Chapter 2 of 4

THE HATED GIRL Hawayenta Sun ɓoye Gaskiya by HAUWA JIBRIN MA'AJI

so Ana sa ran Ayesha, Dua, da wani friend dinsu Haidar,. Ana fita break Ayesha, Dua, and haidar suka hada kansu waje daya suna scheduling time dinda zasuke karatu, Haidar yace ""and is good muna tashi at the middle of night"" Ayesha tace ""Sure"""

Haka suka gama komai sannan suka fara karatu before akoma class..

Amrah nazuwa gida tasamu mummy akan zasuyi third time exams dan har an manna musu exams timetable so ita tasanma this time around Dua ma saitayi kokari

"Mummy tace ""Calm down and I will surely bother her so that she will not have the chance to read"""

Amrah ranta fess ko dan karatunma bata saran fatawa ba saboda yanzu ma birthday din rumaisa suke shiryawa.. JIDDARHTULKHAIR 08110615256

. CHAPTER 7

Knock knock knock

"The knock on the door broke the trail of thoughts that Ayman was having in his mind, ""Oh God, when will I see the girl again?"""

"""Almost 7 years back, may be she's still living in abuja may be she's not..."

"One of the maid that works for them was on the door,. ""Sir your daddy is calling you down"" the maid said and left. Ayman yace, ""Abba kakirani?"", ""Yes I did Ayman"""

Inason zan turaka Germany for supervising my company for just a year

"Ayman yaji kamar ya daura hannu aka yayi ihu, duk plan dinsa bayan ya gama 2nd degree dinsa yanzu ne right time da zaije nemo ""wannan Yarinyar"""

"""the innocent girl with devastated life"""

"Dan shi yaji ajikinsa she's not Alright and he is ready to help her out,. Bayadda ya iya hakan ya'amince wa Abbah.."

"Direct dakin ammi yayi yace ""I dreamt about her today too Ammi"" and all my plan is to find her but, but I would be supervising Abba's company for a year,."

"Ammi tace ""karka damu everything would be solve out In shaa Allah"". Shims yace ""In shaa Allah""."

"Ayman was the only child to his parent, is the kind of child who gets privileges since childhood, Ayman he's the real educated man and handsome, Ayman lives his life as he wants! He is straight forward person when he loves he love when he didn't definitely he didn't.."

"Ayman yayi karatunsa a oxford university London inda ya karanta medicine, sannan yawuce Delhi India for his second degree"

"Alhaji Baba Ahmad shine mahaifin Ayman, mahaifiyarsa kuma Hajiya Aisha shi kadai suka haifa hakan yasa they extremely loves him"

"Dukksn su 'yan kaduna ne,"

"Alhaji Baba Ahmad was politician yana da companies a different countries, kudin kam ba masalar su bane, hakan yasa Cayman tasowa cikin gata da kulawa,"

"But one thing! Sun ba dansu isheshshen tarbiya ga kuma ilimin addini, hakan yasa yake mutunta kowa dukda shidin miskiline balalle ya zauna tadi da mutunba.."

"Yau weekend Dua ta tafi islamiyya sai 4 take zuwa, da aka fita first break karatu kawae suka tayi ita da Ayesha, hakama second break,"

"A hanyar su na zuwa gida suna challenging junansu da question, wani farin ciki sukeyi da sukaga sun iya Almost everything."

"Dua nashiga gida mummy tace tashirya zata rakata duk dan karta samu wani chance din karatu,"

"Dua sai taji abin yamata somehow somehow dan haka ta juyo tace ""mummy are you talking to me?"" tace ""Sure"" Dua tana shiryawa but duk tanajin wani iri, Anya sun taba fita tare?, toh me hakan yake nufi, har tagama shiryawa tana Saka da warwarewa, ahaka har tagama,."

"Sukaje gidan tight friend din mummy, aka sata gyaran store daga nan suka wuce supermarket namma taringa sata dauka kaza, mayar beyimin ba, haka tagaji tayi lisss, sunkoma gida around 9 Dua nashiga daki sai barci,."

"Amrah ta fito da gudu tayi hugging mummy tace saike mummy yanzu haka tayi barci ma, mummy taje taleka aikuwa"

"tayi nisa a barci, haka suka sauka suna dariyar mugunta."

"Around 4:00am Dua ta farka taga Ashe har 4 yayi nan ta tashi tayi Alwala taringa nafila tare da addu'o'in samun nasara da nemawa mummyn ta rahama ubangijinta har gari ya waye,.."

CHAPTER 8

"Gari na wayewa Dua duk tagama wani aikin da tasan za'a sata sukayi clearing everywhere tare da fatima sannan sukayi breakfast tare,"

"Lokacin da suke breakfast ne daddy yace bazai samu daman kaisu ba driver ne zai kaisu, so they have to hurry"

"Duk su biyun suka futo tare Amrah na 'yar wake waken ta Dua kuma na morning Tasbih haka suka shiga, Amrah ce tace da driver ""can you take us to super market first before we go to school?"" Driver yace ""As you say!"" Dua tace ""Amrah what are you saying?"" ""Are you for real?"" ""You know we're having exams and you are talking about something else"""

"Amrah tace ""didn't I warned you?,"" Dua ranta ne ya baci basu taba musu ba Amma this time around tanajin Zasu fara dan gaskiya ba bazata bari tayi missing exams ba tace ""yes you did, but, But that wouldn't stop me saying out what's on my mind, if you are not ready for it just say"""

Amrah ta juyo backseat tana kallon Dua with so much Astonishment

Aranta tace daman tana magana har hakane ko kuma saboda ranta ya baci ne Driver dinne yace toh ina zamu daya

"Dua ce tayi saurin cewa ""if you're not ready to take us to school then drop me here"" daga shi har Amrah sake baki sukayi suna kallonta,"

Shi daman yasan Dua keda gaskiya dole ne yasa ke biyewa Amrah saboda yasan itace ake ji da'ita

"Amrah tace ""drop her them"" ba yadda ya iya dole ce tasa ya sauke Dua sannan ya wuce super market da Amrah Tafiya takeyi saboda batada transport money kawai taji horn a bayanta hakan besa tasaya ba saida motar tazo daf da'ita sannan taga ansauke glass din motar Ashe ma su Haidar ne , Atake taji wani relief, tagaishe da drivern sannan tashiga baya, nan suka kafa chaptern karatu har suka isa school"

"Daddy na zaune a resting chair yana duba messages dinda abokinsa Alh.Abubakar Tukur ya turo masa dangane da meeting dinda zasuyi, ya kuma yadda zasuyi scheduling everything yadda zaizo musu cikin sauki,."

Zahra ce tashigo masa da coffee nan yake bata labarin ai aminin sa zasuzo Abuja da iyalansa sannan kuma zasuyi wani meeting akan international trade nan Zahra ta washe baki tamusu fatan Alkhairi sannan tayi shiru

"Yace ""mata what's wrong"""

"Tace masa ""I guess this would be the right time da zamuyi maganan hada Amrah da sultan Aure"""

"Yace ""Eh nayi tunanin hakan but Amrah she's still young"" Tace ""Ai ba yanzu za'ayi ba, sai tafara university by then"" yace ""its okay"""

As I said earlier Alh.Abubakar Tukur shine babban abokin baban su Dua

"Matarshi daya wato Abidah Sannan dansa daya wato Sultan, Assalinsu yan yola ne but currently suna London da zama dukda bawai fully achan suke ba"

Abidah Sam jininta be hadu dana Zahra ba haka kawae taji Zahra bata mata ba

_wannan kenan_

"Yau Aryan zai dawo daga makaranta hakan yasa ake tamasa hidim dimi an dafa abinci yayi Kala 5 sannan ga snacks Kala Kala, drive ne yaje dauko sa a ""Nnamdi Azikiwe International Airport"""

Aryan yashigo gidansu da murna yaje yayi hugging daddy sannan yaje yayi hugging mommy

"Daddy yace ""you look much handsome yanzu anza babba saura aure ko?"" Dariya duk sukayi sannan suka shiga main parlour"

"Aryan yace ""inasu Dua ne I missed them so much"" daddy yace ""suna third time exams"" mummy kuma hararansa takeyi wato bama inasu Amrah , har yanzu Dua tana bakin sa knn, lalle zata taka masa birki."

"A hanyar su takomawa gida driver yace musu ai Aryan yazo daga Amrah har Dua kowa murna yakeyi, suna zuwa gida suka wuce parlour Dua ce a gaba Amrah kuma nabiye da'ita Dua na ganinsa batasan sanda tayi kansa da gudu ba, haka Amrah ma but Aryan yana ganin haka wajan Dua yayi sannan sukayi hugging each other,"

Mummy ce zuciyanta ya sinke da ganin haka

"Amrah kuma kukan bakin ciki tasa wai baya sonta, sannan yasake Dua yayi hugging kanwarsa,"

"Daki Dua ta wuce da taga ran kowa ya baci da hakan, Amma deep down her taji dadin ganinsa koba komai yau baza'a daketa ba akan misunderstanding dinda yashiga sakaninta da Amrah"

"Bayan Aryan yayi fresh up yafito daga toilet yana goge kansa sannan yasaya a gaban Morro yana kallan kansa yace ""I"

"love you Dua"" mummy data shigo dakin batare da yasan tashigo ba tace ""What Aryan"" da sauri ya juyo yana kallan mahaifiyarsa, ita kuma yadda zuciyarta yake sinkewa ne takasa kwakkwaran motsi...."

Me kuke tunani??

"Kuyi hakuri da typing errors dazu na'iso gida ga gajjiyan amma hakan na daure nayi typing, Nagode sosae da Addu'o'inku na tafi lfy sannan na dawo lfy"

JazakAllah khayrd'

. CHAPTER 9&10

"Mummy ta kwanta bacci but har yanzu takasa baccin tunani Kala Kala takeyi a ranta, Did she had Aryan's word well ko kuma she's wrong?, takasa bacci hakan yasa ta fita takira kawarta nuwairah (her only friend wacca take zugata lokacin aneesa na da rai) tafada mata duk wani abu da yafaru a zuwan Aryan nan ta jinjina maganar sannan tace ""yama za'ayi yafara irin wannan maganar toh gaskiya yakamata yakoma school, gaskiya I'm speechless kibari zamuyi magana gobe.."

"Amrah na waya da wani new boyfriend dinta sai daria takeyi while Dua kuma na Karatun exams din gobe foot step sukaji sannan aka bude door din nan Amrah tayi saurin boye wayan a karkashin pillow, daddy ne yashigo sannan ya saya yana noticing dinsu yasan for sure Dua karatu take but Amrah fah, by mere looking yasan batada gaskiya but what is she hiding, kanshi ne yaji ya tsara masa, yama rasa meya kawo sa dakin kawai yaja musu kofar yafita,."

"Shi yarasa meke damunsa those days he always feel somehow somehow is like akwai abinda yayi missing but what is that? Kanshi daya fara masa ciwo ne ya hakura da wannan tunanin sannan yashiga daki inda yaga mummy itama tana ta tunani kawai ya kwanta abinsa,"

"The following day, After Dua sunzo daga exams suna shiga gida sukaga ya Aryan a parlour duk suka gaishe sa ya amsa musu da fara'a sannan ya tambayesu ya exams nan Amrah tafara basa labari Dua kuma tayi hanyan dakinsu, Bayan tayi lunch ne tafara karatun last paper dinsu tanayi tana duba time kar lokacin islamiyya yayi, Saiga Amrah tashigo tana gama cire uniform kawae ta hau chatting hankalinta gaba daya nakan wayan, kawai Aryan yashigo dakin dukkan su hankalinsu nakan abinda sukeyi so ba Wanda tayi noticing shigowar sa, saida yagama karewa Dua kallo saf yaga karatunta take bilhakki a ranshi yace guru by nature, sannan ya kalla direction din Amrah ya kasa yarda da abinda idonsa ke nuna masa, Amrah na video call da wani kuma half vest ne kawae ajikin ta duk rabin kirjin ta awaje sai dariya take hankalinta kwance, mutumin da suke vid call din ko riga babu ajikinsa sai iya gajeren wando, Azuciye yayi kanta ya wanke ta da mari wani irin ihu tasaka, ya fizge wayar yayi wurgi dashi nan ya sake yin kanta da yafara marinta ita kuma ihun take tana kiran mummy, Dua kuma tana ta bashi hakuri akan yabarta, mummy da zata raka daddy kofar parlour nan sukaji ihun Amrah ai da gudunsu suka haura sama suka shiga dakin duk a tare, turus mummy tayi tana kallon Aryan, daddy ne ya daka masa tsawa sannan ya tsaya, maruka mummy tayima Aryan a fuska duk ranta yagama baci masifa tafara ""how dare you will you beat her in front of that crazy clumsy girl?"" Aryan ya sugunna yana baya hakuri ""I can explain mummy, let me explain you"" daddy da yaga ran mummy ya baci yasan kuma dole tayi laifine Aryan ya bigeta sai yace ""Aryan follow me"" suka tafi sukarsu asaye, Dua naganin su uku suka rage tasan mummy zata iya huce haushin ta akan kawae tayi hanyar toilet da gudu kafin ta karasa shiga mummy ta wurga mata mock garin kwaucewa ta fadi kasan tiles hakan yaba mummy daman kamata taringa dukanta wai ai duk laifinta ne,."

"Daddy yayi kiran mummy akan Aryan zai musu bayani, nan Aryan yafada komai batare da ya boye komai ba, mummy"

"ce tayi tsaki ""Duk marin daka mata is just because of this little thing Aryan toh as from today you should never ever try your stupid self to their room"" Daddy yace ""what Aryan did is right"" nan suka samu misunderstanding kowa yabar gun ranshi a bace, barin ma Aryan how dare him akanshi parents dinsa suka samu misunderstanding abinda be taba ganiba Kenan,."

"Amma yana jin cewa abinda yayi shine daidai saboda yaushe Amrah ta fara rike waya?, yaushe tafara hira?, ya rinya karama like her just 17yrs, Ai dole result dinta kullum bakyau tunda ba katun tasa a gaba ba.."

"Ayesha ta biyowa Dua akan su tafi islamiyya nan taga Dua ko alamar niyyan zuwa ma batayi ba, tagane cewa yauma mummy ta dake ta Kenan, Ayesha taringa bata baki har ta hakura ta sa uniform dinta suka Kama hanya, saiga Aryan yafito daga masallaci ya taresu yace bari zai kaisu a mota, A hangar su Aryan ke tambayen Dua ""yaushe Amrah tafar rike waya Dua?"" Ya Aryan I don't know too but I guess its recently"" Aryan yace ""who bought her?"" Tace ""I don't know too"" yayi shiru sannan chan yace ""yaushe tafara video calls da maza?"" Nanma tace ""I don't know too"" ya kyaleta kawai yasan ba fada masa zatayi ba.."

"Dare nayi Aryan yaje yaba iyayensa hakuri daddy yace ""it's okay komai ya wuce"""

"A dakin mummy fada take mai kamar zata ari baki, shidai hakuri kawae yake ta bata dakyar ta hakura yayi mata"

godiya sannan ya fita..

"Dan yasa Amrah ta huce yakirasu dukkan su biyu yace sukawo masa study material dinsu yayi coaching dinsu through, tunda last paper ne and it's further maths, duk tambayar da zaiyi Amrah bata sani ba sannan Dua bazata bada amsa ba harsai ya tambayeta sannan tafada,"

"Anan ya fahimci Dua *Genius* ce, Amrah kuma sai a hankali, da yaga pass 10 yace suje su kwanta karsu makkara zuwa exams,."

"Yau su Dua suka gama exams dinsu kowa kagani a school din murna yakeyi, Dua, Ayesha da haidar ne suka fito sunata musu akan last question din haidar yace ""wait! Wait!! It seems Dua tafimu gaskiya fa Ayesha"", nan suka duba sukaga Ashe tafusu, suna cik hirar su sai gashi anzo dauka haidar babban yayansu ne yazo, nan haidar yayi introducing friends dinsa ga yayansa, Ahmad yace ""Dua are you shuwa Arab?"" Tace ""Aa no"" yace which tribe are you?"" Tace I don't know"" yace ""you don't know?"" Tace ""Sure"" yace ""Alright kina komawa gida ki tambayi mamarki next time innazo saiki fada min okay?"" ga mamakinsa kawai yaga hawaye a fuskarta, haidar ne yace ""ya Ahmad she lost her mom since when she's 10years"" Ahmad yaci tausayinta yakamasa, yace ""Ayyah sorry dear"" tace ""Thank You"" Haidar yace ""see you next time bye"""

_*GERMANY*_

"Ayman keta supervising companyn Abban sa everything is going well and perfect, ya koma gida yana dan hutawan sa sai ga kiran Abokin sa Ahmad yadaka yace ""Hello dude"" Ahmad yace ""ka kyauta Ashe har Zaka iya dawowa Nigeria baka nemeni ba?"" Ayman yace ""sorry man nazo ko 10 days banyi ba na wuce Germany for supervising my daddy's company"" ""Ohh ayyah sorry so how was the German then"" haka suka danyi hirar su sannan Ahmad yace ""how far kasamu yarinyar?"" No yet banma fara aiki akanta ba nabar gari, haka suka gama hirarsu sannan sukayi sallama"

_*NIGERIA*_

"Yau ake speech and prize giving day iyayen yara duk sun hallara, anyi jawabai akan makarantar da yadda wasu dalibai suke da kokari dan haka anason zasu tafi German zasuyi 2weeks training idan sunci za'a basu scholarship a oxford university London, an bada kyaututtuka ga house din datazo na daya da na biyu a wannan term din sannan aka fara bata prize ma students din,"

"Nan akazo SSS2 inda Aliyu Haidar Suleiman yayi na 3rd, Ayesha Muhammad inuwa tayi na 2nd, Sannan Dua Muhammad Usman as usual ita tasake cin na 1st, nan murna gun iyayen yaran da sukayi kokari Amma banda Dua, lokacin da aka bata kyautar ta tarasa mawa zata kaiwa kamar yadda sauran yaran keyi kawai saita kaiwa ya Aryan, Ahmad da haidar sukazo tayata murna, Ahmad na tsokanar ta wai ya'isa hakan tabarwa kaninsa na 1 saidai kawai tayi Dariya bata cewa komai,"

"Principal ne yayi jawabai ga iyayen yaran da za'a fitar dasu waje karatu sannan yamusu bayanan cewa yaransu they would be safe in shaa Allah,"

"Duk iyayen yaran sun yarda kuma sunyi signing,"

"Ahmad yace akwai friend dinsa dake German zaisashi yana zuwa duba su haidar dan ganin lafiyansu,"

"Anzo kan mummy da daddy inda zasuyi signing na Dua Amma sukace su basu san zancen ba, principal takara musu bayanin ba'inda za'a bar yaran sufita without their consent daddy yace Suyi hakuri Dua she's still young, mummy tace ita ba'inda za'a kai mata 'yarta, Aryan yace but why ba'ita kadai bace bafa, nan mummy tawasa mass kallo dayasa bafita agun ba shiri,"

Yadda fuskar Dua yayi jaa zakasan bataso hukuncin da suka yanke akan taba

Ahmad ne ya kalla Dua sannan yaga iyayenta nan ya fahimci mummy itace Uwar rukonta kuma