yaya Abdul suka yi sallama suka shigo, daman suna waje ne yanzu kuma suka shigo.

“Our Son Iliya da kuke so ku kashe mana.”

Sai a lokacin Mama ta kula da Moses, tun da ta gan shi ta san abokin Uncle Dee ne, kenan waɗan nan iyayensa ne?

“Mama su waye waɗan nan?”

Yaya Abdul ya tambaya, Mimi ce ta ba shi amsa.

“Wai suna cewa ina ɗan su Iliya da ake so a kashe musu.”

“Iliya.”

Duka suka maimaita, su basu san wani Iliya ba, amma Moses da suka gani ya sa suka gane Uncle Dee ne, kenan iyayensa ne?

“Su waye ku?”

Alhaji ya faɗa, wanda ya yi magana ɗazu ya ce.

“Ni uncle ɗinsa ne, wannan kuma babansa ne.”

Ya faɗa yana nuna wanda bai yi magana ba, sai faman cika yake yana batsewa, zuciyarsa a wuya take, wai ɗan sa ne yazo ya sadaukar da jininsa ga masu addini musulunci, ina zai kai wannan abun kunyar? Wanda ya yi maganar ya ci gaba da cewa.

“Wannan mamansa ce, wannan twin sister ɗinsa ce.”

Ya nuna wadda ta yi matuƙar kammanin da Uncle Dee ɗin, sannan ya ci gaba da cewa.

“Wannan kuma wadda zai aura ce, yarinyar wajena, shi kuma wancan ɗan wajena ne, cousin brother ɗinsa.”

Gaba ɗaya mutuwar tsaye suka yi, abin da ke yawo a kan su shine, Uncle Dee ba musulmi ba ne kenan? Kamar ya sani ya ce.

“Mu ba musulmai ba ne, kuma bama son musulmai, a yanzu muna fushi da Iliya kan abin da ya yi, dole sai muje mun yi sadaukarwa da neman yafiya, babban mu Prophet David ya ce lallai ayi sadaukarwa me girma kafin a yanke girman zunubin da ya yi.”

“Astagfirullahal azim, Allah ka ɗauki raina da ganin wannan mummunar ranar, yau ni ce.. ni ce ke shaƙar numfashi ɗaya da masu ƙin addinin Allah.”

Dade ta faɗa tana zubar da hawaye, jikin kowa ya yi sanyi, Husna kam ta yi nisa cikin tsananin tashin hankali da damuwa.

“Yana ina ne wai?”

Wanda yake magana tun zuwan su ya faɗa, dan shi kaɗai ne yaga zai yi magana da su, su sauran gani suke idan sun yi magana ma sun aikata babban zunubi mai girma, da yake ʼyan riƙau ne a cikin addinin nasu, sabida babbansu babban pastor ne.

“Baya nan yana ɗakin gaba.”

Mama ta faɗa ranta na mata soya, ba haushin Uncle Dee take ji ba sabida ya yi musu abin da bazasu iya saka masa ba, amma jin wai ba musulmi ba ne ya yi matuƙar gigita tunaninsu, mussaman idan ta tuna soyayyar sa da take gani a idanun Husna, wanda kuma shine abin da duk ya firgita kowa da ke cikin ɗakin.

Haka suka sa kai suka fice duka zuwa cikin wancan ɗakin. Suna fita Mimi ta ce.

“Husna kin san daman ba musulmi ba ne?”

Husna ta fara girgiza kai, tana zubar da hawaye ta ce.

“Bansani ba, bai taɓa faɗa min ba.”

Yaya Walid ya ce.

“Daman Alhaji ya yi wannan tunanin, amma muka kawar da shi, duba da irin mu’amala, shigarsa da sunansa.”

“Ƙila ma canja sunan ya yi.”

Alhaji ya faɗa, Mimi ta girgiza masa kai ta ce.

“Ko anan ma sun ambacin sunansa sun ce Iliya, kuma a wajensu wannan ba wani abu ba ne, suna sanyawa ʼyaʼyansu irin waɗan nan sunayen.”


Bayan shuɗewar kusan minti goma suka sake bankawo cikin ɗakin, a wannan lokacin har da Uncle Dee kuma Abba ya shigo ana tsaka da bashi labarin abin da ya faru suka sake dawowa. Matsa musu ƙofar suka yi suka shigo, sai da suka gama shigowa a wannan lokacin baban nasa ne ya yi magana.

“A matsayina na babansa, mun yi tsinuwa a kan jininsa da aka bawa ʼyarku, abun bauta ya saka mana zalunci da kuka yi mana. Sannan daga yau muna so ku raba ɗiyanku da namu idan ba haka ba zamu yi mata illah ta zahiri ko a ɓoye.”



Legendspen
08129553971
🔥🔥 *DA JININSA NAKE RAYUWA*🔥🔥


*-Amanar-Janafty-*

(08)


“Ubangijin Annabi Adam yafi ƙarfin duk wani sharrinku, annamimai maƙiya Allah.”


Dade ta faɗa tana huci, dan ita a rayuwarta bata son ta ji an ce mutum ba musulmi ba, ita ko mai wasa da addini ba ta so shi ya sa duka sauran matan Alhaji Musa bata yarda da zama kusa da su ba sai Mimi, a cewarta ita kaɗai ce ta fito daga gidan malamai, kuma taga alamun riƙo da addini a tare da ita, haka ma Mama taga akwai addini a tare da ita da ‘ya’yanta shi ya sa ma take son su.


Ficewa suka yi daga ɗakin suna jan Uncle Dee, basu damu da abin da aka kashe a asibtin ba ko lafiyarsa, suna fita Husna ta fashe da wani irin kuka ta haɗa kanta da jikin bango ta yi ta faman kuka, babu wanda ya ce mata ta daina sabida kowa da jimami a ransa, har dare kowa jigum-jigum babu wani mai karsashi, a daren ma Abba yanemi asallamesu dan dama ta samu sauƙi suka koma gida.


Ko a gida Husna bata ce da kowa komai ba haka ta zauna jigum, ba ta so aka yi wannan rabuwar ba, ita yanzu aina zata sake