Follow us on social media

Showing 39001 words to 42000 words out of 44178 words

Chapter 14 - Uwar Agola Complete Hausa Novel by Maman Afrah

04 Jun 2026

92

ga sun maƙala shi a wani abu" Haule da ta ƙaraso cike da rikicewa ta ce


"Kuluwa ai bokiti ne a kanki" Kuluwa ta ce

"Haba Haule wane irin bokiti dan Allah ki taimaka a san yadda za a rabani da wannan abun na kaina, ni ba na ganin komai sai duhu, zatona ma ko matatar man aljannu ce"


Haule ta ce


"Ba waji matatar man fetur ɗin aljannu wannan bokitin naki ne baƙi" Shiru ta yi rana nazarin shin daman bokitin ta ne aljannun suka ɗauka kenan suka rufa mata amma ta kasa gane dalilin da ya sa abin ba ya ɓaaruwa.

Haule ta ce


"Ni na tasa garin yaya ta faɗa tana yaɓa bokitin amma sai ta ji shi ƙamƙa a kan Kuluwa, nan ta shiga ƙoƙarin ɓanɓarewa amma abin ya ci tura!.Tun tana ja abin yana bata mamaki har ya fara vata tsoro.

Tana kallon Kuluwa cike da tausayawa ta ce

"Kuluwa bokitin nan kamar dai tare da kanki aka yi su a mannr domin ya ƙi fita fa" Kuluwa kamar za ta yi kuka ta ce


"Dan Allah ki cire mini, yanzu idan ƴan kawo amarya suka zo sai a mini dariya fuska a rufe," ,Amsa mata ta yi na Kuluwar ta ce


"Bari in dafa ƙasa ki dage ƙarfin ki na bara ki cire mini amma kar ki bari daidai da ƙwayar gashina ɗaya ya tsige garin cirewa, kin san dai gashi shi ne adon mace" Banza Haule ta yi da ita ta shiga ƙoƙarin raba ta da bokitin amma ta ji shi gamgam idan ta ja da ƙarfi sai Kuluwa ta shiga zandama ihu tana faɗin wayyo gashin ta. Ta jima tana abu ɗaya amma ta kasa gane mene ne ya riƙe gashin daga cikin bokitin ganin abin ba na ƙare ba ne sai ta cewa Kuluwa bari ta je ta dubo Malam Nura a waje, har tana tambayar kuluwa daman bai dawo gidan ba ta ce ai ban da aljani babu wanda ya zo tun bayan fitar su, ba ta san cewa Malam ne aljanin nata ba.

Haule hanyar waje ta kama da sauri tana jin Kuluwa tana rangaɗa mata kira amma ta yi banza da ita, don tana faɗar wai kar fa ta tafi ta bar ta aljanin ya dawo ya ida nufinsa na cire mata mashaya, wai ta kama hannun ta su tafi tun da ita ba gani take ba yanzu.

Malam yana fitowa ya watsa gidan sufagilu ɗin a kwata, ya tafi wata majalisa wajen mai siyar da biredi ya zauna suna ta tsokanarsa mai zai kawo sabon ango majalisa shi da zai tarɓi amarya nan dai ya sanar da su cewar sai gobe ne tariyar. Haule tun da ta fito take ta duba shi bata gan shi ba. Tafiya ta shiga yi tana dubawa wani saurayi ɗan maƙotansu ta tambaya ya ce ya gan shi a wajen me shayi da biredi, nan ta ce ya kira mata shi. Tana nan tsaye sai ga Malam ya taho yana ta sauri tamkar bai san mai ya faru a gidan ba yana zuwa cike da nuna damuwa ya ce


"Haule lafiya dai? Ko ƴan kawo amaryar ne suka zo?" Ya faɗa kafin ya ƙaraso, Haule ta ce


"Malam mutanen ɓoye ne suka yi wa gidanka kutse wallahi suna can sun rufewa Kuluwa kai" Idanu ya zaro kamar dai ba shi ya aikata ba ya ce


"Subhanallahi, subhanallahi mutanen ɓoye kuma? Ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, wane irin rufe kai, ya subhanallah wayyo Kuluwa" Ya faɗa don ba ya ma son ya nuna cewar yana jin haushin ta a kan abin da ta masa shi ya sa ya nuna tausayawa don idan ya sake Haule da shegen wayo za ta iya hango jirginsa.


Haule ta ce


"Wallahi nake faɗa maka bokiti ne suka rufa mata, kuma cikin ikon Allah bokitin ya manne da jikin kanta yadda ka san tare aka halicci bokitin da kanta ko alamar fita ba ya yi"

Hannuwa ya tafa yana salallami ya nuna damuwa, a daidai na Hudu da ya zo zai je neman ɗansa da aka aika bao dawo ba ya gan su tsaye cike da zolaya ya ce

"Sabon ango mai tariya gobe" Amma ganin Haule duk a ruɗe sai ya ce


"Ya na ganku carko-carko lafiya dai?" ,Malam ya ce


"Ina fa lafiya kukar bulukiya a gidana" Ya faɗa yana kwashe abin da Haule ta faɗa masa ya faɗa masa, sosai a jimanta abin suka ɗunguma zuwa gidan Haule ce a gaba kamar za ta ci da ka.

Kuluwa da take zaune inda aka barta kamar an dasa ta bakin ta yana ta faman kai da komowa na addu,ar da duk ta ci nasarar cafkowa a bakin ta jin takunsu kafin su yi sallama ta sake rikicewa tunanin ta aljanin ne sallamar su ta sanya ta sauke ajiyar zuciya. Ko amsawa ba ta yi ba ta hau faɗin


"A kawo ɗauki jama,a idan aka ce a haka zan rayu ni Kuluwa aljanin nn ya shiga haƙƙina" Harara Malam ya aika mata a ɓoye don har yanzu bai ji ya huce daga abin da ta masa ba.


Hudu salati yake ba ƙaƙƙautawa shi ma Malam yana taya shi gudun a zarge shi. Hudu ya kama bokitin ya ja, amma gabaɗaya a manne yake Malam ma ya ja ya ji babu alamar zai fita, hakan ya sa cike da mugunta ya ja da ƙarfi ai kuwa Kuluwa ta zandama uban inu tana faɗin


"Da ciwo waye wannan mai ɗanyen aikin?" Malam ya sanyaya murya cike da nuna damuwa ya ce

"Waye kwa banda mijin ki Kuluwa ni ne nan damuwa na yi da wannan takunkumi da jinnu suka miki, Allah sa dai abin nan ba da shi za ki rayu b... Bai kai maganar ba Kuluwa cike da jin haushi ta ce


"A bakin ka wallahi, wannan ai mugun fata ne, wato in zauna a haka ka ji daɗin rabuwa da ni ka ce na zama makauniya, ko idan baka rabu da ni ba ma " Haule ta ce

"Haba Kuluwa kina kife kamar ƙwarya amma bakin ki ba zai mutu ba" Banza Kuluwa ta yi da ita Hudu ya ce


"Wannan aikin fa ba ƙarami ba ne kawai a kira malam me ruƙiyya" Kuluwa ta ce

"Haba Hudu ni ce fa ba aljannu ne a jikina ba, kawai ɗanyen aiki suka mini idan ka kira mai ruƙiyya zai dakeni a banza ne"


Haule ta ce

"Wannan bokitin babu mai raba ki da shi in ba malam me ruƙiyya ba, idan aka musu karatu dole su saki bokitin"


Malam ya ce


"Kawai a kira shi" Ya faɗa a zuciyarsa kuma yana ayyana Allah sa ya mata dukan kawo wuƙa ko banza ya sake rama masa. Fita suka yi suka je gidansa aka kirawo shi, tsoho ne don har ya fara ranƙwafawa ma, sai wani mayashi da yake riƙe da hiramin nasa, Hudu ya wuce neman yaron nasa don haka daga Malam Nura sai Malam mai ruƙiyya da wannan matashin. Ko da suka shigo Haule tana tsaye a gaban Kuluwa, Kuluwar ta saka hannu biyu ta riƙe ƙafafun Haule wai tsoro take ji kar fa a je aljannun suna jikin bokitin.
Ko da Malam mai ruƙiyya ya zo hannunsa riƙe da carbi mai dubu, yana zuwa da ya gama zagaya Kuluwa buɗar bakinsa ya ce


"Aljanin me a cikin bokitin shi ne ya zama tsani tsakanin kanta da bokitin idan ma ba a yi a hankali ba yana iya raba kanta da jikin wuyanta" Kuluwa fitsari ne ya ƙwace mata jin wai aljani a jikin bokitin da yake manne a kanta da kuka ta rushe tana faɗin
"
"Malam ka yi addu,a su fita daga jiki, wallahi ban san inda zan saka rayuwata ba in suka rabani da kaina ba na so in mutu in bar Malam Nura ya rayu da amarya su soye ni ina can kwance cikin ƙasa!"


Malam Nura a zuciyarsa ya ce


'Ƴar baƙinciki sai mun yi soyayyar kuwa da zamanki da tafiyarki babu abin da za mu fasa' A fili ya ce


"Kuluwa ko kina raye ko kina mace ai zaman Hadiza matsayin matata babu fashi tun da an ɗaura aure, ki ji da wannan abun na kanki don idan har aljannun nan basu yarda an ɓamɓare miki wannan bokitin ba, ni fa kaina zan sa a yi yekuwa a gari, jama,a su zo a kwashe ki a baro a kaiki can dokar daji bakin ruwa, ƴan ruwa su ɗauke ki don ba za mu rayu da rabi da rabi ba domin kin zama rabi aljan rabi mutum" Baki ta buɗe za ta yi masifa duk da maganarta idan ta yi amsa kuwwa take kasancewar kanta a cikin bokiti yake. Malam mai ruƙiyya ne ya kai hannu yana mai yin bismillah ya ranƙwashi saman bokiti sannan ya saka hannu ya ja amma ya ji babu alamar fita.

Yana kallon Haule ya ce


"Babu wani ɗan icce ƙarami haka?" Da sauri Malam Nura ya ce


"Akwai wata ƙatuwar sanda ta dukan ɓarawo da na ajiye a ɗakina" Kuluwa wacce ta san girman sandar cike da ƙaraji ta ce
"Mai za a yi da sanda? Ana batun icce kana batun sanda, kaima malam mai ruƙiyya ina laifin ma ka ce a baka tsinken kwakwa tun da yanzu dai ni ce ba aljani ba kuma duk abin da za a yi ni zan ji a jikina"


Ɗan rakiyar malam ya ce


"Ai dole sai an basu tsoro in ba haka ba ba za su fita ba" Wani yawu ta haɗiye tana jin babu daɗi Malam Nura wani daɗi yake ji a ransa ya ɗakko sandar ya kawo, Malamin ya ce tun da shi ya manyanta ba ƙarfi ne da shi ba, shi ɗan rakiyarsa ya karɓa ya buga a jikin bokitin, amma Malam Nura ya ce
"Malam ita mace fa a ko ina mijinta ne a gaba ka bari na buga mata ina kishin wani ya mata ab... Kuluwa ta katse da faɗin

",Malam kar ka yarda babu wata soyayya da kishi tsabar haushina ne da yake ji wallahi kana bashi sandar nan ba iya bokiti zai rotsa ba har da kaina zai raba a biyu"


Haule ta ce
"Kuluwa mene ne haka ana son nema miki lafiya" Tsaki ta ja ta ce
"Ai kin san akwai takun saƙa tsakanina da shi"


Malam mai ruƙiyya ne ya karɓi sandar ya shiga karanta ayatul kursiyyu da falaƙi da nasi yana tofawa a jikin sandar sai da ya gama sannan ya nannaaɗe hannun rigarsa ya buga sandar Kuluwa ji ta yi kamar a kanta ne aka buga, Malam yana ci gaba da karanto addu,oi, yana tofawa yana buga sandar lokaci zuwa lokacj ganin yadda take zabura kamar mai farfaɗiya ya sa yake danne dariyar muguntar sa tun da shi ya san mene ne ba aljannu ba ne.


Bokitin ya tsaye a biyu amma ƙasan yana manne da gashin, aka yi aka yi ya fita amma ya ƙi, sai da aka duba ta inda aka tsaga domin yanzu tana iya ganin mutane ma tun da an fasa bokiti daga saitin idanunta.

Kuluwa jin Mama mai ruƙiyya yana jan bokitin tamkar wanda yake jan gashin ta ta ce


",Malam gashin nan fa ana gama cire mini bokitin nan zan yi fakin ɗinsa da ribbon ka ga kuwa ka bishi a hankali" Takaici ne ya ishi Haule na maganar da Kuluwar take ita ana so a ceto ta amma ita tana ta gashi duk don saboda ta birge mijin da ba ita ce a gabansa ba.


Malam iya yinsa ya yi amma ya kasa fitarwa Kuluwa bata ankara ba ta ji ya ce


"Kun ga dai duk na cire bokitin gefe da gefe kawai iya tsakiyar kanta ne bai fita ba, shi kuma kamar ma tare aka yi shi da gashin kanta don haka mafita da shawara ɗaya a kira Usaini wanzam mai aski... Tun kafin ya gama magana Kuluwa wacce gabanta ya bada sautin rassss jin an ambaci wanzam ta yi saurin faɗin


"Malam mai ruƙiyya aska zai ara maka ka yanke bokitin?" Malam mai ruƙiyya ya ce


"A,a ni da ba aikina ba ne riƙe aska, shi dai zai so ya saka askar ya askr gashin kanki shi ne mafitar...Tsaye Kuluwa ta miƙe tana faɗin babu wanda zai masa aski babu mai raba ta da gashin kanta ko ziri ɗaya!"

Malam mai ruƙiyya da ɗan rakiyarsa suka fara yi wa Malam Nura sallama za su tafi, Kuluwa har ta kama hanyar ƙofar ɗaki ta shiga ta je gaban mudubin ta ta duba ta ga babu alamar zai fita sai gata ta fito da sauri ta ce


"Haule na shiga uku za a mayar mini da kai babu maraba da na Malam Nura" Haule ta yi tsaki ta yatsina fuska ta ce
.
"To ai sai ki zauna a haka" Tana faɗa ta yi hanyar ɗakin ta, Malam Nura ya ce
"
,Malam tun da fita za ku yi mu je fita zan yi nima na je masallacin isha,i daman amarya sai gobe za ta tare, Kuluwa ta ji daɗi da aka ce sai gobe amarya za ta tare, tana ganin za ta ci karenta babu babbaka tun da ta yi gyaran jiki, duk da tana jin haushi ta so a ce a gaban amarya za ta shige ɗaki da angon ta cusa mata haushi.


Kuluwa ganin za a barta da rufaffan kai ba don ta so ba ta ce ta amince a kirawo shi. Tun da suka fita ta zauna tana garƙama kukan za a raba ta da gashin ta, gashi aljannu ne tana son zazzagin su da musu Allah ya isa tana tsoron sakamako ya biyo baya.




Suna fita Huale da ta fito daga ɗaki ta shiga bata baki, har tana tambayarta mai ya sa ta saka wandon malam amma ta mata banza tana ta kuka, don ta so take taje gashin nan tana cusawa Hadiza haushi, duk da an ce Hadizar tana da gashi kasancewar mahaifiyarta buzuwa ce.

Haule tana gefe zaune a kan kujera zuciyarta cike da jimami kawai sai ta ji Kuluwa tana faɗin

"Wayyo gashina, wayyo zan zama warewa a cikin matan gidan nan, wata ma da gangan za take tamayar fita kitso don in ji haushi" ,Haule tsabar takaici banza ta mata saboda ita a ganinta ita da ta haɗu da iftila,in aljannu ai murna za ta yi da za a raba ta da bokitin.


Zuwa jimawa Malam Nura ya dawo yana rafka sallama shi da Usaini wanzam, Kukuwa ta tashi tsaye hannuwanta biyu a saman guntun bokitin na kanta tana kuka shaɓe -shaɓe Malam Nura a zuciyarsa ya ce
'Ke da Allah ya taimake ki ma ba ƙafafu na cirw miki ba, ai gwara gashi sau dubu in kika ɗaura ɗankwali babu mai sani amma aka mayar da ke gurguwa ai kin tagayyara.

Haule ce ta shinfiɗawa wanzam tabarma bayan ta amsa musu sallamar ta gaishe da shi, ya zauna da ƴar zabirarsa (Jaka) Mai ɗauke da kayan askinsa. Kuluwa tana ta ɓare baki ta zauna a gabansa ya cw Haule ta kawo kujera saboda ya ɗan yi sama, haka ya zauna a kujera yana faɗin

"Sannu baiwar Allah,, Allah ya tsayar a haka, wataƙila ma tun askin suna ba a saki miki aski ba amma gashi yau larura za ta saka a yi, Allah sa haka ne alkairi... Kuluwa ta ɗago tana banka masa harara ta ce

"Ina alheri a aske gashin matar da ba iya kaɗai ba ce a wajen mijin ta, wato tana da kishiyoyi, gashin nawa da nake ta cancanawa ina alkin ta shi, ni ko da aka haifeni ba a mini aski ba saboda gashina bashi da yawa mahaifiyata ta ce a bar min amma yanzu za a aske" Usaini wanzam yana fito da kayan aikin ya ce

"Ƙaddarar kenan" Daga haka bai sake cewa komai ba, Malam Nura yana gefe zaune a kan wata kujerar yana danne dariyarsa ya san da a ce ta san shi ne ummul aba,isin wannan lamarin da mai raba ta da shi sai Allah, duk da yana gudun ɓacin rana watarana amma ya san dai ba za ta taɓa ganowa ba.

Bokitin ya ɗan ɓaɓɓalle, ya ɗakko ruwa da sabulu ya ɗan goga a gaban inda bai riƙw ba da yake tsakiyar kan ya fi riƙewa. Babbar askarsa mai kaifi ya saka ya shiga ɗaiɗaye gashin Kuluwa yana zubowa ƙafa tana kallo sai da ya aske duka amma ban da gefe da gefen Kuluwa ta kai hannu ta ji an mata rantal (ƙwal kwabo) A tsakiyar kan ta taɓa inda bai aske ba duk bai fi faɗin yatsan hannun ba ta ce

"Wannan ɗin fa"

Wanzami ya ce

"Wai idan kin yi ɗaurin ɗankwali sai kike fito da shi kin san gashi adon mace ne!" Kuluwa kamar ta yi kuka ta ce

"Saimka ce wata ƴar bori, za ka bar mini wani gashi kawai ka ƙarasa cirewa" Haka ya cire Haule tana ta jera mata sannu, yana gamawa ya saki kan Kuluwa tana zaune ta shafa da hannu ta ji wayam ta ɗago ta kalli wanzami, ta kalli Haule ta ce

"Haule ki riƙe sannunki tun da ba naƙuda nake yi ba!" Tana faɗar haka ta tashi fuuuuu ta yi hanyar ɗaki, dariyar da Malam Nura yake ta riƙewa ce ta ƙwace tun lokacin da ya yi ido huɗu d akan Kuluwa a hasken farin wata, har ƙyallin haskena farin watan ake gani a jikin kan, tana daidai shiga ɗakin nata ya tsagaita dariyar ya ce

"Kuluwa mai ɗakin tsaka, ɗakko masa kuɗin askin sa" Harara ta juyo ta dallawa Malam ya ce

"Ga ki da riga da wando da askekken kai sai kika yi kamar namiji" Banza t masa ya fita shi da mai askin yana ta dariyae mai askin yana nuna masa rashin dacewar hakan, a fili ya nuna yankarɓa a zuciyarsa ya ce

" Ai baka san wace ce Kuluwa ba shi ya sa'

Haule ma tsintsiya ta sanya ta share gashin ta kwashe ta naɗe tabarmar tana ɗan murmushi ta san da a ce yau ita ce tsautsayin nan ya faɗawa da Kuluwa sai ta yi ta ƙyalƙyalar dariya.

Kuluwa tana shiga ɗaki ta cire kayan ta canja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login