Back to novel

Chapter 4 of 30

NIDA PATIENT DINA Bayan Koma by MRS ISHAM

ta."

Cikin kuka ta ce .

"""Innalillahi wa 'inna ilahir raji'un, Allah humma ajirni fi musibati wa'a khalifni khalifan min ha."""

"""Shi ke nan Mamy kin ruguza Mani rayuwa Allah ba zai bar ki ba. Allah ga ni gare ka ka da kai na dogara"

"ya zuljalalu wal ikhram."""

Kuka take yi sosai ana kiran sallar magrib ta ga ya fita da sandarsa yana dogarawa ya fice daga gidan ba

tare da ya ce ma ta koma ba.

Ta dade tana kuka kafin ta mike tsaye tana goge hawayenta ta ce.

"""Daina kuka Ma'eesha ki daina Sata hawayenki anan zaluncin da aka yi ma ki, ki rungume ™addarar da ta"

"zo ma ki Allah yana tare da ke. Kuka ba bali ba ne ki shirya fuskantar sabuwar rayuwar da kika tsinci kanki a ciki."""

Ita kadai take magana kamar wata zararriya.

Fitilar wayarta ta kunna kasancewar akwai duhu kuma ba wutar nepa.

Waige-waige take yi nan ta lura ashe akwai rijiya a gidan can karshen gidan

Handbag Win ta ta duba ta ciro karamin bottle of water wanda ta shiga shagon saloon da shi ba ta sha ba.

Alwala ta yi sannan ta duba cikin akwatin kayanta ta dauki Šankwali ta shimfida ta gabatar da sallar

magrib.

Tana cikin addu'a aka kira isha'i ta tashi ta gabatar.

Tashi ta yi bayan ta yi addu'a ta nufi kofar fita gidan hannun ta rike da handbag.

Wani shago dake kusa da gidan ta tambaye shi in da ake fitar da tsintsiya da faka ya ce wata bayarabiya

ce kuma tun karfe shida take rufe shago ta wuce gidan.

"""Cikin damuwa ta ce ."

"""Ba wani wajen kuma?"""

"""Gaskiya sai dai ki bari da safe ."""

"""Yanzu nake bukata wallahi."""

""" Daren nan kuma?"""

Ya tambaya yana mamakin yadda ta dage.

"""Eh yau muka tare a wancan gidan, ya yi ™ura dole sai na share kafin mu kwana a ciki."""

"""Allah Sarki, bari na ara Maki na shagona zuwa da safe sai ki dawo Mani da shi ko?"""

"""To na gode."""

Ya mika ma ta tsitsiyar da faka ta amsa ta tafi.

Har ta fara tafiya ta dawo ta fiye ruwar roba gida biyu ta wuce.

Ko da ta koma ta samu makaho tsaye a tsakar gidan hannunsa rike da sandarsa.

Ba ta kalli in da yake ba ta shiga cikin Wakin.

"Yanar gizo-gizo ta fara cire wa a silin da bango, sai da ta kakkaSe sannan ta share Wakin ta kwashe dattin"

cikin faka tana kai wa waje can karshen bangon gidan.

Sannan ta fito ta share simintin barandar ™ofar.

"Tsakar gidan ta fara share wa, sai dai kasancewar kasa ce ba siminti ba ™ura ya addababe ta ta fara"

atishawa da tari sakamakon kuran.

Gefen mayafin abayar dake jikinta ta sa tana toshe hanci da daya hannun daya hannunta tana shafa har

ta gama.

Fita ta sake yi tana tari da atishawa ta koma wajen me shagon.

"Ganin akwai mutane ta tsaya gefe tana jiran a rage, bayan an rage ta samu ta karasa bakin kofar shagon."

"""Hajiya kin dawo?"""

"""Eh dama ina son ne ka bar mun tsintsiyar nan da zuwa gobe sai na siya maka wata, saboda zan wanke"

"toilet da shi ne kuma bai dace na dawo maka da ita ba bayan na wanke toilet."""

"""Ba damuwa ki rike duka na bar ma ki."""

"""To na gode sosai."""

"""Ina son ka ba ni detergent da hypo ne."""

Daidai lokacin da wani mai siyar da robobi yake dawowa daga talla.

"""Dakata mallam."""

Sai ya tsaya ta karasa wajensa ta siya madaidaicin bokintin roba na 1k ta detergent da hypo dama ta siye

ruwa Roba biyu ta kashe 1k ta zuba su a roba ta koma cikin gidan.

Handbag Win ta ta duba tana tafiya ta ga 2k ya rage ma ta cikin 5k da ga bar gidan da shi

Cire kayan ta yi daga cikin bokitin sannan sai ta karasa wajan rijiyar duk da ba ta da tabbacin cewa akwai

guga.

Ta haska torchlight na karamar wayarta ya ga an daure guga jikin karfe dake jikin murfin rijiyar.

Abinda ba ta taSa yi ba a rayuwar ta jan ruwa daga rijiya .

Kamilalliyar muryarsa mai cike da kamala ta s ji ya ce.

"""Me kike ta yi a daren nan ne?"""

Kamar ba za ta amsa ma sa sai ta ce .

"""Ruwan zan ka a rijiya zan wanke Wakin ne da kuma toilet, don ba zan iya amfani da su a haka ba."""

"""Bari na taya ki jar ruwan, ki je dakin sai na kawo ma ka."""

Kallon mamaki ta masa ta ce.

"""Da wake idanun za ka gani ruwan kuka har ka kawo mani?"""

"Ganin bai yanka ta ba kuma kamar ransa ya Saci ta wuce ta ba shi wuri."""

"Laluben rijiyar ya yi har hannunsa ya sauka akan gugar ya janyo ta ya ji nauyi, don dama igiyar na Waure a"

jikin karfe guga na cikin ruwa .

Sau uku ya janyo ya cika bokitin.

Ya kai tana mamaki ya karba ta wanke dakin bayan ta zuba hypo da detergent.

"Sau biyar yana ciki bokitin yana kawo wa tana wanke wa tana sharo ruwan a waje, tana kashewada faka"

har ta gama ta wanke barandar.

"Daga nan kuma ta nufi toilet Win, nan ma siminti ne irin toilet na tsuguno na gargajiya."

Sai dai ya kawo ma ta ruwa bokati uku ta Wauraye toilet Win bayan ta wanke.

"Tana kallon ikon Allah makaho da Wibar ruwa a rijiya, yana rike da bokitin a daya hannu yayin da daya"

hannun kuma yake dogara sandarsa ta makafi.

*KADUNA*

Bayan Nadra ta katse kiran wayar da take yi da Ya Sayyadinta.

Cikin ´ar damuwa ta ce .

"""Goggo har yanzu ban san in da Aunty Sidra ta shiga ba, tun dazu nake zagaye gidan nan, ko dai ta fita"

"ne?"""

"""Eh kada ki damu ta je gyaran jiki ne kuma a'ba za ta dawo da wuri ba."""

"""Allah ya dawo ma na da ita lafiya."""

"""Amin ya Allah. Yauwa ki tashi yanzu nan direba zai kai mu wajen gyaran jiki da kitso."""

"""Waye za'a yi wa?"""

"""Da ni da ke."""

"""Goggo ke ma kin san ba na son kitso, saboda gashin kaina yana da yawa sosai, tsayin kitson ma yana"

"damuna."""

"""Sai da an yi shi don haka ba ba™i mintuna Talatin ki yi breakfast ki fito."""

"""Toh."""

Ta fada duk da ba ta son kitso sai dai ta dun™ule kanta kanta ta cusa cikin hula ko Šankwali. Amma

kasancewar ta ba mai musu ko gardama ba ne ya saka ta tashi ta nufi bathroom don yin wanka.

"Bayan ta fito ne ta shafa man ta mai sanyin ™amshi ta shafa, wanda yake karSar ba™aar fatarta mai she™i."

Ta shirya cikin kayan doguwar rigar material ta saka. Sannan ta sanya dogon Hijabinta ta dauki handbag da wayarta ta fice bayan ta saka flat shoe.

Wayar Sidra take sake kira har lokacin switch off.

Part Win mahaifiyar ta ta nufa saboda tana son sake duba jikinta. Sai dai an fada mata Umma na part Win

Abba. Kamar sa ta bi ta can sai ta fasa

Tana fitowa ta ga jama'a kowa na kallonta jama'ar dake falon dangin Abban ta ne.

Wata ma daga cikin su ta ce.

"""Allah Sarki Nadra rabon dai ke za ki riga yar taki aure.?"""

"""Ni kuma ?"""

Ta tambaya cikin mamaki. Matar za ta sake magana kenan sai Goggo Laraba ta dakatar da ita ta hanyar

"girgiza ma ta kai."""

Hakan ya saka matar ta fahimci Nadra ba ta san da ita za'ayi auren ba.

ShagwaSe fuska ta yi ta ce

"""Goggo lalle kawai nake so jiya fa na je saloon aka gyara mun kai na """

Murmushi Gwaggo Halima ta yi ta ja hannun ta suka nufi ™ofar fita suka fice .

Direba ne ya kai su har shagon da Gwaggo Laraba ta sanar da shi

Bayan sun fita ya tsaya jiran su yayin da suka shiga.

Nadra ta zauna yayin da Goggo Laraba ta yi wa mai saloon maganar uzuri suna sauri kuma amarya ce za

"su je reception ne, take ta kira Waya daga cikin yaran aiki ta ta karasa yi wa wata lalle, ita kuma ta fara tsantsara wa Nadra lafiyyarnb zanen lalle mai dauker hankali."

*Maman Ihsan ce.*

09065327995

Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z

*MAKAHO NE*

*NA*

Maman Ihsan ce

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=15969875

11055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

(J.W.A)

"_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ™asaitacciyar baiwa su sauya"

tunanin al'umma cikin sau™i_.

page

Nadra ta zauna yayin da Goggo Laraba ta yi wa mai saloon maganar uzuri suna sauri kuma amarya ce za

"su je reception ne. Take ta kira Waya daga cikin yaran aikinta ta karasa yi wa wata lalle, ita kuma ta fara yi wa Nadra lafiyyarn zanen lalle mai Waukar hankali."

"Kamar yadda ta nuna ba ta son kitson haka aka yi ba'ayi ma ta ba, sai sai gashin na ta ya sha gyara sai"

she™i da wani ni'imtacen ™amshi take yi.

Abun da ya sake ba ta mamaki bayan na gama ma ta sai ta ga Mama Laraba ta ce su je ta shiga ciki za'ayi

ma ta gyaran jiki.

"""Mama wani gyaran jiki kamar wata Amarya?"""

"""Ai ke ™anwar Amarya ce ya kamata duk abin za'a yi ma ta a yi ma ki?"""

"""Amma Mama ban taSa jin in da aka yi haka ba."""

Ganin za ta ba ta ma su lokacin kuma tana son su koma gida akan lokaci ya sa ka ta ce.

"""Nadra ki shiga don Allah ana jiran mu."""

"""To Goggo Dinner da za'a yi ai sai bayan an Waura aure ne, karfe biyar aka..."""

"Ganin yadda Goggon nata ta tsuki fuska ya saka ta ja bakinta ta yi shiru, kasancewar tana da gudun Sacin"

ran mutum.

Shiga ciki ta yi aka ce ta cire kayan jikinta. Aka ba ta wasu ™ananun kaya ta saka aka shigar da ita wani

ruwa mai kumafa da ™amshi.

Matar sai lallaSa ta take yi tana cewa ban san har da gyaran jikin nan za'a yi ma ki ba da shi muka fara yi

kafin muka yi lalle.

Ita dai ba ta ce komai ba sai faWuwar gaba da take tsintar kanta a ciki.

_Makaho_

Sai da ya gama dibar ruwar yana daukar hannu daya da bokitin ruwa hannu daya da sandar dogarawa

har ya gama.

Don sai da Nasara ta wanke banWakin nan tas da detergent da hypo. Duk da cewar ba tile ba ne a toilet

ba ne siminti ne.

Bayan ta gama ne ruwan karshe da ya kawo ta ajiye a banWakin ta fito.

Duk abinda take yi hawaye bai tsaya daga tsiyayar da take a idanunta ba.

Kiran sallar isha'i ake yi don haka ya ce ma ta .

"""Zan je masallaci."""

"Ba ta ce ma sa komai ba, shi ma bai jira cewar ta ba ya fice."

"Tsayawa ta yi tana kallon Wakin da take haskawa da wayarta, tana tunanin dakin zai dauki lokaci kafin ya"

bushe.

"Kawatin kayanta ta buWe ta Wauki wani rigar sanyinta da yake da kauri ta san zai kashe ruwa, ta dauka ta"

dinga goge Wakin har ya tsane ba ruwa a kasan simintin dakin.

Šankwalinta ta shimfida sannan ta fita ta Wauro alwala ta fito ta gabatar da sallar isha'i.

Bayan ta idar ta tsaya ta yi addu'o'i tana kai kukanta ga Allah ya ba ta karfin zuciyar cinye wannan

jarabawar.

Tana zaune ta ji ya yi sallama.

"""Assalamu alaikum."""

"""Wa'alaiki Salam."""

Ya dinga lalube har ya ji Wakin sannan ya shiga bayan ya cire takalminsa a waje.

Shiru ne ya biyo baya har tsawon mintuna biyar ba wanda ya yi magana a cikinsu.

Maganar zuci da take yi ya fito fili ba tare da ta sani ba.

"""Mamy ba zan yafe ma ki ba, kin aurar da ni in da kike ganin zan tagayyara, kin san cewa rayuwata za ta"

iya inganta ta hanyar amfani da kuWaWena. Kin amshe ATM card kin je kin kwashe kudint.

Makaho ya gyara tsayuwar sa tare da jingine sandarsa a jikin bango ya ce.

"""Ba lallai sai ta ATM card kawai ba, ta yi multiple withdrawal (cire kuWin sau da yawa a ATM daban-"

daban. Ko ta yi transfer ta amfani da USSD (*737# *901# da sai sauran su saboda ta san Pin ta samu damar yin hakan. Ba zai yiwu ta fitar da miliyan goma a ATM lokaci guda ba amma a cikin awa biyu za ta iya gama komai . Don idan har lissafi na ya yi daidai lokacin da kika fahimci ba kudin a cikin asusun ki an yi awa biyu da barin mu gidanku. Ta kwashe kudin ne ta hanyoyi daban-daban (ATM + Transfer kasancewar ta san Pin da bayanan asusun. Sa™onnin bankin sun nuna cewa kuWin sun fita ne ta hanyoyi

"daban-daban a cikin awa biyu duk da sahihin Pin?"""

Da mamaki take kallonsa kafin ta ce.

"""Sa™onnin bankin sun nuna mani cewa ba ciro kudin aka yi ba, an kwashe kudin ne ta USSD da canja"

"wuri (transfer) a cikin awa biyu duka da sahihin Pin."""

Mamaki ya kama Ma'eesaha ta ce.

"""Ya aka yi ka san irin waWan nan tsarukan na banki?"""

"""Ba abin mamaki ba ne, don ni ma wasu na ji suna fira ina kwance a masallaci ina jin su."""

"""Su waye?"""

""" Da wani idanun zan gane su? Wata rana bayan an sallame sallah Waya yake faWa wa wani an kwashe ma"

"sa miliyan goma ta hanyar amfani da ATM card na shi to wannan da aka fada wa ya fadi bayanin nan da na maki."""

"Shiru ta yi dai tana kau da idsnun ta daga kallonsa, ita babban damuwar ta yadda idan Mallam Iro ya zo"

"karSar kudin haya wani bayani za ta ma sa kan dubu hamsin, bayan ya ma ta taimako a daren nan ba ba su gida. Su zauna."

Ganin ga lokacin na tafiya kuma tauna ya addababe ta ne ga karfe tara da ta yi ne ya saka ta mike tsaye

ta Wauki handbag Win ta sauran 2k Win da ya rage ta dauka ta rasa me za ta siyo da za su ci a daren.

Ita kanta ta san 2k ya yi kadan ya siya ma ta irin abincin da za ta ci ballantana ga makahon mijinta. Kuma

idan ta kashe kudin duka da me za su yi breakfast da safe?

Don haka ta Wauki Wauki 1k ta fita da shi sannan ta bar 1k a cikin handbag Win ta.

"Wajen me shagon dake kusa da gidan ta nufa, yanzu ma yana da jama'a. Don haka sai ta jira daga gefe"

har aka rage.

"""Mallam nawa ne coke na roba?"""

"""Hajiya Wari huWu da hamsin ne."""

"Shiru ta yi idan ta siye guda biyu kudin ba zai isa ba, don haka sai ta ce."

"""Ka bani guda Waya nawa kake siyar da bread. Biredin nan akwai na dubi daya da Wari biyar, akwai na"

"dubu daya da Wari uku akwai na dubu daya, akwai na Wari biyar dai kuma karamin nan na Wari uku."""

"""Ka bani na Wari biyar Win."""

Ta amsa bayan ya saka ma ya a leda ya ba ta canjin Naira hamsin.

"Tana tafiya tana hawaye, da a baya ne kafin yau canji ko nawa ne idan ta siye abu ba ta karSar canji sai"

dai ta bar wa mai kayan. Amma yau ita ce da karbar canjin Naira hamsin.

Murmushi ta yi tana goge hawayenta ta ce.

"""Alhamdulillah ala kulli halin."""

"Ta shiga gidan, sannan ta mai da ™ofar langa-langan ta rufe tare da saka sakata."

"Shiga gidan ta yi kasancewar ta fita da hasken fitilar wayarta, sai ta bar shi cikin duhu shi kadai a Wakin."

Ita a tunaninta tun da ba gani yake yi ba ai ba amfanin bar ma sa haske da za ta yi.

Ta shafa ta same shi tsaye tana mamakin yanda ba ya gajiya da tsayuwa.

"Tana kallon Wakin yanzu ina za su kwanta ne, ba tabarma ba katifa."

"Zaninta ta Wauko guda biyu ta shimfiWa Waya a in da take zaune, sannan ta ciro daya ta shimfiWa ma sa a"

inda yake tsaye ta ce.

"""Ka zauna a nan."""

Kamar bai ji ta kuma ya ji ta ya san me take cewa .

"Coke din ta ciro tare da bread Win, ta Webi Biredin kaWan sannan ta Webi rabin cike Win cikin robar ruwa"

da ta yi alwala da shi.

Ta ajiye wanda ta Wiba a gabanta sannan ta ajiye sauran da kuma ladar bread Win.

Coke dake cikin goran ta ajiye ma sa da robar coke din da ta Wiba ta bar ma sa sauran.

"""Ga bread nan da abun sha na ajiye ma ka."""

"Shiru bai ce da ita komai ba, sake kallonta ta yi tana maimaita abun da ta faWa, nan ma shiru bai amsa ba,"

"don haka ta yi shiru tana kallon da da mamaki, har shi zai dinga ji da kansa waye shi?"

Murmushin takaici ta yi ta zauna a saman zanen da ta shimfiWa.

"Da kyar take cin bread Win don ba ta taSa cin irinsa ba, daure wa kawai take yi ba wai don dadi ba sai don"

yunwa.

"Haka ta cinye wanda ta Weba tare da coke Win, sannan ta janyo bottle wataer da ta siya guda biyu ta"

"buWe daya ta sha, sannan ta rufe ta ajiye ."

"""Za ki iya kwana a nan Wakin kuwa?"""

Wani kallo ta ma sa kafin ta ce.

"""To ya zan yi kana da gidan da ya fi wannan ne da za ka kai ni na kwana?"""

"""Babu ni ma a masallaci nake kwana."""

Ba ta ce komai ba ta daga kai tana kallon rufin Wakin.

"""Na kwanta a nan ne ko kuma na tafi masallaci da na saba kwana a ciki ne na kwanta?"""

"""Wannan kuma ra'ayin ka ne."""

Shiru ya yi kafin ya ce .

"""Bai dace na bar ki ki kwana a nan ke kaWai a cikin wannan gidan."""

"""To idan ka kwana akwai abun da za ka yi mani ne? Ko za ka iya kare ni ne daga cutarwar wani abun?"""

"""Saboda ina makaho ba na gani ko?"""

"Da alama maganar ta soke sa a zuciya, bisa la'akari da yanayin amsar da ya ba ta ransa a Saci ko bai fada"

ba.

Sandarsa ya Wauka ya fice daga cikin Wakin ya nufi hanyar fita ba ta ce komai ba.

Tana ji ya fice daga cikin gidan.

"Sai anan take ta ji babu dad'i, ga wani tsoro da ta ji ya dirar ma ta lokaci guda. Ko ba komai idan tana jin"

motsin mutum kusa da ita ai ya fi da ta zauna ita kaWai.

Tsoron gidan ya kama ta ta mike zumbur ta fita daga cikin gidan ita ma tana cewa.

"""Wallahi ba zan iya kwana ni kaWai ba."""

_Sidra_

"Suna zaune a katafaren falon gidan, wanda kallo Waya za ka yi ma su ka gane wayayyun ´an mata ne ma"

su ji da kansu.

Wata daga cikin su ta kalli Sidra ta ce .

"""Yanzu ba za ki ha™ura da wanann burin naki ki koma gida tun lokaci bai ™ure ma ki ba?"""

"""Khadijah kenan, ai ba zan koma gida ba har sai burina ya cika."""

"""Matsalarki kenan ki ce ke ba wanda zai fi ki sai dai ki fi kowa? Idan Allah bai yi