Back to novel

Chapter 6 of 20

RUGAR SAJE Farashin Tsira by Nusaiba Ayuba

mazan ma bai raga musu dan mugu ne lamba daya.



Duk wata kulawa da wani gata Mairoji tana samunsa awajen yan uwanta, kowa so yake ya jata ajiki(kunsan duk kudinka idan baka da kyau, ba kowa ne zai ce yanayi dakaiba, amman idan kana da dan kyanka, har fariya ake anunaka amatsayin kawa ko dan uwa=Ø4Þ=Ø6Þ).



Da haka aka fara shirye shiryen biki, dan sun bari idan aka gama hidimar bikin zasu dunguma zuwa can Rugar Saje, dan ganin juna.





++++



"Malik...wai da gaske zuwa Maid dinna zakayi, watau kaima ka koyi giringidishi bikin kawar kawa ko?".



Murmushi yai yace" broh....na fada ma badan bikinnan zani Maid ba, wllh ji nake kamar kirana akeyi acan din, kuma kaima ka sani Salman tsohon aboki na ne, duk da ba shi ya bani katin bikinsa kai tsaye ba, amman ai cewa yai atabbatar ya iso gare ni, ni dai tunda ba zaka ba kawai ka dena min magana, ba ruwana da kai, har na dawo".



Yanda ya karasa maganar yana tura baki, sai ya bawa Ahmad dariya yace"sory....dan autan Mamah, dan autan yayansa, kaima kasan banda asatin sama zan koma wajen aiki iada tare zamu ko, kayi hakuri kaji bansan na kumayi laifi irin wannan karo, kusan shekara biu kenan ziwan da mukayi kaga sai dana kara kusan sati uku ban koma ba, kuma duk saboda kai, kayi hakuri to ai bikin naku ne, kune angwayen, Allah yasa kana zuwa ka hadu da yar furanniya ta min gaba da zuciyarka".



Cime da sakalci ya dafe saitin zuciyarsa yana lumshe ido yace"broh...ina ajiki na wannan furanniyar data dade da tafiya da zuciyata kamar ita zanje gani, kar ka damu, nest hutun da zamu dawo sai maganar aurena".



Ya fada mai yana kanne mai ido daya, duka Ahmad ya kai masa akafada, yana dariya yace"yaro ya girma fa, dole ma na maka aure matarka ta karata da kai da shirmenka".



Cike da kaunar juna Ahmad ya taimaka masa ya hada kayansa awata yar jaka kamar ta goyo mai kyau, dan washe gari zai tafi Maid bikin tsohon abokinsa Salman.



   *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



   _11_



   Ranar da mata sukayi taro kamu , ya kama laraba ne, kamu sukayi irin na asalin kanuri, hatta da kofunan wajen kamshi suke, haka duk wanda ya gifta sai kaji kamshi na tashi.

   Awajen ne wani dan uwansu Gimba ya makalewa Salme, da fari taki kulashi, sai daya fito da wayarsa da aka kirashi ya daga, zaro ido tayi cike da mamaki domin, iphone 12 ce, ita tunda take bata tabajin ance gamai irinta ba, sai dai tana tsintar labarinta amakaranta bakin kawayenta.

   Sai bayan ya gama wayar ne ya dawo kanta yace "Salma, kinyi shiru da gaske nake fa, bada wasa nazo ba, tun zuwanku da ganinki hankalina ya kwanta, nasan na samu matar aure na".

   Kai ta sunkuyar tana sakin murmushi, itafa ko kadan bai mata ba, kawai dai taga kamar yana da masu gidan rana, dan haka zata je dashi ne, kafin ta samu wanda ya fisa.



Ganin ya samu karbuwa ne ya nemi ta bashi number dinta, amman sai tace ai bata da waya, wayarsa ya daga yai kira, bayan kamar mintuna goma sai ga wani yaro ya shigo wajen da ake taron, mika masa leda yai ya fita shi kuma ya mikawa Salman yace ta bude.

   Ido ta dan zaro ganin kwalin sabuwar wayar infinix hot 8, dagowa tayi ta kalle sa zatayi magana, yace" u deserved it baby, indai kin amincewa aure na baki da matsala dani".



    Marairaice fuska tayi tace "amman kyautar tayi yawa, wayace fa mai tsada, kuma daga haduwar farko?".



    Shima langabe kai yayi yace" ai duk tsadarta bata kaiki ba, kodan mu bar wannan maganar, muyi abinda zai fi mana muhimmanci ko".



+++



    Washe gari sukayi wani taron su na maza da mata(na manta sunan sa, amman baribari kun san shi ai), awajen ne ango zai bawa amaryarsa kyauta, ta bajinta, idan dangin amarya sunga kyautar ta musu, sai su rama masa bayan ankai amarya, da duk abinda suka san zai sai mata daraja.



  Aranar ne Baba Gana yaga Simrah, dan tun zuwansu bai ganta ba, tana can yan mata na daukarta, dan yarinyar badai farin jini ba da shiga rai, kura mata ido yayi cike da faduwar gaba, cikin sarkewar harshe yace"kai ku nemo min Bara'u, maza".

da saurin su kuwa aka kira Baba Bara'u awaya, aka sanar dashi kiran da Baba Gana yake mai, koda yazo bai saurari gaisuwar daya kawo masa ba ya nuna Simrah, bakinsa na rawa yace "sak fuskar Saddiq, wallahi wannan jinin Saddiqu ne, duk inda yake wannan jininsa ne".



Kallon Mairoji yayi yana hawaye yace, " yar nan, ina kuka ganemin Saddiqu na, wannan 'yar sace na tabbata, wannan jininsa ce".

Abun daya ke ta maimaitawa kenan, hawaye nabin fuskarsa, kwantar mai da hankali akai, da cewa ai Saddiqun ya kusan zuwa akarshen watannan, da haka suka lallaba suka baro wajensa.

Adakin da yan matan suke taruwa Mairojin take tambayar wata Fannah, waye Saddiqun da ake fada.



Gyara zama tayi tace"Ya Saddiqu alabarinsa babu abin dauka,shi ne jikan Baba Gana na fari, mugu ne na bugawa ajarida, idan yana gidannan bamu isa muja numfashi da kyar ba, ko mazan gidan tsoronsa sukeyi, yanzu shekara kusan bakwai kenan baya nan, ba'anan inda ya tafi ba, amman awasu radi radin ance, ya hadu da yan kungiyar tada kayar baya ne, da shi yaron su ne, kafin shi ma ya zama ogan kansa, kuma ahakan kaf cikin jikokin Baba Gana yafi son sa, bama iya Baba Gana ba, har sauran iyayen mu maza da mata, yana da wani irin farin jini duk da wannan mugayen halayen nasa acikin families dinnan namu, yan mata da dama suna jarabar son sa, uhm....idan nace miki zan fayyace miki waye Ya Saddiqu , batun zai kaimu har dare bamu gama ba, kawai abinda zance miki ki iya takunki idan ya dawo, dan bai san bako ba shi".



Tunda ta fara Salme da Mairoji ke kallonta tare da al'ajabin wannan da kowa yake kaico da dawowarsa gida, sabanin wasu da suke murna idan wani nasu da ya dade baizo gida ba, zai zo.



Watsar da zancen sukayi anan, suka shiga harkokinsu, domin gobe ne za'a daura aure.





++++



Wajen hudu na yamma Salman shi da wani abokinsa suka taro Malik , ahanya banda shagiyanci babu abunda suke mai, Salman harda cewa " Katon tuzuru, har yanzu shiru dai, ka bari kawai idan nayi auren zan fada ma yanda yake, idan na haifi yarinyata ta fari sai na ma kiyo".



Harara ya maka mai yana tsaki, cikin sanyin rai yace"ajiyata......ajiyata nake jira ta kirani, zaku sha mamaki idan na tashi aure na".

"Zaka auro yar sha tara ne, malam mai akidar auren karamar yarinya".

Baki ya tabe yace " ko ma dai meye, idan nayi aure, sunana mai gida, kamar yanda za'a cema maidiga".



Dayan abokin da suke tare yace"wai Salman wannan ba dan ball dinnan bane, dana sani kamar Malik B.M?".



Salman yace "shi ne mana, rabona dashi tun da mu kayi makaranta a Ringim, kusan shekaru shida kenan bamu ga juna ba sai yau, wai dan ma muna danyin waya jifa jifa".



Bakin abokinnasa har kunne, yau gashi ga shahararren dan wasan nan, da kowa kesan ya gansa koda sau daya ne, lallai bikin Salman yazo mai da abunda bazai manta ba.



Har suka karasa gida, Salman tsokanar Malik yake, da katon tuzuru.





+++

Akaguce Salman ya runtsa yana tsimayin zuwan gobe, anan ne shima Malik ya rama, suka hadu suna mai tsiya.

Washe gari kuwa kafin tafiya daurin aure Salman ya ce su shiga su gaisa da Ammyn sa, da kuma Kawu, har Malik din na ce masa shi fa kunya yake ji, takanas baije Kano gaida Ammy da Kawu ba sai da bikin sa, dariya Salman din yamai yace" wannan kuma matsalarka malam, zuwa dai ya zaman ma dole".



Yana sinsinke kai ya gaida Ammy, bayan sun danyi raha kamar yanda aka saba, har da Huda data gama mai tsiya, tace "kai Malik, rabon mu dakai tun a Ringim, lkcn kuna gaba dani, amman bazan manta lokacin ba, sai dai ka kyauta daka zo, Allah yabar zumunci".



Amsawa yayi da amin, sannan suka tashi fitowa, karo suka kusan yi, yai saurin ja da baya, cike da jin haushi, bai ko kalli wadda suka so bangazar juna ba ya sa kai zai fice.

Har ya fita yaji Salman yana magana, da sauri ya juyo yace " maimaita abinda kace, wane suna naji ka ambata yanzu".



Cikin mamakin sauyawarsa daya gani lokaci daya yace"cewa nai Mairoji an sha kyau, ko kaine Mairojin da zaka nemi rudewa?".



Cikin fitar hayyaci ya cakumo rigar Salman yace "a ina kasan ta, tana ina, ina take?".

Gaba daya ya rude, yanda kuma yake maganar murya asama sai ya janyo hankalin wanda ke wajen.



" Ya Malik...!".



Da sauri ya juya yana kallonta, aiko cikin mata dubu ne zai gane ta, kuma ko wankan inji za'a mata, sai ya gane kayansa, da sassarfa ya karaso wajenta, baiyi wata wata ba janyota jikinsa ya rungume ta tsam, yana hadiyar zuciya, itama rungumesa tayi tana sakin wani kuka, yayinda shi kuma ahankali yake bubbuga bayanta alamar rarrashi.



Jin an dafa bayanta yasa ta sake shi ta juya, ganin Ammy yasa ta kuma sakin wani kukan, tace"Ammy yaya nane, dan wan Mamata, kuma dan kanwar babana, shi ne ya Malik dinmu, wallahi shi ne Ammy".



Kawu ne yai gyaran murya yace"yanzu dai lokaci na kure mana dan haka mu karasa wajen daurin auren , tunda abu yazo duk na gida ne, daga baya sai a tattauna".



Fita sukayi dukansu, amman Malik sai waigen Mairoji yake, gani yake kamar idan ya dawo za'a ce masa ai mafarki yayi, ko kuma gizo idonsa yamai.



 

*RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*





–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo



*œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



_12_



Bayan an dawo daga daurin aurenne, aka kuma taruwa ababban falo, sai da Malik ya kuma ganin Mairoji da idonsa sannan ya yarda ba mafarki ne ko gizo ba, Baba Lawan ne ya bude taro da addu'a, sannan ya tambayi Malik dangantakarsa da Mairoji, babu wani dogon bayani ya fada musu yanda suke da ita, take wajen ya kaure da hayaniyar murna, sai da Baba Bulama ya yi magana sannan akayi shiru, Ahj Bara'u ne yai gyaran murya yace"to Abdulmalik kamar yanda ka fada mana dangantakarku, muma nan zamu fada maka dankantakarmu daku biyun duk da ita Maryam din ta sani, kaine dai baka sani ba".

Nan ya sanar da Malik yanda suke, da kuma yanda su Mairoji suka zo hannunsu, kamar yadda Kawu ya musu bayani. Idon Malik taf da tsantsar tausayinsu yake kallonta kamar ya maidata ciki, haka yake ji.



Bikin sai ya zamana anyi shi cike da jin dadi, domin kowa ka gani da farin cikin faruwar abubuwa da dama atare dashi.



+++



Bayan sati komai ya gama kintsuwa na hidimar da akayi, sannan ne aka fara haramar zuwa can Dutse tunda Malam Ahaji ya koma can da zama, babu yanda Mairoji batayi ba da Malik ya kira mata Goggoji awaya yaki, ta nemi ya bata lambar da zata samu wani na gidan ma amman yaki, yace bazata yake son yi musu ne.

Sauran kwana biyu su tafi haka ya dauketa da sauran yan matan family da zuwansa gidan duk suka tare agidan, domin ba kyarya, ya tafi da imanin da dama daga cikinsu, ko da suka fito za'a tafi ma sai da wata Sakeena ta bata mai rai, abin daya faru kuwan.



Sun fito sai Mairoji ta bude gidan gaba zata shiga, zaraf sai sakeenan ta rike murfin motar tace wa Mairoji ta koma baya, to ta girme mata, sai batayi musu ba juya zata shiga bayan, shi kuma yana ganinsu tunda yana mazaunin direba ne, bai kula su ba sai data shogo ta zauna ne sannan shi kuma yace ta koma baya itama, kallonsa tayi taga kamar bashi yai magana ba, ita ma sai ta dauke kanta, dan ta nuna mai tanada aji , ransa ne ya baci dan bai fiya son yana maimaita magana daya ba kamar karamin mutum, kin tada motar yayi , a karshe ma sai ya fita ya koma kusa da maigadi ya zauna yana laluben waya.

Takaici ne yasa Sakeena fitowa tana watsawa Mairoji kallon tace "saiki koma gaban ai, sai kuci uwar da zaku ci".



Ita dai Mairoji ba tace uffan ba ta koma gaba ta zauna, sauran yan matan suna kallonsu, daga masu hararar Sakeena sai masu hararar Mairoji, kamar mintuna biyar sannan ya shigo ya tayar suka tafi.



Wani babban Supermarket ya kaisu, yana cikin motar bai fita ba dan yaga wajen da mutane, kuma yana fita zai janyowa kansa hayaniya, cemusu yai kowacce taje ta dibi abinda take so, har sun fita ya kira Mairoji ya bata card dinsa bayan ya fada mata code din da zata sa, sannan suka shiga cikin wajen.



Suna shiga kuwa Sakeena ta karbe card din tana harararta, murmushi tayi aranta tace 'zaki dawo dashi ne' . Kaya suka zage suna diba kamar ance musu kyautane, abin harda hauka da fariya, masu hankalin cikinsu sune suke daukar abun da zai amfane su.

Mairoji kam, bangare turare ta nufa wani mai dan karen dadi ta dauka, irin na maza, sai agogo na maza, mai kyau da tsada, sai necktie, ko wanne hurhudu ta dauka, sai bangaren abin hannu dana kafa, ta zabi masu kyau kusan set uku, iya abin data dauka kenan,sai man zafi data dibarwa Goggoji, dan tace shi kadai zata kai mata tsaraba, sai bangaren kwalam data nufa, anan suka ci karo dashi, dan da fari bata gane sa ba, sai daya dago kansa sannan ta gansa, riga mai hula ce ya dora akan kayansa, ya rufe kusan rabin fuskarsa, kallo daya ya mata ya dauke kai yana kallon tarkace cakulatin data kusan cika kwandon hannunta dashi, rabawa yai ya wuce wajen jallabiyun mata da jakkunkuna.



Sai da aka zo wajen biyan kudinne, sannan Sakewna taji wata kunya, don cewa akai ta fadi code din amman bata sani ba, har mutumin na mata kallon tuhuma, Mairoji da tun tuni take bayanta tana mata dariyar mugunta ta matso, ta fada masa, bayan ya saka ne da karanbani Sakeena ta mika hannu zata karba, shi kuma ya hanata ya mikawa Mairoji harda karin nasa card din yana murmushi, yace"idan an huta gajiya, dan Allah atabo ni ta wannan lambar".



Murmushi tamai kawai ta wuce, suna fito wa suka hangosa har lokacin yana zaune amota yana shan vanilla icecream, suna shiga, ta mika masa katin amaimakon ya karba kawai sai ya share ya dora mata ragowar icecream din akan kafarta.



Zata dauka Sakeena tai saurin daukewa tana murmushi yake tavmce"yayanmu ba ka sani ba ai Maryam bata shan kayan sanyi, da dai mune nan mufa fi kauri".

Ta cikin mirror ya mako mata wani bahagon kallo, amman sai ta mayar masa da murmushi tana lasar labbanta data jikashi da icecream din.



Kai ya kaudar yana jin takaicin yarinyar, rawar kanta ya fiye yawa, da alama sai ya saita mata kai tukun zasu daidaita, wai Maryam bata shan kayan sanyi, to shi yanzu kaf duniya akwai wanda ya kaisa sanin wace Maryam, aiko Goggoji data tashi agabanta ba zata ce masa tasan Mairoji sama dashi ba, amman tabban idan taci gaba damai wannan shisahigin zai ya maganinta ne.



Koda suka koma gida, kowacce taje ta nunawa uwarta kayan da Malik din yasai mata,tuni iayaen suka fara yiwa yaran fanfo, ta yanda yarinya zasa same sa cikin sauki, tunda Allah ya yishi mai sakakken hannu ai dole ma ayi tafiyar dashi.





+++



Ranar da zasu tafi, da wuri suka shirya duk da cewa jirgi zasu bi, Mairoji har kuka tayi ita ba zata hau jirgi ba, amma haka Malik yai banza da ita, karshe mai sai yabar gidan dan zuwa tai tasa shi agaba da fitina, shi kuma baya son jin kukan ne.





+++



Kamar yadda suka wayi gari da daukin zuwa gida, haka suma mutan garin Dutse suka tashi da hidimar zuwan Haj Tako da sauran matan kanne da suke zaune tare dasu.



Tun dare Malam Saje yake jin faduwar gaba da tsinkewar zuciya, amman bai bari Goggoji ta kula ba dan yanayin jikinta, sai da safe ne ma Abba yake fadamai ya kwana da wani irin yanayi, nan shima Malam Alhajin yace mai ai shima haka ya ke ji tun dare, to sun dai barwa kawunan su batun, tare da addu'a Allah yasa alkhairi ne ke kusantosu.



Uku da wani abu na rana suka sakarwa mai gadin gidan Alhjai Badamasi horn, da azamarza ya bude yana mamakin daga ina, dan manyan motoci ne guda biyu sai kananu uku, kusan duk wani babba dake cikin motar gabansa ya tasannata bugawa dan basu san da wane ido yau zasu kalli dan uwansu kuma uba agurin wasu, hakanan kaka agun wasu.



Sai