Chapter 2 of 26

DA JININSA NAKE RAYUWA Ƙauna Mai Zafi By Amanar Janafty

ya ce tana ina ta miƙe, tasan ƙarfine da shi kamar shari’a, a kan ta ya yi faɗa da Yaya Walid da yake yayansa kuma Yaya Walid ɗin aka zane, ko a waje ma da haka ake faɗa da shi a kan kowa na gidan, itama idan suna faɗansu na sakwanni haka yake jibgarta sai ya gama yazo yana bata haƙuri, sabida ita ɗin ce idan ta so rigimarta duk haƙurinka sai ka biye mata. Miƙewa ta yi ta sauka daga kan gadon ta tsaya a bakin ƙofa cikin shirin ko ta kwana, idan takama ma su yi doki doka da shi, tun da duk sun rufe ido sun ce son zuciyarsu suke so, itama zata rufe ido ta yi yaƙi da kowa a kan son na ta zuciyar.



Ya kuka ji salon wannan labarin? Ina fatan zaku bini sannu a hankali na feɗe muku biri har wutsiya.



Legendspen
08129553971
🔥🔥*DA JININSA NAKE RAYUWA*🔥🔥

-Amanan-Janafty-


(02)


“Husna!”

Alhaji ya ƙwala mata kira tun kafin ya ƙarasa shiga cikin ɗakin, yana ɗaga labule ya yi ido biyu da ita a tsaye, cikin fushi ya ce.

“Wai me yake damunki ne haka? Mahaukaciya kika zama ko me? Bakisan iyayenki ba ne, bakisan darajarsu ba?”


Kallonsa kawai take yi yanda yake magana har jijiyoyin wuyansa suna motsawa, ga jijiyoyin kansa sun fito raɗau da su, alamar ya kai ƙololuwar ɓacin rai, ta sani yan sonta, ita ma kuma tana son sa kuma duk cikin ‘yan uwanta yafi kowa fahimtar ta, amma ta rasa gane me ya sa a kan wannan lamarin ya turje, muryarta a raunane ta ce.


“Idan kowa yaƙi fahimtar halin da nake ciki har da kai? Idan kowa ya gaza gane halin da zuciyata ke ciki har da kai? Na buɗe ido ban san komai ba sai soyyaya, na sami soyayya na sami aminci, na ta shi inda komai na yi so ake, yaba min ake, amma lokaci ɗaya na tsinci kaina inda ko na yi ko ban yi ba uwarsu ɗaya, inda babu wanda ke kula da abin da nake bare a yaba min, sai shi kaɗai, ya sadaukar da komai domin na rayu, ya sha wahalal da har na miƙe yana kwance, ya za ayi na ƙi shi? Ya zaayi na guje shi, tabbas a kan sa a shirye nake da na rasa kowa da komai.”


Duk da maganganunta sun so su taɓa shi ta wani ɓarin, amma bai ga dalilin ja da addini ba, sam sam ma shi bai gan shi ba.


“Soyayya da sadaukarwa har ma da hallacin da kike magana a kai har ya kai girman addinin ubangiji, har ya kai ki yi watsi da faɗar Allah? Me ya shiga kan ki ne Husna?”


“Soyayya, ni a yanzu duk wanda bai zai goyi bayana ba to ya bar ni, daman ai duk ba sona kuke ba tun asali, shi ya sa har kuka kasa gane abin da kuke so? Shi ka ɗai yake sona.”

Wani irin zafi ne ya ziyarci zuciyar Alhaji, sai ya ji ma kamar an daɓa masa wuƙa a zuciyarsa ne, wai ƙanwarsu Husna ita ke haɗa soyayyarsu da wani, wanin da ta sani ƙasa da shekara shida, yaushe ne ma suka fara soyayyar da shi?

“Husna.”

Ya kira sunanta da babbar murya, ya ce.

“Tun da har kin gamsu da soyayyarsa kije,Allah Ya baki sa’a sai dai ki sani ba anan ba, ba a gidannan ba. Idan har kina so sai dai ki bi shi ku tafi can ku yi duk abin da zaku yi, kuma zan roƙi Allah Ya ɗauki raina kafin wannan ɓaƙar ranar.”


Yana faɗin haka ya fice, Husna ta zube a kan gado ta fashe da wani irin kuka mai zafi, domin tabbas maganar Alhaji ta doketa, ta shiga zuciyarta. Ina za ta iya rayuwa babu ‘yan uwanta, abun da ciwo waɗanda suka fi kowa ƙaunar suka kware ma baya, su dage a kan sai ka rabu da abin da zuciyarka ke ƙauna, ta ina za ta fara wannan?


*Asalin labari*.


Alhaji Abubakar Sheshe haifaffan Unguwar Sheshe ne da ke cikin garin kano, gidansu babban gidan malamai ne a cikin gari, mahaifinsa malam Isma’il babban malamin zaurene da ke ba da ilimi, yana da tarin almajirai sai dai shi ba irin mai ɗauko yara daga ƙauyunka ba ne, ko iyaye su kawo su ajiye masa, mafi tarin almajiransa ‘yan uwana sai kuma waɗanda suke daga asalin garin su Ƙiru.
‘Ya’ya tara Allah Ya bashi daga wajen matansa biyu, sai kuma almajiransa da suka taru suka raya gidan.

A cikin ‘ya’yansa maza biyar kowanne cikinsu mahaddacine har da waɗanda ma suka rubuta Al Qur’ani ma, ciki har da Abubakar, kasancewar lokacin ilimi boko bai wadatu ba, ‘ya’yansa maza ne kaɗai suka taɓa suma iya matakin primary, sai kuma na ƙarshe ƙarshen da suka ka kai har secondary. Abubakar shine na huɗu cikin gidan baki ɗaya, dan haka baya cikin waɗanda suka kai matakain secondary.
‘Ya’yansa mata kam duk basu sami wannan damar ba, dan tun suna shekara tara ake aurar da su ga almajiransa da suka nema. Haka mazan ma duk daga gidan malamai suke auro na su matan, kamar Abubakar da Amina wadda take daga gidan babban malami, Malam Isa ƙofar mata, sai dai ita jika ce kuma sun sami damar yin karatu dan har ta kammla junior secondary suka yi aure, ba auren haɗi ba ne, Abba da kan sa ya ganta ya ji ta yi masa, ya yi magana a ka ba shi izinin ganinta ita ma ta ji ya yi mata. Hajiya Bilki kuma ‘yan uwan juna suke da Mama dukkaninsu jikokin gidam Malam isa ƙofar mata ne, tun tasowar suke aminta ta amana, soyayyar ‘yan uwantaka na ratsa jininsu har suka yi aure, Hajiya Bilkisu ta auri babban ɗan kasuwa Alhaji Musa Ɗankaka, ita kuma Mama ta auri Abba. Kowacce zaman lafiya take yi tsakaninta da mijinta, Hajiya Bilki tana da kishiya guda ɗaya da suke kira Hajiya Babba sai kuma bayan aurenta da shekara biyar aka yi mata amarya Hajiya Kubrah. Abba ya mayar da Mama makaranta ta ƙarasa secondary ɗinta sai bayan ta kammala ne ta sami haihuwar fari, a lokacin kam Hajiya Bilki har ta yi haihuwa ta uku ma, dan dama ta riga Mama Aure.
Abba ya kasance ɗan kasuwa da ke juya na shi kuɗin, yana da arizƙi daidai gwargwado da rufin asiri, ya tsayawa iyalinsa a kan duk wata biyan buƙatar rayuwa dan har NCE Mama ta yi. ‘Ya’ya biyar Allah Ya ba su.
Abdulƙadir shine babba, wanda ya ci sunana mahaifin Mama, an haife shi kwanaki kaɗan bayan rasuwar mahaifin Mama, shine Abba ya mayar da sunansa ana kiran sa da Yaya Abdul, a yanzu yana matakin ƙarshe a jami’a inda yake karantar ɓangaren kasuwanci, sai kuma mai biye ma sa Isma’il da ya samu sunan mahaifin Abba, ana kiran sa da Yaya Walid, shi kuma yana matakin aji uku a jami’a shima yana karantar ɓangaren kasuwanci ne, wattani kaɗan da suka huce Abba ya buɗe musu shago a cikin kasuwa inda suke siyar da atmfofi, laceses da shaddoji, babban shago ne a cikin kasuwar kwari da aka kashe maƙuden kuɗaɗe a cikinsa, yanayi ƙwazon su a kan kasuwanci ya sa Abba ya buɗe musu na su shagon, kuma a yanda kasuwancin na su ya fara kwalliya zata biya kuɗin sabulu. Sai kuma Muhammad Kabir da kusan kowa yake kiransa da mai babban suna, amma ainahin sunan sa na sakaye shine Alhaji, sunan Aminin mahaifin Abba ne, wanda a wajensa su Abba suka sami ilimin farko, shi kuma yanzu ya shiga jami’a amma ɓangaren Science yake dan ko kasuwa idan aka ce ya bi su Yaya Abdul tun suna zuwa shagon Abba sai ya ce shi a’a, sai kuma Asma’u da ake kira da Husna, wadda ita dai bata san inda ta samu wannan sunan ba, tun da dai ba sunan mahafiyar Abba ko Mama ba ne, haka a ‘yan uwa na kusa da ta sani bata san mai wannan sunan ba, idan ma akwai to ba ta ci ayi mata takwara da ita ba, sabida tsiran shekarun su ba ma su yawa ba ne, bayan Husna kuma sai autan su Muhammad Ashir, shi ɗin ma babu wanda zai ce ga sunan da ya ci, dan basu da wani Ashir a cikin ‘yan uwa, ana kiransa da Ashir, amma kuma Abba yana kiransa da Ashiru na goma, sai ya yi dariya daga baya aka ji wai wai ɗin sunan Aminin Abba ne amma zancen ba shi da tabbas dan daga bakin Alhaji aka ji.


Cikin gidan kowa da sanyin halinsa, ba barin Yaya Abdul, yafi kowa sanyin hali ba shi da wata damuwa ko faɗa ba ya yi, sai dai yana sakewa ya yi hira sosai a cikin ‘yan uwansa, Yaya Walid ɗin ma haka take, amma shi yana da ɗan fushi saɓanin Abdul da ko kaɗan bashi da fushi. Alhaji ne ma yake da ɗan faɗa domin yana da ƙarfi sosai.

Sai dai kuma duk wani zafi, taurin kai, tsiwa, surutu da rigima aka haɗe aka zubawa Husna. Sai kuma aka bawa Ashiru surutun dan itama Husna ba ta cika surutu ba. Mazan gidan guda uku dukkan su sai bayan sun yi haddar Al Qur’ani suke tafiya makarantar secondary, daga nan kuma sai su kuma ɗaukar karatun dare wajen Abba wanda yake yi musu kullum tare da wasu matasan unguwa, kowa ana yi masa ƙarin Al Qur’ani daban, daga nan kuma sai ayi musu ƙarin sauran litttafai irinsu Hadisai daban daban, Akdhari, sira da wasu ƙarin littaffan na Addini, Abba da Mama ‘yan ɗarikar Tijjaniyya ne, amma kuma ba irin wannan zazzafar da ake yi ta zamani ba, duk wata bidi’a babu su a ciki suna yin komai na su bisa tsarin addini Allah da manzon sa, ko hoton Shehu babu a cikin gidansu ko a jikin abun hawan su, sannan kuma Abba yana mu’amala da ‘yan sunnah mu’amala mai girma da muttuntaka.
Tsakanin Mama da ‘yan uwan Abba lafiya lau ne, dan ko irin abun nan da ake cewa dangin miji ita dai ba ta fuskanta, sai dai kuma bata sani ha ko dan mijin nata yana da rufin asiri ne? Dan ko ‘ya’yanta suna da alaƙa mai girma tsakaninsu da ‘yan uwansu. Idan aka zo tsakanin Husna da ‘yan uwanta na gida, to ba ita ba, duk wani mutumi da ya yi zama da su ko na awa guda ne zai iya bada shaidar cewa Husna ita ce farin 1888iki da sanyin idanun kowa a cikin gidan nan, idan akwai abin da yafi soyayya nuna ƙauna, to tabbas shi Husna ke samu daga wajen ‘yan gidansu, Mama ce kawai ke ɗan sassauta soyayyarta amma har Abba babu ruwansa, kar azo ga Yaya Abdul da Yaya Walid, ko tarin Husna ba sa son ji, Alhaji ne ka ɗai suke hawa sama su faɗo da shi, kuma shi ka ɗai take yi wa rashin kunya, sabida ya kasancewar su sakwanni a wajen haihuwa duk da ta zarar su ta kai shekara uku, shine ka ɗai Husna bata ganin soyayyarsa sai a lokacin da bata da lafiya, Har gwanda ita tana iya jurewa amma shi kam har kuka yake, haka Husna ma tana son ‘yan uwanta so mai ratsa jinin jiki da jijiya, ita kaɗai a zaune take jin soyayyarsu na tuƙuƙi a zuciyarta, ba zata iya misalta son da take musu ba, kamar yanda suma baza su iya misalta na ta son ba, amma Husna ta yar da a zuciyarta tafi son Alhaji a kan kowa, hatta yanda take jin Alhaji wani lokacin sai ta ji kamar tafi son Alhaj a kan Mama, ta san ba za ta iya cewa ga adadin son Alhaji a ranta ba, amma tabbas ta san tafi son sa sama da kowa ma a rayuwata, duk da ko yaushe cikin faɗa suke, dan ita Husna ma bata iya jure su yi zaman lafiya da shi.


Lokacin da ta zo shiga matakin secondary gaba ɗaya a hadda ba ta huce izifi talatin ba, ta gama Isra’i ta gaza shiga Khafi, sai ta kwashe sama da wata uku tana sake bitar surah kafin ta shiga ta gaba, duk ‘yan gidan sun fita kwashewa a harkar karatu, a yanzu ma har Ashir da ke shekara goma ya daɗe da huce Maryam ma, ya barta baki sake, ba wai kuma dan bata da ƙoƙari ba, sai san hallitar ƙwaƙwalwa da Allah Ya yi mata na Slow learner.

Mutane da ‘yan uwan da ba iya musu sun ce wai gatan da ta samu ne ya hana ta mai da hankali a kan karatu, wasu kuma su ce ta sa rigima a a ranta, ita kuma ta gaza gane a wane matsayi take a harkar karatu. Sai dai Alhaji ya fahimci matsayin da ƙwalƙwalwarta take, shi kaɗai ya fahimta, idan aka zo zancen karatu kowa rufe ido yake ya yi ta yi mata faɗa, akwai ranar da Mama ce mata.

‘Kina nan zaune Ashir ne zai zo yanayi min ƙarin karatu.’

Abun ya taɓa ran Husna sosai da sosai. Alhaji ne kaɗai ya fahimci a hankali take ɗaukan abubuwa, ƙwaƙwalwarta ba ta son a haɗa ma ta zafi, yanzu zata rikice wanda ta ɗauka ma a baya ya gudu.


Ana wannan ƙadamin tazo shiga makarantar sakandiri, inda Mama ta nuna sha’awarta a kan a kai Husna makarantar kwana a lokacin tana da shekara goma sha biyu. Haka ta tsayar da Hadda a wannan lokacin ta tafi makaranta da alƙwarin Abba duk hutu idan ta dawo sai ta kawo masa haddarta ta baya, kafin ta tafi sai adinga yi mata ƙari. A lokacin ne Mama ta shirya Husna suka je gidan aminiyarta Hajiya Bilki.


Gidan Hajiya Bilki wani irin gida ne, na kissa da makirci, ba zaki taɓa zuwa gidan nan kiga sun faɗa a tsakaninsu ba, ko ɗaya na magana da ɗaya cikin fushi, komai cikin izzah, isa, da gadara suke yin sa, kowacce na taƙama da alfahari, Hajiya Babba na taƙamar da ita aka yi arziƙi, Hajiya Kubran na taƙamar daga gidan manyan masu kuɗi ta fito, Hajiya Bilki ce dai ba ta biye musu, shi ya sa kullum cikin cutar da ita suke, sai dai ta inda Allah Ya taimake ta ‘ya’yanta sunfi na kowa nutsuwa cikin gidan, Hajiya Babba ‘ya’yanta manya maza uku ne ajere ta haifesu, sai dai dukkansu a lalace suke, daga mai shaye shaye, sai min bin mata, shi na ukun ma ɓarawo ne, dan ba a jima ba ya tafkwa Alhaji satar kuɗi har naira miliyan ɗari biyar, kaɗan ya rage Alhaji bai kai shi prison ba, sai da Hajiya Babba ta dage, amma da ya fito da miliyan ɗari uku da hamsin ciki, sai kuma mata huɗu su kuma suna nan zaune sun ƙi aure sai gayyar tara samari. Sai kuma Hajiya Bilki ‘ya’yanta mata biyu ne manya sai kuma ƙaramin Ashraf shi kam a ƙasar waje ma ya yi karatun shi ɓangaren kasuwanci kuma shi ya fara kula da kasuwanci mahaifinsu bayan ya dawo, sai dai ‘yan bani na iya suka dinga shiga cikin abun har ya haƙura ya ajiye aikin ya buɗe na sa kamfanin, shine Alhaji Musa ya ɗankawa Lemmah da ke aure a Abuja ita kuma ta bar auren ta dawo, Nusaiba kuma tana gidan aurenta, sai Hajiya Kubrah itama maza ne guda huɗu kuma uku ciki sun girmi Ashraf dan babban ɗanta ya kai shekara 38 sai dai suma sun gaza nutsuwa, kullum suna Abuja gantali, hakan ya sa duk suka sanya Hajiya Bilki a gaba, ita kam ta yi imani da Allah, kuma ta yi ƙoƙarin ɗaura ‘ya’yanta a kan tafarkin maaiki, duk da zurfin karatun bokon da suka yi bai hanasu samin na addini ba, kuma sun tsaya a kan sa.


A lokacin da Mama ta sanar da ita tafiyar Husna ta haɗa mata sha tara ta arziƙi tare da yi mata nasiha. ‘Yan mazan gidansu Husna sun nuna mata gata lokacin tafiya, duk da wannan lokacin basu tsaya da ƙafafuwansu ba, amma kowa ya iya yin sa. Haka sune suka kai ta har makarantar FGGC MUNJIBIR sai da aka gama yi mata komai sannan suka juya suka tafi suka barta da kewa.

Kamar dai farkon kowacce ɗalibar makarantar kwana, haka Husna ta dinga rusa kuka, kafin daga baya ta saba, a hankali ta fara sakin jiki inda ta yi ƙawaye guda biyu, Ruƙayya Said Kibiya, da ake kira Said Kibiya, ‘yar kibiyar jihar kano ce, sai kuma Binta Ali Kaita da ake kira Ali Kaita, ‘yar ƙaramar hukumar Kaita ce jihar Katsina, sai ita kuma suke ce mata Abubakar Sheshe, wannan ɗabi’a ce ta ‘yan makarantar kwana.

Ƙawancesu ya fara ne daga faɗa tsakanin Husna da Said Kibiya dan itama mafaɗaciyace kamar Husna, ba sa neman sauƙi sai dai ita tafi Husna haƙuri sosai da sosai, daga nan suka koma aminci a tsakaninsu, dama kuma Said Kibiya da Ali Kaita ƙawayene daga nan suka ɗinke, har ya zama sun koma tamkar ‘yan uwa, wata ba ta da shamaki tsakaninta da kayan wata, har ya zama Husna ke yi musu ƙari a kan karatun Qur’ani, sai dai duk sun fita saurin kwashewa a karatun boko haka zasu dawo hostel su yi ta mata bayani da hausa har sai ta fahimta. Ko ina a ka gan su an san akwai aminta mai zafi a tsakaninsu, tun daga Js one har suka dawo js two, suna shirin shiga Js 3 ne ƙaddara ta fara haɗa Husna da shi.

Ranar da ta fara ganinsa ranar taga abin da ban taɓa gani ba daga wani namiji a tare da shi.

Ranar Asabar da ƙarfe sha biyu da rabi, sun dawo daga massallaci ita da Said Kibiya, suna tafe Said Kibiya na ta faman yi ma Husna mita a kan taƙi bari Yaya Hafsa ta yi mata karatu, Husna ta taɓe baki ta ce.


“To na mene za ta yi min? Kin jin yanda take karatun akwai gyara a ciki, kuma ta maimaita ta sake kinga kuwa a haka take yi, kuma wannan ba ɗaukan gyara za ta yi ba, kuma ce ta za tanka ni mu daku wallah….”

Ba ta ƙarasa maganar ba idonta ya