Follow us on social media

Showing 27001 words to 30000 words out of 44178 words

Chapter 10 - Uwar Agola Complete Hausa Novel by Maman Afrah

04 Jun 2026

93

Malam Nura ya ɗan zaro ido ya ce

"Ai ba na so ta kunyata ni a cikin mutane fa, ka san dai mun yj maganar shadda na saka, to ya zan yi tunda wannan mai kunnen ƙashin ta ƙona shaddar, ko dai kana ganin in faɗawa Hadiza cewar Kuluwa ta ƙona wandon?" Hudu ya zaro ido ya ce


"To wallahi idan ka kuskura ka faɗa mata ka sani yaƙin duniya ne na uku za a yi a gidanka, don gabaɗaya sai an ƙone gidan"


Malam Nura ya ce

"Mai ya sa ka ce haka?"

Hudu ya ce


"Kana ganin Hadiza za ta bar maganar nan ne, kana faɗa mata za ta tada zaune tsaye, ita ma Kuluwa ba ƙyaleta za ta yi ba, su je su ringa bala,i, gwara kake saran shuka kana kallin gatari!. Idan baka takatsantsan kishin Kuluwa da Hadiza mai zafi ne, a wannan kishin sai ka gwammace kiɗa da karatu" Shiru Malam Nura ya yi ya ce

"Ka rabu da su kowacce ka san daidai da zamanin ta nake ita ma Hadiza dama ce na ara mata, sai ta shiga gidan zan nuna mata asalin waye malam waye Malam Nura don duk wannan iyayi da juyannin da take kamar waina a tanda ba ɗorewa zai yi ba, idan har na wawuri abin da zan wawura na daga dukiyarta to da wasu daga cikin kuɗin zan yi amfani in gallo wani sabon auren!" Hudu yana kallonsa yana jijjiga kai ya ce

"Ka ƙaddara gidanka ya kama da wuta kenan, don ni yanzu haka ina hararo irin zaman da za a yi tsakanin Hadixa da Kuluwa" Tsaki ya ja ya ce


"Rabu da su daidai da su nake, kowacce ta yi tsarara kamar shayi!"

Ayarin jama,a suka biyo makaɗa suna aikin su na kaɗe kaɗe, ango sai wani jin kansa yake, yana tunano irin garar da zai kwasa idan an kai amarya ta tare, don yanzu yana tunano cewar la,asar sakaliya tana yi zai aarasa haɗe sauran magungunan da Hudu ya siyo masa a Kano ya shanye don ba zai tsaya kallon ruwa kwaɗo ya masa ƙafa ba!. Dole ya sha amarci don yana rayawa a ransa cewar Hadiza sai ta yi wata guda currr tana amarci kuma ita kaɗai ce za take zuwa turaka amma su Kuluwa sai dai suke tuƙa tuwo babu mai zuwa ɗakin miji, ya saka hakan a ransa sai dai a yi wacce za a yi duk nacin Kuluwa kuwa dole ta haƙura su barwa amarya Hadiza turaka daman ya san ita Haule baiwar Allah ba za ta ƙi amincewa ba, Kuluwa ce uwar ƴan taurin kai.


Ana tafiya Hudu yana danne dariyarsa idan ya kalli Malam Nura ya san ƙarfin hali ne domin duk da yana cika baki amma ya lura yana tsoron Hadiza ta ce ba za ta yi hoto da shi ba. Gabaɗaya mutane kowa ya kama gabansa, daga Hudu da Malam Nura sai wasu abokansu guda huɗu ne suka nufi gidan su Hadiza, don masu kiɗan ma Hudu ya ce su je can gidan Malam Nura su jira su.

Suna tsaye a ƙofar gidan abokansu suna ta zolayarsa, sai yaƙe yake musu don hankalinsa ba a kan su yake ba, yana fatan ya tsallake rijiya da baya. Wayar Hadiza ya shiga kira, Hadiza kuma ganin kiransa da sauri ta tashi daga cikin mutane don daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, damab kar jira take saboda ta yi ta kira bai ɗaga ba, yanzu kuma faɗuwa ta yj daidai da zama tun da gashi ya kira da kansa, har sauri take don ta shiga ɗaki ta kora masa kashedin kar ma ya dosk gidansu idan aka ɗaura auren nan, domin ta fasa hoton sannan ta ƙara faɗa masa cewar ya aiko da takardar saki ta fasa auren. Tana dab da shiga ɗakin Babanta wanda shigowarsa kenan sun dawo daga wajen ɗaurin auren ya hango ta ya ce


"Ke Hadiza!" Da sauri ta juyo ta ce


"Na,am Baba"

Yana kallon ta ya ce


"Malam Nura ba ke suke tsaye a waje suna jira ba, shi ne kika bar su a tsaye"

Ranta ba don ya so ba ta ce


"Yanzu zan fita daman" Ɗakin ta fasa shiga ta juyo ganin Baban ya ja ya tsaya, Bintu ma ta tashi, sauran ƙawayen ma duk suka fara miƙewa suna faɗin

"Ah lallai ashe ango ya samu ƙarasowa bari mu je" Hadiza kamar ta yi inu haka ta ji, amma babu yadda za ta yi, haka ta biyo bayansu suka fito. Baban ma juyowa ya yi yana faɗin


"Zainaba ɗakko mun kujera zan fita waje saboda masu zuwa, wanda suka rasa ɗaurin aure" Zainaba wacce take sanye da shaddar ta ta taso ta ɗakko kujerar ta biyo bayansa.

A can ƙofar gida kuwa Malam Nura ya fara zargin ko dai wani ya ƙyanƙyasawa Hadiza cewar bai saka kaya ba, gani yana kiranta bata ɗauka va, wata zuciyar kuma tana faɗa masa ko dai kiran da ta yi ta masa ne bai ɗauka ba ya sa ta ƙi ɗauka.


Kamar daga sama ya hango ta sun fito ita da ƙawayen ta, gabaɗaya tsabar kyan da ta yi ya sa kwata -kwata ya sha,afa da kayan jikinsa, kwalliya da ɗaurin ɗankwalin Hadiza sun tafi da hankali da tunaninsa, bai ma lura da yadda ƙawayenta suke rarraba idanun neman ango mai sanye da shadda kalar ta ƙawarsu amarya ba.


Hadiza kuka ne kawai bata saki ba, gashi babu halin ta masa wani rashin mutunci tun da ga Baban ta can a waje a wajen inuwa shi da mutane, bata ma san haka yadin jikin nasa yake ba sai da ta gani ido da ido ta gane cewar ashe dai wayar da ta ganshi a hoto a wayar Salmanu hoto ya gyara yadin. Hudu kuma Malam Nura kawai yake bi da kallo ganin gabaɗaya ya raja,a da kallon amarya ya manta da laifin da ya mata.


Malam Nura wani ɗan ƙaramin tari ne ya suɓuce masa, a take ya yi gyaran murya ya ce



"Amarsu ta ango, aure ya ɗauru, mun zama tsintsiya maɗauri ɗaya, na zama naki kin zama tawa buri ya cika" Wannan kalaman da ya yi su ne suka ankarar da ƙawayen nata cewar angon nata ne wannan!.

Hadiza rasa ma bakin magana ta yi ta ce


"Uhm an ɗaura" Ya washe baki tamkar mai tallar makilin ya ce


"Yau sai kwanan gidan Malam Nura" Kafin ta bashi amsa mai hoton da ta tsayar ya ƙaraso wajen domin daman yana cin abinci ne, kuma da ya ji Babanta ya ce ango da abokansa sun zo shi ne ya ƙarasa ci ya taso. Yana fitowa daga gidan camerarsa a hannunsa, Malam gani mai hoto ya ce

"To ai sai mu fara abin da ya kawo mu" Ya faɗa yana jin wani daɗi, haɗe da saka hannunsa ya gyara zaman hularsa da ta ƙara kifuwa a kan tamkar ya saka hula dara. Irin hular nan da ba a mata kari.


Abokai haka suka shiga yi wa Hadiza Allah sanya alkairi, tana amsawa kamar an mata dole!.Ƙawayen ta kuwa kowacce ta shiga danne dariyarta ganin abin da yake faruwa, sai dai ta yi alƙawarin abin da ango ya mata ba zai tashi a banza ba sai ta rama. Umarnin mai hoto suka bi wajen layuwa aka shiga yin hotuna, sai dai tun da aka yi na jam,i sai mai hoto ya ce saura amarya da ango. Amarya daman bata tsaya a kusa da ango ba da aka yi wancan hotunan, kusa da Hudu ta tsaya, duk abin da take ango yana lura da ita kuma hakan ya ɓata masa rai, da Hudu ya ga amarya ta ƙi tsayawa a kusa da ango sai ya fita daga hoto ya koma gefe .


Hadiza ta kalli inda su Baba suke ta ga hankakinsa ba ya wajen, ta ɗagawa mai hoto da yake kai camera idanunsa zai walla musu hoton ta ɗaga masa hannu ta ce


"Dakata!" Daga mai hoto har malam da idanu suka bi ta, ta mayar da kallon ta kan Malam ta ce

"Nura! Gaban Malam Nura ne ya faɗi amma ya yi kokarin dakewa ya zuba mata idanu ba tare da ya amsa ba, tana zaro idanu tare da kama ƙugu da hannu ɗaya tana wani karkaɗa jiki na rashin arziƙi ta ce

"Nura ni ka sincewa zani a kasuwa ko? Ni ka sakawa wannan yadi ka je wajen ɗaurin aurena! Bayan ka ɗinka shadda saboda ban isa ba, kuma matsayina bai kai a saka babbar shadda a je ɗaurin aurena ba shi ne ka saka wannan yadin mai kama da likkafani don ka zubar mini da mutunci, ka sa na yi wa ƙawayena ƙarya, ashe wannan dalilin ne ya sa kake ta ɗago hannu kamar katako a wajen kafinta, to ina so ka sani darajar babana ka ci na fito don haka yanzu ba sai an jima ba ka bani takardata" Kamar mai raɗa haka take faɗar maganar, abokai da kawaye basu san mai take faɗa ba kuma ta yi hakan ne don kar hankalin su Babanta ya dawo kansu, amma da sai kowa ya ji abin da za ta masa.


Yana kallon ta ya ce

"Hadiza aure ya ɗauro, kuma ki sani tamkar auren zobe ne babu saki!." Kafin ta furta wani abu Babanta ya juyo inda yana magana da wasu mutane hakan ya sa ta kama bakinta duk da zugin da zuciyarta take mata.


Malam Nura ya sake gyara zaman hularsa ya matsa kusa da ita ya ce mai hoto ya ɗauke su, ai kuwa da sauri ta matsa ta ce sai dai a masa shi kaɗai, mai hoto ya masa, Malam Nura ya waiwaya wajen Baba ya ga hankalinsu ba ya waje yanzu, da sauri ya matsa kusa da ita ya kamo hannunta tana fisgewa amma a haka aka ɗauke su tare, ƙawayenta da abokansa ganin ya kama hannunta suka shiga musu tsiya yana ɗauka ta fisge da ƙarfi ta kalli mai hoto ta ce

."Idan ka sake ka wanke wannan hoton sai ranka ya ɓaci" Malam Nura ya kalle shi ya ce

"Idan ka wanke ka kawo zan biya ka da kuɗi mai tsoka" Hadiza rai ɓace ta matsa kusa da Hudu da bai ma san ta tsaya kusa da shi ba ta ce


"Ɗaukemu da abokin ango" Kafin Malam ya juyo sai ganin hasken camera ya yi wal an ɗauki hoton, Hudu ma bai san da shi za a ɗauka ba sai bayan an ɗauka, ta yi haka ne domin ta turawa malam Nura haushi, ai kuwa ya shaƙa domin kawai ransa ne ya ɓaci, ƙololuwar ɓaci daman ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya, wato dai saboda bashi da kaya mai kyau shi ya sa ta yi hoto da Hudu saboda kayansa masu kyau ne.


Wani haushin Kuluwa ne ya tokare masa maƙoshi, idan ya tuna cewar duk ita ce silar faruwar komai. Ta kalli Malam Nura ta taɓe baki ta cewa mai hoton ka wanke hotunan duka amma banda wanda ka mana ni da ango!" Tana faɗar hakan ta juya za ta shige cikin gidan, daman ƙawayen ta sun shige, suna son su ware kafin ta shiga gidan su yi gulmar kayan jikin mijin, tana dab da shigewa gidan ya ce


"Hadiza ki jira fitowata da yamma sai kin kasa gane ni, ya maganar jere na ga baku kai kayan ba kin san dai yau za ki tare ko?" Yana faɗar hakan ko amsa masa bata yi ba ta ja ƙaramin tsaki ta shige gida, Hudu da sauran abokan suka fara takawa ana ta hira, Zainaba wacce take laɓe a wani waje ta fito, lokacin Malam Nura yana ƙoƙarin barin wajen tana zuwa ta ce


"Ango bai sha ƙamshi ba, ango da kaya marar kyau, wallahi babana ya fika iya kwalliya gwara ma Innata ta koma gidansa" Tana faɗar hakan ta zuga da gudu cikin gidan, Malam Nura ya shaƙa, musamman da ya ga Zainaba sanye da shaddar da shi ya saya, amma shi ya ƙare a tsohon kaya.


Su Hudu da suke tafiya suna hira ana dariya, fuuuuu suka ga Malam Nura ya zo ya wuce su, suna masa magana bai amsa ba, sai sauri yake kamar ya ci ƙafar kare. Haka suke tafiya yana gabansu suna bin sa a baya amma da tazara a tsakaninsu. Ko sallama bai yi wa su Hudu ba ya shige cikin gidan, makaɗan da suke ta kiɗa a ƙofar gidan ma bai bi ta kansu ba, Hudu ne suna zuwa ya sallame su, suka tafi shi ma gidansa ya wuce don lokacin rana ta yi kuma ya san abokinsa da maƙo babu abin da aka girka na auren. Don su ma abokan tafiya suka yi.

Ko sallama bai yi ba ya shiga gidan kamar an koro shi, fuskarsa sam-sam babu fara,a, hayaniyar matan maƙota da suke ta magana ce ta masa dirar mikiya, yana shigowa gidan cike da mata suna cin tuwon masara da miyar ɗanyar kuɓewa sai hira ake yi, daman Haule ce ta yi don saboda da mutane masu shigowa.


Ana ta gaishe da shi babu wanda ya kula, domin su ne da suka zo suka dakatar da shi daga ɗaukan mummunan mataki a kan Kuluwa. Kuluwa ya gani zaune a ƙofar ɗaki ita da su Mariya sun saka tiren funkaso da taushen da suka kawo mata, sai ci suka suna hira, daman bayan fitar Malam ta yi wanka ta saka kaya ta cokara ɗaurin ture ka ga tsiya, don yanzu ransa ya mata ɗan sanyi saboda ta ƙona shaddar ɗaurin aure. Yana shigowa kallo ɗaya ta masa dariya ta taho mata, hannu ta sanya ta toshe bakinta da yake cike da funkason da ta saka, fuuuuu ya zo ya wuce hula a hannu, don har lokacin yana hango kallon tsanar da Hadiza take masa a matsayinsa na sabon mijinta angon ta.

Yana dab da shiga ɗaki, Haule wacce ta fito daga ɗakin ta ta hango shi ta kwashi guɗa, amma tsabar takaici ko waiwayowa bai yi ba, yana jin matan suna cewa ango ango amma babu wanda ya amsawa yanzu hankalinsa yana kan yadda zai birge Hadiza ya kankarowa kansa guntun mutunci a wajenta da kawayenta ma da ya ga suna masa kallon ɗaya saura kwata.


Yana shiga ɗakinsa da wandon shaddar nan da Kuluwa ta ƙona ya yi tozali, ransa ya ƙara ɓaci yana tuno ranar da ya karɓo a wajan ɗinki amma yanzu ya zama gajere, gajeran ma iya cinya. Hular ya cillar a kan katifarsa. Yana rayawa a ransa cewar yau komin dare sai Kuluwa ta girbe shukar da ta yi domin ba za ta ci bulus ba. Rigar shaddar ya ɗauka, ya saka a leda, ya ɗauki gajeran wandon ya saka a ledar, wani tsohon wandonsa ya ɗauka na yadi ya saka a ciki, ya ɗakko kuɗi ya fito, fuuuuuuu yana tafiya kamar zai ci da ka, yana dab da shiga zauren Kuluwa da muryar dariya ta ce

"Ango ka sha ƙamshi" Ta faɗa cike da sheƙiyanci, domin a tunanin ta fasa auren ma aka yi tun da ta ga sai muzurai yake yi.


Tun da ya fito yake sauri, burinsa ɗaya ya ganshi a shagon ɗinki, yana zuwa ya samu mai ɗinki ya ce


"Ibra wajenka na zo"


Ibra da yake saka maɓalli a wata riga ya ce


"Ango ango, ango ka sha ƙamshi, a mini afuwa ban samu zuwa ɗaurin aure ba, ina ta ɗinkin muta... Malam Nura ne ya katse shi da faɗin



"Aure dai an ɗaura!" Sai ka bari ma haɗu a wani ɗaurin auren" Dariya sosai Ibra ya saki ya ce


"Haka ne fa mutumina, kai ai baka wata uku cikakke ba ka yi sabon aure ba!" Malam Nura bai bashi amsa ba, domin yanzu hankalinsa ya karkata ga yadda za a yi masa wandon nan ya saka kayan da yamma ya je wajen Hadiza ko ta huce ya lura in bai yi kyan nan da take naci ba, wataƙila a samu matsala, shi ya ga ko tsinke ba a kawo gidan ba, kuma ya gama sakawa a ransa yau amarya za ta tare amma kuma ya ga babu niyya wai ango ya kwana da wando.


Cike da jimantawa ya fito da kayan daga leda yana faɗin


"Ka ga dai ɗinkin da ka mini, duba ka ga yadda Kuluwa ta mayar da wandon nan, don abin kunya da mazaunai suka mutu suka bar zani wai da wannan yadin na je ɗaurin aure!" Salati Ibra ya ɗauka yana riƙe da haɓa cike da zuga ya ce


"Wannan shaddar mai tsada da kyau, shaddar da shugaban ƙasa yake saka irin ta, amma saboda kishin banza ta ƙona, amma dai ka hukunta ta ko?" Baki Malam ya dantse yana cewa


"Barni da ita, wallahi ƙafafu na so datse mata kawai dai lokacin cirewar ƙafafun ne bai yi ba amma dai na san zan cire mata ƙafafu ta koma tuƙa keken guragu" Ya faɗa yana cika yana batsewa.


Ibra ya ce


"Yanzu ya za a yi da wannan?" Malam Nura ya ce


"Faci za ka yi"

Da mamaki yake kallonsa ya ce


"Haba Malam Nura wane irin faci kuma, ai wannan ka haƙura da shi kawai, amma faci sai ka ce wata tayar keke"

Malam Nura kamar zai kai masa duka ya ce



"Ibra idan ba za ka yi ba ka faɗa mini na kai wani shagon, an ce maka sai keke ake yi wa faci"


Ibra ya ce
.

"Ina jinka yi min bayani"
,

Malam Nura ya ce



"Wannan wandon yadin nawa za ka datse shi daga gwiwa zuwa ƙasa, sai ka yanke ƙasan rigar shaddar ka haɗa ƙyallan da ka ciro a jikin riga, da wandon nan ƙonanne da wannan guntun ƙonannan wandon ka yanka mini ƙafar wandon zuwa gwiwa, idan ka yanka sai ka ɗora a kan wannan wandon yadin da ka yanke, sai ka ɗinka mini, ka ga idan na saka babu wanda zai ga saman tun da rigar ta rufe, iya ƙafafun ne za a hango, so nake in yi wankan kece raini na fita kunya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login