Back to novel

Chapter 14 of 52

CHEF ZEEY Hanyar Nasara By Azizat Hamza

am Froud of you sosai Wallahi. Karatun mace yana da mahimmanci. Amma ki sani, karatu ba zai hana ki yin aure ba. So, kada ki damu, ba wani furoblem. Ki gabatar mana da saurayinki, mu kuma sai mu yi bincike akansa idan mun gamsu da shi babu wani Furoblem, sai a shirya muku aure."

"Sai cewa yake babu wani Furoblem, bayan ni na san akwai babbar Problem a ™asa."

Baffa Adamu ya ™ar™are bayaninsa da cewa sun bani wata uku na turo musu saurayina idan bai zo ya

gabatar da kansa ba kuma za su bayar da aurena ga Alhaji Nafi'u tunda su Baffa Lawalli da Baffa Zakari sun yi bincike akansa sun tabbatar mutumin kirki ne.

"A zuciyata na ce dole su ce mutumin kirki ne mana, tunda sun je sun ciyo uban bashi a wajensa."

Lokacin dana bar falon na dawo sashenmu faWawa kan gado na yi ina maimaita addu'ar samun sau™i a

"zuciyata. Kaka tana tambayata me su Baffa Adamu suka faWa, amma ban kulata ba."

"Wata uku na ke da shi in samawa kaina mafita, kafin a min auren biyan bashi da Alhaji Nafi'u."

To kodai kawai na fito fili na faWawa Baffa Adamu gaskiyar abinda ke faruwa ne?. To kuma idan na faWa

"masa ma ba lallai ya yarda ba, dan na san Baffa Lawalli ya riga ya gama hure masa kunne."

Yanzu ni Ziyadatu ta ina zan fara nemo saurayi mai suna Muhammad?.

"Yaya Aminu ne ya faWo mini rai. Allah Sarki! Ba dan matsalar da ta katse mana soyayya ba, ai da ba za ma"

a kawo wannan gaSar ba.

Gaba Waya yinin ranan har dare a Waki na wuni. Daga baya na faWawa Kaka abinda su Baffa Adamu suka

"yanke sai ta ce za ta musu magana su ™ara min lokaci, saboda ita ta san bani da Saurayi."

Na ce mata ta barsu ba sai ta musu magana ba. Babu amfanin maganar. Kaka bata da zafi. Idan suka fara

"kawo ™abli da ba'adi na karatun mahimmancin aure sama da karatun Boko babu abinda za ta faWa sai ""To! Allah ya kyauta""."

Bana so ma ta Waga hankalinta ne akaina. Tana da hawan jini. Idan na nuna mata na damu da abinda

"suka shirya mini, to abin zai tsaya mata a rai ne."

Yanzu dai ina da kwana casa'in na producing musu Saurayi mai suna Muhammad da zai aureni.

Tunda bani da gatan uba a raye ai Akwai Allah!.

"Tun da watan Ramadan za mu shiga, zan bi dare na ro™i Ubangiji ya turo mini miji na ™warai kafin"

wa'adin da aka bani ya cika. Ko kuma dai ya yi ikonsa har maganar Alhaji Nafi'u ta banje.

"Na Waura aniyar zan yi tsayuwar dare, zan yi sadaka. Sannan zan kira Ummana na ce ta sakani a addu'a."

Ganin na samarwa kaina mafita sai kawai na mi™e na fita na je na Waura ruwan zafi. Bayan na fito daga

wanka na samu Kaka har ta zubo mini tuwo a kwano.

"""Kuma aka ce miki zan ci tuwon ne"" na faWa ina tura baki duk da ™anshin miyar yana bugan hancina."

"""To me za ki ci, 'yar lelena? Wai na ga tun da kika dawo da rana baki ci komai bane"" ta faWa cike da"

damuwa.

Allah Sarki! har ta ban tausayi.

"""Wasa na ke, zan ci tuwon"""

Bayan na saka kaya sai na zauna na jawo tuwon na fara ci. Ina fara cin abincin sai na ji komai ya dawo

"mini. Hawaye ya cika mini idanu yana shirin zubowa. Na yi saurin gogewa, na tura lomar tuwon Masara da miyar kuka bakina. Cin tuwon nake ina kukan zuci. Bana so Kaka da ke can gefe tana fama da buga rediyonta da ya ™i tashi ta gane ina kuka."

Cin tuwon nake bana jin taste Winsa saboda Wacin dana ke ji a zuciyata. A haka na cinye shi tas. Kaka tana

tambayata ko a ™aro mini na ce mata ya isheni.

Bayan na kai kwanon kitchen sai na dawo na zauna kusa da Kaka a ™ofar Waki na ™urawa Taurari idanu...

***

JAYKAY

"Ana meeting, amma hankalin Jalal baya wajen. Tunaninsa ya yi nisa ne wajen nemowa kansa mafita akan"

"maganar Hajiya. Shi ba yaro bane. Hajiya ba za ta iya tursasa shi ya yi abinda baya so ba. Amma kalamanta na safiyar yau sun fi kama da umurni ba shawara ba. Idan a baya shawara ta ke bashi na ya ™ara aure, yanzu kam umurni ta ke masa."

A baya ya bijirewa umurninta lokacin da ta ™yamaci aurensa da Cassandra. Idan ya sake bijire mata a

"karo na biyu, bai kyauta mata ba. Yanzu da babu Jamal, babu Daddynsu. Hajiya da Janan sune mutanen mafi kusa da shi. A London aka haifeshi. A nan ya taso ya yi sama da shekara talatin na rayuwarsa. Duk da suna zuwa Nigeria lokaci zuwa lokaci, amma har yanzu ba shi da wani Wan'uwa na kusa da ya saba da shi a Familyn MAIYA˜I."

"Tun asali Jalal mutum ne very private. Baya shiga harkar da ba tasa ba, kuma baya so wani ya shiga"

"harkarsa. Balle tunda ya auri Baturiya sai ya zamo saniyar ware a cikin 'yan'uwa. Duk wanda zai yi kwatance da shi to da matar da ya aura zai fara. Idan za a banbance shi da Jamal, cewa ake ""wannan Wan Hajiya Layla da ya auri Baturiya Winnan"". As if ba shi da wani abu bayan aurensa da Cassandra. Mantawa suke shi pilot ne, da ya kai matakin Captain Win jirgi. A wajen mutane, shi Jalal Kabeer Maiya™i, mijin Baturiya ne. Duk wani abu, sai dai ya biyo baya wannan."

Ba zai so ta dalilinsa Hajiya ta sake shiga damuwa ba. Laifinsa na auren Cassandra zai iya raguwa a

"zuciyarta idan ya auri wata matar. Sai dai kuma, idan ya ce zai auri wata a yanzu, tabbas zai samu matsala da Cassandra. Auren kotu suka yi, dan haka a dokar ˜asar England da Wales ba shi da damar auren wata mace har sai idan ya rabu da Cassandra."

Rabuwa da Cassandra kuma a daidai wannan gaSar ba abu bane mai sau™i. Sannan babu makawa

Cassandra za ta yi amfani da Junior ta muzguna mishi ta hanyar Waukeshi daga wajensa.

Wani tunanine ya faWo masa. Idan har zai samu wacce zai aura cikin sirri ba tareda Cassandra ta ji labari

"ba, to zai iya samun damar cika umurnin Hajiya."

"Kotu ta Waura musu aure da Cassandra, wacce zai aura kuma aure za su yi na musulunci. Na bayar-Na"

"karSa, cikin sau™i a shafa Fatiha ba tareda an yi wata hayaniya ba. Then a hankali sai ya san yadda zai samu mafita daga auren Cassandra, ta yadda za su rabu kuma a bashi custody na ri™on Wansa."

Saudah ce ta fara zuwa masa lokacin da ya keSe a office shi kaWai bayan sun ™ar™are meeting Winsu

wanda fiye da rabin abinda aka yi a wajen bai sani ba.

Ya girgiza kai saboda Saudah ba za ta taSa yarda ta yi auren da babu hidima ba. Idan kuma har ta amince

"to ba lallai Mommynta da sauran 'yan'uwanta su yarda ba. Ko lokacin da aka shirya aurenta da Jamal, ba"

™aramin biki na gani na faWa aka shirya ba. Sai kuma Allah bai nufa ba.

"Sannan, auren Saudah na nufin ba zai taSa yun™urin rabuwa da ita ba, saboda Hajiya."

Ba shi da aboki a garin nan. Sau tari abokanan Jamal ne ya ke Wan fita da su idan har ya bu™aci shiga

mutane. Bai san ina zai samo budurwa da zai convincing ta yarda ta aure shi ba.

"Haka dai ya wuni a office, rabi aiki, rabi tunani."

Bai dawo gida da wuri ba. Lokacin da ya shigo gidan sai ya samu Hajiya da Junior da Janan suna cin

abincin dare.

Ya gaishe da Hajiya sannan ya wuce sama.

Ganin Cassandra yayi ta ajiye kwalin pizza a kan gado tana aiki a Laptop Winta.

Ya fara ™o™arin cire blazer Winsa ko magana bai mata ba. Sai ta kalleshi ta ce masa wai ya nema mata

"inda ake siyar da pizza mai daWi, wannan da Janan ta kawo mata babu daWi da ™yar ta ci slize Waya."

"""When are you going back?"" Ya tambaya ba tareda ya amsa ™orafinta ba."

"""Missing me already, ain't ya?"" Ta faWa tana wani faWaWa murmushinta."

Juyawa ya yi ya cigaba da cire kayansa bai kulata ba.

˜arfe shaWaya da rabi na dare da ya kwanta bayan ya gama bitar schedules Winsa na gobe sai ya ji

"hannun Cassandra tana ™o™arin wasa da sandar girmansa. Ta cigaba da ta™alarsa har sai da ya biye mata. Duk da ya biye mata Win, amma jikinsa ne kawai ke goganta amma zuciyarsa da nitsuwarsa basa tareda ita. Ita kanta ta ji banbanci tsakanin jiya da yau. Sau Waya da suka yi sai ya lafke with the pretense cewa a gajiye yake, amma deep down sha'awarta ce baya yi."

Wani abu ne ya faWo masa. Akwai wacce ta driving daWewar da ya yi yana gurzan Cassandra jiya. Ba wai

"saboda ya jima bai taSa mace bane. Ba wai saboda ya missing Cassandra bane. Duk da yana hana kansa irin wannan tunanin, amma macen da ta saka shi cikin matsananciyar sha'awa jiya ,ba Cassandra bace."

Da safe da ya je gaida Hajiya bata kawo masa maganar da suka yi jiya ba. Maganar rabon kayan sadaka

da ake duk Azumi ta fara masa. Ya ce mata ta rubuta masa budget idan ya dawo sai ya duba.

"Yau Asabat, ba zai je office ba. JK Plaza zai je ya duba da kuma wasu gidajensu da ake ginawa."

Ranan Monday Cassandra za ta koma London. Idan ta tafi zai samu nitsuwar zama ya nemawa kansa

masalaha ta hanyar binciko yarinyar da ta dace da sharuWWan Hajiya.

˜arfe biyar na yamma ya shigo gidan bayan ya gama duba duka sites Win da ake yi musu aiki.

Dariyar Hajiya ya fara jiyowa tun kafin ya shiga falo.

A tsaye ya samesu. Hajiya na yiwa yarinyar da ke ri™e da ™atuwar leda magana. Kamar tafiya za ta yi

amma maganar Hajiya ya tsaida ita. Kallo Waya ya mata ya ganeta. Ba ya tunanin zai iya mantawa da cute lips Winta nan kusa.

Jalal ya gaishe da Hajiya zai wuce ta ce masa dan Allah ya kai mata Ziyada gida Direbanta baya nan.

"""Hajiya da kin barshi kawai, ina fita zan tsai da keke"" yarinyar ta faWa tana avoiding idanunsa."

"""Haba Ziyadah, ai ba za a yi haka dani ba. Ba zan tasoki daga gida kuma na ce ki kama hanya ke kaWai ba,"

"ga Magariba ta doso"""

"Hajiya ta kalli Jalal ta ce ""please, ka sauke mini ita a gidansu"""

Juyawa ya yi waje ba tareda ya ce komai ba. Yarinyar ta sake yiwa Hajiya godiya sannan ta biyoshi.

"Ta wutsiyar ido ya hangota ta bayansa tana tafiya a hankali, kamar tana tsoron idan ta bishi zai saceta."

"Matsoraciya ce, amma sai baki."

"Idan har akwai wani dalili ma da zai sa ya saceta, to abu Waya ne. Those damn kissable lips."

Shi ya fara shiga motar yayinda ta ja ta tsaya a bakin ™ofar gaba. Jiya Direbansa ya Wauki uzuri ya tafi gida

"wai za a yi bikin ™annensa biyu, dan haka tun jiyan shi yake driving kansa."

Tana tsaye bata buWe ™ofar ba. Ya kalleta ta cikin window sai tura baki ta ke kamar akwai abinda ta ke

faWa. Probably part 2 na masifar ranan ta ke yi.

Ganin bata shigo ba sai ya danna horn wannan ya sa ta yi saurin buWe ™ofar ta shigo.

"Yana gani ta zauna can nesa kusa da window, ko kallon inda yake ta ™i yi."

Ya ja motar suka fita daga compound Win. Sai da suka yi nisa bata yi magana ba sai ya Wan juyo ya

"tambayeta ina ne anguwarsu ""Ghetto"" ta faWa tana kallon cikin idanunsa."

"Ta ™ara da cewa ""ka ajiyeni a titi zan hau Keke na ™arisa gida. Na san mota irin taka bata da ce da"

"anguwar ghetto irin namu ba"""

"Wani Wan faint murmushin gefen baki ya yi. Hasashensa ya yi daidai, Wazu practicing part 2 na masifar da"

za ta masa take. Wato har yanzu bata manta da abinda ya faru a restaurant ba.

""" Na farko umurnin Hajiya na ke cikawa. Na biyu idan ba zaki mini kwatancen unguwarku ba, zan juyar"

"da motar nan na mayar da ke wajen Hajiya"""

"Shiru ta yi tana tura baki, sai can ta faWa masa sunan unguwarsu. Ta juyar da kanta gefe tana kallon titi,"

"sai ya ji ™asa-™asa tana faWin ""sannu Wan Hajiya, mijin Baturiya, Mtssw""."

"""Da ni kike?"""

"Juyowa ta yi da sauri ta ce ""ni ba da kai nake ba"""

"Ya Wan kalleta kaWan bai ce komai ba, sannan ya maida hankalinsa kan tu™in da ya ke yi..."

CHAPTER EIGHTEEN

ZEEY

Yau Asabat ina wanki da safe kusan ™arfe goma nema sai na ji wayata na ringing a Waki. Na je da sauri

zan Wauka sai na ga wayar ta katse. Hajiya Layla ke kirana. Na danna mata kira amma sai ta kashe kiran ta sake kirana.

"""Ziyadah, yanzu na ga wani video a page Winki. Ai Wallahi kin tayar mini da kwaWayi sai ki san yadda za ki"

"yi dani"""

Ta faWa bayan mun gaisa.

Ni dai na san ban Waura sabon video ba. Akwai dai wani video na tallen garin Wanwake dana yiwa wata

kwanaki shine ta ce dan Allah za ta biyani na sake reposting mata a page Wina tunda za a fara Azumi. To shine na sake sakawa yau da safe. Ba sabon video bane.

To ko kuma dai videon Wanwaken take nufi?

"""Ziyadah ai ki zo ki min Wanwaken nan a gida na ci. Ya yi min kyau a ido"""

"Ashe shi Winne. Na sa dariya nace ""Hajiya ai kin girmi Wanwake"""

"""Ziyada ai ba za ki gane ba. Ni dana shekara Arba'in a turai ina gudun abincin gida, sai gashi na dawo"

"Nigeria yanzu babu abinda na fi so sama da abincinmu na nan. Kin san shiyasa fa na sallami Chef Win daya ke mana girki da. Na sa aka kawo mini Hassana"""

Ta ™are da cewa idan bana komai wai na zo gida na yi mata Wanwake. Na ce mata wanki nake amma na

kusa gamawa idan na gama zan zo. Daga haka ta min sallama.

"Ni garin Wanwaken dana yi amfani da shi a videon ma ya jima da ™arewa, amma dai zan duba a Kasuwa."

Lissafina na zuwa gidan Faty yau sai dai kuma gobe. Dama cewa nake idan na gama wanki zan je gidanta

"na faWa mata halin dana ke ciki, dan ta tayani jaje. In ma akwai wani tsohon saurayinta mai suna Muhammad da za ta iya haWani da shi sai na duba na gani ko za mu dace."

Bayan na gama wanki sai na shirya na fita. A hanya na tsaya na sayi garin Wanwake. Ban samu wanda

"nake nema Winba, amma dai na samu wani mai kyau dana taSa amfani da shi. Na wuce gidan Hajiya Layla."

Tana ganina ta fara murna kamar irin ta ga ™awarta Winnan. Gaskiya matar bata da girman kai.

Har kitchen ta biyoni ina kwaSa Wanwake tana min hira. Ta tambayeni ya shirin Azumi na ce mata

"Alhamdulillahi. Ta ce akwai abincin sadaka da wata mata ke musu duk Azumi tana tunanin ko ta bani aikin wannan karan, sai na ce mata gaskiya ba zan iya ba, saboda muna exams kuma idan na gama zan je Kaduna ziyara wajen Ummana. Ta ce mini babu komai."

Ina cikin jefa Wanwake bayan Hajiya ta tafi amsa waya a Waki sai ga wata Baturiya ta shigo kitchen Win. Da

farko sai dana Wan tsorata dan motsin mutum kawai na ji. Na Wauka ma Hassana mai aikin Hajiya ce sai na ga wata farar Baturiya kyakykyawa tana sanye da wando blue jeans da farin v neck top.

"""Are you the new Maid?. Where's the other one?. You know what, just make me some tea, I'll be on the"

"balcony"" ta juya ta bar kitchen Win tun ma kafin na bata amsa."

Sai da ta tafi ma na ji haushin meyasa ban ce mata ni ba Maid bane.

Da Hassana ta shigo kitchen Win sai na ce mata wata Baturiya ta shigo tana nemanta wai ta haWa mata

tea ta kai mata.

"""Ke bar jarabbiyar matar nan fa. Sai shegen jarabar shan tea. YallaSai idan zai sha koffee ko shayi shi da"

"kansa yake shigowa kitchen ya haWa abinsa. Da wuya kiga ya saka ni aiki. Amma wannan matarsar komai sai an mata. Idan an matan ma fa Wan Tank you Win nan ba zata faWa ba sai dai ta dinga ™orafi ba a haWa mata shayin da kyau ba. Shegiya."""

Na buWe baki ina kallonta. YallaSai?. Jalal Maiya™i take nufi. Shine ke auren Baturiya. Awwo! Ashe

"shiyasa ya ke cewa idea Wina bai dace da restaurant Win da zai buWe ba, saboda shi ya ™i jinin ba™in fata a rayuwarsa. Tsabar bai yadda da matan Hausawa ba, da Baturiya ya ™are. Lallai da zafinsa mijin Baturiya."

Haka dai na ™are aikin da zan yi. Dana gama Wanwake na zubawa Hajiya. Tana ci tana santi wai duk randa

take son cin Wanwake ni zata kira na zo na mata saboda nawa ya fi na Hassana daWi. Na yi murmushi kawai