Chapter 2 of 46
ZANEN QADDARA TA Farashin Zaɓi by Ramlat Abdulrahman Manga
ba.
Kaga yadda suke da Aminu haka yayi hakuri da abinda yayi mata, balle kai da
rashin jituwarku da Anum yayi."
Shiru yayi murmushi daya daga cikin su yayi sannan yace mata.
"Umma! Nifa abinda Anum tayi banga laifin ta ba, sabida ita kanta Maman mu taki
zuwa dubata, sannan tana jin zafin Anum ne sabida rashin shayar da Yarinyar nan,
kuma abinda na sani da ace Anum ta amshi yarinyar toh ba makawa ba zata nutsu ta
fahimci girman Soyayyar da Malam yayi mata ba.
Ko jiya ta turo min sako tana kuka tare da cewa, ita tana sane da itace ajalin
Malam, ba kamar yadda ake fada bane, hatsari yayi ba! Wallahi duk sai naji ta bani
tausayi, duk da fushin da nake da ita, sai naga babu amfanin na cigaba da wofantar
da ita. Domin Allah ya gani ba ita bace sanadin malam hatsari ne yayi kuma ya zo
dai-dai da ya fita da b'acin ranta, shi yasa take ganin kamar itace tayi sanadin
shi."
"Eh mganarka haka yake, Usman amma kuma ai laifinta kafewa da tayi akan ba zata
shayarda yarinyar shi ya fusata kowa, sannan Ni da kaina naji ba wani bane ya gaya
min tana faɗin wallahi babu rabon shayar da yar matsiyaci a jikinta, dan haka duk
abinda zai yi yayi.
Kuma da na karanci al'amarin sai na fahimci, tana fama da kansa Allah yayi
mata ne, tana tutiya da abinda Allah ya bata ne, da ace Allah bai bata kyau da
tsarin halitta ba, da babu abinda zai saka ta rena Maude."
"Yusuf kenan! Kana wasa da ƙaddara, matukar Allah ya zana maka haka a cikin
ƙaddarar ka babu yadda zaka goce mishi, shi yasa ake fatan kyakyawan kaddarar."
Inji Nura.
Su hudu ne, mazan tunda suka fara su uku na hudun wanda yafi su Shekaru bai ce kome
ba, asalima mik'ewa yayi tare da kallon agogon hannun shi. Ya mike tare da cewa.
"Allah ya kyauta, Ni da wannan mutumin zai ji da ya hakura da zuwa gurinta, sabida
yanayin da take ciki bata bukatar damuwa."
"Yawwa Ya Sadiq nima abinda nake nufi kenan, a barta ta samu nutsuwar zuciya."
Inji Bashir. Haka suka yi tattaunawa har kusan tara na dare, kafin
suka fita daga asibitin dake suna emergency ne, kallon Umman Sadiq yayi sannan yace
mata.
"Zan turo Rulwani da bargon yanzun nan yau ban ga Aminu ba,!"
"Eh shi yayi ta dawainiyya da mu, ya kawo abincin amma bai kuma dawowa
ba, ina ganin halin da Yarinyar take ciki ne yaki dawo dashi."
"Toh ba damuwa, Sai da safe." Yace mata, ta amsa da.
"Allah ya tashe mu lafiya"
A hankali ya fito, daga cikin yaba kallon yan uwan shi da suke jiran shi, yana
zuwa ya bude motar ya shiga, dukkansu suka shiga ababen yawan su, suka bar asibitin
koyarwa na jami'ar Abubakar tafawa balewa.
Bayan minti goma sha biyar, can sai ga wani matashin Amma ba yaro bane
domin ya kai irin talatin da daya ko da biyu. Cikin b'ata rai ya gaida Umma sannan
ya kalli inda Anum take kwance yacewa Umma.
" Ba dai abinda nake ji a gari bane yake damun ta?"
Wani banzan kallo Umma tayi mishi sannan ta cigaba da abinda take.
"Umma ina magana kin ki kula ni?"
"Wallahi ka fita idanu na, kafin na fitar da kai da karfin tsiya, mara kunya kawai,
idan shi yake damunta kai sai ka shirya zama da masu lafiyar, Rulwani bana son
abinda ake fa? Bana son damuwa fa"
"Toh Umma Allah ya huci zuciyar ki!" Daga haka ya ajiye barguna biyun ya koma gefe,
yana kallonta, mik'ewa tayi ta dauki daya ta lullubeta da shi, sannan ta koma gefen
tana cigaba da cin abincin ta.
"Umma!"
"Ina jinka"
"Umma!"
"Kunne ke ji!"
"Hmm! Dama nace zaku jima ne a asibitin?"
"Anan zamu tabbata!"
"Kai Umma kome nayi sai ki zafaffa, kawai tambaya nayi fa!"
"Idan banji duka ba, ba zan daina zafaffawa ba!"
Shiru yayi tare da cewa.
"Toh shi kenan, tunda Anum ba zata yi laifi ba,.kowa kaiwa Anum magana, sai a
shiga jin haushika."
"Tashi ka tafi tunda baka da hankali."
Ba musu ya bar asibitin tare da mata sallama, dan matuƙar akan Anum ne Umma sai ta
iya kaiwa mutun duka babu gaira Babu dalili.
...
Haka suka kwana a cikin asibitin, Umma kan ita sallah ma take, dan tasan karfe huɗu
na asuba zasu farka ace kowa ya fito waje za ayi shara, da goge goge.
Haka ce ta faru kuwa, asubar farko aka tashe su, Ita mara lafiya na gado,
ku kuma masu jinyar su, za a koraku waje.
--- Da sassafe Maman Aminu tazo, dauke da abin karyawa tare da kayan Anum kala
biyu, sai na Umma.
"Sannu Maman Abubakar, ya kwanar sauro?"
Dake tasan Mama bata da wani hausa sosai, dan haka tace mata.
"Alhamdulillahi! Ya kema kika kwana?"
"Lafiya lau, ya me jikin?" Ta tambaye tare da kallon kofar Emergency,
"Da sauki kenan zamu ce ba, tunda kirjin yayi mata sauki!"
Tab'e bakinta tayi sannan ta tura mata abincin gabanta, tana faɗin.
"Ga abin karyawan ku!"
"Mungode!"
Nan suka yi shiru, kafin can Aminu yazo, nan suka tab'a hira dan bai tsammani zuwan
Maman su ba, kawai ya dai ganta ne har da abin karyawa, dan haka cikin lalluma da
rarrashi ya shiga bata baki tare da nuna mata, idan laifin da Anum tayi ne yaci ace
ta yafe mata, amma mata magana akan lafiyarta, tashin hankali ne. Ba laifi nasihar
ta shige ta, tare da yi mishi alƙawarin zata k'iyayye gaba.
---
A iyakan rayuwata na aikata laifukan masu mugun yawa, na b'ata sunana da sunan
gidan mu, na yiwa kaina tambari da munannan aiyuka,.sam ban saurari soyayyar da
iyayena ke min ba, nayi ta aikata kusakurai masu girma, har yau ina tsanar kaina da
kaina, nayi rashin jin maganar iyayena wanda shi kawai ya ishe ni ganin bakin cikin
rayuwa.
Da ace abinda na aikata zai gogu wallahi na nasaka kilina na goge shi baki
ɗaya daga cikin rayuwata, Ni da kaina na zana ƙaddara ta, na kuma goge shi kai ba
zan tab'a yarda na aikata abinda zai tab'a mantawa a ƙaddara ta ba, naga
kaddarorrin rayuwa masu yawa da girma, sakamakon bijirewa mahaifina.
Naga sabuwar rayuwa masu yawa, na kuma fada tashin hankalin rayuwa, nayi
laifi masu yawan gaske, wanda haka ya ruguza min rayuwata, ina da zan ga Baba
Malam, na bashi hakuri? Ina da zan kuma ganin shi yace min nayi abu koda kuwa shine
hanyar mutuwata zan aikata.
Banyi Zina ba, amma kasancewar nayi rayuwar da take tare da ma'abota shi, yau
ana jifana ne da dattin zina, ban tab'a kawowa a raina zan yi mugun abu ba, amma
yau sakamakon rashin jin Maganar iyayena ya sa ana min kallon mazinaciya.
Duk rayuwar da zaka dauki nauyin rayuwar wasu, ka dauki al'adar wasu ka daurawa
kanka Tabbas wata rana kai da kanka aka wayi gari duniya ta juya maka baya.
Duk da iyayena sune mafarin ƙaddara ta, amma a zahirance ba hakan bane
sabida su, soyayyar da suke nuna min, da ace sun tankwarar da Ni, toh da yau haka
bai faru dani ba.
Yan uwana ciki daya, da kuma mahaifana, sun taka rawar gani a rayuwata,
sun nuna min soyayyar da ta hananin ganin laifin kowa, shi yasa nake ji a a raina
ba zan tab'a yarda wani ya koyawa dan shi irin soyayyar da aka nuna min wanda bai
janyo min kome ba sai damuwa.
Ba laifi bane Iyaye dan sun so yaran su, amma kasancewar irin mu soyayyar da
ake gwada mana, Soyayyar yaran karshe SOYAYYA ce da matukar iyaye basu tsaya da
gaske ba, toh akwai matsala, kamar yadda aka nuna min nawa.
Share kwalla nayi, a yau nake tirr da kasancewata auta, wanda
bahaushe ke kira da mowar ƴaƴa, na taso cikin soyayyar da ta gaza amfanar dani
kome, na wayi gari ban san lokacin da kome ya warware min ba, da ace nasan haka ce
zata mamaye rayuwata, da ban fara amsa sunan autar malam ba.
A yau kome ya faru dani ne sakamakon wannan yanayin da na tsinci
kaina, na tsani kalmar autar malam, na tsani rashin zuwana a matsayin Ƴa ta tsakiya
sai ta karshe wacce ta tattaro kayan bakin ciki a haihuwarta.
Wani irin kuka ne ya kwance min, yau na zama abinda na zama ne
sakamakon rashin adalci da banyiwa Iyayena da mutumin da ya maidani mutum, na
rintsa idanuna ga hasken da yazo mini, na bude akan duhun damina maganin me
kwaɗayi, kowa ya dibo da zafi aka ce bakin shi, yau na kwaso abinda ya dame Ni?
Tun bayan tafiyar shi shekara daya kacal kenan, ban kuma hada tsabga ta kowani
namiji ba. Amma yau nice ake zargin da abin maza, Innalillahi wa'inna ilaihi
rajioun, Ya Allah nayi kusakurai da yawa Ubangiji Karka kama ni ta wannan hanyar,
kalmar tayiwa rayuwata giɓɓi, haka na wuni ina kuka koda likita yazo duba ni, ya
samu jini na ya haura, kadan dan haka yace kar a dame ni da yawan magana ina
bukatar hutuwa.
Duk da fushin da yan uwana, suka dauka bai hana su zuwa dubani ba, asalima
sun zo dukkan su, amma fushi suke dani, dakyar Aunty Hafsah da Safiya suka gaishe
ni. Aunty B da take kusan tsaye akai na, duba magangunar tayi sannan tace min.
"Anum, don Allah ki rage nauyin tunanin da yake damunki, zuciyarki fa ta kumbura."
"Toh Aunty B! Zan gwada.."
Maganarce ta makale, sakamakon shigowar Aminai na, wanda sune umul a'ba'isin fadawa
ta wannan hanyar tare da Aunty Aina'uh Kishiyarta, da muka zauna a gidan
Kwamishina, uwargidan shi. Sai Mahaifiyar shi, Hajiya Turai.
Beauty da XOXO, murmushin mugunta na gani akan idanun su, kafe su nayi da ido,
sannan na dauki Kofin tea da aka hada min na fara sha ina murmushi, isowarsu.
Kallon Tagwayen ta da suka koma kamar marayu tayi, sannan ta mika musu hannu, sai
da suka kalli XOXO da tare da sauran matan.
"Kuzo gurin Mama!"
Nace musu, had'iye yawun tsoro suka yi, sannan suka coge a gurin, kallon XOXO nayi
domin nasan aikinta ne, juya cokalin dake cikin cup din Tea din nayi jikinta ne ya
dauki rawa, tace.
"Yan biyu kuje gurin Mama!"
A hankali suka tako, kallon ta nayi sannan na sake murmushi, kafin na ajiye cup
din, ina kallon ta sauke boyayyen ajiyar zuciya.
D'ago su nayi muka zauna, ban kuma kallon su ba, amma cikin iko nace
musu.
"Zaku iya tafiya, ku turo Ibrahim yazo ya dauke su, sannan idan suka dawo, ina da
labarin abinda yake faruwa dasu, idan da alamun watan tozarta masu zaman hayan
dogon gida zai fara, a Cigaba da tab'a min bugun zuciyata."
A fusace suka juya nacewa Beauty.
"Kazamar rayuwa bata dace da uwar da ta haifi Ƴaƴa mata ba, sannan da ake yawo dani
a cikin bakin kura, ina sane da! Beautiful face."
"Hajiya Turai! A gayawa Ibrahim gaskiyar maganar da. Maman Aymaan!
Ki rike kimar ki, da gaskiyar ki Allah zai datar dake alkhairi. " Ban kuma magana
ba, har suka fita, sake rungume yarana nayi ina jin wani irin tausayin su a raina,
sabida su na kuma tabka kuskuren da nayi, babu wanda yayi min magana a cikin yan
uwa na. Ganin yarana sun taimaka min sosai gurin saukar jini na, domin har dare
muna tare dasu.
Bayan isha yazo ya dauke su, har zai tafi nace mishi.
"Bayan hakkin Jama'a da yake jingine bisa kafadarka, nauyin yaran da aka raba su da
Mahaifiyar su yana bisa kanka, Ka bibiyi rayuwar su, don Allah karka sani jin kai
kuka na inda za a tsaya min."
Juyawa yayi tare da gyada min kai, ya fita daga asibitin.
Wani siririn hawaye ne ya zubo min, lokacin da na fahimci. Har da shi a
matsayin wanda ya b'ata lokaci na.
---, kwana na biyu aka sallame ni, sakamakon jini na da ya sauka, haka ya
faru ne ta sanadin yaran da Ibrahim yake kawo min, ranar da na koma da su, a ranar
naga sauyi daga fuskar Mama da Yan uwana, waɗanda muke ciki ɗaya dasu, ban damu ba
na share batun su.
Sati na daya Zakiyah matar Ya Sadiq ta haihu, nasan babu abinda zai dawo min
sai tashin hankali, aka'idar gidan mu idan aka haihu ranar suna a nan gidan zaayi
abincin suna, dan haka tunda na fahimci haka na kaura cewa fitowar waje ranar sunan
gudun kar yayuna mata da muke daki daya su azabtar dani da bakaken Magana.
Dan haka yau da ta kama sunar ina....
#Mai_Dambu[1/31, 11:27 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA...!!
_Rayuwar Aure a Arewacin Najeriya_
Mai_Dambu
Farga daji....
BABI NA UKU
--------------------------------------
Ina jin hayaniyar yan uwana, amma sabida kasancewa ta, mujiya a cikin su, ya sani
kara lafewa a gadona, ina had'iye yawun, sakamakon kamshin soyar namar da ake na
sunan Ikilima matar Ya Abubakar, wacce ta haifi d'a namiji aka sami shi sunan Baba
Malam.
"Mama yar sarki me rigar mutum ba zata fito bane ayi aikin da ita? Wato ga
bayinta su gama mata, ta zauna ta cinye?" Inji Aunty Hafsah, yayata ce da muke ciki
ɗaya.
D'aga labulen Yaya Binta tayi dan ita ce ya ta farko a cikin gidan mu, ta
kalle ni na tashi zubur ina zare idanuna da suke cike da kwalla. A hankali ta sake
labulen sannan tace musu.
"Da bata yi aikin sai ya kashe ku? Hafsat da Safiya kuna bani mamaki. Da akace
karta na yawan shiga damuwa shine bari kuyi ta sirka mata rashin mutunci?
Hmm! Zuciyarta yana tabuwa da abinda kuke mata, idan rayuwarta ce baku so!
Shi kenan, zaku iya Cigaba da abinda kuke."
Daga haka ta wuce dakin Mahaifiyar su. Cikin jin haushi Safiya tace.
"Yarinya ta gama rashin kunyarta tare da mana sanadin mahaifin mu, amma ake ganin
bata yi kome ba, har abada ba zan tab'a yafe mata ba, taji kunci da Baba Malam yaji
lokacin da yake rokonta arzikin da bai mata ba, amma fir taki kula shi."
Haka suka yi ta mita, tare da jin haushin yar autar su. Wato Anum.
... Duk ina jin su, amma bani da ikon fitowa wajen domin ina fitowa zasu min
caaa, dan haka na cigaba da zama a d'akina. Har zuwa azhar da na fito alola, naga
yadda suke kallona, jikina ne ya dauki rawa, kamar zan kifa, dan har tsalleke
abubuwan nake sakamakon tsawar da Aunty Hafsah ta daka min.
"Ke wata irin dabba ce? Kin zo kina niman zuba mana, ruwan butar a cikin abincin da
muke banza akuya, karya k...."
"Hafsat!" Ya Aminu ya daka mata tsawa, cikin jin haushi ta ce mishi.
" Ba ajiyar bace? Ko ba karyar bace? Wallahi har kunyar nunawa kawayena wannan yar
iskar cikin mu daya, sabida yadda ta zama taxi.."
"Kina da ƴaƴa mata, sannan kina zagin yar uwarki ciki ɗaya, sabida ajizanci."
Take kowa yayi mata caaa, ni kam nasan haka zai faru, da bi bango na isa d'akina,
na zauna tare da sake kuka me mugun ciwo, wanda su kansu yan wajen duk sai da suka
ji yo ni.
Kallonta kowa yayi cikin jin haushin abinda ta aikata, sannan suka ce mata.
"Yayi miki kyau!"
Maman su da take jin abin a cikin ranta, share su tayi amma tasan duk abinda
Khadijah Anum tayi ba laifinta kadai bane har da nata,a matsayin ta na Uwa ta gaza
tsawa yar autarta ta zama abin alfahari.
Itace ta gina mata kome na rayuwar da tayi, ita ce ta nusar da ita abinda zata
aikata, ita ta nuna mata kudi da kyau sune cikon muradinta,. Ba lallai sai ta zama
mace ta gari ba, zata iya zama mace mafi daraja indai zata hadu da me daraja.
Haka ta share kukanta a cikin dakin ta, dan bata son yaranta su gani wutar
k'iyayyar da take ruruwa a tsakaninsu ya kuma tashi.
--- bayan sun gama kome, suka shirya tare da barin gidan, suka nufi gidan da
ake taron sunan wanda yake Makara huta, dake garin bauchi. Suna shiga aka shiga
tambayar su.
"Ina Anum? Aunty Hafsah"
Inji wata budurwa wacce ba wuce shekaru ashirin da hudu ba, duk da bata girme Anum
ba, amma kuma zasu iya zama kusan shekaru daya.
"Shukrah, yaushe kika zo daga Kano?" Murmushi sannan tace mata.
"Yau kwana biyu kenan, don Allah Aunty Anum zata zo ne?"
Tab'e baki Hafsat tayi sannan tace mata.
"Ban sani ba, ko zata zo ashe."
Ta wuce Shigowar Mahaifiyar yarinyar ta mike tare da amsar jakarta, tana faɗin.
"Ammih Aunty Khadijah Anum ba zata zo bane?"
Shiru tayi sannan tace mata.
"Kuma na manta da sakonki, Amma Insha Allah zata zo dan naji tana cewa idan kanta
yayi mata sauki zata zo."
"Toh Ammih, Allah yasa kin san yanzun Aunty Anum ta zama wata iri ne tsoro ln
shiga mutane take."
Kallon ta Uwar tayi sannan ta girgiza kai, ta wuce komawa gurin Kawayenta
tayi tana gaya musu, bata zo ba amma Insha Allah idan ta kama suje bakin kura sai
suje.
---
"Toh ishashiya, kowa ya tafi gidan sunan shine ba zaki tafi ba!" Inji Mamarta.
Sunkuyar da kai