Back to novel

Chapter 7 of 20

RUGAR SAJE Farashin Tsira by Nusaiba Ayuba

dai gani Malik acikin daya daga cikin motocin yasa mai gadi maida mamakinsa, yana musu sannu da zuwa, kowa gidan yake karewa kallo suna yabawa tsarinsa.

Dungumawa sukayi zuwa cikin gidan kamar yadda Malik ya musu jagora, afalo suka yada zango dai dai lokacin Abba na saukowa daga matakalar bene, idonsa ne ya hangomai mai kama da mahaifinsa sak, sai ya danfi mahaifinnasa girma da shekaru, da sassarfa ya karaso yana aro juriya ya daurawa fuskarsa dan jin zuciyarsa kamar zata fado, kafin ya samu damar musu magana ne yaji muryar da bazai manta da ita ba ta daki dodon kunnensa.



"Abbah na...!"



Da saurin sa ya juya yana kallon Mairojinsa kamar amafarki, da gudu ta karaso wajensa sai dai ta ja ta tsaya tana sakin kuka, kafadunta ya kama cikin rawar murya yace"uwata.....kece? kece Mamana, Mairoji ta, ke nake gani ? Alhamdulillah, ya Allah na gode maka daka nunan baiwarka, Allah na gode maka".



Mama ya kwalawa kira da itama kamar taji muryar Abban na kiran Mairoji da sauri ta sakko tana kallon mutanen dake wajen kusan rai ashirin manya da yara, duk da ta ga Mairojin amman sai ta dake ta tarbi bakin da ta gani wanda hakan shiya janyo hanaklin Abbah shima ya tarbe su aka shiga gaisawa, Kawu ne ya fara magana yace "baku waye damu ba, amman idan babu damuwa muna son ganin Muhammad".





Babu bata lokaci Abbah ya cewa Malik yaje ya taho dashi daga can bangarensa, bayan kamar wasu yan mintuna sai gashi tare da Goggoji data matsa sai tazo taga wa yake neman mijinta, suna shigowa Baba Gana daya kafe kofar shigowa da ido ya mike yana nuna Malam Saje da hannu bakinsa na rawa yace " Autan Ya Mallam".

Duk duniya Malam Saje yasan babu mai kiransa da wannan sunan sai yan uwansa, shima jikinsa har rawa yake ya zube agaban Baba Gana cikin rikicewa yace"Baba Gana, Yaya Lawan, Yaya Baraka, Hajja Yaana".

Yana gama fadar sunansu ya fashe da kuka mai mugun cin rai, Lawan ne ya riko kafadunsa ya tashe sa ya dawo dashi tsakiyarsu yana share mai hawaye, shima kukan yake amman kira yake"Autan Ya Malam, kuka ya kare ai, ya isa haka kaji".



Vda kyar dai aka samu tsoffin nan sukayi shiru da kukan murnar ganin junansu, sannan ne kuma su Goggoji suka kula da Mairoji da sai cika take wai Mamah bata kulata ba, baki taru zata fara musu abinda aka dade ba'ayi ba, Malik ya watsa mata kallo, sannan ya mike yace "Part dina yayi kura, kije ki gyaran, minti talatin na baki, kafin na fito daga bangaren Mamah ki tabbata kin gama".



Cikin rashin sanin maganar ta fito fili tace " daga dawowata, ko hutawa banyi ba, ban gana da iyayena ba, afara da bani aiki, ni dai gaskiya...."



Juyowan dayai yana kallonta ne yasa ta gane yaji mai tace, tashi tayi ta nufi hanyar fita dan pard dinau da Ahmad na tacan bangaren ajiye motoci.



Babu wanda ya kula ta, sai Baba Bulama ne ma zai magana Malam Saje ya tare sa"kyale ta, dole ai ta sabawa hidimarsa, tunda wataran karkashinsa zatayi rayuwa idan Allah yaso".





    *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



_13_



  Bayan fitar ta ne sannan aka shiga bawa juna labarin bayan rabuwa, kiran sallahr la'asar ne ya tada su, matan  bangaren Mama aka kaisu, yan matan kuma dakunan su Ummie, Laure yar rawar kai har ta samu abokiya dan tuni suka dinke da Sakeena, samarin ma bangarensu Malik aka kaisu, kowa dai da inda aka kaisa dan ya huta.



    Bayan isha aka kuma haduwa, dan zuwa lokacin su Haj Tako sun zo, Mairoji da Ummie suna dakin Mamah dan can maman tace ta koma, shira suke  cike da kewar juna, wayarta ne yai kara tana dubawa taga bakuwar lamba, kin dagawa tayi har kusan miss call biyar, sannan aka hakura da kiran, bayan kamar mintuna uku sai ga Mamah ta shigo kallon yanda sukayi baja baja akna gadon tayi ta girgiza kai tace"an hadu kuma, ba sauki sai na Allah, kije yayanku na kiranki, yace ki hada masa shayi da abu mara nauyi yunwa yake ji".



   Kamar zatayi kuka haka ta tashi, ta daura hijab akan kayan baccin data saka, kicin ta shiga ta na tunanin me ya kamata tayi masa to, taliya tadauka, bayan ta dauko kifi a frige ta gyarasa ta dora akan gas, tana gama tafasashi ta dauko kabbage da yakan spieces, nan danan ta hada mai miyan kifi da kabbage, bayan ta dafa mai taliyar fara, tana juyewa taji an shigo, dubawa tayi taga Sakeena ce da Laure, dauke kai tayi dan tasan halinsu ba kai ne da su ba, yanzu zasu nemi yi mata tijara.



   Ashe wai suma sun je nemantane dan Sakeena nason karban wannan card din na Malik, shi ne Mamah tace musu tana kicin.

   Kallonta sukayi awulakance, Laure ta fara bude flaks din data gani arufe, kamshi miyarne ya daki hancinta, ta hadiyi wani mugun yawun kwadayi, dayan ta kuma budewa taga faran taliyace, wani faranti dake gefe ta dauka zata diba, dan bata bi takan Sakeena dake titsiye Mairoji ina katin yake ba, burinta kawai ta dibi abincin dan da gani miyarnan zatayi dadi.



    Dagowa tayi zatawa Sakeena tayin diban abincin, karaf idansu ya hadu yana aika musu da wani kallon idan na kama ku, da sauri ta ajiye farantin tana sunkui da kai.Sakeena ce itama ta kalli sashen da yake, cikin inda inda ta fara neman kare kanta, dan ya ganta ne dumudumu ta murdewa Mairoji hannu.



Bai musu magana ba, illa farantan daya diba da abin dazai bukata, fita yayi bayan yawa Mairoji kallo daya, ya dauke kai.Itama babban faranti ta dauka ta jera komai akai har da flaks din shayi haka ta raba ta gefensu ta fita.



Sai bayan fitar ta ne, sannan Sakeena ta sauke gwauron numfashi tace wa Laure"wllh gayennan karshene, ya gama tafiya dani, amman waccen shegiyar yarinyar da alama kanta na rawa, kuma zan saita mata shi, Malik ai mijin manyan yara ne ba, irinta kwailaye ba, ni fa kinga ko da bazai aureni ba, zan iya basa kaina, dan da gani zai bada wuta, Allah ya basa irin zubin da nake so ajikin namiji, wllh ko zan rasa komai na bazan yarda na rasa wannan hajar ba".



Baki Laure ta tabe tace"ai wllh duk haduwarsa bai kai yayan saba, tab....ke kinga Ya Ahmad kuwa, karshen kyau da haduwa".



"Au daman yana da yaya, amman ba'a nan yake ba ko, dan tunda muka zo ban gansa ba".



" yana da wa, wanda suke uba daya, babarsa kanwar Hajiyarmu ce, auren zumunci aka musu, amman ta rasu tun bayan ta yaye sa, sai dai fa yafi kanin nasa dadin sha'ani, yanada da dadin zama".



Sakeena tace "wowww amman zanso na gansa gaskiya, naji kince yafi wannan haduwa".

Harara laure ta maka mata tace" ki kama kanki, Ya Ahmad nawa ne ni kadai, abinda zai fi miki shi ne ki kama Malik, dan dashi kika fi dacewa".



Shiru Sakeena tayi dan ta tabbata Laure ta fita buyagi, kuma ta fita iya tafka rashin mutunci dan haka taja bakinta tayi shiru, har suka karasa dakinsu, sannan suka shiga wata shirar, anan Sakeena take fadawa Laure ai Mairoji cikin shege fa tayi shi ne ta haifi wannan yar tata, nan tayi ta mata famfo, tare da zugata akan ta tabbatar yan uwansu na nan sun san abinda Mairoji tayi, domin karta bata musu sunan gida.





++

Ahankali ta tura kofar falon ta shiga da sallama, yana kwance rigingine da kananun kaya kamfanin addidas, rigar armless sai wandonta treequarter, remote ne ahannunsa yana serching na wasu tashoshin ball, bai kalle ta ba amman ya amsa sallamar aciki.

Ajiye tiren tayi akan center tabble dake tsakiyar falon, faranti daya ta janyo ta fara hada masa abincin, bayan ta gama ta hada masa shayi awani babban kofi, sannan ta mike tayi hanyar fita, sai data kama handle din kofar sannan yai magana yace"waya baki izinin fita?".



Cak ta tsaya sannan ahanakli ta tako ta dawo gefensa ta tsaya tana cura baki, dan ita barci take ji, yana hankalce da ita amman sai ya share ta, bai ankara ba sai gani yayi tana sharar kwalla, tana jan shessheka, tashi yai zaune yana kara daure fuska, tuni ta hadiye kukan da take shirin saki, gefensa ya nuna mata alamar ta zauna.



Ba musu ta zauna tana takurewa waje daya, farantin data hada mai abincin ya turo mata gabanta, murya can ciki yace"cinye kibani flat din".Shi kuma ya dau kofin shayinsa yana sha, ya maida hankalinsa kan tv.



Adan raunane tace"nifa na koshi".

"Kina batan lokaci".

" Allah ni dai na koshi, kuma ni barci nake ji".

"Raini ya fara shiga tsakaninmu ko?".

Jan hanci tayi tana sauke wasu kwalla, ta janyo abincin ta fara ci, tan matsal kwalla, da yake gulmaammiya ce sai gashi ta kusan tashi da fiye da rabin abincin, ruwa tasha tana sauke gyatsa, tare da yin mika tana hamma.



Harararta yayi yace" dalla sauke hannunki kasa, kin wani cikamin hanci da warin hammata, kazama kawai, tashi ni kibani guri".



Tashi tayi tana cura baki ta fita, tsayawa tayi abakin kofa ta daga hannunta tana shinshina hammatarta taji wai ko da gaske warin yake, karamin tsaki tayi jin banda kamshin sure babu abinda ke tashi, hararar kofar tayi tana sakin kwafa, sannan ta wuce bangarensu, tana shiga ta tarar da Ummie har tayi barci ita da Simrah, rabawa tayi gefensu itama ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya.





++++



Mutanen Maid sun dau kusan sati sannan suka fara haramar juyawa, Babagana ya dage lallai sai da Mairoji zasu tafi, magana dai har takai gun baban Mairoji shima ya shiga ciki, da kyar aka barta akan zata na zuwa Maida ita da sauran yan uwan na nan don karfafa dankon zumunci.

Salme ma an mika ta ga ahalinta, sunyi murna sosai kuma sunyiwa Kawu godiya daya tsaya mata har ta kammala sakandire, anan ne kuma suka nuna aure zasu mata, tunda ta isa, Baba Lawan ne ya nemawa Gimba aurenta, tunda shine jikansa na fari, kuma basu taho da iyayensa ba, dukda su iyayen Salme sunji dadi kuma sunyi na'am da abun, sai dai ita Salmen ba haka taso ba.



Burinta ta auri wanda zai tayata nunawa duniya itama wata ce, so take tayi auren da ko yaushe za tayi wa mutane alfarma akan komai nasu, burinta tayi auren da zata nunawa Mairoji ba ita kadai bace mai sa'a arayuwa, yanda kusan ko da yaushe Mairojin sai tazo wajen ta cin arziqi da neman alfarma.

Duk yanda iyayent suka so ku nuna mata dacewarta da Gimba abun yacu tura, karshe sai da wani kanin babanta ya mata dukar kawo wuka sannan aka samu sauki akanta, dukan daya sata daumar alwashin ramuwar gayya akan Mairoji, tunda duk kusan ita ce taja mata, da ace ta bar mata farinjinI da daukakar da take dashi ai da ba haka ba.



Bayan tafiyar yan Borno ne, da sati biyu Malik ya tattara ya koma, bayan dogon kashedin daya samu daga wajen Goggoji kan cewa yana kuma samun hutu ya dawo ayi maganar aurensa da Mairoji, amsa mata yayi da to sannan ta barsa ya tafi, dan Malam Saje yabi yan uwansa zuwa Maid.





+++

"Khaura Abdullahi Mahangi, ya ta uku awajen Ahj Abdullahi Mahangi, dan majalisa ne daya rike mukamai kafin wannan matsayin da yake kai, gaskiya gidansu ba laifi akwai tarbiya, kuma akwai wadatar ilimin addini, idan tayi maka, zan iyama jagora".



Numfashi ya sauke, sannan ya ce" ka fara min iso ga mahaifinta tukun, duk yanda yace sai mu ga me zamuyi akai".



Nan sukayi sallama, bayan tafiyar mutumin shi kuma ya kira Malik awaya, nan ya sanar dashi komai dan basa iya boyewa junan su duk abin daya shafe su irin haka.

Shima yayi na'an da batun cewa ya fara tuntubar mahaifinnata tukun, sannan ya sanar dashi abinda Goggoji ta fada mai, tunda daman tuni yasan da dawowar su Mairojin, dariya Ahmad yasa yace"kasan kuwan Goggoji ta rigani furtawa ne, amman nima abinda ke.raina kenan, atsaida maganarku kawai kowa ya huta".



Iska ya fesar daga bakinsa, yace "broh....wancen dan kwayar fa, ya dage lallai sai dai shi zaya aureta, Allah banda ina ganin darajar Hajiya da saina sa an kullen shi, bayan komai ya daidaita ya fito".

Ahmad yace " wai kana nufin Mamudan Hjy Tako?".



"" shi mana, yaron ya mugun shigarmin hanci da kudundune, kawai dai ana barin halas ne dan kunya, amman da yaga aikin yan kwaya wllh".



Dariya kawia Ahmad ke.masa dan babu abun dayake fahimta amutmryar Malik din sai tsagwaron kishi, samu yai ya lallaba sa sannan sukayi sallama.





_Allah ka bawa babanmu lafiya=ØOÞ_.





    *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



   _14_



Bayan wasu yan lokuta aka tsaida ranar bikin Malik da

Mairoji, da kuma na Khausar da Ahmad, domin sun tattauna atsakaninsu, sun aminta da juna kuma.

    Ranar da aka sanar da sa ranar bikin, Mairoji tayi kuka kamar idanunta sa fita, dan ita tunda take bata taba son Malik da sunan so na aure ba, Ahmad take so, shi ta taso da soyayyarsa, kuma shi take fatan kasancewa da shi amatsayin mijinta.



   Acan Maid ma ba karamin rikici akayi ba, dan Sakeena ta daga hankalinta ita Malik ne zabinta, so an tsaida magana akan cewa sai dai tayi hakuri, dan ba za'a so ta dalilin haka zumunci ya samu tangarda ba, da fari kowa yayi na'am da wannan zancen kuma an barsa, amman bayan wasu yan kwanaki sai ga Babagana ya kuma tada maganar yace dole ne abawa yarinya abinda take so, to sudai iyaye basu da ta cewa tunda Babagana dai shine babba dole sai abinda ya yanke za'a aiwatar.



  ++

Da Malik yaji zancen bai ce komai ba, Mamah tayi zaton zaiyi bori kamar yanda ya saba idan za'a masa abinda ransa bai so ba, sai dai abindaya fada mata ya sata wasi wasi, da kuma dora ayar tambaya akansa.

"Mamah...da Maryam da Sakeena dukansu kannaina ne, babu banbaci sai na halayya, kuma ko wacce dai da halinta zata zauna, illa iyaka dai wadda tamin rashin da'a, za ta gani akwaryar cin tuwanta".



   " amman Malik anya kuwan zaka iya rike mata biyu, zaka iyayin adalci atsakaninsu, karfa agarin gyaran zumunci abata zumunci".



Dariya kawai yayi yace "Mamah ki bar batunzanyi adalci ko ba zanyi ba, kawai idan kukaga yarinya na ware ta , to ku tabbata tana kawo min danyan kaine".



   Shiru tayi tana saurarensa, sai can ta ce"bazan boye ma gaskiya ba d'an Maliki, Maryam banyi maka sha'awar aurenta ba, Ahmad nayi wa sha'awar ya aureta, tunda da bakinka ka fada min ita zabin Malam Alhaji ce, gaskiya bazan baka yata ba kuje kuna gasamin ita kaida waccen yarinyar daba hankaline ya wadacetaba".



   Shiru yayi yana saurarenta, baice mata komai ba ya katse wayar dan bashi da kuma abinda zai fada mata, Ahmad ya kira ya fada masa komai, shima dariya kawai yayi yace " kaji Mamah da wani zance wai ni tayiwa sha'awar aurenta, to ai ni kallon kanwata nake mata, banda wannan ban taba kallonta da wata manufa ba, kaga share kawai maybe ta fadi haka ne, dan ganin ba iya yarta kadai zaka auraba, kasan mata ita nan tana taya yarta kishi ne".



  Baki ya tabe yace"koma dai miye, ni duk su biyun ai ba zabi na bane, idan sunce ma ba zasu bani ba, ban damu ba daman dan sun matsa nayi auren ne , banda haka ai da wannan maganar ma bata taso ba".



Cikin tsokana Ahmad yace"har ajiyar taka ma ba zabinka bace?".

   Shiru yai bai amsa masa ba.

"Ok....zan fadawa Mamah ahada ta da Mamuda, tunda shi tun asali ya nuna ita zabin sa ce".



Jin shiru bai amsamai ba yace " Boy....kana ji na?".



  "Yah......zamu dan fita ne da K2 , mayi waya daga baya". Tun kafin ya amsa mai ya kashe wayar yana jin haushinsu duk su biyun, daga Mamah din har Ahmad din.



++

  Ko abangaren Hjy Tako ma abun bai musu dadi ba, amman idan ta tuna ai namiji mijin mace hudu ne, sai taji ba tada matsala mai yawa, tasan yarta zata iya zuwa anan gaba matsayin matar Ahmad din, kuma burin da take ci dai sai ta cika shi.



Haka tasa Laure agaba har gurin wani badiddige yai mata wankan sa'a, da wani koren ruwa sannan suka dawo gida bayan ya basu tabbacin matukar Laure ta shafi jikinta dana Ahmad din to sai buzunsa dan zai zame mata kamar jela ne.

    Tun daga lokacin take taka tsantsan da hada jiki da wani, dan sharadin kenan, kar ta hada jiki da kowa sai shi, koda da kuskure ne, kuma ko tsaohon shekara zai kai baizo ba, kar ta damu, abun yana jikinta, makarinsa dai shi ne hada jiki da wani.



_______



  Maiduguri

    ______



Yau gidan kowa ya tashi da nutsuwarsa, domin sanarwar zuwan Saddiqu zuwa yamma, kowa ka gani acikin nutsuwa yake, duk da bata Allah da Annabi bace ta tsoron fadawa fushin Saddiqu ne.



    Aunty Yaana ita ce kusan babbarsu akaf matasa da yan matan gidan, ita kadai Saddiqu yake dan jin maganarta, ita tazo gidan dan atarbe shi da ita.



  Kamar biyar na yamma, suka iso shida yaransa kamar ko yaushe kusan su bakwai, ahakan ma ya rarraba su ne domin ayarinsu sunfi su talatin kuma shi ne ogan