Chapter 3 of 10
AISHATUL MUBEENA Dama Ta Biyu by Miss Hafcy
makarantarsu a harkar zane sosai,,Kuma cikin
ikon Allah Ya ameen ne ya fara gano haka kuma
ya bata kwarin gwiwa sosai,,Duk wani abu datake
buk'ata a harkar zane da kudinshi yake siyowa ya
bata! AISHATUL MUBEENA ce t zaune akan Farar
kujera a compound din gidan,Kur'ani ne a
hannuta tana karantawa a hankali,,, YA ABDUL ya
shigo da motarsa ya faka ta a wajen fakin din
motoci,,Sanye yake da Bakin wando da riga sky
blue yayi bala'in kyau,,Ya k'ara girma ya kuma
k'ara kyau A hankali ya tako wajen datake karatun
yana sauraron k'ira'arta me masifar dadi,, Taji
kamar alamar mutum da sauri tajuyo suka hada
ido,,Bashiri ya kauda kai,,ya tsuke fuska yace "
Ke me kike yi anan? Murya na rawa tace "Daman
karatu nake yi," yace "Toh shi karatun ba'ayinshi
a ciki ne? A sanyaye tace "Saboda naga suna
kallo ne banason na dame su" yayi dan k'aramin
tsaki sannan ya bar wurin,,Ita kuwa ajiyar zuciya
tayi ta cigaba da karatunta Ba'a dade ba sai ga
Ya AMEEN nan ya taho daga dakinsa yana ta
mata murmushi(Dan bashida aiki week din) Tana
ganinshi tayi wani yalwatatacen murmushi ya
k'araso yana mata murmushi "SIS karatu ake ne?
Tayi murmushi "ina wuni bros" yace "Lafiya lau
sis karatu ake ne? Tace "Eh suratul khaf nake
karantawa kasan yau juma'a kuma sannan jibi
insha Allahu zamu yi musabak'a ! Ya wangale
yabaki "Masha Allah my l sister am very very
proud of you,,Allah ya bada sa'a insha Allahu ke
zaki ci,, Tace "ameen nagode bros" Yace "Ga
wani albishir din kuma;, tace inaji bros" yayi
murmushi " Yanzu uncle hashim(teachern su
aishatul mubeena) yace min aiy an zabe ki a gasar
zanen da za'ayi a Schools din dake kano wanda
kuma idan kinci shi ze bada damar ki wakilci kano
gabadaya a gasar da za'ayi da states din dake
nigeria.... Ta zaro ido da gaske bros? Yace
"kwarai kuwa! Tace anya zan iya kuwa? " yace see
you! Zaki iya mana insha Allahu se kin cinye
mudai kawai mu cigaba da addu"a,, Tace
"Nagode bros" Ya harareta "To meye na godiyar
kinsan dai banaso
Like · 3 ·
[12:24AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: by Hafsat
◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [65]-[70] Ta sa hannu
ta rufe bakinta toh shikenan na dena, yace
"Yauwa ko kefa" Bayan sallar isha,Aishatul
mubeena na zaune akan sallaya tana
muraji'a,Husna ta shigo da kur'ani a hannunta,Ta
zauna kusa da ita tace " Sis pls biya min nan,Ko
sau daya ne" Aishatul mubeena na k'ok'arin
dauka sai ga ummi nan ta shigo,Ta kalli husna"
Ke husna me yasa zaki dinga damunta kinsan dai
Musaba'ka garesu gobe ki barta tayi tilawa mana"
Husna tace "Kai ummi kawai fa cewa nayi ta biya
min shafi nan sau daya" Ummi tace "eh duk da
haka,Kije umma ta biya miki mana" Aishatul
mubeena tace 'Ummi dakin bari ma na k'ara
mata" ummi tace "Aah dai gwanda ta barki kiyi
karatunki" Husna na zumbure zumbure ta bar
wajen......... To Yaune dai zasu tafi musabak'ar
tun safe ta shirya tsaf cikin hijab har k'asa
uniform din makarantarsu Tayi kyau sosaii,,Ya
ameen ne da kanshi ze kaisu,, ita da su husna da
kuma k'aninta Amir( Yaron da Umma ta haifa a
gidan) dayake duk makarantarsu daya.... ,,(Da
harda su umma za'a amma zasuje Gaisuwa zaria
wani dan uwan abba ya rasu) A lokacin da suka
isa Mutane an taru sosaii,Makarntar dazasu yi
gasar da ita har daliban sun iso da kuma wanda
zasu kara da Aisha....Bayan an bude taro da
addu'a,Aka fara.... Cikin ikon Allah kuwa Aishatul
mubeena tayi kok'ari sosai,,Gyra da aka mata
basu da yawa,,bayan an kamala aka Aka kirawo
malam salisu(Babban malami ne shi) dan yazo
yayi jawabi sannan ya fadi sakamako,,,,,Sai da
malam ya fara jawabi ya kuma ja hankalin dalibai
da su dinga maida hankali wajen karatu sannan ya
fara karanto sakamakon kamar a haka: "A
musbak'ar Alkur'ani mai girma da muka gabatar
tsakanin makarantar,khalid ibn walid islamiya da
kuma Nana khadija Islamiya,, Makarantar nana
khadija islamiya wadda ta samu wakilcin Aliyu
sani tana da maki sha biyar (15) a cikin maki
talatin( 30)A mata kabara,,(Dalibai suka dauka
Allahu akbar) Sannan makarantar Khalid ibn walid
islamiya wadda ta samu wakilcin AISHATUL
MUBEENA MUHAMMAD AMEEN tana da maki.....
ashirin da biyar(25) a cikin maki talatin(30)! ku
musu kabara(Dalibai suka wage baki Allahu akbar)
Aishatul mubeena dake gefe wata ajiyar zuciya
tayi tare da Hamdala bata san sanda ta fara
hawayen murna ba,, Mal ya cigaba ' Wannan ne
ya tabbatar mana da cewa makarantar khalid ibn
walid itace ta cinye wannan gasar karatun
Alkur'ani me girma,, ku sake rangada musu
kabara(Dalibai aka dau kabara da karfi,nima
danake gefe wage baki nai nace Allahu akbar)
Dan haka an shirya kyautuka masu tsoka ga
wandanda suka yi Musabak'ar domin mu k'ara
k'arfafa musu gwiwa dama sauran dalibai,, Dan
Haka yanzu zan fara da Aliyu sani,, Alhaji Abdu
mai nerori ya bada kyautar Dubu Da kuma
Alk'urani me girma izu sittin ya kuma ce a bawa
wanda ya zo ta biyu a wannan gasar karatun
Alk'urani me girma,, Aliyu sani sai ka fito ka
amshi kyautar ka,, Ba dadewa aliyu sani yazo ya
karbi kyautarsa ana ta masa kabara Malam ya
cigaba sannan Zamu kira AISHATUL MUBEENA
MUHAMMAD AMEEN domin ta amshi
kyaututukanta,,Ba'a dade ba sai gata ta taho
tana cangala kafarta malam ya cigaba " Alhaji
Audu mai nerori ya bada kyautar Naira dubu dari
(100),Ga duk wanda yazo na daya Sannan
Shugaban kamfanin jirgin **** ya bada kyauta
kujerar umara shima ga wanda yazo na daya,Sai
kuma haj asabe ta bada kyautar atamfa guda uku
(3) itama ga wanda ya lashe gasar karatun
alkur'ani Dan Haka Malama Aisha se kizo ki karbi
kyautarki ta matso ta karba ana ta daukan
hotonta mussaman ma da'aka lura da nakasar
dake jikinta,, Ita kuwa se hawayen murna takeyi
hannu na rawa ta karba aka dinga kabara,, Malam
daga k'arshe yace,Dan haka sai muyi wa bayin
Allah nan addu'ar Allah ya saka musu da alheri ya
kuma k'ara budi.... Yayi addu'a sannan ya koma
ya zauna.... Tana dawowa daga wajen Karbar
kyautar kai tsaye wajen Ya ameen ta nufa ta
mik'a masa kyautar sannan ta koma ta zauna ta
kifa kai a gwiwa tana kuka,Ya ameen kuwa
rarashinta ya fara "Haba sis ki dena wannan
kukan mana Godewa Allah ya kamata kiyi ba kuka
ba! Ta dago idonta ta share hawayen sannan tace
" Toh bros insha Allahu na daina " yace "Toh
yimin murmushi mana" Batasan sanda murmushi
ya kubce mata ba,,Shima murmushi yayi yace
"Yauwa ko kefa" mutane se zuwa yimata Allah
sanya alheri suke mussaman ma dalibai da kuma
malaman makarantarsu kai hadda baki.... Bayan
an rufe taron Har zasu tafi gida tace a tsaya ta
zata je ta dawo,Suka ce toh......Kai tsaye wajen
shugaban makarantarsu ta nufa ta tsuguna har
k'asa ta gaishe shi ,Ya amsa da murmushi "Tashi
mana Aisha,Gaskiya kin burge mu sosaii muna
alfahari dake Allah ya saka miki da alheri ya k'ara
buda miki kwakwalki ,,kin k'ara fito da
makarnatar mu ba abinda zamu ce miki sai
godiya da fatan alheri"" Tayi murmushi "Malam
aiy nice da godiya,Nice ya kamata nayi muku
godiya ma,,Nagode nagode Allah ya saka muku
da mafificin alheri Ameen" Malam yace "Ameen
Aisha,Allah ya sa sauran dalibai suma suyi koyi
dake" Tace "Ameen" sannan ta bude jakarta ta
zaro envelop din nan da aka bata na Naira dubu
dari(100)....
Like · 2 · Reply · Ed
[12:25AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [70]-[75] Ta mik'awa
Malam Iro (Sunan shugaban makarantar tasu)
murya a sanyaye tace "Malam ga wannan kai da
sauran malamai ku kasa sauran abinda yayi
ragowa kuma a siyo butoci da tabarmu akai
massalacin makaranta " Malam ya zaro ido "Haba
a'eesha(Dayake haka yake ce mata) Ai kudinki ne
ba namu ba,Ki rik'e kudinki kinji Allah ya samu su
albarka mukam mun gode bama karbi kudinki ba
gaskiya" ta ja numfashi sannan tace "A'ah malam
dan Allah ka k'arba,Ba a maida hannun kyauta
baya!" Malam yayi murmushi " To sai da mu dauki
dubu ashirin(20) ta ishe mu" tace "A'ah malam
dan Allah ka karba duka" Yace "Toh shikenan
raba a biyu ki bamu rabi Allah ya sa albarka" ta
wangale baki " Yauwa malam gashi(Ta mik'a masa
kudin duka) ya ciri dubu hamsin (50) kamar yadda
Yace sannan ya mik'a mata yace "Gashi nan
a'eesha mun gode sosaii Allah ya saka miki da
alheri ba abinda zamu ce miki sai godiya" tayi
murmushi "Godiya nake malam Allah ya biyaku"
Sannan ta koma wajen motar tasu suka nufi gida
Suna isa gida a harabar gidan ummi da sauri tazo
ta rungume ta,Tana ta murna "yata kin burgeni
gaskiya,Am soo proud of you My daughter,Ina
alfahari dake Yata, aishatul mubeena tayi dariya
"Nagode ummina" Umma itama ta zo wajen cike
da murna Ta rungume yarta ta,Batasan sanda taji
hawaye na zuba ba duk iya kok'arin datayi na
ganni hawayen basu zuba ba amma sai da suka
zuba,,A firgice ta kalli umman tata "Umma kukan
me kike yi?" Da sauri ta share hawayen nata
"Kukan murna ne mubeena kukan murna
nakeyi,,Dama na dade ina jiran irin wannan
rannar Sai yau Allah ya nuna min,, ina ma
zanga........Da sauri ta canza zancen nata ,,muna
alfahari dake Allah ya k'ara buda miki
kwakwakarki,,Dake da sauran yan uwanki!" Su
Husna dake tsaye suka ce Ameen..... Ya abdul ya
fito daga dakinshi,Ya tsaya turus Yana kalonsu
"Meya faru ne? Ummi da sauri tace "Abin arzik'i
ne ya faru,,k'anwarka ce taci Gasar karatun
Alkur'ani me girma " Yace "Masha Allah wacce a
ciki?" Ummi tayi murmushi "yo waka sani banda
mubeena,Kasan wadanan sakarkarun(Ta nuna su
husna) Ba abinda suke tsinanawa" ya tabe baki
"Okay" ummi tace Sai kayi mata murna ai,Ya juyo
ya kalleta ya k'irk'iro murmushi yace "Congrats"
yana rufe bakinsa da sauri ya koma dakinsa,,Ya
ameen har a zuciyarsa beji dadi ba dan haka ya
yanke hukuncin yaje ya sameshi ya mai
magana,,Ya bishi dakinsu yayin dasu ummi suka
shiga ciki (Abinda yasa suka san itace ta lashe
gasar shine, Ya ameen ne ya kirasu ya sanar
dasu,,jim kadan bayan an gama fadan
sakamakon) Ya murda kofar ya shiga a zaune ya
ganshi yana kallon system dinshi dake kan
Bedside drower,,Ya shigo da salama sannan ya
zauna a kusa dashi, Yace "Ahki(My brother
dayake haka yake cemai) Gaskiya abinda kayi yau
baka kyauta ba"" Ba tare da ya kalleshi ba yace
"Me nayi" Ya ameen yayi murmushi,, "okay
bakasan me kayi bama? Ya kallesa "Yes
eh,Bansani ba" Ya ameen yace "To abinda kayi
yanzu a harabar Gida nasan nasan cewa umma
bataji dadi,Dan Allah ka dena yiwa yarinyar nan
haka kodan nakasar ta ai ka sota,,Kamar
k'anwarka fa take,,Dan Allah ki dinga janta a jiki
ka dena hantararta dan Allah na rok'e ka" Ya
abdul ya nisa sannan yace "To bakomai,Amma ni i
dont knw why(Bansan meyasa ba) kwatakwata
bata burgeni,Inaga jinin mu ne be hadu ba!!
Kuma dama kasan halina ai,,ni ban cika san
shigewa mutane ba and kar ka dauka wai ko dan
ba blood sister dinmu bace,No ko su husna ma
kasan ba wani sakar musu fuska nake ba Ya
ameen yace "To shikenan amma ya kamata ka
rage wannan halayar,Wani in ya fahimce ka wani
baze bayi ba,Dats why(shiyasa) mutane ke maka
Kallon me girman kai " ya abdul yace "Wannan ya
rage nasu ni ban damu cuz nasan ba halina bane"
lets keep this aside (mu aje wannan gefe) Wai ni
ina maganar FATY ne naga yanzu baka
maganarta,, Ya ameen ya bata fuska "kai ni daina
min maganarta mu b'ata" ya abdul ya kalleshi da
mamaki "Why meyasa" ya ameen ya nisa sannan
yace "Waifa daga taga pics dinmu da Mubeena
shikenan ta dau zafi, Wai budurwa tace,,inata
k'ok'arin na mata bayani amma tak'i yanzu bata
daga wayana ma" ya abdul yace "Tayiwa
kanta,Amma i bet you dakanta zata dawo tace ku
shirya" Ya ameen yace "oho mata" Ya kalli ya
abdul "Kai dama wayo kake min ko da wasa baka
min maganar budurwarka" ya abdul yayi
dariya"Wayaga me budurwa,, Hhh ni banda
budurwa ai" ya ameen yace "Ban yadda ba,Duk
yan mata dake binka kace bakada budurwa
wannan shayi ne kake mun" Ya abdul ya k'ara
dariya sannan yace ................ Kuyi hak'uri kunji
ni kwana2 biyu shiru
Like · 1 · Reply · E
[12:27AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [75]-[80] Yayi dariya
sannan yace "Kasan Allah? Ni har yanzu ban ga
wadda tayi min bane,Ni kaga ba kula mata ma
nake ba,In banda yan-uwa sai kuma classmates,"
ya ameen yace "Kuji shi kamar gaske" ya abdul
yace "Wallahi da gaske,," ya ameen yace " To
shikenan Allah ya zaba mana mafi alheri, nidai
kaga a shekarar insha Allahu zan yi aure na barka
(yayi masa gwalo)" Ya abdul yayi dariya,,wayar sa
ce tayi ruri da sauri ya dauka" Yace salamu
alaykum" dayan bangaren akace "wslm abdul ka
fito ina kofar gida" ya kashe wayar ya kalli ya
Ameen "Hafeez ne frnd dina bari naje ltr zamuyi
magana" Ya ameen yana k'ok'arin tashi yace
"okay nima bari na tafi". Kai tsaye falon umma ya
nufa inda ya tarada Nana(Aysha) Na chatn a
waya,Husna na kitchen,Aishatul mubeena Na
zaune Tana koyawa amir assignment,, Ya shigo
yana murmushi hade da kallan Mubeena' Hafizar
mu" tayi dariya "Kai bros" yace "Ko nayi k'arya?"
Da sauri Nana tace "a'ah bakayi k'arya ba ya
ameen, gaskiya ce" Yanzu kaga yan islamiyar mu
sai cemin suke nace suna taya ta murna da fatan
alheri, hadda masu sa pic dinta lokacin suna
musabaqar a display Picture(Dp)kaga(Ta mik'a
mai wayarta) ya karba "Masha Allah,Ai yau
kwanan farin ciki za'ayi a gidan nan" Nana tace
"Aikwa dai" Ya zauna akan kujera yana dana waya,
Nana ta kalleshi "yauwa na tuna,Ya ameen kasan
wata faty? " da mamaki yace "Yes nasanta" Nana
tace " A layin nan take?" Da sauri yace "A'ah a
unguwar nan dai suma suke,,me ya faru wai?"
Tace "Amma ni bansanta ba,Wani ta aiko da
sak'o dazu wai abaka,Am sorry mantawa nayi,,
da sauri yace "sak'on me? Fada min" tace "bari
na dauko maka" yace "yauwa" ala-ala yake ta
kawo masa yaga ko mene ne Bata dade ba kuwa
sai gata da yar k'aramar jaka a hannunta ta mik'a
masa, cike da zumud'i ya karba yana washe baki,
,Mubeena kuwa bata ce musu komai ba shiru tayi
kamar ma bata san abinda suke ba ,, Yana karba
ya fice abinshi ya nufi dakinshi. Kan gadonshi ya
baje da sauri ya dauko jakar yana bud'ewa wani
kati ya gani ya sha kwalliya cikin hanzari ya bude
ya fara karantawa kamar haka "" Remember the
good times we had spent together,And the
beautiful future we had dream of,,Darling i never
wanted to create a distance between us...please
let us bridges the gaps,,. Wani tsale murna yayi
ya rungume kati a fili yace "Bakomai my faty na
hak'ura!" Wayarsa ya dauko yayi dailing number
ta,akace a kashe take,,Yayi tagumi yana sake
kalan katin shi abin mamaki yake basa ma ashe
dai abdul da gaske yake da yace da kanta zata
dawo su shirya!,, Wayarsa yagani tana ruri da
sauri ya dauka,, Ashe faty ce cike da murna Yake
tambayarta ta canza number ne tace masa eh,,
bayan sun gaisa tace "Kayi hak'uri ya ameen
rashin fahimta ne ya kawo hakan, amma yanzu na
gane komai,ina neman yafiyarka" yayi murmushi
"Bakomai faty darling Allah ya barmu tare
sweetheart" tace ameen dear suka cigaba da
hirarsu ta soyayya. Aishatul mubeena bayan ta
gama yiwa Amir assignment din ya tafi wajen su
umma,,ta juyo ta kalli nana, "Ya nana wacce
FATY wai" Nana tayi murmushi "inaga fa
budurwasa ce !Dan dama rannar na labe naji suna
hirarta shi da ya abdul ""Mubeena bata san dalili
ba sai kawai taji gabanta ya fadi a sanyaye tace
"Amma nikuwa bai taba fada min ba" Nana ta
harareta da wasa "Ko ni dana girme ki be fada
min ba saike yarinya" mubeena tayi murmushi "To
yaya baba" nana tace "Kinsan mu akwai san
girma" Mubeena tayi dariya ...Ta tashi ta shiga
cikin daki ta zauna jikin gado tayi tagumi Tana
tunane-tunane kala-kala a zuciyarta.. Umma ce
ta shigo dakin,,kusa da ita ta zauna a hankali ta
dube ta tace "me yafaru naga kin yi shiru kina
tunani? Meke damunki?" Mubeena da sauri tace "
bakomai ummana kaina ne ke ciwo kawai" umma
tace "toh kuma ai se ki sha panadol,bari na
dauko miki magani kisha" Ta tashi ta dauko
mata,, ta k'arba da kyar ta sha maganin duk jinta
take wani iri,, Ta d'an yi jim,Can ta tuno wani
abu da sauri ta kalli umma tace "umma dan Allah
wata tambaya zan miki amma dan Allah umma
kimin alkwarin zaki bani cikakiyar amsar"" umma
ta danyi jim sannan tace "inajinki indai inada
amsar insha Allahu zan baki ita" Mubeena tayi
murmushi "yauwa ummana" sannan tace.. "Umma
DAN ALLAH WAYE MAHAIFINA? Gaban umma ya
fadi sosaii cikin dauriya tace "Wai ke mubeena
me ke damunki ne? Sau nawa kike tambayata
nace miki Abba ne babanki,Abba shine babanki
kar ki sake yi min wannan tambayar tunda kinsan
amsar"" mubeena ta runtse idonta se
hawaye,cikin murya kuka tace "Umma Abba
bashine mahaifina ba, Na dade da sanin haka,"
Ummi cikin muryar masifa tace "to sai ki fada
min waye Mahaifin naki,tunda ni baki yadda dani
ba Mubeena ta fashe da kuka "Umma ba haka
bane,Umma Dan Allah ki fada min,Kar kisa na
fara tunanin ko ni yar shege ce,,Ba ta hanyar
Aure aka haife ni ba!! Umma da sauri ta juyo
idanunta fal da hawaye tace "Auzubillahi" "ke ba
yar shege bace! Ke yar halak ce! Idan bakyason
bacin raina to ko da wasa kar na kuma jin
maganar nan,,tana gama fadan hakan ta fice
daga dakin tana share hawayenta!
Comment as:
Subscribe to: Post Comments (Atom)
Saturday, 15 October 2016
Posted by MissHafcy at 08:00
AISHATUL MUBEENA 85-105
[12:29AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©NA MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [80]-[85] Mubeena
kuwa kukan ta ta cigaba dayi daga baya barci
b'arawo ya sace ta. Da asuba ta tashi tayi
sallolinta da kuma nafila,,Tana zauna tana karatun
Alkur'ani har gari ya washe.. Bayan ta idar da
karatun ta tashi ta nufi dakin Umma,,zaune ta
tadda ita akan sallaya Tana addu'a,A bakin gado
ta zauna tana jiran Umman ta kamalla addu'oin
ta,, bayan Umma ta idar ta juyo ta kalli
mMubeena,da sauri Mubeena ta k'ara duk'awa
k'asa ta gaishe ta cikin sanyin murya "Umma ina
kwana,kin tashi lafiya?" Umma tayi murmushi
"Lafiya lau Mubeena" Mubeena tace "Umma dama
ina neman yafiyarki naga jiya kamar na b'ata miki
rai,insha Allahu baza ki sake jin maganar daga
bakina ba" Umma tace "Ban yi fushi ba
Mubeena,bakomai komai ya wuce" Mubeena ta
washe baki "yauwa Ummana nagode sosaii"
Umma tace "muje muyi karin kumalo(breakfast)"
Mubeena tace "Toh" Bayan sun gama cin
abincin,suna zaune ya Ameen ya shigo sanye da
kayansa na pilot ya rik'e hular a hannunsa sai
murmushi yake yi, Har k'asa ya duk'a ya gaida
umma ta amsa da fara'arta,Mubeena ma ta
gaishe shi ya amsa. Bayan sun gama gaisawa ya
kalli Mubeena"Sis ni kinga yau zan koma aiki" ta
canza fuska "Da gaske bro? ai nazata sai next
week" yayi dariya "Yauwa dan Allah inaso ki
maida hankali akan gasar zanen nan da za kuyi
kinsan Ran monday zaku fara,Ku goma(10 )Aka
zaba kuma a cikinku ne za'a zab'i ta d'aya( 1)
Please inaso ya zamana kece ta dayar nan! Zaki
iya, ga wannan(ya mik'a mata leda) duk wani
items da zaki buk'ata a harkar zane yana ciki
inaso ki fara practice tun yau,,Please ki dage "
tayi murmushi "Toh bros nagode sosaii insha
Allahu zan fara daga yau mu dage addu'a,insha
Allahu bazan baka kunya ba." Yayi murmushi
"Dats my sis,ki kuma sa a ranki zaki iya,indai kin
yadda da hakan to baza ki samu matsala ba insha
Allahu". Sai a lokacin umma tace "Gaskiyane Allah
ya bada sa'a" Dukansu suka ce "Amin."
Gabad'aynsu hadda Abba suka rako shi harabar
gida,Mubeena kuwa daurewa kawai tayi dan ji
take kamar tayi kuka idanunta sun yi rau-rau
alamar me shirin yin kuka, shikuwa sai k'ara
jadada mata yake akan ta dage sosai, itakuwa
tana cemasa "insha Allahu zata dage sosai" su
Abba suka mai fatan alheri suka kuma mai
addu'ar Allah ya kiyaye hanya,sannan suka shige
ciki,suka barshi daga shi sai Mubeena datake jikin
motar tayi jim ta kasa magana ,daga baya ta
kalleshi tace "Yanzu bros sai yaushe? " yace
"Gaskiya