Chapter 1 of 6

MAI DAKI Ilimi Da Talauci BOOK 1 BY Nana Haleema | Hausa Novel

ÿþMAI DAKI...

NA

HAJ. HAFSAT C. SODANGI

(Mrs. Yunus Abdullahi Dabai)

1

MAI DAKI... (1)

"auwa'u Idris."" Nayi maza na"

Lmike tsaye tare da amsawa

saboda tun kafin ya kira sunana dama na

"riga na harhada littattafaina, na zuba su a"

cikin Jakata.

Ya waiwayo ya zub. mun ido sannan ya

ci gaba da kallon dogon littafin da ke ajiye

"a kan teburin gaban nashi, wanda yake"

littafin sunayen dalibai ne wadanda suka

"biya kudin Makaranta, da kuma wadanda"

ake bi bashi.

Ya ci gaba da kiran sunayen daliban

daya-bayan-daya duk wacce ya kira kuma

to zata tashi.

Sai da ya gama kiran sunayen ne sannan

"ya waiwayo ya kalle mu ya ce, ""To"

tsayuwar me kuma ku ke yi a nan?

Cikin sauri kowacce ta fara nufar inda

"yake, tana fada mishi uzurinta, wata ta ce"

"""Malam Babana yayi tafiya ya ce na bada"

"hakuri kafin ya dawo, sati mai zuwa."

7

"Wata ta ce ""Malam ni Babana ya ce ayi"

"hakuri kasuwa ce tayi gardama, zuwa wata"

mai kamawa. Cikir sa'a kuma duk wacce

ta kawo uzurinta yana sauraronta tare da

ba wata dama.

Sai dai ni kam ban ma doshi inda yake

"ba, don kuwa a wannan karon ban san me"

zan cewa Malam Ali ba.

Ya waiwayo a karo na biyu ya sake

"kallona ""To ke tsayuwar me ki ke yi a"

nan? Ko kuwa kina da wani abin da ki ke

son fada ne?

"Na ce, ""A'a a hankali ya ce ai ke ko ma"

me za ki ce mun a wannan karon babu

abinda zai sa na saurare ki.

Ni na dade ko ma na ce tunda nake a

cikin Malamtaka ban taba haduwa da

dalibar da ke cin garabasar karatu irin naki

"ba. Haba! Wane irin abu ne wannan?"""

Na rataya Jakata na juya tare da kokarin

"fita a cikin ajin, cikin sanyin jiki lokacin"

8

"da naji an kira sunana cikin sauri, na amsa"

tare da juyawa.

Sadiya Tanimu ce dalibar da ke zaune a

kujerar da ke bayana.

"""Ba ni littafina da ki ka karba dazu."""

Na dora Jakata a kan bencin da ke

gabana na fara kokarin binciko mata

littafinta na darasin English (Turanci) da

na ara a safiyar yau don kwafar rubutun da

aka yi a lokacin da bana nan.

"Malam ya ce, ""Uhum, ba ka ji abin ba,"

zat tafi miki da littafi. Allah dai ya

sauwake irin wannan abu to wai idan uba

bai tsaya yaga ya ilmantar da ya yanshi a

wannan zamani ba me zai yi mishi ne na

gata kuma?

Da irin wannan wahalar banzan da ki ke

yi na kullum kina cikin wadanda ba su

biya kudin Makaranta ba dama aure aka yi

miki ki ka huta don ban san yadda za a yi

kici jarrabawar gama Makaranta ba a irin

wannan tambelen da karatunki yake yi.

9

Ni halina da Hausawanmu kenan wai ba

za su tsaya suga sun biyawa ya'yansu

"kudi sun yi karatu ba, amma idan an tashi"

aurensu sai kaga mata ta sunkuya

karkashin gado tana zaro 'yan marofiya da

"masu hannun katako."""

"Yan aji suka kwashe da dariya,"

yayinda na mikawa Sadiya littafinta na

kama hanyar barin ajin.

"""Ki hutar da kanki kada ki dawo, don"

kuwa sai dai idan ban gan ki ba ko a ina ne

kuwa za a kore ki gida.

In tsaya cewa maganar Malam Ali bata

"6ata mun rai ba ma to zance ne, kuma ku"

"san kullum haka yake yi mun, idan yazo"

ajinmu koran kudin Makaranta ba zai bar

"ni da takaicin koran kawai ba, sai ya bini"

da bakaken maganganu.

Ni kuma ba abin in yi zuciya na ce na

daina zuwa ba tunda idan na ce haka ba

"zan yi karatun ba kenan, don kuwa ba biya"

mun din za a yi ba.

10

Duk wadannan takaicin da nake sha

"lada ne akan a ce an fara jarrabawa, ranar"

da duk wani dalibi yake. dokin zuwanta

saboda lokaci ne na nuna bajinta da kuma

gwaji kan abin da aka koyar da kai da

kuma gane irin fahimtar da ka yi. ab

Sai dai ni takan zo mun ne cikin

"tsananin fargaba, don kuwa rana ce ta babu"

"sani babu sabo, idan har ana binka ko da"

kwandala ce daya to babu ko shakka za a

kore ka gida.

Na rinka bin Malamai kenan ina kamun

kafa wadanda za su tabuka mun wani abu

ma wadanda babu wani taimako da za

su yi mun ba.

Wani lokaci ma kaga an bar wasu sun

shiga ajin jarrabawar wata kila saboda su

"din kudin zango daya ake bin su, ko kuma"

wasu sauran canji da ba su gama biya ba

N1 kuma a hana ni ko wani Malami ya

tausaya yasa baki sai ka ji Malam Ali yana

11

cewa ai ko an barta ta shiga da alkawarin

biya ba biya zata yi ba.

Ana binta bashin da ya kai na shekaru

"uku, don haka barta nan kawai ta karaci"

zamanta ta tafi.

Idan har akwai wani abu da nake burin

"yin shi a rayuwata, to kuwa karatu ne, sai"

dai ina ji ina gani abin yana nema yafi

karfina.

"Babana ba shi da karfi, ba zai iya biya"

"mun kudin Makaranta ba, haka nan bai"

ciyar da gida ba. Har a yanzu da muke mu

"bakwai 'ya'yan Mamanmu, shi din"

albashinshi a wurin da yake aiki bai fi

Naira dubu goma sha biyar ba a wata.

"To da me ya ciyar damu, da me ya biya"

mana kudin Makaranta da kuma sauran

hidindimu na rayuwa? Ta kai ma shi

kanshi ya hakura da karatun kannena maza

"ya saka su a sauran wurare irin su, koyon"

dinki da kuma kanikanci don ganin ya

12

maida hankalinshi kan nawa karatun ni

kadai amma abin ya gagara.

Don kuwa da albashin nashi kafin wani

watan ya zagayo an lamushe shi a bashi.

Dan sauki-saukin da muke samu to na

sana'ar dinkin da Ummanmu take yi ne

inda wani lokaci takan samu tayi cikon

cefane har ta adana mana dan abinda muke

hidima da shi na sallah.

ldan shekara ta zagayo babban abu guda

daya kuma mai muhimmanci a wurinmu

gaba daya shi ne muna da kwanciyar

hankali da nutsuwa tare da addini mnai

yawa a cikin gidan namu.

Don haka zama muke yi cikin

kwanciyar hankali da nutsuwa.

Na kamo. hanya don komawa gida

"zuciyata cike da kunci, don kuwa wani irin"

nisa ne a tsakanin gidanmu da Makarantar

wanda kuma a kullum da kafa nake zuwa

nake kuma dawowa.

13

Sannan a mafi akasarin lokuta na kan

"tafi ne ba tare da nayi karin kumallo ba,"

don kuwa na kan kasa hakurin jira don

kada nayi latti.

Tafiya zan kuma tafi ne ba tare da ko

sisi ba har sai na dawo ne zan ci abincin da

na samu an yi.

Ina karyo kwanar unguwarmu na hango

Abdussamad zaune kan dakalin shagon

askin dake makwabtaka da gidan su.

"Wani irin faduwar gaba na samu, nan"

take na juya na koma ta daya hanyar duk

kuwa da cewar ita din tafi nisa zan iya

cewa kusan kullum aka koro ni kudin

"Makaranta, to sai na ganshi matukar ba"

komawa tashi Makarantar yayi ba.

Na kane da niyyar na share shi nayi

"kamar ban ganshi ba, don haka na"

sunkuyar da kaina na ci gaba da tafiyata

har na dan gota su.

14

"Sai naji ya ce ""Barka da dawowa, ranki"

"shi dade. Cikin wayancewa na ce ""Af, ai"

ban ganka ba ne. 9 Tare da dan murmushi.

Ya mike ya nufo ni tare da kakkabe

wandonshi yayinda yake karasowa inda

nake. Ya dan tabe baki tare da cewa.

"""Da dai kamar ban sanki ba ne ki ka"

"fada mun haka, to dana yarda."

Na fara gaishe shi bayan mun faraa

tafiya yana amsawa. Na ceAshe baka

koma ba har yanzu?

"Ya ce, ""A'a na koma jiya dai na sake"

dawowa da yamma saboda wani yajin

aikin da Jami'o'i suka fara satin can da ya wuce.

"Na ce, ""Cabdijam! Abin dai babu dadi"

"Ya ce, ""Eh to, kusan hakan, kin san"

yanzu babu ranar komawa dai kenan

"halin yajin aikin kasar nan, idan ba"

matukar sa'a muka ci ba sai mukai

watanni biyar nan gaba zaune Gwamnati

15

bata dauki wani kwakkwaran mataki a kai ba.

"Tunda su babu ruwansu, don talaka ne a"

matsala tunda mu ne muka cika

"cikin Jami'o' i kasar, su nasu suna can Turai"

"suna karatun cikin kwanciyar hankali, mu"

kuma muna nan muna gwagwagwa.

Karatun da zai dauke ka shekaru hudu

idan ba matukar sa'a kayi ba sai ya kai ka

shekaru shida kana yi ba ka gama ba.

Shi yasa ai tun yanzu muke muku

addu'a komai ya gyaru kafin zuwan naku

"lokacin, sai dai banga alamar ke za ki yi"

"nisa ba, nafi zaton aure za ki yi da alama."

"Na kalle shi na ce, ""Uhum! Sai anjima."

Na shiga gida saboda karasowar da muka

yi kofar gidan mu.

Akwai mutunc1 mai yawan gaske a

"tsakanina da Abdussamad, don kuwa duk"

"shariyata da mutane suke magana akai, shi"

kam muna gaisawa har ma mu dan yi hira

saboda shi ko na wuce shi to zai yi mun

16

magana har ta kai ma ba na ma iya wuce shin.

"Makwabcinmu ne sosai, haka nan"

Babana da Babanshi suna mutunci sosai a

tsakaninsu.

"Nayi sallama na shiga gida, yan"

kananan kannena ne suke wasa a tsakar

gida da alama Umma ta hana su fita zuwa

kofar gida ne.

"Tasi'u da Sabi'u, a guje suka taho suna"

rige-rigen karbar Jakar Makarantana. Na

mikawa Tasi'u saboda nasan Sabi'u ba iya

"dauka zai yi ba, na kuma yi mishi dabara"

ta hanyar daukanshi na cilla shi sama na

cabke.

Don kada ya saka mun rikici muka

"karasa shiga dak1, suna yi mun hirar su ta"

shirme Umma tana zaune a kan tabarma a

"tsakar dakinta, yanka take yi na atamfa."

"Na tsugunna nayi mata sannu da gida,"

ta amsa ba tare da ta tambaye ni dalilin

17

"dawowana ba, don ta riga tasan abinda ke"

dawo da ni a irin wannan lokacin.

"""Shiga ki tube kayan Makarantarki ki"

"saka na gida, ga dumame nan sai ki diba"

"kici. Na ce, ""To."

Sai dana gama cinye dumamena daa

muka ci tare da su Tasi'u sannan na sake

hada kwanukan da sukalalacena wanke na

"sake gyara gidan, na wanke bayan gida"

sannan na sake dawowa wurin Ummana

"ce, ""Umma za a dora wani abu nea"

wuta?

"Ta ce, ""Dan saurara dai tukuna muga"

"dawowar Auwalu ko?"" Na ce, ""To."" Na"

mikena shiga dakina dake tsakar gida na

dauko littattafaina na Makaranta don na

dan yi bita.

Har karfe daya na rana shiru Auwal bai

"dawo ba, hakan ne ya sani sake tashi na"

shiga cikin kicin dinmu na dauko dan

sauran garin kwakin da ke ajiye don na

jika musu.

18

Na kawo sugar na saka na mika musu

cokala sannan na dauki buta don yin

alwalar sallar Azahar.

"Haka rayuwarmu take a gidanmu, kusan"

kullum muna kwanciya ne da daddare ba

tare da mun san abinda zamu ci idan gari

ya waye ba.

Haka nan idan safiyar tayi muka samuu

"muka karya kumallo, to ba ma sanin abin"

da zamu ci idan rana tayi.

"Saukin abin ma shi ne, yanzu Auwalu"

ya kawo karfi yana kuma matukar

taimakawa.

"Auwalu shi ne wana da nake bi, shi ne"

kuma da na fari a wajen Iyayenmu baki

daya.

A yanzu haka makanike ne a cikin

"babbar kasuwa, sai dai har yanzu ba"

"kwarewa yayi ba, amma yana matukar"

samun' alheri ba kadan ba.

19

Saboda sa'ar da yayi na haduwa da

"shugaba na kwarai, illa ko yau ma shi ne"

ya shigo da cefane a hannunshi

Don haka na shafa fatiha cikin sauri na

fito na karbe shi.

"""Akwai itace ne? Na ce, ""Bari na"

"duba. Na leka kicin din na ce, Akwai,"

amma dai babu yawa.

"Ya juya ya fita, yayinda ni kuma na fara"

"kacaniyar dora girkin, ya sake shigowa da"

itace kai biyu a hannunshi ya zuba tare da

miko mun Naira ashirin.

"Ki bai wa Tasi'u ya sayo miki maggi,"

"ni na manta ban siya ba. Na ce, ""To."" Ya"

juya da niyyar komawa wajen aikinshi.

Tuwon masara nayi tare da miyar

"kubewa danya, saboda ita na gani a cikin"

"cefanen, ta kuma yi dadi da yawa na tuka"

don mu samu na dumamen safe.

Na kwashe na adana na kowa tare da

rufewa na janye itacen na dora ruwan

20

wankana a kan garwashin sannan na

kawowa Umma nata.

Sai da nayi wanka na yiwo alwalar

"sallar La'asar, don kuwa zan iya cewaa"

yanzu dabi'ata ce hakan saboda kusan

kullum abincin yamma muke yi.

Na idar da sallar La'asar na jawo

kwalbar maina da Auwalu yake kawo mun

mai kamshi.

"Duk da ba wani mai tsada ba ne, shafa"

shi yana sani naji ni'ima saboda kamshin

shi.

Na murza hoda da dan kwalli na jawo

atamfata na daura sannan na fito nazo 1in

da Umma take na zauna don naci nawa

abincin.

Muka dan fara hira wacce yawancinta

"akan Makarantata ce. Tace ""Sai ki"

"yawaita addu'a, Allah ya zabar miki mafi"

"alheri a ciki, ko karatun idan zai yiwu."

21

ldan kuwa ba mai yiwuwa ba ne to sai

kiyi aure a kai ki dakinki kema ki nutsu ki

zauna a wuri daya.

Babban burin Iyayena bai wuce na

"ganin nayi karatu ba, ko da kuwa wacce"

irin wahala za su yi don ganin hakan.

Hakan ne yasa da Umma tayi mun

wannan maganar gabana yayi matukar

"faduwa, ta soma hakura kenan ko ya ya?"

"Na ce, ""Umma aure fa ki ka ce?"

"Ta ce, ""Eh shi na ce idan karatun ba zai"

yiwu ba menene amfanin zaman gidan

tunda kin riga kin isa auren.

Shi ma Babanku ai ya nga ya fara

hakura tunda naga an kwan biyu ba tare da

yayi maganar Makarantarki ba.

"Jikina yayi matukar yin sanyi, dafin"

maganar Umma sai dai ban ce mata komai

"ba, don ba maganata ba ce tunda ba zan"

iya tuna ranardas wata magana

makamancinyar wannan da ta danganci

aure ta hada ni da ita ba.

22

Aunty Hauwa'u kizo in ji Yayan su

Lubabatu. Na waiwayo na zuba ma

"Tasi'u ido, na ce ""In zo fa ka ce?"

"Ya ce, ""Eh shi ne ya aiko ni gashi nan"

"ma a zaure. Umma ta ce ""To ki ka sani ko"

wani abu zai tambaye ki?

"Na ce, To bari naji naga bai taba"

"aikowa gidanmu a kira ni ba."" Hijabina na"

sako na fita kofar gida inda yake tsaye.

Wata gaisuwar muka sake yi yana

"kallona ""Ya na ganki fuskarki wata iri?"

"Na dan yi murmushi na ce, ""Ai da ka"

"kirani ne baka ji yadda zuciyata tayi ba, sai"

da gabana ya fadi.

"Ya ce, ""To da alama dai ba ki da"

"gaskiya kenan."" Na ce, ""A'a rashin"

gaskiyar me? Na dai dauka wani abu ne ya

faru kuma ka san ban saba hakan ba. 99 Ya

"ce, ""Eh to, ai komai dama farashi ake yi"

ko?

Ua juya inda su Tasi'u da Sabi'u suke

harkokinsu ya mika musu Naira ashirin ya

23

ce a siyo biskit suka karba tare da fallawa

da gudu don sayowan.

Ba wai don yazo wurina ko kuma kofar

"gidanmu ba ne yasa shi yin hakan, dama"

can dabi'arshi ce inda duk ya gan su to zai

saya musu ko biskit ko cakulet.

"Ya waiwayo inda nake ""To ya ya"

"yanmata ya karatu? Na ce, To mun"

"gode Allah, ni yanzu kina aji nawa ne?"""

"Na ce, ""SS1."" Ya ce, ""Dama nayi zaton"

"kina tafiya ne tare da su Luba, sai dai a"

hanya za ki tsaya tunda ban ga alamar kina

mayar da hankali tare da bada himmar yin

"karatun ba."""

"Na ce, ""Me yasa ka fadi haka? Ya ce,"

A'a na gane kamar aure ki ke so.

Wayancewa nayi tamfar maganar bata bata

mun rai ba.

Kuma kafin na samu amsar ba shi sai na

hango Babanmu yana tahowa daga wurin

"aiki kuma yake na ce ""Ni zan shiga gida"

ga Baba nan ya dawo.

24

Har kasa Abdussamad ya tsugunna ya

"gaida Babana, sannan ya wuce ni kuma na"

shigo gida ina yi mishi barka da zuwa.

Ban wuce dakina ba abincin Babanmu

na dauko na kai mishi dakin Umma tare da

ruwa. Yana sanye da kayan gida da alamar

har ya cire na aikin shi sannan na sake

mishi sannu da zuwa na wuce dakina.

Washegari da sassafe kamar kullum sai

"da na hada mana abin karyawa, kunu da"

dumamen tuwo sannan na saka uniform

dina na dauko hanyar Makaranta.

Kamar daga sama ina shiga ajinmu

"kafin na zauna sai ga Malam Ali ya shigo,"

"ya ce ""Maras zuciya, ai dama nasan yau"

ma sai kin dawo shi yasa na bugo

sammakon zuwa ajin naku don na gani.

Ba kuma zan bar ki ko darasi daya ki

"samu ba. Juya kawai ki tafi."" Na juyo na"

"kamo hanyar dawowa gida, yau kam ta"

lungun unguwarmu na biyo don kaucewa

idon Abdussamad.

25

Ban tsaya yin komai ba kan yar

yamushashshiyar katifata na hau na

kwanta ba zan iya cewa ga iyakacin abinda

"Zuciyata take gaya mun ba, illa iyaka dai"

"kawai nasan babu mamaki, ni din ba zan"

samu cikar burina ba ne a rayuwata shi ne

"na ni din na zama Nos, wato Malamar"

jinya.

Nayi kuka har na gaji ban san sanda

"barci ya dauke ni ba, na dai farka ne naji"

ana kiran sallar azahar.

Na mike tare da yin salati da na tuna ko

"abincin rana ban dora ba, tunda idan ina"

gida ni ce mai yi. Na fito cikin sauri na

samu har Umma ta riga ta sauke tana rabo.

"Shinkafa da wake ne, da mai da yaji."

Nayi mata sannu sannan na shiga bandaki

don kama ruwan in alwala.

Har na gama hidimomina na gida yau

ko waiwayon littafan Makarantana ban yi

"ba, don kuwa na fara fidda rai abinda"

kwata-kwata ban saba yi ba kenan.

26

Dabi'ata ce kullum Zan yi bitar

littattafai na koda nake da matsala wajen

biyan kudin Makaranta ni din ina cikin

daliban aji da suke da matukar kokari.

Tunda har Malamaina ma sun shaida

"hakan, to amma ya zan yi? Malam Ali ya"

"taso ni a gaba, bana kuma ganin laifinshi"

tunda aikinshi yake yi.

Duk wadannan tunanina ne kafin

"wayewar gari, don kuwa tsintar kaina nayi"

"da fara shirin Makaranta, har na fito tunda"

sammako nayi ina yiwa Babana sallama

wanda a yau din zan riga shi tafiya.

"Ya ce, ""Ke Hauwa'u ba Ummanku jiya"

ta ce mun satin nan kaf idan ki ka je

Makaranta koro ki ake yi ba?

"Na ce, ""Eh haka ne Baba."" Ya ce, ""To"

amma a hakan ke gara miki kiyi ta zuwa

ana korarki? Maganar gaskiya shi ne nayi

niyyar baki wani abu ki kai Makarantar

taku.

27

To sai dai mu mamatsalar wurin aikin

mu yawa ce da ita tunda wannan watan shi

ne wata na wajen uku da ba a bamu

"albashi ba, amma daga zarar an bamu wani"

abu zan ba ki ki kai musu ko da babu yawa

ne. Sai ki ba su hakuri yau din idan kin

"je."""

"Na ce, ""To Baba."" Na fito daga gida ina"

tafiya tare da tunanin maganar Babana ni

ba abin in ce mishi ai yanzu ta kai ma ko

saurarona basa yi ba.

sli Babu amfani tunda ba da gangan yake

Rin biya ba.

Na shiga aji na zauna a darare ganin har

"karfe tara tayi Malam Ali bai zo ba, sai na"

waiwaya bayana inda Sadiya Tanimu ke

zaune.

"Saidai ban ganta ba, don haka na ce wa"

wacce suke zaune tare rmai suna Zubaida.

DunsDon Allah dan bani aron littafinki ná

Chemistry na dan fara kwafa kafin a

tashi.

28

Ta kalle ni ta dan tabe baki tare da

"girgiza kanta kafin ta ce, ""A'a a gaskiya ba"

"zan miki karya ba, ba zan iya ba haka"

kawai azo a kore ki na manta ki wuce mun

da littafi.

Bari dai wacce ta saba baki tazo don

naga itama kamar ke karatun ba damunta

"yayi ba, bambancinku kawai ita ana biya"

"mata kudin Makaranta."""

Na juyo na ci gaba da wasu sabgogin ba

tare da na tsaya bai wa Zubaida amsa ba.

Ba a ko kai mintina biyar ba bayan nan

sai kawai Malam Ali ya shigo. Tun kafin

ya fara kiran suna na mike na kamo hanyar

"dawowa gida, zuciyata cike da kunci da"

6acin rai.

Har naZO zan shiga gida sai naji ana

"kirana,Abdussamad ne. Na tsaya ya"

karaso inda nake.

"Hauwa'u kenan, yau ma kin kasa zama"

ne kiyi karatun har zuwa lokacin tashi?

29

Wani gululun bakin ciki ya taso ya

"tokare ni, wai wannan me yake nufi ne?"

Na dago kaina da niyyar ba shi amsa.

Sai dai na kasa saboda dama kiris nake

"jira, don haka da na lura kawai kuka zai"

kubucemun sai na shige gida ba tare da na

sake sauraronshi ba.

Ina shiga gida wurin Umma na wuce na

"durkusa, kuka na kama yi babu"

"kakkautawa, ba tace mun komai