Chapter 5 of 26
DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty
Kalaman Abba suka sanyaya jikinsu, a take Yaya Abdul ya nufi fita ba dan ransa ya so ba, sai dan ya nuna girma da darajar mahaifinsu.
“Za ku iya zama duka, ai akwai enough seats.”
Likitan ya faɗa, duka suka sami waje suka zauna, sabida akwai doguwar kujera daga jikin bango, Abba da Mama kuma suka zauna a kujeru biyu da ke kusa da tebur ɗin likitan. Bayan ya yi gyaran murya, ya ce.
“Ina so ku saurare ni da kyau, kuma ku daure zuciyoyinku.
Sakamakon jininta da muka fito da shi daga lab ya nuna muna fuskantar wani babban yanayi na gaggawa. Jinin 'yarku Husna ba kawai raguwa ya yi ba... ƙonewa yake yi kuma mutuwa yake a kowane sa'a guda da ke wucewa.
Mutum daidai wanda yake da lafiya yana da matakin jini (PCV) tsakanin kashi 36% zuwa 46%. Amma a halin yanzu da nake magana da ku, jinin Husna yana kashi 11% kacal
Wannan yana nufin garkuwar jikinta ta rikice, tana yaƙi da lalata ƙwayoyin jinin jikinta a maimakon ta kare su. Zuciyarta tana gudu fiye da ƙarfin da aka halitta mata domin kawai ta rarraba ɗan sauran Oksijin da ya rage a jikinta. Idan har wannan adadin ya sake sauka zuwa kashi 9% ko 8% a tsawon mintuna 45 masu zuwa, zuciyarta za ta daina bugawa gaba ɗaya, abin da ake kira da Heart Failure a turance."
Legendspen-Sayyid
08129553971
🔥🔥DA JININSA NAKE RAYUWA🔥🔥
*-Amanan-Janafty-*
(05)
https://chat.whatsapp.com/DyVX8bRFbq66I04yzM5rLp?s=cl&p=a&mlu=0&ilr=4
Gaba ɗaya ɗakin ya yi shiru, babu abin da ake ji sai ƙarar fanka, kowa ya shiga duniyar tashin hankali. Likitan ya yi gyran murya domin su dawo hayyacinsu, sannan ya ce.
“Abin da ke ƙara dagula al'amarin shi ne, Nau'in jininta O-Negative (O-ve) ne. Wannan irin jinin yana da matuƙar ƙarancin gaske a duniya, ba kowa ke da shi ba. Ko da a Blood Bank namu na AKTH gaba ɗaya ba a samun wanman nau’in jini, domin da ya samu akwai tarin mabuƙatan sa, a yanzu haka bamu da ko leda ɗaya ta wannan jinin a ƙasa.
Idan har ba mu sami wanda yake ɗauke da wannan nau'in jinin na O-Negative a nan kusa ya bada an ɗauka an fara sa mata a cikin tsawon sa'a guda ba... ba za mu iya ba ku tabbacin za ta kwana da rai a duniyar nan ba."
Kamar waɗanda aka ɗaurawa dutse haka suka ji kansu ya yi mugun nauyi, kowa ya kasa magana sai maimaita hasbunallahu suke yi a cikin ransu, da ƙyar Uncle Dee ya buɗe baki ya ce.
“To likita, ai a cikin mu nan ba za a rasa mai wannan jinin ba, a duba mana.”
“Eyh, babu lallai a rasa kamar yanda idan ba a samu ba ba zai zama abun mamaki ba. Amma abu ɗaya da yakamata kusa ni, O-Negative is kind of Rare Blood Types, nau'in jinin da ba a fi samun mutane 1 zuwa 2 cikin 100 da shi ba, to kunga wannan yawan naku ba shike da tabbacin za a same ku da shi ba.”
Walid ne ya ce.
“A gwada mana, sai dai na san jini O-Possitive ne, haka ma na Mama, amma a sake gwadawa dan Allah.”
Likitan ya danna wani abu da ke kan tebur ɗin shi, ba jimawa wata nurse ta shigo, ya nuna mata su ya ce.
“Ki ɗauki su kuje ku gwada jininsu, O-Nagative ake nema.”
Tashi suka yi suka bi bayanta, da sauri likitan ya ce.
“A’a Baba ban da kai.”
“Me ya sa?”
Abba ya tambaya, likitan ya yi murmushi wanda suka fahimci ɗabi’arsa ce a haka, ya ce.
“Shekarunka, Baba sun wuce yanda za a deɓi jininka.”
“A’a Likita ina da cikakkiyar lafiyar da za a iya ɗiban jinina, ka barni kawai.”
“Baba idan har muka yi kuskuren cire maka leda ɗaya ta jini, to ba shakka sai mun sanya ma leda biyu na jini, to kaga ai anyi ba ayi ba.”
Allhaji ya ƙara dagewa a kan lallai sai na ɗebi jininsa, da ƙyar likitan ya samu ya lallaɓa shi ya haƙura.
A can wajen gwada jini, na Yaya Abdul aka fara gwadawa, sai dai ba a sami jinin da ake buƙata ba, aka sake gwada na Walid kamar yanda ya faɗa aka sami posstive, Alhaji ma na shi posstive ne, a lokacin da aka gwada na Uncle Dee sai aka yi sa’a yazo iri ɗaya O-Negative, daman shi ya san hakane, amma baya son ya yi katsalandan ne tun da ga 'yan uwanta, nan suka dawo suka sanar da likitan, ya bada umarnin a ɗebi jinin da za ayi scanning aga lafiyarshi ƙalau ko akasin haka, cikin ƙanƙanin lokaci aka gwada jininsa aka ga lafiya ƙalau yake, likitan ya bada umarnin a ɗebi leda ɗaya a sanyawa Husna, sannan ya sanar da su Abba su tambaya cikin ‘yan uwa, ko Allah zai sa asamu, sabida a yanzu haka leda huɗu ake nema na jini, leda ɗaya babu abin da zai yi mata.
Hankali su Abba ya ƙara tashi, Abba ya fara bugawa ƙannensa waya, ya manta ma dare ya yi nisa, nan aka samu har mutum uku suka zo a daren, amma duk jininsu baiyi ɗaya da na Husna ba, tashin hankali bai dawo sabo ba sai da likita ya sanar dasu jinin da aka zuba mata na farko ya ƙone, ana buƙatar wani cikin ƙanƙanin lokaci domin samu rayuwarta.
Waje Mama ta samu ta zube a ƙasa dirshan ta fara kuka, abin da ya sake ɗaga hankalin su Ya walid suka ba zama cikin asibitin, Uncle Dee da ya dawo daga cin abinci baya an ɗebi jininsa ya ga su Walid suna tafe fanjam fanjam.
“Walid me ya faru?”
Ya faɗa cikin tsantsar tashin hankali.
“Wai jinin da aka sanya mata ne ya ƙone, dole sai an ƙara wani, yanzu ‘yan uwan Abba har uku sun zo amma duk ba a sami jinin da ya yi daidai ba.”
Walid ya faɗa, yanayin da muryarshi ta fito kaɗai ya isa ya sanyayawa mai sauraro jiki.
“To muje asake ɗiban nawa mana.”
Uncle Dee ya faɗa yana wucewa, Walid ya rufa masa baya suka shiga cikin asibitin, a can wajen ɗiban jinin masu ɗiba suka ce ba zasu sake ɗiban jininsa ba a yanzu, sabida ba a jima da ɗiba, amma fir yaƙi ya ce lallai sai an ɗiba. Sai da aka fara auna Bp ɗinsa sannan suka sake ɗeban leda ɗaya aka sake sanyawa mata. Wannan leda ɗayan shi ya riƙeta har safiya.
Washe gari Abba ya ci gaba da kiran al’ummar annabi ana neman jini samfurin O-Nagetive, na sadaka ko na siyarwa amma shiru kamar malam ya ci shirwa.
Wajen ƙarfe 12 na rana likitan ya sake sanar da Abba dole fa a nemo jinin domin a samu ta daidaita dan har yanzu bugun zuciyarta yana nan da ƙarfinsa, Mama ta bada shawarar a sanar a gidan rediyo ko Allah zai sa a samu, suna cikin wannan halin Uncle Dee ya shigo shi da wani mutumi wanda bai yi kala da musulmai ba, bayan sun gaisa ya ce da Abba.
“Abba, wannan sunan shi Moses, shine babban abokina da zai iya sanya hannu a duk wani abu nawa, ya biyo ni ne dan ya zama shaida zan sanya hannu a takardar Consent cewar na aminta a ɗauki jini na ko nawa ne ko da rayuwata zata shiga haɗari.”
“Dee are you out of your mind? Daman abin da ka kawo ni nan na yi ne?”
Moses ya faɗa yana kallon Iliya da mamaki, shi bai ma san yaushe ya dawo gari ba, kawai ya gan shi a wajen aikinsa ne ya ce wai ya zo ya rakashi wani waje, ashe abin da ya zo yi kenan? Sadaukar da ransa ya cike high risk form, kuma ma a kan yarinyar BaHaushe, ‘yar musulmai mutane da basa son su basa ƙaunar su.
“Na kira ka nan ne dan ka yisigining a matsayin ɗan uwana, bana kira ka dan na ji raayinka ba ne.”
Uncle Dee ya faɗa yana mamakin Moses, bai san yanda yake jin yarinyar a ransa ba ne, shi ina ma zai sa rayuwarsa idan ya rasa Husna, bai tabbatar da irin son da yake mata ba sai yanzu da ya ganta a halin rai ko mutuwa, aiko duniya zata tashi babu wanda ya isa ya hana shi bada jininsa a sanya mata, ko da kuwa shi zai mutu ya yarda indai Husna za ta ci gaba da numfashi a doran duniya.
“Malam Iliya, ba za ayi haka ba, ka yi iya ƙoƙarinka mun gani mun gode, Allah ma Ya shaida mun gode maka, sai dai fatan Allah Ya yi maka sakayya da gidan Aljanna. Amma a yanzu an wuce matakin da za a ɗebi jininka.”
“Baba.”
Uncle Dee ya faɗa yana matsowa kusa da Abba, ga mamaki sai ga shi ya zube a kan gwiwoyinsa, cikin sanyi murya ya ce.
“Ka yi haƙuri dan Allah, ka barni na sanya a hannu a form ɗin nan, ina so Husna ta rayu, ta yi numfashi mai kyau, ta ci gaba da karatu. Har yanzu ina da damar taimakawa, dan Allah.”
“Wannan kasada da rai ne.”
Yaya Abdul ya faɗa, duk da halin da suke ciki amma bazas u iya rufe idonsu su sanya mutum a haɗari ba.
“Zan iya fa, ni na ce zan iya.”
Uncle Dee ya faɗa muryarshi da alamun taurin kai, dan shi fa babbar kasadar da zai yi ita ce barin Husna ta mutu, ya san ba zai taɓa yafewa kan sa ba.
“Kana ji muje wajen likitan, idan ya ce ba za a ɗauka na dole a haƙura.”
Mama ta faɗa, a ranta tana addu’ar Allah ma Ya sa ace za a iya ɗeba, tashi suka yi gaba ɗaya suka nufi ofis ɗin likitan, Moses ya jawo Iliya baya, ya fara masa magana cikin raɗa.
“Ka sha wani abu ne? Jininka fa, zaka sa rayuwarka a haɗari a kan yarinyar musulmi, baka da hankali?”
Haɗe rai Iliya ya yi sannan ya ce.
“Lafiya ƙalau ma kasan bana shan wani abu, bare kuma yanzu da nake wannan halin, wannan yarinyar ita ce farin ciki zuciyata, ina son yarinyar nan sama da kowacce mace a faɗin duniya.”
“‘Yar Musulmi fa?”
Moses ya faɗa, Uncle Dee yi banza da shi ya bisu cikin ofis ɗin, a lokacin da shi ya shiga cikin ofis ɗin har su Abba sun faɗawa likitan abin da ke tafe dasu, yana shigowa Abba ya ce.
“Shine wannan.”
Likitan ya yi gyaran murya, sannan ya ce.
“A ƙa'idar dokar asibiti, mutum guda ɗaya mai ƙarfi da lafiya ana ɗaukar Leda 1 tak (450ml - 500ml) a lokaci guda. Wannan shi ne adadin da jikin mutum zai iya jurewa ba tare da ya suma ko ya shiga haɗari ba. Amma mun karya doka mun ɗauki leda biyu a dare ɗaya a jikinka wanda ya haura leda 1,000ml - 1,500ml. Dan haka a yanzu bamu da damar sake ɗaukan wani jinin daga jikinka, sai dai kuma a yanayin binciken lafiyarka da muka duba kana da nauyin jini tun da gashi har jikinka ya bada 1,000ml na jini ba tare da ka raunana ba, sabida haka idan har zaka sanya hannu a high risk form ɗin to mukam zamu ɗeba.”
“Yes doctor, zan san ya hannu.”
Uncle Dee ya faɗa jikinsa na rawa, likitan ya sake kallon shi ya ce.
“Rayuwarka zata iya shiga haɗari fa?”
“Na amince.”
“Ina wakilinka?”
“Gashi.”
Ya faɗa yana nuna Moses, bada jimawa ba likitan ya sa aka kawo form ɗin Uncle Dee ya cike, zuciyarsa a ƙeƙashi babu alamun danasani ko niyar canja raayi, haka ya shiga za ayi musu blood transfusion.
Bayan sa’o’i saba’in da biyu.
A hankali Husna ta fara ƙoƙarin buɗe idonta, sakamakon sautin motsi da ta fara ji ya shiga kunnenta, bata san aina take ba, amma yanayin jikinta ya bata tana wani waje daban ba makarantar da ta kwanta bacci ba, jikinta akwai alamar gajiya sosai da sosai, ga wani irin ciwon kai da take ji duk da idonta na a rufe, abin da ya fara dawowa zuciyarta Uncle Dee, yana ina? Sai kuma ta yi tunanin ita ɗin tana ina ma, ko mutuwa ta yi ne ma? A hankali ta fara buɗe idonta da ya yi mata nauyi sosai da sosai, haske tarwai ya shiga idon, ta runtse shi da sauri.
Bayan kusan minti biyar ta sake ƙoƙarin buɗe idon, a wannan lokacin ta yi nasarar buɗe shi tarwai. Sai dai inda ta ganta ya sa zuciyarta bugawa da wani irin sauri, ta tabbatar asbiti ne, amma mai ya kawo ta nan, kwananta nawa anan? Juya jikinta ta fara ƙoƙarin yi sai dai ta ganta ɗaure da injinoni.
“Hasbunallahu wani’imal wakil.”
Ta furta murya can ƙasa, sai kuma ta mai da kallonta zuwa gefenta na hagu, wani mutumi ne kwance a irin gadon da take, a fili ta furta. ‘Waye shi? Me yake yi anan? Ko shima bai da lafiya? Ni meke damuna?’ Haka ta hau jerawa kanta tambayoyin da suka sa kanta ya ƙara fara sara mata, ba shiri ta fara ƙoƙarin dakatar da ƙwaƙwalwarta daga tunanin da take shirin shiga. Kamar daga sama ta ji an ce.
“Doctor kamar fa wannan tana motsi.”
Buɗe idonta ta sake yi, daidai lokacin da kyakywan farin likitan ya zuro kansa, idanunta suka faɗa cikin nasa, ya yi mata murmushi, sannan ya kalli nurse ɗin da suke tare.
“Alhamdulillah, ita kam ta tashi sauri shi.”
Likitan ya yi maganar da ta haifar mata da tunani, ita, saura shi? Waye shi? yaya Abdul? Yaya walid? Alhaji? Ko Ashir? Yaushe ne ma wai ta kwanta wannan jinyar? A hankali ta buɗe baki ta ce.
“Ku cire min ƙarfunan nan.”
Babu wanda ya tanka ta har ta fara mita a cikin ranta, sai kuma ta ji kamar ma ana sauketa a ƙasa, ba ta tantance ba sai da taga ana tura gadon daga ɗakin za a fita da ita waje, haka kawai taji zuciyarta na tsinkewa kamar tana nesa da wani abu mallakinta.
A haka aka dawo da ita ɗakin da mutane zasu iya ganinta, ko minti biyu likitan bai yi da fita ba su Mama suka shigo da su Ya Walid har da Abba da wasu cousins ɗin ta, har da Hajiya Bilki da Ya Leemah, duk suka shigo ana ta mata sannu, kowa fuskarsa da fara’a yana cikin farin ciki, sai da mazan suka tafi sallah ya rage Mama da Hajiya Bilki, Ya Leemah ta tafi da sauran ‘yan uwan da suka zo, Husna ta ce da Mama.
“Wai ya aka yi na zo nan? Daga school aka kawo ni?”
“Eyh Husna, daga makaranta aka kawo ki, mumu nan muka sameki da yayyunki sunƙi sanar da mu, a tunaninsu zasu iya kula da rashin lafiyar sai dai ba haka ba ne.”
“Yau kwana nawa kenan anan?”
“Kwanakin huɗu.”
Mama ta faɗa tana miƙa mata tea ɗin da ta haɗa mata, sai da Husna ta karɓa sannan ta ce.
“Daga makaranta ba wanda ya kawo ni, kuma na wanda ya nemeni?”
“A’a akwai malaminku mana, Iliya ne sunansa ko?”
Da sauri Husna ta ɗaga kai ta ce.
“Eyh, malamin maths ɗin mu ne, kuma shine malamin ajinmu, Uncle Dee.”
“To shi ne kam.”
“Yana ina yanzu?”
Husna ta sake tambayar Mama, sai da Mama ta gyara zamanta sannan ta ce.
“Ba ki ga wani a cikin ɗakin da aka fito da ke ba?”
“Na gan shi Mama, waye shi?”
“Shine malamin naku.”
Mama ta bata amsa jikinta a sanyaye, da tsananin tashin hankali Husna ta ce.
“Me ya same shi kuma?”
“Ya sanya rayuwarsa cikin haɗari ta hanyar baki jinin da ya wuce ƙa ida, a yanzu haka ya yi faduwar jini mai tsanani sakamakon ƙarancin jini a jikinsa hatta Kwalwalwarsa da zuciyarsa sun rasa sinadarin da ke fitar da iska, ya faɗa cikin doguwar suma.”
“Doguwar suma kuma Mama?”
Husna ta faɗa tana jin kanta na wani irin sarawa, a take ta fara jin wani azababben jiri yana ɗebanta, idanunta suka fara rufewa ta fara ganin zallan duhu, kafin ka ce kobo ta zube ƙasa sumammiya.
Akwai shafi na gaba a arewapen
https://www.arewapen.com/book?id=6a933361f3eaa6dc8f5ff715
Legendspen-Sayyid
08129553971
🔥🔥DA JININSA NAKE RAYUWA🔥🔥
*-Amanan-Janafty-*
(06)
“Husna! Husna!.”
Mama ta fara jera mata kira, Hajiya Bilki har sauri take ta idar da sallar da take yi, tana sallamewa ta ce.
“Kema mene na faɗa mata wannan maganar fisabillahi, kin san halin da za ta shiga.”
“Ina na sani Aminiya, ni banyi tunanin haka ba. Na ɗauka kawai malaminta ne, kuma za ta ji daɗi idan ta ji irin sadaukarwar da ya yi mata.”
“Ɗalibarsa kawai zai sanya rayuwarsa a haɗari sabida ita, to sonta yake ita ma son shi take, kina ji ta ce a makaranta babu wanda ya nemeta.”
Hajiya Bilki ta faɗa tare da ta shi ta fice kiran likita, ta fuskanci ita Mama ma kwata kwata ba ta yi tunanin wani kiran likita ba, tana fita ta ci karo da Yaya Abdul da Abba zasu shigo.
“Yawwa Abdul, dan Allah kira mana likitan nan, jikin ta ya dawo.”
A sukwane Abdul ya yi wajen ofis ɗin likitan, Abba kuma ya rufa mata baya suka koma, lokacin da suka shigo ko mumfashi ɗaya Husna ba ta fitarwa.
“Me ya sameta, ko kawai gani kika yi ta yi haka?”
Abba ya tambayi Mama, cikin murya kuka Mama ta ce.
“Daga ce mata malaminsu ya shiga
doguwar shine ta faɗi, kalli ko numfashi ba ta yi, Allah Ya sa itama ba doguwar suman ta yi ba.”
“Kina da jan jafa’i wallahi.”
Hajiya Bilki ta faɗa tana makawa Mama harara, dan ita taba ta haushi da ta yi wa Husna wannan maganar. Ita dai Mama ta dirarance har likita ya shigo, an sha matuƙar wahala kafin aka samu numfashinta ya sake daidaita har sai da aka canja mata ɗaki zuwa ɗakin hutu, amma ba wanda aka fito da ita da farko ba.
Abba ya yi wa Mama faɗa sosai da sosai, bayan ya gama Hajiya Bilki ma ta hau tata mitar, har sanda ta tafi gida.
Sai washe gari aka sake fito da Husna daga cikin ɗakin da aka shigar da ita, ba wai dan ta warke ba sai dan sun gaji da halinta, babu abin da take yi sai kuka, an ce mata zai iya shafar lafiyarta ta ce ya shafa ɗin,