Back to novel

Chapter 2 of 20

RUGAR SAJE Farashin Tsira by Nusaiba Ayuba

sukayi gaba dasu,can yankin maiduguri suka yada zango, amman cikin unguwar umalare, sai dai wannan karon gidane babba mai dakuna kusai bakwai, iya su kadaine aciki sai ko yaransa da suka rarrabu.



     Kullum banda kuka babu abin da suke yi, sun rokesu akan su maida su ga ahalinsu, amman sai ogan yayi dariya kawai, yace "ai mun gamu kenan, ku da danginku sai dai alahira, nan da shekara uku zaki zama matata, bayan wata tara kuma ki haifa mi yaro, dan an miji nake so ahaihuwar farko, wanda zai gaje ni, dan haka ku fitar da ran komawa wannan kazamar Rugar taku".



    Gaba daya dariya yaransa suka sa, suna nuna su Mairoji , wani kallo ogan ya musu nan danan sukayi shiru kowa ya koma bakin aikinsa, ahaka suke rayuwa kamar wasu marasa gata, kusan wata guda kenan Bad'ejo na fama da kanta, tun lokacin da abun ya faru take halin cuta,  sunyi tunanin rashin lafiya ne dako wace mace takeyi yayinda aka karbi budurcinta, sai dai ganin abun bana kare bane Mairoji da take ganin kanta wayayya acikinsu, tunda tayi karamar sakandire tuni tsohon karatun da aka dan taba ya motsa.



    Matsowa tayi kusa da Bad'ejon tace " ha...mu gani".

   Ba musu kuwan ta bude bakinta, nan Mairojin ta gama dube duben ta sannan tace ta rufe, idan ta ta dan bude ta duba gefe da gefe sannan ta tashi tana kallon oga daya fito daga bandaki, tabe baki tayi tace "malam sai ka fara tanadin kayan yaro da kuma ragon suna, da abin da za'a ci, da wallahi inta sauka lfy sai munyi taron suna".



    Kallon rashin fahimta yayi mata ya dauke kai, har zai shiga daki kuma sai ya juyo yace" wai dani kike...?"



Cike da turawa mutum haushi tace "ah...ah, da inuwarka nake".



   Murmushi yayi kawai ya shige daki, dan yanzu shi kam, wata irin soyayyarta ke dawainiya dashi.



    Kallonta bad'ejo tayi ta sa kuka tace " dan Allah Mairoji ke taimakan na zubda cikinnan, wallahi idan na koma da dan shege ruga kema kinsan kashe ni za'ai, ki taimaka karna haifi abinda zai zo ya zaman kalu bale ga rayiwata".



    Tsugunnawa Mairoji tayi tadan rungumo kanta, tana shafa bayanta alamar rarrashi, cikin kwantar da murya tace"kar ki damu bad'ejo muna tare dake, ba za'a zubar da cikinba dole.ne ki haifesa, sai dan da za'a haifa ya zame musu babban kalubale ga rayuwarsu, insha Allah ba bu wanda zai miki koda banxan kallo, bare yai tunanin cutar dake idan muka koma Ruga".



   Da kyar dai ta rarrasheta ita da salme dayar abokiyar tasu.



++++

   



     Da d'an sassarfa ya karaso wajen kujerun da aka ajiye dan hutawa, robar ruwa ya dauka ya kafa wa bakinsa, bai sauke ba sai da ya shanye shi tas, sannan yadau wani dan towel yana tsane dan gumin daya dan tsattsafo mai.

   Kallonsa k2 yayi cikin shakiyanci yace, "ya dai man.....ka fara tunanin wasan ne, naga sai zabgewa kake, ko dai aljanar take ce ta kawo maka ziyara take tsotseka ne bamu sani ba".



   Tsaki Malik yayi ya tashi ma yabar wajen yaci gaba da zagayen da yake, dariya k2 da sauran abokan wasansu suka sa masa, Kamal yace " kai guys ku dena dariya fa, gaskiya ku kula da MBM yana cikin damuwa, duk da bai damu da magana ba amman yanayinsa kadai ya nuna yana da damuwa, kune abokansa na jiki ku zaku fuskancesa ku gane mai yake damunsa".



      Shiru K2 yayi yana nazarin abinda Kamal ya fada, tashi yai ya bi bayan Malik din suna gewaye cikin sassarfa amman K2 yana kule dashi, tabbas yaga yana cikin damuwa amman yasan halinsa bazai taba fada masa ba, har yamma suna atisayen kafin kowa ya kama gabansa, kwanan biyar ya rage musu zasu fara karamin wasa, da kungiyar Bounmuth.





+++



Ayanzu kam su Mairoji har sun fara sabawa da zaman Maiduguri, duk da basu taba futaba tunda suka zo, kusan wata biyu kenan, ga laulayi da ya sako Bad'ejo agaba, kamar ba zata kai ba, da haka suke rayuwarsu cike da takura, duk dama ba bu wani abu da ake musu na rashin kyautatawa.



Yau garin sun tashi da fargabar wai wasu yan bindiga sun shigo, tun daren jiya oga suka fita shi da yaransa, sai suka kulle gidan ta waje, to basu kwanan agida ba har gari ya waye, wajen goma na safe aka fara harbe harbe, ga karar tashin boma bomai daya karade unguwanni, kuka Bad'ejo tasaka ta kamo hannun Mairoji tace mata"dan Allah karki bari wani abu ya same mu, kiyi wani abun kina jin mutane unguwa sai gudu suke, amman mu an kulle mu acikin gida, ina da buri akan wannan cikin na jikina, so nake ya zame min makamin da zan yaki wannan azzalumin dashi, ki taimaka mana mu bar nan dan Allah".



Ita kanta Mairojin duk dauriyar sai gashi tasa kuka, ta tabbata yau kam tasu ta kare, dan babu makawa mutuwa zasuyi awannan gidan.



Tashi tayi tana bin gidan da kallo cike da nazari, ta cen wajen bandaki katangar ba tada tsayi sosai, sai bata san ta cen baya ba kuma ya take, tsanin dake jingine agefe ta fara kokarin dauka sai dai yafi karfinta, hakan yasa ta kira Salme ta taimaka mata suka daga shi, suka jingina shi, sai data fara lekawa ta ga yanda tsahon katangar take ta baya sannan ta sauko, Salme tace ta fara hawa ta dira, sannan Bad'ejo sai ita ta karshe, ganin mata da yara na gudu kawai suma sai suka shiga cikinsu.



Tun hantsi suke gudun ceton rai, basu yada zango ba sai kusan la'asar, lokacin sun bar cikin gari sun shiga jeji, ga k'ayoyi da suka taka, dan Mairoji ma jin babban dan yatsanta take kamar ba'a jikinta yake ba, sai da suka tabbatar da sun tsira sannan suka zazzauna ajikin wani dutse, ban da kishi da yunwa ga gajiya da bakar azabar da kafafun su ke musu.



Bad'ejo kam tun tana amai da kuzarinta har ta koma kakari, dan babu komai acikinta, wata matashiya haka acikin wadanda suka tsira ta kalli yanda Bad'ejon ta lafe ajikin Mairoji tana sauke ajiyar numfashi da kyar, cike da tausayinsu tace"sannunku....ina kuka nufa daga nan?".



Cikin haki Samle tace"Rugar Saje muke son komawa, amman bamu san hanya ba daga nan".



Cikin kulawa, matashiyar tace"awane gari kenan, dan nan fa muna cikin Maiduguri ne, kuma ni haifaffiyar nan ce, ban taba jin sunan wannan garin ba".



Mairoji da tadan fisu sanin sunan garuruwa tace"amakartar mu dai nasan wani malami dayake zuwa daga Kano, yace mana babu nisa sosai tsakaninmu da da garin, kuma garin da yayan babata yake akwai duwatsu, sosai dan wani ma kamar ya fado miki idan kina tafiya".



Jinjina kai tayi , aranta tace"maybe irin yan mazauna kan karshen kanon nan ne, kuma garin da take nufi, ko can Dala ne, tunda ai akwai sauran duwatsu har yanzu acan.



Dafa Mairoji tayi ta mata murmushi, tace"shikenan ni ma wan babana yana kano ne, kuma nima can zan koma, inshaAllah sai mu tafi tare, kafin agano inda kuke sai akaiku".



Cike da murna suke ta mata godiya, sannan suka kuma daukar hanya suka nausa, dan so suke, su isa bakin titi kowa sai ya kama inda ya nufa.

Kuyi hakuri mutuwa aka mana sai yau na samu damar muku update, sory 4keep you waiting guys.=ØOÞ



   *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S. Sarkin zango.





*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*





–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo



*œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*

(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE.



_4_



    Sunyi nisa suna ta nausar hanya, wani abokinsu ne ya bada shawarar arabu, kar maharan su farga dasu, na'am su kayi da batunsa inda suka rabu kashi kusan biyar dan suna da yawa maza da mata, yara da manya, zugar su Mairoji suka nausa yamma, wasu kuma kudu, wasu arewa haka dai kowa ya nufi inda yake ganin matserata ce.



    Sai gab da magaruba su Mairoji suka iso bakin titi, zama sukayi suna haki dan sunyi matukar gajiya, sun dade anan ma kafin wata sharon  tazo wucewa sai daga mata hannu suke, amman bata tsaya ba, sai da tayi nisa sosai sannan ta dawo da baya direban ya kallesu yaga suna da yawa, dan sun kai kusan su ashirin, kallonsu ya kuma yi yace"kunyi yawa, da saina daukeku gashi can cikin gari ahargitse yake, amman idan zaku iyayin goyo ku shigo, nima nakai fasinjane, kuma ban samu na dawowa ba, sai wasu su zauna a boot".



   Gosiya suka mai matan suka yi goyon biyu, mazan kuma wasu a boot sai wasu agaba, suma sunyi goyon, koda suka ga sunyi nisa da tafiya sai kowa ya fara sauke ajiyar zuciya, gudu kawai direban yake shararawa basu shigo kano ba sai gabanin asuba.



   Atashar Kano line ya juye su sannan ya musu fatan alkhairi ya tafi bayan yasha dubban adduo'i daga bakunan su, dan ko kwandalarsu bai karba ba, zama sukayi awajen har gari ya gama wayewa , masu hankalin cikin su suka tashi sukai sallar asuba.

    Wajen shida da wani abun kuma kowa ya kama gabansa bayan sunyiwa juna fatan alkhairi, suma su Mairoji fitowa sukayi suka samu me napep fada musu unguwar da zasu matashiyarnan tayi sannan suka tafi, agaban wani dan madaidaicin gida suka tsaya , nan ta tsaida me mashin din kan zata karbo masa kudinsa, shi kuma yace bai yarda ba, kawai taje tayi zamanta, suna haka aka bude get din gidan wata bakar prado zata fita , kallon motar tayi tana sauke ajiyar zuciya, shima na cikin motar kallon ta yake da mamaki da sauri yai fakin ya fito ya karaso wajensu hannunta ya kama yace "Shahuda...kece da sassafennan, maza mu shiga ciki daman Kawu bai fita ba".



   Mai mashin din ta kalla tace" sallame shi tukun, sannan mu shiga da wadannan yaran".



Kallon su Mairoji yayi, yana bata fuska, zai magana ta kama hannunsa ta dan girgiza mai kai, shiru yayi ya karasa wajen mai mashin din ya tambaye sa kudinsa, bayan ya sallame shi ne ya kuma kallon Shahuda yace"Hudaa....wadannan yaran fa masu kama da bararoji, wai tare kime dasu".



   Bata kalle sa ba, ta kamo hannun su Mairoji tace"kumu je, akun gidan mu ya fara zuba".

   Awajen ta barsa yana ta bata fuska, kafin daga baya ya bisu shima, afalo suka tarar da matar gidan tana jera abin karyawa akan dinning, ai da gudu Huda ta saki hannun su ta isa ga matar ta rungume ta tana kuka, shafa kanta matar tayi tana murmushi"ya isa mana kukan, ya isa.....maza shiga ciki kiyi wanka sai kizo ki karya".



Kanta ta gyada tana share hawayenta, ta ce"Ammy tare nake da wasu yara, suna bukatar taimakon mu Ammy pls..."



  "Ba komai Huda, ai d'a na kowa ne, ki kaisu daya dakin su gyara jikinsu akwai kayan Laylah sai auyi amfani dasu, in kun gama sai kuzo ku ci abinci".



Cikin farin cikin Huda ta rungume ta tace " na gode Ammy na, Allah ya kara girma da daukaka".



Da "ameen "ta bita tana murmushi, daki Huda ta kaisu Mairoji bayan ta nuna musu yanda zasuyi amfani da kayan bandakin sannan ta fita ta tafi dakinta dan kintsa jikinta.







+++



    Karamin hauka yake musu agidan, duk ya hargitsa komai banda sambatu  babu abinda yake, babban yaron sa Lala shi ya samu ya kama sa zuwa daki, cikin kwantar da murya yave" haba oga...akan wannan yar tatsitsiyar yarinyar zaka daga hankalinkai, haba dan Allah ga mata nan manyan , ga hajiyoyin dake son hulda dakai amman oga ka maida hankalinka akan wadda batafi yar cikin ka ba zaka nemi shiga wani hali...."



    "Kai dalla kamin shiru, ita din yarinyar ruhi na ce, rayuwata ce kuma fitar numfashi na ce, akan na rasa ta, gwara na rasa duk wani abu dana mallaka, ba zaka gane son da nake mata ba, ina jinta har bargo na, ga kuma waccen dake dauke da jini na, d'ana ko y'ata bansan mai zata haifamin ba, tun kafin yazo duniya nake jin kaunarsa, kace wai dan me zan damu?".



    Abun da Lala bai taba gani ba kenan, hawaye a idon oga, ja da baya yayi ya zauna ya rasa ta inda zai fara lallaba ogan nasa, da kyar ya aro dauriya ya samu ya lallashe shi, sannan suka samu saukin karamin haukan daya fara musu.





+++++

 

     " Huda dan Allah meye hadinki da wadancen bararo din....? Allah ni ji nake basu min ba, ga karni idan zuka zauna awaje".



   Murmushi tayi tana kallon Ammy da Kawu dake shigowa falon, bayan sun zauna ne Kawu yace ta kira su Mairoji, suna zuwa zuka gaidasu da hausarsu dahar yanzu bata gama fita ba, nan suka nemi jin asalin su yan ina ne,ba wani bata lokaci Mairoji ta fada musu dun abin daya faru dasu, har zuwa gudowarsu, numfashi suka sauke Kawu yace"yanzu kenan ke Bad'ejo juna biyu ne dake, harna kusan wata biyu da wani kwananaki, ba komai Allah ba azzalumin sarki bane, kuma ba azzalumin bawansa bane, sai shi nawan ya zalinci kansa".



     "Ammyn su, ga amanar yara nan ahannunki, ki kula dasu kamar yaranki duk da bani da matsala dake ta wannan fannin, fata na Allah ya taya mu riko, kuma inshaAllah zan cigita anemo ahalinsu".



Kai Ammy ta gyada tana jin kaunar su dukansu tare da dinbin tausayinsu, Salman kuwa banda bata fuska babu abinda yake, dan shi kam baiji dadi ba zasu zauna musu agida, Allah yayi shi da dankaren tsantsani.



    Gwalo Huda take mai dan tuni ta gano sa, daman kuma gasu abokan fada.



Cikin dan kankanin lokaci sai ga rayuwarsu Mairoji ta fara sauyawa, awata biyu da sukayi har anyi musu cuku cukun makaranta, Salme zata fara daga primary 4, Mairoji kuma js 3  tunda dole sai an sake mata wasu takardun, Bad'ejo ce dai suka bari saita haihu, tunda ita tana js 2 daman abunnan ya faru.



++++



    Acan Rugar Na-ma'u kuwa Goggoji hawan jini ne ya kada ita, dan ta kasa fidda rai da ganin Mairoji, ada can tana yawan mafarki da ita tana neman dauki, amman adan kwanakin bayannan, batayi sai dai da zarar ta tuno ta gabanta zai ta faduwa.

    Ga Tako da take bata kulawa sosai, haka daga Dutse kusan ko yaushe Alhaji Badan yana hanya shida matarsa dan ganin lafiyar Goggojin, Ahmad tuni ya koma bakin aikinsa, sai dai ko yaushe suna waya da Tako yana jin yanda jikin kakar tasu yake, da kuma sanin halin da ake ciki akan Mairoji.



     Asalinsu.

Alhaji Muhammad Saje, haifaffen Borno ne, mahaifinsa shi ne shehin Borno, su biyar ne agun babarsu awajen uba kuma su goma sha daya ne, atsakanin iyayensu mata babu kazamin kishinnan, domin suna zaune ne lafiya.

    Kishiyar babarsu suna kiranta Hajja Yanzi, babarsu kuma Hajja Gana, yaran Hajja Gana biyar, Mahmud, Falmata, Baraka, , Sa'adatu, Muhammad.

   Ita kuma Hajja Yanzi tana da shida, Baba Gana, Hajja Yaana, Safiyya, Saminu, Lawal, sai Aliyu.

   Mahaifinsu wanda suke kira Ya Malam, yana matukar kaunar 'ya'yansa, kuma hakan bai hana ya basu cikakkiyar tarbiyya ba mai kyau, sun taso cike da son karatu na arabi dana boko, sai dai yan ubancin dake tsakaninsu ya musu katutu.



Muhammad kaf cikinsu shi ne karami, kuma sai Allah ya bashi farin jinin yan uwa dan dukda yan ubancin dake tsakaninsu yan dakin Hajja Yanzi suna sonshi sosai, ya samu yayi karatunsa lokacin daya gama sakandire Allah yaiwa Shehu rasuwa, bayan gama zaman makoki aka daura Mahmud shi ne zai gaje shi, da fari ya amince, sai da ya rage kwanaki a nada shi sai ya samu iyayenshi da zancen baya so abawa Baba Gana, Babarau bata ji komai ba, sai fatan alkhairi da tayi kawai , amman sauran yan uwansa sunji ba dadi dan sai da suka nuna hakan, bayan an nada Baba gana,  sai yazam kamar wani mulkin garin aka bashi gaba daya, sai ya fara takurawa yayan Hajja Gana, inda ya sa aka kullawa Mahmud sharri wanda yaja dole suka bar gidan, suka koma can wata unguwa daban, anan ma basu tsira ba, shekarsu biyu ya kuma hada musu wani tuggun daya fitar dasu daga borno gaba daya, yankin Hadejia suka yada zango, iya su uku, tunda matan suna gidajen mazajensu bada su suka tafi ba.



     Inda suka sauka kyauye ne sosai, can gaban wani kogi mai suna *Gilima*, sun dauki kusan shekara biyu sannan Mahmud yayi aure, yana zaune da matarsa bafulatana, mai suna Hasiya, sunyi haihuwa ta biyu Allah ya yiwa Hajja gana rasuwa, bayan nan da shekara biyar shima Muhammad yayi aure.



   Kasancewar Allah ya bawa Muhammad yalwar saje da cikar gashi afuskarsa sai mutan wajen suke kirkiransa da malam saje, tun baya son sunan har ya hakura ya ke amsawa, ahankali kuma sai ya fara tara shanaye da kananun kiwo, ganin yawancin fulanin kusa dasu duk sun dawo wajen da zama, kafin cikar shekara biyu sai ga shi ya zama babban gari, to kusan Malam Saje da Malam Mahmud su ne masu alimin cikinsu sai mutan wajen suka nemi da Mahmud ya zama shugaban yankin, amman yaki yace su bawa kaninsa shi yafi dace wa tunda shi ne matashi.



    Sunyi na'am jama'ar wajen, nan auka bashi matsayin shugaban yankinsu inda aka sawa wajen da suna *RUGAR SAJE*, kafin wani lokaci sai gashi rugar ta bunkasa dan harda yar kasuwa aka samu awajen, matar Saje tana goyon danta na Fari Badamasi, Allah ya karbi Malam Mahmud sakamakon motar shanu da tabi takansa, Saje yaji mutuwar nan dan ya tashi ba shida kowa nasa sai matar sa da yaran da Mahmud ya bari.

    Bayan Hasiya ta gama takaba ta koma garinsu mai suna Darai inda madakin garin ya nuna yana