Chapter 2 of 10
AISHATUL MUBEENA Dama Ta Biyu by Miss Hafcy
asibitin garin dayake akwai wanta yana aiki a
asibitin,,,Basu dade ba se ga mota ...nan nan da
nan taja sukai asibitin
Emergency aka shiga da ita aka shiga bata kulawa
ta gaugawa,,Ma'u se kuka takeayi dan ita ganni
take kamar mutuwa zatayi,,Khadija ce ke
rarrashinta
Bayan dan lokaci likita ya fito yana share
gumi,Ma'u tana kuka tace "likita ya take? Ya jikin
nata?" Likita ya ce a gskiya yanzu bamu gano
komai ba,amma dai yanzu zamuyi mata test na
aika lab,Se kujira kan result din ya fito" Ma'u tana
kuka tace "toh likita Allah yasa muga alheri,,"
Yace ameen ya fice,Ma'u kukan nata ya k'aru
sosaii; khadija itama se ta fara kuka dan suna
bata tausayi sosaii, Tace "kiyi hak'uri maman
mubeena komai yayi zafi maganinsa Allah,Inshaa
Allah zata tashi cuta ba mutuwa bace !" Ma'u ta
share hawayenta sannan tace "Toh khadija Allah
yasa amma se nake ganni kamar bazata tashi ba!"
Khadija tce"A'ah insha Allah zata tashi,Bari naje
can gida sena na sanar dasu iya su san abinda
ake ciki"
Tana isa kai tsaye gidan iya ta shiga bayan sun
gaisa ta sanar da iya,Abun mamaki iya se ta nuna
damuwarta ba laifi ta sakko hijabi tace suje
asibitin,sannan tabar sako da a nemo mal sule a
fada mai halin da'ake ciki A kuma fada mai ya
samesu a asibiti!
Har suko isa ma'u kuka take se rarrashinta suke
yi, a dan lokaci nan duk ta fita hayyacinta
idanunwanta duk sun k'ank'ance saboda kukan
datakeyi,
Suna zaune se ga likita ya fito a razane ya kallesu
yace............................
Share
AISHATUL MUBEENA 30-40
[12:19AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS
[30]-[35]
Likitan ya kallesu yace "ku biyoni office!" Ma'u ko
takalmi bata sa ba ta bishi da sauri suma su
khadija suka biyota
Bayan sun zaune likita yaja numfashi sannan yace
"ki nutsu ki fada min al'momin da ta fara kan
ciwon yayi tsanani, Ma'u ta share hawayenta
sannan tace "Ta fara da ciwon kai da dadewa
amma jefi jefi in na bata magani takanji
dadi,sannan takance kafarta na ciwo,to shine yau
tun safe abin yayi yawa tana ta kuka,Ga zazzabi
ga ciwon kafa" Likita ya share guminsa yana
jinjina kai
Likita ya maida numfashi sannan yace "Ana wa
yarinyar rigakafin Cutar poliomyelitis (polio)
kuwa?" (Gaban ma'u ya fadi)"A'ah ba'a taba yi
mata ba" Likitan a fusace yace ' u see,kun ganni
(ya daga murya) Duk k'ok'arin da gwamnati
takeyi akan yak'i da cutar polio tana turo mutane
su bi gida-gida dan yin rigakafin cutar,Kuna
ina????Meyasa baku basu damu su mata ba,Dan
nasan tabbas suna zuwa amma kuk'i basu
dama,,,meyasa???!!!"" Ma'u ta fashe da kuka
"Wlhy likita BA LAIFI NA BANE laifin babanta ne
ba yadda ban yi dashi ba amma sam yak'i,," likita
yace "Toh shikenan yanzu kun janyowa yarku,A
iya gwajjin da mukayi.....Am sorry to say,,
kwayar cutar polio ya riga ya gama bin
jikinta,kuma kafarta ya taba "A YANZU HAKA
YARKU TA RASA KAFARTA TA HAGU,ZEYI WUYA
TA SAKE TAKAWA DA KAFAR !!DOMIN KWAYAR
CUTA TA FI K'ARFI A KAFARTA!!!
Innalahi waina ilaihi raju'n Khadija ta shiga
maimaitawa iya kuwa kasa magana tayi,,Ma'u
kuwa sulalewa k'asa tayi sumamiya!! Da sauri
sukayo kanta nurses suka zo da gado aka dora ta
Likitoci sun dade akanta,,Anci sa'a kuwa mal yazo
shima yadan damu ba laifi ,Se wani kumbure-
kumbure yake Likita ya fito yace," ku biyoni
office",a gigice suka bishi ya kallesu cike da fushi
yace "wai ku dan Allah meyake damun kune,?
Matar nan tana da hawan jini amma baku taba
kawo ta asibiti an gwada taba,Yanzu jinin ta ya
hau over,,Allah ne yayi kiyaye da wlhy zata iya
samun mutuwar barin jiki stroke! Suka zaro ido
gaba daya banda mal,khadija tace "likita wallahi
bamu sani ba,bata taba fada mana ba "likita ya
nuna mal" kaine mijinta,, Ya galla masa harar
sannan yace "Eh nine ya akai yi ne?" Likita a
fusace yace "Amma wlhy baka da tausayi
sam,wacca irin zuciya ce dakai?? Ka yi sanadin
nakasa yarka sannnaan kana nema ka nakasa
matarka ko ka hallaka ta har lahira,Kai wani irin
mutum ne?
Mal ya kalleshi kallo na rainin hankali sannan yace
"Kaine bakada hankali,Ni nasan abinda
nakeyi,kuma ba ruwanka da harkar
gidana,mutumin banza kawai'' likita yayi
murmushi "Ni bazan tsaya cacar baki da kai ba
saboda ni bana cacar baki da jahilai irinku!
[12:19AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [1:33PM, 12/02/2016] Miss Hafcy:
◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS
[35]-[40]
Mal yana nema ya cakumi wuyan rigar likita da
sauri iya ta tare shi" Wlhy ka sake kayi fada dashi
sena maka baki mara hankali kawai' Ya kalleta
yayi tsaki sannan ya fice daga asibitin,likita
girgiza kai yayoi cike da takaici ya cigaba da yi
musu bayani
An sanar da yan gidansu ma'u mamanta da
goggo ne sukazo se kuka sukeyi da kyar aka
lallasheshu,,,Ma'u kuwa bata dan fara dawowa
daidai ba se datayi kwana2 a kwance Aishatul
mubeena kuwa tana can an ware mata gadon ta
daban likitoci ne kawai ke zuwa dubata
Ma'u ta dan murmure,Tana shan magugunata
sosai sannan likita ya mata nisiha sosai aka ta
kwantar da hankalin ta,Addu'a ce ya kamata ta
dinga yi,,Yawan damuwar datakeyi ne yasa ta
hawan jini!
Bayan ta dan warware hankalinta na kan
yarta,,Hakan yasa tace suce wajen likita ya musu
bayani,,bayan sun shiga,Ma'u cikin sanyi murya
tace "Likita yanzu ba wani magani Da za'ayi mata
ta sami sauk'i kafarta ta dawo daidai tunda naji
kace kafarta Ta riga ta shanye"
Likita ya nisa sannan yace "Malama ma'u kiyi
hak'uri,Hanya daya da za'a iya maganin cutar
shine....... RIGAKAFI! wanda ku kuma bakuyi wa
yarku ba! Amma cutar polio in har ta riga ta
kama mutum BATA DA MAGANI!!,Amma yanzu
muna bata painkillers wanda zasu maganin
wannan ciwon kai da zazzabi,da kuma ciwon
kafar,,Kuma Alhamdulilah yanzu ta fara samun
sauk'i,,,,Sannan batun kafarta na fada muku cewa
bazata iya tafiya ba due to weakness na
kafar,Yanzu zamu bata WHEEL CHAIR in ta k'ara
girma kuma se ta fara amfami da FOREARM
CRUTCH,lokacin kafarta ta dama ta k'ara
kwari,Dan kunsan itace me lafiyar kuma yarinya
ce,Kafar ba wani kwarin kirki tayi ba" Ma'u ta
fashe da kuka yayin da mamanta,iya,Goggo,Da
khadija suka Jin jina kai cike da tausauyi,,(Dan
yanzu iya ta saduda ta gane laifinta,Har kuka tayi
da tana bawa ma'u hakurin abinda tamata a
baya)
,Likita ya cigaba "Ba kuka zakiyi addu'a zaki ki
kuma godewa Allah dayasa nata yazo da
sauk'i,Dan akwai wanda take ja musu
paralys,Amma ita ai kafarta ta hagu kawai ta
taba kuma zata iya komai dinta nrml,Nan da sati1
zakiga ta dawo daidai se dai kawai kafarta ta
hagu da ta tabu ne!" Ma'u da murya kuka tace
"shikenan likita,Allah ya raya ta,ya kuma sa
k'arshen wahala kenan! Gaba ki daya sukace
ameen,,
Mama(maman ma'u tace) " Ma'u kiyi hak'uri ki
fawala Allah komai,Yana tare dake kinji kiyi
hak'uri duk da nasan kinayi ki dora akan wanda
kike yi"Ma'u ta rungume mama "toh mama insha
Allahu" khadija ta runtse idonta se hawaye
tausayinsu duk ya cika mata ciki...
BAYAN SATI 1
A yau aka salame su,Gwamnati ce dama ta dau
nauyin duk wata dawainiyar sh,,Da zasu tafi aka
basu wheel chair da kuma forearm crutch,kyauta
shima,se godiya suke yi,,AISHATUL MUBEENA
kuwa ta warware har dariyar ta takeyi,,Amma
rannar data koma normal se data kalli ma'u tace
"Umma,kinga kafata yadda ta dawo,A haka zatai
ta zama?" Ma'u ta fashe da kuka a hankali duk da
tana k'ok'arin kada ta gane ta dage tace "a'ah
aishatul mubeena zata warke yi hak'uri,," Tayi
murmushi tace "toh umma"
A rannar da suka koma yan'uwa da abokan arziki
suka dinga zuwa dubiya,kowa ya zo se yaji
tausayin aishatul mubeena,ita kuwa dayake da
yarinta haka take dariyarta tana harkar ta ba
ruwanta,ita a wayonta ta zata kafar tata zata
warke ne kamar yadda mamanta ta fada mata,,,
Mal ne ya shigo gidan yana masifa 'Bazan iya
bafa,baze yiwuba,Ayi ta zagina a gari anacewa
inada ya gurguwa! Ma'u a fusace tace "Mal ya
isheka fa,Waye ya ja mata? Ba kaine ba,Azzalumi
kawai,Me bak'ar zuciya! Ya juyo da mamaki "lallai
ma'u kin rik'a,Amma saurara kiji,Yau din nan
zanyi maganinki!" Ma'u wani murmushin tak'aici
tayi ta tana kallansa,,Ina sauraronka,,
Yayi wata dariyar mugunta sannan yace............
Comment as:
Publish Preview
No comments:
AISHATUL MUBEENA 45-60
[12:22AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [45]-[50] Likita ta
ganni tsaya a jikin mota yana murmushi,,kasa
magana tayi ta tsaya kawai tana kallansa cike da
mamaki,,Dayaga shirun yayi yawa se yace
'Malama ma'u ya kika tsaya anan k'araso mana"
jiki ba kwari ta karaso ya durk'usa ta gaishe shi
ya amasa tare da murmushi sannan yace "nasan
zakiyi mamakin ganina" Ta gyda kai alamar eh Ya
cigaba"Hak'ik'anin gaskiya tunda na ganki ke da
yarki nake tausayin ku,inason taimakon ku kuma
Cikin ikon Allah Se akamin transfer na koma
Asibitin aminu kano,Shine kwanaki na kawo ziyara
garin nan se nake tambayarku se ake cemin ai kun
rabu da mijiniki,,To gskia bazan boye miki ba tun
daga nan nake jin sonki a zuciyata daga baya
shine na yanke hukunci nazo na nemi amincewarki
dan Da aure nake sanki ba da wani abu ba! Ma'u
tayi murmushi "Toh likita zanyi shawara insha
Allahu nagode kwarai,Se dai kuma bansan sunan
ka ba", Likita yayi murmushi sannan yace "
Sunana DR MUHAMMAD AMEEN" Ma' u tace
"Toh Dr nagode,' yayi murmushi sannan yacr
"Inason zanyi magana da magabatanki in har kin
amince dan na dinga zuwa wajen ki" tace
"Bakomai Insha Allahu ba matsala" yace "Masha
Allahu amma nagode da wannan tarba me kyau
da kika min,, ma'u tace bakomai ai,,,Yace "ina
yartawa take? Ma'u tace tana ciki bari na fito
maka da ita" yace toh ya bude motarsa ya dauke
wata leda sannan ya kulle motar Ma'u bata dade
ba se gata da aishatul mubeena tana turota,Ita
kuwa tana murmushi tace "Ina wuni" yace lafiya
lau my daughter, Ya jikin naki? Tace da sauki,, Ya
mik'a mata ledar da kyar ta karba ma'u tai ta
godiya Sun dan yi hira Kadan yana bata shawara
akan yadda zata dinga kula da aishatul mubeena
dagabaya sukai salama Bayan ta koma gida tayi
wa mama bayanin komai mama ta ji dadi ta kuma
ce zata fada wa kawaunan ta da kuma yaya basiru
Abu kamar wasa zancen har ya mik'a yau Dr yazo
da magabatansa bayan sun Gaisa kawu na katsina
(Kawun su ma'u) yace,"Zamu iya sanin ka sosai"
dr yayi murmushi yace "Nidai sunana DR
MUHAMMAD AMEEN inada mata daya da yaya
guda hudu : Ameen(Abba) ,Abdulhafeez,Se
Husna da Aisha,,Ni baban likita ne yanzu a aminu
kano ina zaune a kano da iyalaina unguwar
lamido cresent,,Wayan nan kuma (ya nuna
kawunansa) daya k'anin babana ne dayan kuma
k'anin mamana ne wannan kenan Kawun katsina
yayi murmushi "Masha Allahu"Yanzu zamu kirawo
ita ma'u muji daga gareta kaga tunda bazawarace
in ka amince yau se a daura auren,Amma se munji
daga bakinta "dr ya gyda kai "toh bakomai" Yaya
basiru ne yaje ya kirawota kanta na k'asa ta
gaida su cikin girmamawa suka amsa ,,Kawun
katsina yayi mata bayanin komai sannan yace
"Yanzu yardar ki muke neman in kin amince se a
daura aure!" Gaban ma'u ya fadi ashe dai da
gaske ne ita bata zata abun ya kai ga haka ba har
ana cewa za'a daura auren yanzu,,Ta sunkuyar da
kanta tace..................
Like · 4 · Repl
Share
[12:22AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆◆ NA MSS HAFCY
®ONLINE HASA WRITERS [50]-[55] Tace "To
shikenan Allah ya zaba mafi alheri"Dr wani dadi
yaji a ranshi,Tana gama fadan hakan ta fita daga
falon,,kawun katsina yace "To Masha allahu tunda
ta amince yanzu se muje masalaci tun dan naga
ana kiran sallar la'asar bayan an idar se a daura
auren,ince dai a shirye kuke(Ya kallesu)? Dr yace
eh mal muje" Cikin K'ank'anin lokaci aka daura
auren Muhammad ameen da Asma'u (ma'u) akan
sadaki dubu10,Ango yayi alkwarin wani satin ze
aiko da Kayan lefe se ta tare.. Tuni dama ya
sanar da matarsa Hajiya Hadiza,Dayake tana da
mutunci sosai kuma ba ruwanta addu'ar fatan
alheri tayi masa,Ta kuma ce inshaAllahu zasu
zauna lafiya,Indai ta bangarenta ne baza'a samu
matsala ba Yau ne tariyar ma'u,Bayan tayi yar
walima a gidansu,,Ita kadai aka kai gidan mijinta
banda Aishatul mubeena a cewar mama insunyi
sati 1 se akawota,Dan dr da kanshi yace ze dauke
ta ya dau nauyin komai dinta kamar yarsa ta
cikinsa Gida Masha Allah me kyau da shi bene ne
sama da k'asa,Hajiya hadiza tana sama yayinda
ma'u ke k'asa falo ne dan madaidaici da kuma
dakuna biyu se kitchen da bandaki da dan tsakar
gida ,,Dan yaya basiru da su kawun katsina sunyi
mata kayan daki ba laifi,,,Kowa se yi mata murna
akeyi mama ta mata nasiha sosai akan ta zauna
lafiya da uwargida ta kuwa dauka dan ita ba
ruwanta bata san hayaniya ma Dr ya tarasu yayi
musu nasiha baki daya kuma sun nuna mai sun
dauka suka mai alkwarin zasu zauna lafiya,, Bayan
sati Dr da kansa yaje ya dauko aishatul mubeena
da kayanta tana ta murna za'a kaita wajen
ummanta,Rannar da'aka kaita suka fara sabawa
da husna ;Sa'arta kuma akwai san mutane tafi
aisha san mutane sosaii nan da nan suka saba
kamar dama sun San juna,Husna tana shekara 4
ita kuma Aisha shekara 6 Suna zaune a falo dasu
husna YA ABDUL ya shigo fuska ba yabo ba
falasa, masha Allah kyakyawa ne sosai,Ga shi
akwai tsayi,duk da befi shekara 15,Ya gaida
Umma(ma'u)ta amsa da fara'arta tana mai sannu
da zuwa dan boardn skul yake yi yau ya
dawo,,Husna da Aisha da sauri suka taso zasu
mai oyoyo cak! Suka tsaya sakamakon muguwar
hararar da ya wurga musu,,"ku meyasa ba kuda
hankali ne ni zaku zo kuna wa oyoyo ?banzaye
kawae" ya fada cike da fushi daidai shigowa haj
hadiza(ummi haka suke cemata) tace "kadai abdul
Allah ya shirye ka ,kai da yan -uwanka Kana
hantararsu kaji kunya wlhy" Yace "To ummi akan
meye zasu zo suna min oyoyo se kace yaro
sa'ansu!" Umma datake dariya se a lokacin tayi
magana " Anty na ,ai da gskiyar sa ya girma fa"
ummi tayi dariya "halinsa ne kenan fa,ni rasa
gane irinsa,Haka yake,hira ma basa yi ,Suna mai
magana ya hantaresu wai shi baya san raini,dadai,
YA AMEEN,,kikace shine ba ruwanshi,yaranan
kamar k'awayensa haka ya daukesu,,suyita hira
suna raha abinsu abin sha'awa" umma tace "
shima ai yanason su,Da alama magana ce bata
dameshi ba ,(ta kalleshi)Rabu da ita Dana bari na
kawo maka abinci kaci,, Yayi murmushi "Toh
nagode" be sake magana ba ,umma ta tashi ta
nufi kitchen dan zubo masa abincin,,,yayin da ya
zauna a kujera yana jiranta,, se a lokacin ya lura
da Aishatul mubeena dake kan wheelchair tayi
tsuru-tsuru,dan har ta fara tsoronsa,, Ya kalli
ummi da mamaki "Ummi wannan waccece??
L
Share
[12:23AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [55]-[60] Ummi tayi
murmushi "k'anwarka ce,Yar antynka ce" yace
"Allah sarki,But yana ganta a wheelchair ciwo taji
ne? Ummi ta kada kai "A'ah polio victim ce! Ya
zaro ido ya maimaita "polio victim kuma??!,garin
yaya? Ya akai ta samu? Ummi tace "Kai kaga
bansan tambaya nima bansani ba, Allah ne ya
dora mata,ya isheka haka, yace toh ummi,, Kallo
daya ya mata ya kauda kai a fili yace "Sannu kinji
ya sunanki? A tsorace tace "Aisha..tul..mubeena"
ya gyda kai "nice name" Daidai lokacin umma ta
shigo da tray na abinci a hannunta ta dire mai a
gabanshi yayi godiya ya kai loma daya kenan
daga waje suka jiyo murya "Salamu alaikum
Ummina my lovely sisters kuna ina?? Hakan ya
tabbatr musu da cewa YA AMEEN ne,, Da gudu
aisha da husna suka tashi suka nufi wajen sa, ya
ware hannunsa suka taho da sauri suka rungume
shi Yayi murmushi "Nayi missing dinku Deariz"
suka amsa muma munyi missing dinka bros Ya
rik'e hannunsu suka k'araso wajen su ummi ,
ummi tayi murmushi ta kalli umma "kingani ko
dama na fada miki wuyata ya dawo,shi ba
ruwansu ba kamar wannan sakaran ba!" Umma
tayi murmushi ya k'araso wajen ummi ya
rungumeta, Da sauri ta kwace "kaga ni bansan
wannan shashashacin" yayi dariya " ummi nayi
missing dinki dayawa" tace "nima haka dana"
Yace "Finally dai mun gama secoundry skul Nan
da yan shekaru zan zama PILOT,, Ummi tace
"Insha Allahu munan muna ma addu'a yace "Dats
my ummi" Ya juyo ya kalli umma ya gaisheta da
girmamawa ta amsa,,Tare da yi masa sannu da
zuwa da kuma murna kamala sakandire,,Yayi ta
godiya,,Se a lokacin ya lura da Aishatul mubeena
Ya kalle ta yace "Fine girl bakida lafiya ne? Ya na
ganta a wheel chair? (Ya kalli su ummi)Umma tayi
murmushi ta sunkuyar da kanta,, Da mamaki se
sukaji tace "Ni polio victim ce!" A tare ummi da
ya abdul suka zaro ido,,Lallai yarinyar nan daga
fadan abu har ta gane ta haddace,, Haka Ya
abdul yace a zuciyarsa"Ya ameen yace 'Eyyah
Subhanalahi " ya kalli ummi " Ummi da gaske
take? Umma da sauri tace"Da gaske take Ameen,
kawai se ta fashe da kuka,, Ummi ta shiga
rarashinta shikuwa ya ameen be san sanda
hawaye suka fara zubo masa ba nan da nan
tausayinta ya cika mai zuciya,, yaji kuma wani
santa a zuciyarshi,,jinta yake tamkar k'anwarsa
uwa daya uba daya ! ya matso kusa da ita yayi
murnushi "Ya sunanki" ta wangale baki "Sunana
Aishatul mubeena! Yace wow nice name " zaki sha
sweet?" Tace ' eh" yace " toh zomuje na siya
miki, umma da sauri tace" aah ameen ka bari ka
huta mana, daga dawowarka? Yace bakomai
umma yanzu zamu dawo Ai nan kofar gida ne,,
Ya ja wheel chair din suka fita Jin haka husna da
aisha suka ce zasu je suma,ba musu yace su taho
yaja wheel chair din yana mata murmushi "Muje
na siya miki sweet koh? Tace "Ehh tana wangale
baki" suka fice Abdul kuwa tabe baki yayi, ya
cigaba da cin abincinsa ,Umma kuma dadi taji a
ranta sosai Basu dade ba se gasu sun dawo Kowa
da sweet a hannunshi se wangale baki
suke,,Aishatul mubeena ta kalli Ya ameen kainu
wajen umma,,Yace toh yaja wheel chair din wajen
umma ta wangale baki "Ummana kinga ya siyamin
sweet" Umma tace"nagani angode" Ya ameen
yace "Niwa? Ya sunana? Tace "Bansan sunan kaba
ni" umma tace "Auu baki san sunan shi ba?" Tace
"Eh ya sunanka" Yayi wani murmushi sannan
yace...
AISHATUL MUBEENA 60-80
[12:23AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [60]-[65] Sunana Ya
ameen amma kin san me zaki dinga cemin? Ta
gyada kai "A'ah" Yace toh ki dinga cemin "Bros"
ya abdul dayakr k'ok'arin tashi ya fashe da
dariya,"Wayaga bros! Su bros manya" ya tsuke
fuska kamar ba shi yayi maganar ba sannan ya
tashi ya fita,, Ya ameen yace "Ka dai ji dashi dan
rainin hankali" Aishatul mubeena kuwa maimaita
sunan ta shiga yi "Bro...s Yau ma kamar kullum
bayan sallar magariba suna zaune gabadayansu a
falon Abba suna hira ,,Ya ameen yace "Abba
nikuwa inada shawara" abba yace inaji "Abba me
ze hana aishatul mubeena ta dinga gwada tafiya
duk da dai tafiyar bazata zama daidai ba? In ba
haka wlhy tafiya da Forearm crutch din nan ze
mata wahala sosai" Abba ya numafasa sannan
yace "To ka dinga koyawa mata takawar
muga,Indan tana takawa shikenan ba matsala
idan kuma ta kasa kaga dole sai dai tayi amfani
da forearm crutch din" yace to insha Allah za
dinga gwada mata,, Umma tace "Angode fa Allah
saka da alheri" yace "Bakomai umma" Yau da
yama ya ameen Ya sauko da ita daga wheel chair
din yana koya mata tafiyar,Ba laifi ta na dan
k'ok'artawa yaji dadin Haka kullum addu'arshi
Allah ya taimake ta,Ta fara cangala kafar tata
dan a ganin shi hakan yafi da yawo da sanda"
YAU DA GOBE SAI ALLAH yanzu dai Aishatul
mubeena tana ss2,tana iya takawa amma saidai
tafiyarta ba irin ta masu lafiyar kafa bace cikin
ikon Allah tana iya cila kafarta tayi tafiya,,,, Ta
k'ara girma ta zama yan mata,,Tana da shekaru
16 Duk da ba lallai ka gane hakan ba saboda yar
k'arama ce kuma gata Ba k'iba saboda cutar
polio ta k'ara motse ta,,Amma duk da hakan
kyanta yana nan akwai kyau Masha Allah,,, Ya
abdul yana final year dinshi a university inda yake
karantar Engineering danshi dama burin sa kenan
ya zama engineer yayin da Ya ameen Ya zama
cikaken pilot har ya fara aiki ma Allah mai baiwa
duk da nakasa irinta Aishatul mubeena,,Amma
Kuma Allah ya bata kwakwala Tanada masifar
k'ok'ari mussaman ma a fanni Ilimin addini harda
na bokon ma,,,sannan kuma cikin ikon Allah,Allah
se ya bata fasahar yin ZANE yanzun zata kalli abu
ta zana shi tsaf kuma