Chapter 2 of 5

FUREN ZUCIYA Fure a Sarkafe By Nasreel R.L. | Karanta Cikakken Labarin

smiling takeyi ear to ear kamar wanda take watching comedy show, dajin sallamar Miral tayi saurin daga idanunta ta sauke ma Miral wani mugun kallo kafin a kule tace  dalla malama jiranki akeyi ubanwa kika ajiye kike wani sallalabewa agurin nan . Da sauri Miral ta karasa gaban ummi dan nesa da ita ta tsugunna cikin sassanyar muryanta so soft kamar ana shafa maka feathers tace  Kiyi hakuri Ummi, wanka na tsaya yi. ina kwana . Sannan ta juya ta kalli matar dake opposite din Ummi kamar zata gaisheta, kamar wanda ta tuna wani abu saita"

fasa ta dago idanunta daidai yanda zataga Ummi.

Yarfa hannu Ummi tayi alaman ta gaidata sannan ta juya idanunta a kasa ta gaisheta. Bata ansa taba kawai binta da ido tayi dama Batayi tsanmanin zata ansa ba dan kusan duk kawayen

Ummi banda kallon kaskanci babu abunda yake hadasu.

Sunkai wajen 5 minutes amma ji Miral tayi kamar ta shekara goma a gurin har gwiwoyin ta sun fara sagewa tarasa meya kawota nan tunani takeyi ta tashi ta tafi ne? dan tanada aiki saidai ganin Ummi bata ce ta tashi ba yasa ta hadiye confusion dinta ta zauna. Chan kuma saiga

muryar matan  tashi tsaye . Ta fada a harshen turanci. Mikewa Miral tayi still idonta a kasa.

Ummi tace ta cire hijab na jikinta a sanyaye ta cire tanajin kirjinta na dukan uku uku jin yauma ansata cire hijab. Me hakan yake nufi? Dan tabe baki matar tayi tanabin jikinta da kallo sama da kasa kamar wani product dazata siya. Alama tayi mata da ta matso kusa dayake idanunta na kasa batagani ba. Tsawa Ummi tayi mata akan ta dago idanunta ta matsa da sauri jikinta na kyarma ta dago sannan ta matsa inda matar take ganin ta kara hade rai yasa ta kara matsawa

dab da ita.

Kare mata kallo tayi tas sannan tayi mata alaman ta matsa. Ummi ne ta tambayeta koh zata iya tafiya ta gyada kai dan haka ummi tace ta wuce ta jeta fara aikinta. Da sauri ta dauki jilbab din ta fita cikin hanzari zuciyarta na bugawa tana sauke ajiyar zuciya dan Allah Allah dama takeyi

tabar palourn.

A bangaren Ummi kuwa bayan Miral tafita ta juyo ta kalli matar gefenta cikin tausasa murya

tace  Miss kamila zatayi kuwa? Naga kamar batayi miki bah idan abunda zamu iya chanzawa ne sai musan yanda zamuyi tunda wuri .

"Dan kyabe baki matar takarayi tana wani mutsika face a gadarance tace  Kin tabbata bata san namiji bah? Karki bani wahala kinsan inda hakan zai kaiki . Da sauri Ummi tace  A a na tabbatar, dukda yarinyar tayi abubuwa a baya da bazasu furtu ba amma banda bin maza"

intabbatar miki ma ko saurayi bata taba yi ba yarinya ce sosai .

"Dan jim Miss ayra tayi sannan tace  shekaranta 18 kikace? Kin kuma dauketa na shekara biyu yanzu bayan barin gidan iyayenta, kin tabbatar bata taba sanin namiji ba, sannan kuma kince tayi munanan abubuwa kafin su koreta? Yarinya yar shekara 16 kenan a lokacin? Metayi ne"

haka? .

"Dan jan nunfashi ummi tayi sannan tace  Ina tabbatar miki Miss kamila yarinyar nan 18 take, sannan a shekara sha hudu na dauketa, abunda tayi duk babu wanda bai dagama hankali ba dan babu mai zaton yarinya kamarta zatayi, a tana sheru 13 tana shirin shiga 16 tadawo"

makaranta ranar& .. .

"Katse ta Miss arya tayi tace  banason ji, munada bayanan ta already babu abunda yake a boye a gurinmu, sannan duk abunda tayi matsalar tace. gobe zansa azo a duba mun ita idan abunda kika fada gaskiya ne. Idan har akaga cewa she is pure toh zamu aiwatar da plan din. Zaki kawo mun ita ghair muaddal, daga nan zan dauketa, daga ranar dana dauketa ban sanki ba, baki sanni ba Halima, bamuyi maganar yarinyar nan dake ba, bakuma wani zaiji zancen nan ba."

Bakuma zaki saka a ranki cewa zata dawo ba dan ta tafi kenan . Gyada kai Ummi tayi sannan

ta cigaba.

" sannan naga ciwo a goshinta, face dinta a kumbure yakuma faffashe, banason sake ganin wani tabo ko ciwo a jikin yarinyarnan bama anfani da masu ciwo, sannan a bata abinci mai gina jiki zansa a kawo supplement dan she s too skinny for my liking . Tana gama fadin hakan kuma ta tashi ta dauki channel bag dinta. Ansawa da ok Ummi tayi tabude baki kamar zatayi magana saikuma ta fasa tadan sunkuyar dakai tana wani dan smile kamar wanda ke son yin wani abu"

yakasa.

"Dan juyowa Miss Kamila tayi ta kalleta cikin wani annoyed voice tace  kyautar ki sai bayan komai ya tafi daidai, idan an tabbatar mun gobe gaskiya kike fada toh ranar da kika danka mun yarinyar nan a ghair muaddal ranar abunda kike buri zai cika, sannan koda kuwa kin chanza ra ayinki mun riga mun ansheta, bama chanza magana, sannan idan kikayi yunkurin tona maganar dake tsakaninmu toh lallai kinsan waye mu, bama fadan hukunci, saidai hukuncin mu"

"nada tsanani, wanda sukayi yunkurin yaudaran mu basu shaba ."

Tana fadin hakan tayi wucewarta ta fita ta exit. Har waje Ummi ta rakata zuwa garage inda wata Arniyar bentley take a parke ga wasu bodyguards su biyu a gefen motar. Bata ko kalli Ummi dake mata sallama ba daya dage cikin bodyguards din ya bude mata kofar baya ta shiga sannan ya shiga mazaunin driver dayen bodyguard din ya shiga gaba suka ja motar da gudun

gaske suka fice.

Sauke wata nannauyar ajiyar zuciya Ummi tayi sannan ta juya ta shige gida ranta fes dan tasan

yau burinta ya cika.

"A bangaren Miral kuwa aikinta ta fara yi dukda takasa cire tunanin abunda yafaru tun daga daren jiya zuwa yau. Har yanzu maganar Ummi nacewa zasu taimaki juna take tunani. A iya saninta babu abunda zataiya taimakon Ummi dashi, kudi Allah ya bata, yaya bataso tun bayan data samu hanat tace bazata kara ba, kuma ta ishe ta dabakinta ta fada batason kari, tanada miji mai sonta, ga kawaye da yan uwa masu sonta. Babu wani abu datake da bukata da zata iya"

batashi. Dan haka sosai abun ya girgiza kuma ya razana kwajwalwar ta.

"Gakuma wasu sabbin questions din dabata da ansar su. shin waye wannan mata datazo yau? Meyasa Ummi zata bukaci ganinta takuma sanyata cire hijab matar ta kare mata kallo? Kodai siyar da ita Ummi zatayi ne?. Dan dariya ne ya kubce mata a tunanin datayi saurin denashi sakamakon zafi daya ziyarce ta a fuska dan marikan jiya har yau kamar sabo take jinsu. Babu yanda za ayi Ummi ta siyar da ita. Bayan Ita Ummin da kanta ta dauketa dukda batada niyya da farko? Kuma itadin dukda ba sonta takeyi sosai ba ai yayar mamanta ce, aunty dintace bazata"

taba yin hakan ba. Barta dai da yi mata azaba amma baza ta taba siyar da itaba.

"Wanke hannunta tayi tareda karasa jera plates din data wanke a cikin dishwasher, dan haka Ummi tasata duk wanke wanke da akeyi a gidan ita takeyi idan tagama wankewa saitasa a dishwasher yakara wankewa. Tasan salon kawai wahalar da itane dan babu wasu ayyuka a"

gidan masu aiki keyin yawancin su.

"Wucewa tayi tafara gyaran kitchen din a hankali dan duk wani motsi datayi saitaji ribs dinta na ansawa, addua kawai takeyi Allah yasa ya warke da kanshi dan tasan ba kaita hospital za ayi ba indai ba gani sukayi ciwon na neman kasheta ba. Saida ta gyara shi tsaf sannan ta nufi wani mini fridge da ake ajiye leftover abinci da ba a sawa a main fridge, cikin sa a taga wani plate na scrambled eggs dadan yawa da sausages wajen 5 cikin sauri kamar wanda za a kwace mata ta"

dauko shi ta juyeshi a cikin wani rubber container dan ba a barinta taci a plates na yan gida.

Straight dakinta ta nufa ga yau da alaman ana rana dukda bata leka waje ba a yanda dakinta

yawani dau huci kamar oven ga babu window bare tasamu wani ventilation wani dum ta shiga kawai ta zauna kan yagalgalallen bedsheet dake shinfide akan simintin dakin.

A hankali tasa hannu tafara cin eggs din saida ta gama ci sannan ta dauki sausages din suma taci. Alhamdulillah tayi tana godema Allah atleast yau tasamu abunda zata kai bakinta kafin ta fita sharan waje. Tunawa da bata dauko ruwa ba yasata sauke ajiyan zuciya tun batayi wani komai ba harta gaji. Dan kwanciya tayi tana maida nunfashi tunane tunane na dibanta saidai jin yanda hucin zafin dakin ya rufeta yasata mikewa tareda daukar container ta fice daga dakin dan

yau bazata iya zaman dakin ba a cikin zafin nan gwara ko kitchen ne taje ta zauna tasha iska.

Koda ta koma kitchen saitaga har chefs sun fara preparations na lunch dan haka bata yi kokarin zama ba kafin Headservant ta shigo tayi mata bala i akan kitchen ba gurin zama bane. Abun

"shara ta dauko kawai ta nufi waje, fili ne babba sosai ga wani open garage a karshe mike idan"

ka shigo gate din gidan da motoci guda 4 a parke Mercedes biyu sai lambo biyu daya pink daya black. Body guards ne guda hudu biyu a gurin gate biyu kuma suna zagaye babu wanda ya nuna ya ganta cikinsu sai guda daya dake bakin gate daya kureta da ido tunda ta fito. Yi tayi

kamar bata ganshi ba yanda tasaba dan idan da sabo ta saba.

Daga gurin motocin tafara sharowa irin dogon tsintsiyan nan da ake using dinsu a tsaye. Ko rabi batayi ba tafara nishi tana gumi dan wata irin rana ake kwallawa kamar ana dafata. ji tayi kamar ta cire hijab dinta saidai sanin wannan mutumin nanan yasa mata ido bazai barta ta iya cirewa

ba dan a hakan ma idanunshi kamar ya chinyeta.

Da kyar tanayi tana zama ta huta tasamu ta karasa saidai batakai har gurin gate dinba ta kwashe adan nesa ta shige cikin gida. Nishi takeyi da karfi da karfi duk nunfashi daya sai kirjinta ya ansa. Ta jike sharkaf da gumi sai diga takeyi. Straight dakinta ta wuce a kofar data shanya rigan data cire ta tsaya tadan huta sannan ta ja rigar data kusa gama bushewa ta fita tayi part na masu aiki. Dayake kusan sun gama aiyyukan su banda masu girki dan haka a palour ta

gansu wajen su 3.

"Gaishesu tayi a hankali basu ansa ba babu ma wanda ya juyo ya kalleta kawai ta shige toilet din. Daya daga cikinsu ne wata yar budurwa cikin daga murya tace  kada ki taba mana ruwan heater dama, ba tsoho ya siya ba . Tana fadan hakan kuma Suka wani kwashe da dariya harda"

tafawa.

"Tajisu sarai saidai tayi kaman bata jisu ba, dukda sosai abun ke damunta saidai tasan yes da gaskiyar su tsohonta bai siya ba, dan a cewarshi mutuwarta shine babbar kyautar da zata mishi. Haka ta kunna ruwan sanyi dan da tayi niyyan tayi wanka sosai saidai ganin bazata samu ruwan zafi ba kuma tana tsoron mura kawai ta dauraye gumin jikinta ta sanya rigarta ta wanke"

wandata cire tareda jilbab din sannan tafito.

A kofar fita part din sukayi karo da wata yarinya da bazata wuce 17 years bahaka. Yar head servant ce dukda ita ba aikin takeyi ba kawai dai takanzo ta yini a gidan ta tafi da dare. Sauke kanta Miral tayi tana dan rabeta ta wuce. Saurin riko hannunta khalisa tayi tana dauke da murmushi akan cute arab face dinta tadan jawota baya tabude baki zatayi mata magana kawai Miral ta fincike hannunta idanunta suka wani yi ja sukayi ciki ciki tareda cikowa da hawaye

tafara girgiza kai tareda yin baya baya daga khalisa kamar taga aljana.

"Danne kunnuwanta tayi hawaye na gangarowa daga idanunta bakinta na rawa tana furta  no no, ban aikata ba wlh, Layla ki fada musu gaskiya Layla , Layla . Tarinka maimaita hakan a dimauce khalisa ta matsa baya tana zazzaro ido batasan metayi ba, waye kuma Layla? Saurin shigewa ciki tayi sauran maids din dake zazzaune a cikin palourn suka juyo suna kallonta dayan cikinsu kawai ta fashe da dariya harda rike ciki tana fadin  Jama a akwai mahaukata fa a gidan"

"nan, Layla dake ake fah ."

Ta fadi hakan tana nuna ta gefenta da alamun itace Layla. Dan zazzaro idanu tayi tana nuna

kanta kafin ta kwashe da wata shegiyar dariya tana fadin  Ni Layla menayi? Yaushe nazo gidan

nan ko wata daya banyi ba shegiyar yarinya ko magana bata taba hadamu ba. zata fada uban me nayi mata kuwa yau . Da fadin haka ta mike a zabure sauran biyun na dariya kamar zata kashesu suka mike suka bita suka nufi Miral datake zaune a kasa ta janye gwiwoyinta zuwa

kirjinta ta kifa kanta akan gwiwoyinta sai surutai takeyi tana girgiza kai.

FUREN ZUCIYA.

Flower of the heart.

By Nasreel R.L.

A hausa love story& & .

Chapter 3;

"Su Layla basu karasa inda takeba Khalisa tayi saurin tsayawa a gabansu tayi musu tsakani, cikin dan daga murya tace  Yane badaku takeyi ba, babu ruwanku da ita . Wani kallo wanda ke bayan Layla tayi nata sama da kasa kafin tace  ke yarinya matsa mana anan kafin bakinki yayi"

jini banason rashin kunya anan niba sa ar yinki bace .

Kallo khalisa tabisu dashi tareda folding hands dinta a kirji tana kara gyara tsayuwanta alaman bafa zata matsa ba. Gaba Layla tayo kamar zata daketa saikuma dayar dabata yi magana ba tun tuni saidai dariya tayi saurin riko ta tana mata kallon warning. Layla sarai tagane me take mata warning akai. Tasan idan har ta taba khalisa toh lallai yau head servant zata nuna musu masifarta na da ba komai bane dan wlh saita sa an kore su. suda samun wani aikin kuma sai

"wani ikon Allah, sannan ana biyansu sosai anan bakuma wani aiki sukeyi ba."

Kamar bazata hakura ba dai ganin ita zata chutu hakan yasa kawai ta juya tana ballawa Khalisa

harata aranta tana fadin zasu hadu da Miral saita gyara mata zama.

"Khalisa ganin sun koma a hankali ta tsugunna dan nesa da Miral sannan cikin tausasa murya tace  Miral kiyi hakuri, bansan mena miki ba ni kawai kawance nakeso muyi naga bakida kawa ko daya, amma yanzu kiyi hakuri bazan sake ba idan ma wani abu nayi miki. tashi ki tafi daki"

kada wayannan marasa mutuncin suyi miki wani abu .

Kamar Miral batajita ba dan still girgiza kanta takeyi tana furta abubuwa dabama zaka gane komai daga cikinsu ba. Takai wajen 5 minutes agurin kafin ta dago kanta da fuskar ta tayi sharkaf da hawaye idanunta sunyi ja fatar face dinta shima yayi ja kamar tomato. A sanyaye ta mike idanunta a kasa ta dauki jilbab da rigar daya fadi kasa ta fita daga part din. Dakinta ta wuce ta shanya kayan a jikin kofa sannan ta shige kawai ta kwanta kan bedsheet din tana

shasheka tareda maida ajiyar zuciya.

Ko 15 minutes batayi ba bacci ya dauketa bata tashi ba sai washe gari wajen karfe 6am na

safe. Wani irin ciwo jikinta kemata batasan ko dan tun jiya da rana take bacci bane kokuma dan

cewa kan cement ne da bedsheet kawai take kwance? Mika tayi sannan ta mike aranta tana

fadin yau babu zafi sosai saikuma ta tuna maybe dan safiya ce rana bata kwallo ba.

Mikewa tsaye tayi tareda jujjuya wuyanta daya sage kamar an buga mata katako a gurin. Wata yauwa ne ta ziyarceta cikinta yayi wani kara tanajin hanjin cikinta kamar an daure mata su.

Saurin daukan jilbab daya bushe akan kofa tayi ta zura hannunta nadan rawa kwata kwata

batajin kwari a jikinta.

Kitchen ta nufa ta tarar chefs na cooking breakfast kanshi natashi taji yawunta yawani tsinke. Kara cikinta yakara yi da sauri ta fita daga kitchen din ta wuce waje ta zauna a terrace dan saita jira sun gama idan da ragowa da ba ayi serving ba saita dauka. Wajen 10 minutes tayi amma

jitake kamar yunwar zata kasheta idanunta sun dan cicciko da kwalla.

"Kamar tayi ihu takeji, a rayuwanta ta tsani yunwa. Zata iya jure komai amma banda yunwa duk kankantan yunwa saita gigitata. Jin an bude gate yasa ta juya don ganin waye, ganin khalisa ne yasa tayi saurin dauke kai tafara wasa da siraran yan yatsunta dake daukeda farata masu kyau"

daidai hannunta.

"Tanajin yanda ta karaso har inda take saidai bata dago ba harta tsaya dan baya da ita kadan idanunta a kanta. Dan sauke ajiyan Zuciya Khalisa tayi sannan tace  Hello, Miral . Tana fadin hakan kuma ta cigaba da tafiya zuwa cikin gidan. Dan dagowa Miral tayi jin tabude kofa a tunaninta ta shige tana kallon kofar kuwa suka hada ido. Taso tadauke kai saikuma tadan yi dan guntun murmushi tareda daga mata hannu tanajin nauyin abunda tayi mata jiya dan ita"

batamasan tayi bah.

"Smile din Khalisa ta mayar mata sannan ta shige tareda rufe kofa. Miral ta juya ta cigaba da wasada yatsunta tana tunane tunanen yanda rayuwa ta kawota nan. Ba uwa ba uba babu ya babu kanwa. Ba kawa babu maisonta, toh inma tanadasu mezasu kara mata banda ciwo?"

Ciwon da har abada bazai taba warkewa bah? Nunfashi ta sauke tareda mikewa ganin rana

yafara dukantanta gari yafara zafi ta shige ciki.

"Kitchen ta shiga wanda ta tarar da head servant a ciki tana ba maids orders din ayyukan da za ayi, alamun chefs sun gama kenan. Kallo head servant ta wurgama Miral tareda dauke idonta tana yamutse fuska. Babbar matace zatakai maybe 50 years tamada bitch face irin me tsorata yara ga wani black lipstick datasa a bakinta da kwalli daya dambaro batada tsawo ko"

kadan ranta a hade kamar mala ikar mutuwa.

Sunkuyar dakai Miral tayi sannan ta nufi side din kitchen da ake wanke wanke ganin har an fitoda plates da mugs da sauran abubuwa na wankewa yasa ta nade hannun jilbab din ta wanke komai tas tas sannan ta sakasu a dishwasher ya gama ta kashe lokacin head servant da sauran

maids din duk sun tafi yin ayyukan su.

Fridge din leftovers ta bude saidai yau babu sa a dan babu koh faranti a ciki tawani waro ido da

nandanan yaciko da kwalla tai narai narai da fuska kenan yanzu bazata samu breakfast ba?

Kodai ta duba main fridge ne? Saurin girgiza kai tayi tuna