Chapter 4 of 4

THE HATED GIRL Hawayenta Sun ɓoye Gaskiya by HAUWA JIBRIN MA'AJI

gudunta, Abidah tayi shiru for some seconds sannan tayi dakinta, saiga sultan shima yashigo amma shima tunanin yakeyi, Amrah nashiga dakinsu Dua tajiyo tana kallonta ba wadda yace da wani komai, har Amrah tayi wanka tafito still tanajin ta wani irin tasa sleeping dress ta kwanta kawai saitaji Dua tace ""Amrah from where mummy ma tazo bata sameki ba?"" Amrah tayi saki sannan tace ""inda naje is non of your business okay?"" Dua bata sake cewa komai ba kawai tayi Addu'o'in bacci takwanta."

"Yau agidan antashi da wuri saboda Yau su daddy zasu meeting, as usual Dua ta house maid dinsu Fatima suka fara aikinsu, mommy ce ta sauko ta fada musu breakfast dinda zasuyi sannan ta koma, sultan da Aryan sunfito zasu fita jogging nan sukaga Dua sai uban aiki yakeyi nan ta dan kallesu tace ""good morning ya Aryan, good morning ya sultan"" suka ansa mata fuska asake sannan suka mata sannu da aiki suka fita, sultan aransa yace why all those work Dua only, Ina Amrah fah?"

"Ummi tafito daga dakin da tasauka zataje ta gaishe da mijinta, nan tahadu da fatima da Dua sai aiki sukeyi, suka gaisheta ta amsa sannan tawuce zuwa gun Abbah su gaisa sannan suka dan taba hira tace masa tana zuwa, dazata koma dakin da ta sauka still Dua da fatima aiki sukeyi tace ""wai Ina Amrah ce ita bazata tayaku bane naga aikin yamuku yawa?"" Dua tace ""tagama aikinta yanzu tawuce sama"" ummi tace ""aiho"" Fatima tace ""Ummi karya fa Dua take miki"" tajuyo tace ""okay fadamin gaskiyan?"" Fatima tace ""Ai Amrah bata taba daukan sinke da niyar aiki ba koda kuwa kan gadonta ne, Dua keyin komai na dakinsu sannan tasoko kasa nuyi na nanma tare"" Ummi tajinjina maganar sannan ta girgiza kanta tayi hanyar hawa sama, aikuwa da gudu fatima taje tana cewa ""Ummi dan Allah karki kafawa kowa wollah nashiga uku idan kika fada, halanma akoreni"" Ummi tace ""you have no problem with me karki damu"" tace ""okay ma thank you"""

"Before 10 daddy sunfita agidan sunkama hanyar wajan meeting dinsu, sauran yan gidan da basuyi breakfast ba sune suka fitoyi, mummy taga Amrah har yanzu bata fito ba kawai tayi deciding taje ta dubata,"

"Tana zuwa taga Amrah kwance tana kallon ceiling, Amrah kuma tayi nisane atunani, What if ya sultan ya tambaye ta Ina taje, what if in Ummi tace baza a hadasu ba, sai kuma tace zan fadawa mummy before surigani nasan No matter what mummy will surely be with me especially when it comes to backing, kawai taji an tabata ta kalla wanda ya tabata tayi Ashe mummy ne, nan tayi murmushi ta tashi ta zauna sannan tace ""Good morning mummy"" mummy tace ""morning darling"" why the sudden change?, you haven't take your breakfast kuma yana yinki yanuna kamar kina da damuwa?, Nan ta fada mata duk abinda ya faru but bata bata labarin pick and obey ba, mummy tace Kinga irinsa ai you should've told me da duk hakan bai faru ba but anyway ai wannan its just a tiny thing ne so karki damu, and I guess zan turaku hutu kaduna, tace ""kince mu kardai harda Dua?"" Mummy tace sure saboda naga sultan da uwarsa suna yawan kallon ta so I have to send you both Kinga daganan saiku karasa hutunku, nan Amrah taringa jin dadi zata gun kakannin su dinsu.."

By jiddarhtulkhair`