Chapter 4 of 26
DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty
“Har yanzu fushin ne?”
Girgiza kai ta yi ba ta ce komai ba, ya sake cewa.
“Ba zaki yi min magana ba ne?”
“Ni ba fushi nake ba.”
“To me ya sa kika daina yi min magana?”
Shiru ta yi sabida abin da ya faɗa, wai ta daina yi masa magana, to daman magana take masa? Ko me yake nufi.
“Ina so mu yi magana da ke, amma ina ga zan bari sai kun shiga next class lokacin kun zo final kuma kun ƙara girma.”
Da sauri ta girgiza kai, sannan ta ce.
“A’a ka faɗa min, yanzu ma na girma.”
Sai da suka tsaya jikin bishiya sannan ya ce.
“Ranar nan kin ce ina son Aisha Sharif ko? Me ya sa kika ce ina sonta? Me ya sa sai ita kika yi tunanin ita nake so ba ke ba?”
Legendspen
08129553971
🔥🔥*DA JININSA NAKE RAYUWA* 🔥🔥
-Amanan-Janafty-
(04)
https://chat.whatsapp.com/DyVX8bRFbq66I04yzM5rLp?s=cl&p=a&mlu=0&ilr=4
Ji ta yi ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ba ta taɓa tunanin idan ya yi mata maganar soyayya za ta ji haka ba.
“Husna, ke ce mace ta farko da na fara jinta a jinin jikina a ranar da na fara ganinta, sai dai wasu dalilai suka sa na nesanta kaina da ke, na farko ke ɗaliba ce a makaranta kike, dokar makaranta ta haramtawa malami nuna wani abu da ya dangancin soyayya tsakaninsa da ɗalibarsa, kuma ko ba haka ba, ba girma na ba ne yin haka, sannan kuma akwai wani dalili mai girma da zai iya tarwatsa mu’amlata da ke dan haka naga ya kamata na nesanta kaina da kasancewa kusa da ke, sai dai zuciyata ta gagara yin hakan kwata kwata, har yanzu da nake tsaye gabanki yin zuciyata ne ba yin kaina ba.”
Husna ta yi matuƙar jindaɗin kalamansa, ashe wai shi ma yana sonta amma ya dinga ja mata rai yana nuna bai ma san da ita a duniya ba, koda yake ance abu mai daraja yana da wuyar samu.
“Husna.”
Ya kira sunanta, ta ɗaga kai ta kalleshi ya yi gaba nesa da ita, sai ya zama hasken rana ya rage mata ganin fuskarsa sosai, cikin sanyin murya amma yanda zata ji shi ya ce.
“Na san kina gani kamar na yi baya daga gare ki ne saboda ban damu da ke ba, ko saboda ina son ganin wata daban. Ba haka ba ne, kece ka ɗai macen da nake so da sha’awar gani, kowane tsuntsu yakan so ya tashi a sararin samaniya inda yake da 'yanci, amma idan ya hango hadari a sararin, yakan ja da baya domin kariya.
Ke yarinya ce mai daraja, mai kyau da ilimi, murmushinki ka ɗai abun tsayawa a kallane, bare kuma rigimarki. Amma ni na san waye ni, kuma na san duniya da ƙa'idojinta. Akwai tsakankanin da ke tsakaninmu wanda ya fi ƙarfin tsawon bishiyar nan da muke tsaye a ƙarkashinta. Ina tsoron kada soyayyata ta zama sanadin da za a kalle ki da wani kallo na daban, ina tsoron soyayya ta zame miki matsalal da zaki sha wahala. Ina tsoron kada na ba ki zuciyata, sannan a tsakiyar tafiya al'ada da addini su sa mu miƙa wuya, mu bar zuciyoyinmu a tarwatse.
Ban koya miki darasin lissafi domin ki kasa yin lissafin makomarki ba. Idan har kina jina a cikin jinin jikinki kamar yadda nake jin ki a nawa, to ki yi min alƙawari guda ɗaya.
Ki kula da kanki, ki zama mai ƙarfin gwiwa, kuma kar ki taɓa yarda wani abu ya ruguza farin cikinki... koda kuwa ni ne zan zama sanadin. Ni dai na san zuciyata ta riga ta zaɓeki, amma lissafin ƙaddara ba a hannunmu yake ba."
Yana kaiwa nan ya juya da baya ya ci gaba da tafiya, tafiyar da bai waigo ba har ya ɓacewa ganinta, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi kamar an watsa mata ruwan sanyi, ta rasa gane inda zancen nasa ya nufa, wai addini da al’ada. Aina addini da al’ada zasusa su miƙa wuya har su bar zuciyoyinsu a tarwatse, ya ce bai koya mata darasin lissafi domin takasa lissafa rayuwarta ba, me yake nufi? Ya yi mata magana a cakuɗe ta inda ba za ta iya tsintar komai daga ciki, haka ta koma cikin hostel jikinta a sanyaye gaba ɗaya a sanyaye, ko da ta bawa Said Kibiya labari suma basu iya tsintar komai a cikin maganar ba, amma sun bari daga baya zasu tattauna a kai, ko ita Husna ta tambayeshi abin da yake nufi da abin da ya faɗa, haka suka ci gaba da al’amuransu a yinin ranar har ita dai Husna da ta ta zauna babu abin da ke yawo a kanta sai kalaman da ya faɗa mata, mussaman kalmar da ya ce Ki kula da kanki, ki zama mai ƙarfin gwiwa, kuma kar ki taɓa yarda wani abu ya ruguza farin cikinki... koda kuwa ni ne zan zama sanadin.
Ni dai na san zuciyata ta riga ta zaɓeki, amma lissafin ƙaddara ba a hannunmu yake ba. Sai ta yi ta tambayar kanta wacce irin ƙaddara, ya ce wai addini da al’ada gaba ɗaya ta rasa gane kanta a wannan ranar, gashi daman tun safe ta ta tashi jikinta babu ƙwari, har sun shirya zasu clinic na makaranta kuma ta ce ta fasa, ga waɗannan kalaman da suka saukar mata da kasala, su jefa ƙwaƙwalwarta cikin duhun tunani, duk yanda ta so ta yakice wannan tunanin abu ya gagara gaba ɗaya, har dare lokacin da suka zo kwanciya, su Said Kibiya ne suka lallaɓata ta kwanta, sai da tana kwanciyar ta soma jin wani irin zazzaɓi yana shirin rufe ta, wani irin sanyi ya dabaibaye rayuwarta ta fara rawar ɗari, a take kuma kanta ya fara wani irin sarawa kamar ana sara shi da gatari, tana daga kwance amma jiri yana ɗibanta.
Ba iya S Kabiya da Ali Kaita ba, duk waɗanda ke cikin Hostel ɗin hankalinsu ya tashi da yanayin da Husna ta shiga, mussaman gurnanin da take yi wanda shi ya jawo hankalin kowa kanta, gaba ɗaya suka zagaye ta ana faman yi mata sannu, amma ba tasan inda kanta yake ba.
Tun suna ganin abun kamar wasa har ya girma ya huce dukkan tunaninsu, ba shiri suka garzaya da ita Sickbay, domin sun tsorata da abin da yake shirin faruwa, wata cikin student ɗin ta danna ƙararawar da ke isar da Quaters ɗin malami sanarwa ana buƙatar su cikin makaranta, lokacin da malaman suka iso Sickbay ɗin ya cika ya batse da dandazon ɗalibai, Said Kibiya da Ali Kaita kuka kawai suke fuskarsu ta yi jage jage da hawaye, wasu daga cikin ɗaliban suna ta faman rarrashinsu.
Yana ganin Said Kibiya da Ali Kaita na kuka kuma babu Husna ya ji zuciyarsa ta bada wani iriin bugu mai zafi, ya san ba mutuwa ta yi ba tun da yana jin motsinta a cikin a zuciyarsa, sai ya san tana cikin wani hali, kuma ya yi imanin wannan abun shi ya hana shi tafiya gida weekend.
Shiga ɗakin suka yi suka tarar da ƙaramar nurse a kanta, kasancewar weekend ne babu manyan, ana barin guda ɗaya daman sabida emergency, yana shiga ya tarar da nurse ɗin tana duba hannun Husna da ya yi fari fat.
“Doctor how is she?”
“Sir jikinta ya yi rauni sosai, numfashinta da bugun zuciyarta suna tsananin sauri, ga kuma Bp ɗinta ya yi low sosai da sosai, gashinan har fuskarta ta canja launi saboda ƙarancin jini.
Kayan aikinmu na nan ba za su iya auna taƙamaiman abin da yake faruwa ba, ina tunanin kawai a kai ga Federal Hospital na cikin gari ƙarƙashin kulawar makaranta."
"Jikin nata ya yi tsauri har haka kenan?"
Ya faɗa jikinsa a sanyaye, nurse ɗin ta gyaɗa kafin ta ce.
"Sosai sir, akwai buƙatar a sanar da iyayenta dan ana buƙatar wani nata, tun da yanzu ba wani dare ba ne, anan cikin kano take kuma AKTH za a miƙata."
Jikinsa ya yi sanyi ƙalau, ya rasa abin da zai yi, nurse ɗin ta shiga rubuta letter da zasu kai asibitin, bayan ta gama ta miƙa masa tana faɗin.
"Ga shi Sir, bari na sanar da school driver ya fito da Ambulans."
Karɓa ya yi, sannan ya ce.
"Bari na sanar da shi, sannan kuma gida kuma ba sai an sanar dasu ba, sabida kar a ɗaga musu hankali, zan iya duk wani abu da gidan zasu yi.”
“No sir ya kamata a sanar da su, yanayin jikinta dole sai wani yazo daga gida, nasan ba su da wani nisa da asibitin."
“Okay, zaku iya kiransu.”
Ya faɗa yana ficewa, itama nurse ɗin fita ta yi zuwa ofis ɗin da ake kula da duk wani information na Student, da yake ta san Husna da ƙawayenta, kuma a yanzu ta duba number tag ɗin Husna 418, ma'ana ita ce ɗaliba ta 418 a kaf Federal Government Girls College, Munjibir (FGGC Munjibir), tana dubawa taga lambar wayar farko.
Ta ɗauka lambar ma ta mahaifinta ce, shi ya sa ta kira, a can gida kuwa Yaya Abdul ya dawo kenan daga zance yana ƙoƙarin shigar da mashin ɗinsa wayarsa ta soma rigining, Alhaji da ya dawo daga makatantar dare ya ce.
“Yaya, ita antin nan tamu ba za ta barka ka shiga gida ba ne, ko ta manta daga wajenta kake?”
Murmushi Yaya Abdul ya yi, ya sa hannu ya zaro wayar, sai dai ganin lambar ba suna ya ce.
“To ka kwantar da hankalinka ba ita ba ce.”
Matsawa kusa da shi Alhaji ya yi, yana karɓar mashin ɗin zai shiga da shi ciki, shi kuma Yaya Abdul ya ɗaga wayar tare da yin sallama. Daga can ɓarin Nurse Hauwa ta amsa sannan ta ce.
“Ina magana da mahaifin Husna ne?”
Sai da gaban Yaya Abdul ya yi wani mugun bugu, murya a hankali ya ce.
“Eyh nine, babanta ne kuma yayanta.”
Duk da ya yi maganar ƙasa ƙasa sabida kar Alhaji yaji, amma hakan bai hana shi ji ba, cak ya tsayar da mashin ɗin yana sauraron abin da za a sake cewa.
“Yawwa toh thank god, Husna ba ta da lafiya sosai da sosai, yanzu haka sun shiga motar school zasu zo nan asibitin Aminu Kano Teaching Hospital (AKTH), so idan ba damuwa ku kasance cikin shiri, school Ambulans ne nan da minti 30 zata iya zuwa.”
“Innullahi wa’inna illahir raji’un, Allahuma ajirni fi musibati…”
Alhaji ya yi saurin cefashi da cewa.
“Wa’aklif ni khairin minha? Me ya samu Husnan dan Allah?”
Ya ƙarashe kamar zai yi kuka, da ƙyar Yaya Abdul ya ce.
“Ba ta da lafiya ne, wai yanzu ma sun taho da ita daga makarantar zasu zo asibitin malam, ƙarƙashin kulawar makarantar."
Hawaye Alhaji ya ji yana bin fuskarsa, kamar wanda aka sanar masa da mutuwa, Yaya Abdul ya ce.
"Yanzu zan shiga gida, zan ce da Mama za muje unguwa, idan dare ya yi su kulle kar ka bari su ji wannan maganar.”
“Tom Yaya, bara na juya mashin ɗin kafin ka fito.”
Alhaji ya faɗa, idanunsa duk sun yi jazir, hawaye na zubowa.
Da sauri Yaya Abdul ya shiga gida, a lokacin Mama har ta kwanta, sai Abba da Walid suna ɗaki suna ɗaukan karatu sai kuma Ashir da ke na shi karatun daban.
“Walid.”
Yaya Abdul ya faɗa daga bakin ƙofar, dan bazai iya shiga ciki ba, ba ya so ma yaga fuskar Abba, Walid ya tsayar da karatun ya ce.
“Lafiya ba zaka shigo ba?”
Abba ma ya ce.
“Babban mutum lafiya?”
“Lafiya ƙalau Abba, saƙo zan ba shi.”
Walid bai jira amsar Abba ba ya miƙe, dan yanda ya ji muryar Yaya Abdul ya san da damuwa a muryarsa, haka Allah Ya hallice su kowa ya san damuwar kowa, ba sa taɓa iya ɓoyewa junansu damuwa, ko da bai faɗa ba, su suna ɗauka a cikin maganarsa da mu’amala sa.
“Me ya faru?”
Walid ya faɗa ƙasa ƙasa yanda Abba ba zai ji ba, shima Yaya Abdul ƙasa ƙasa ya ce.
“Za muje unguwa da Alhaji, idan bamu dawo ba ku kulle gidan?”
“Mu kulle gidan kuma? Ina zaku? Me yake damunka?”
“Babu komai fa, mura nake.”
“Yaya wallahi ba mura kake ba, ina zaka? Bari nazo muje tare.”
“Idan kazo wa zamu bari a gidan, zan yi ma text ɗin inda mu kaje.”
Yana faɗin haka ya fice, a can makaranta kam lokacin da aka fita da Husna a Ambulans sai da sauran Students suka riƙe Said Kibiya da Ali Kaita, sabida kuka suke suna bin motar sai an tafi da su, daga nan kuma Ali Kaita ta zube a ƙasa sai aljanu, nan sauran ɗalibai suka hau zubewa aka bar ragowar malamai da faman kwashe su da yi musu karatu.
09:47pm suka iso asibitin Aminu Kano Teaching Hospital (AKTH), Yaya Abdul da Alhaji suna ganin motar suka bi bayanta zuwa emergency unit (A&E) na cikin asibitin, motar na tsayawa suka yo kanta sai dai kuma ma'aikatan gaggawa suka fito da gadon tura marasa lafiya zuwa bakin motar.
Uncle Dee a lokacin idanunsa sunyi jazir sabida yanda zuciyarsa ta yi rauni, suna tafe mota yana kallonta, ji yake kamar ya bawa idanunsa damar zubar da hawayen kukan da zuciyarsa ke yi, Allah ne ya kawo sa asibitin lafiya amma numfashinsa gaba ɗaya ya sarƙafe, duk da yanayin da yake ciki bai gaza ganin zalla kammanin Husna a tare da Alhaji da Yaya Abdul da ke tsaye suna kallon motar, idanun Walid sun kaɗa sun yi jazir kamar gauta, na Yaya Abdul kuma sun rene sun fara zama yellow alamun shi yafi Walid dakiya da taurin zuciya.
Lokacin da aka fara tura Husna zuwa Triage Room dan bata taimakon gaggawa dukkansu suka rufawa likitocin baya, sai dai lokacin da aka shiga da ita Ressuscitation Room, ɗakin da ake ba da agajin gaggawa na ceto rayuwa aka umarce su da su tsaya, ba dan sun so ba suka tsaya kowa ya jingina da bango, daidai lokacin kuma wayar Yaya Abdul ta fara ƙara, yana zarowa ya san Walid ne ya miƙawa Alhaji tare da faɗin.
“Ka ce masa komai ma, ni ban san me zan ce masa ba.”
Karɓar wayar ya yi, shima ɗin bai san abin da zai ce ba amma ya san ko hauka yake ba zai iya sanar da iyayensa suna asibiti Husna ce a kwance ba, sai da ya saita nutsuwarsa na ɗan lokaci sannan ya ɗaga tare da faɗin.
“Yaya gamu nan, idan bacci zaku yi ku kulle gidan.”
Daga can ɓarin Walid ya yi magana rai a ɓace.
“Bangane mu kulle gidan ba gaku nan zuwa, kuna ina? Gaba ɗaya kun ɗagawa wa mutane hankali.”
Alhaji yana shirin yin magana wata nurse ta fito, a yanayin da ta fito kana kallonta zaka ga zallan tashin hankali a tare da ita.
“Ana neman mahafin yarinyar nan.”
“Wace yarinya, kuna ina wai?”
Walid ya faɗa, sabida yanda maganar ta shiga kunnensa kamar yana wajen aka yi maganar.
“Yaya muna asibiti, Husna ce aka dawo da ita daga makaranta, mun so mu ɓoye muku kuma likitocin sun ce ana buƙatar iyayenta.”
“Wane asibiti ne?”
“AKTH, muna Triage Room.”
“Gamu nan.”
Walid ya faɗa tare da katse wayar, Abba da ya sa shi a gaba ya kira su ya ce.
“Mene ya faru?”
“Abba wai Husna ce ba lafiya, an dawo da ita daga makaranta yanzu ma suna Asibitin Malam, kuma a yanzu ma muna wayar na ji ana cewa ana buƙatar iyayenta.”
“Hasbunallahu wani’imal wakil.”
Abba ya faɗa, daidai lokacin Mama ta fito daga ɗaki sabida taji duk abin da suka faɗa a kiɗime ta ce.
“Husna ce ba lafiya?”
“Eyh ita ce.”
Abba ya faɗa yana shiga ɗaki, bayan ‘yan mintuna ya fito.
“Walid shege muje, ke ki zauna anan za muje mu ga abin da ke faruwa."
“A’a dan Allah, ba zan iya ba wallahi bari na ɗauki Ashir muje tare kawai.”
Yanayin da ta yi maganar ya bayyana duk wani hali da zuciyarta ke ciki, nutsuwa ta yi nesa da ita.
Walid ne ya shiga ɗaki ya ɗauko Ashir da ke kwance ya ɗaura shi a kafaɗarsa suka fito daga gidan, a cikin motar ma Walid ne ya tuƙa su har zuwa asibitin. Lokacin da suka shiga cikin asibitin suka tarar da Alhaji zaune zaman dirshan ya haɗa kai da gwiwa yana rusa kuka wiwi, shi kuma Yaya Abdul yana zaune kan kujerun asibitin shi ya zabga tagumi, Uncle Dee ma yana tsaye daga gefen Alhaji idanunsa a lumshe da alama ya runtse su ne ko zai sami nutsuwa.
Walid ne a gaba su Mama da Abba a bayansa, Ashir ma ya farka yaga sun a asibiti amma baisan waje wa suka zo ba, Alhaji ne ya fara ganinsu yana kukan ya tawo idan suke, kukansa duk ya ɗaga hankalinsu duk da sun san Alhaji ya saba kuka idan Husna ba ta da lafiya, amma wannan ya tsorata su sosai.
“Abba, sun ce wai ba zasu faɗa mana komai ba, dole sai mahaifinta yazo, mun ce musu zamu iya yin komai amma sunƙi yarda.”
Alhaji ya faɗa yana kuka, maganarsa ta sa Uncle Dee buɗe idonsa ya sauke su a kan Abba, mutumin da ya yi masa wani irin kwarjini mai ban tsoro, duk kammamin Husna da yake gani a tare da ‘yan uwanta, sai ya ga ashe ba komai ba ne idan ka haɗa ta da Abba, wanda suke kamar an tsaga kara, haka Ashir ma sak kammaninsu. Yaya Abdul ne ya ce.
“Abba, yana wancan ofis ɗin dan Allah muje.”
Ya yi maganar yana ƙoƙarin riƙe hannun Abba ya kai shi, alamun duk ya fita a hayyacinsa, Abban ma miƙa mai hannun ya yi sabida gaba ɗaya jikinsa ya saki a yanayin da ya ga ‘ya’yan nasa.
Abba yana gaba suka rufa masa baya duka cikin ofis ɗin har da Uncle Dee, wanda banda yaya Abdul da Walid da ya gabatar musu da kansa a matsayin malamin su da ya kawo ta daga makaranta, babu wanda ya san waye shi, kuma babu nutsuwar da zasu fahimci ma da shi.
Likitan yana zaune ya gansu sun shigo ɗuuu a tare, suna neman cika mai ofis.
“Wasu su jira a waje mana.”
Ya faɗa ba tare da ya amsa sallamar da suka yi masa ba, ganin kowa yaƙi motsi ya sa shi cewa.
“Abin da zan faɗa muku bai da daɗin ji, dan Allah ku bar mahaifinta kawai, kai kuma ba malaminta ba ne? Zaka iya komawa yanzu mana.”
Likitan ya ƙarashe maganar yana nuna Ilya, sai a lokacin Abba da Mama da Walid ma suka kula da shi, Abba ya yi magana cike da dattaku.
“Idan zai yu