Back to novel

Chapter 3 of 20

RUGAR SAJE Farashin Tsira by Nusaiba Ayuba

sonta, kuma daman abokin Mahmud din ne, Saje shi ya shiga ya fita yaga abun ya tabbata dan yasan kamar ta koma wa gidan Mahmud ne.

   Yaran dda ta bari, Maryam matar Saje ita taci gaba da rikonsu, Aminat, suna ce mata Tako, sai Mariya wadda taci sunan Hajja Gana, suna ce mata hajja, sai Sa'ada wadda taci sunan babar Hasiya kuma kanwar Mahmud, duk kan sau Goggoji matar saje ita ke rikeda su, lokacin tana goyon Safiyya.



    Bayan wasu shekaru yan matan duk sun tasa dan har aurar da Tako da Mariya, sai sa'ada da batayi aire ba dan ita kan dan uwanta take so Badamasi.



    _Wayyo....hannuna, wayyo ido na=Ø%Þ=Ø%Þ=Ø%Þ=Ø%Þ_

*Mmn Mu'ayyad.*





    *RUGAR SAJE*



  By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*

(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_



_5_



    Arayuwar Sa'ada babu wanda take so sai Yaya Badan, Allah ya jarabceta da soyayyarsa, yayinda shi kuma yake nuna bai san tana yi ba, bawai ko bata da kyau ba ko kyan kira, ah ah kawai dai shi baiji sonta acikin ransa bane banda na yan uwantaka, Malam Saje da Goggoji duk sun san da wannan abun amman sai suka zuba musu ido kawai, Sa'ada taci gaba da korar manema aurenta, shi kuma Badan ya maida hankali kan karatunsa da yake acan garin kano.



    Bayan ya kammala makaranta ne sai aikinyi ya gagare sa, tunda ba wani babba bane dashi daya sani bare ya kai masa kokon neman alfarma, ganin haka sai kawai ya koma sana'ar gado noma da kiyo, ina nan danan ya gida wani karamin gidan gona, ya zuba shanaye da tumakai, ga kaji da zabbi , cikin kankanin lokaci sai gashi Allah ya dafa masa, masu kudin makotaka dasu suna zuwa siyan shanaye dan shi baya kai dabba kasuwa, awannan kasuwancin daya fara ne, Malam Saje ya matsa masa da batun auren Sa'ada.



   Da fari, kin amincewa yayi sai dayaga bacin ran iyayennasa sosai kafin ya yarda, ba wani bata lokaci aka tsaida ranar biki, tunda abu ne na gida ba wani tsayawa za'ayi bata lokaci ba.



    Madakin garin Darai shi ya zama wakilin ango, Malam Saje ya zama na amarya haka aka bikin cike da farin ciki, da kwanciyar hankali, shekararsu biyu ta haifi danta na miji, ranar suna da yamma ciwon ciki ya turnike ta kafin akaiga asibita rai yayi halinsa, Badan yaji mutuwar kamar zaiyi hauka, haka aka share zaman makoki, aka watse,bayan kamar shekara biyu da rasuwar Sa'ada,  wani uban gidansa dake garin Dutse shiya sama masa aiki a ma'aikatar ruwa ta jihar, sannan ya hada da basa kyautar 'ya sukutum, wannan karon baiki ba ya karba iyayensa sunyi farin ciki sosai sukamai fatan alkhairi da dacewa.



   Yarinyar da aka bashi da wayewarta dai dai ta zamani kuma t ataso agidan dattijai, wanda suka san girma da arziki, bayan bikin ta nemi alfarmar ya dauko mata Ahmad dake hannun  Tako, ita zataci gaba da rikesa, da fari danginnasa sunki, amman da ta matsa sai suka yarda ya dauke sa ya bata, wani abin mamaki da farin ciki shi ne yanda ta dauki son duniya ta daurawa Ahmad, komai ta samu shi, gashi har kusan shekara da auren bata taba yin koda batan wata ba, Ahmad nada shekara hudu ta samu ciki danginnan sunyi murna sosai.



     Safiyya kanwar Badan, mai kimanin shekara sha shida ita tazo ta zauna mata saboda laulayin take yi mai matukar ban wahala, tana gidan kafin hutunsu ya kare, wan Anty Aisha matar Badan ya kawo musu ziyara anan yaga Safiyya ya kware mata, so abunka da duk gida ne shima ba'a dau lokaci ba aka aura mata shi.



    Lokacin ya'yan Goggoji biyar ne, Badan , Usman, Mahmud, Safiyya, sai autansu Abdulmalik, 'yayan Mama Hasiya kuwa, Aminatu, Mariya, Sa'ada, sai wadanda tayi agidan madaki, Rabi'u, Ibrahim, sai Salma. Kusan wadannan ahalin sunajin kansu ne kamar uwa daya ce ta haifesu, don wani irin soyayya da kulawa suke bawa junan su.



Aisha da danta na miji wanda yaci sunan dan autan su Badan kuma sunan mahaifinta Abdulmalik, tun da ta yaye shi take zuba idon ganin wani cikin amman Allah bai kawo ba, tun tana sa rai har ta hakura ta fawwalawa Ubangiji, dan tasan yana sane da ita, Ahmad da Malik sun taso da wata irin kaunar juna, ko kadan daya bayason gainn bacin ran daya, haka idan daya baida lafiya to tabbas zaka samu shima dayan yana tayashi, haka suke taso tamkar tagwaye, dan kuwa Malik badai girman gabba ba, babu wanda zai kalle sa yace Ahmad ya basa shekaru har biyar, abangaren halaye kam, Ahmad nada saukin kai, sannan kusan ko yaushe fuskarsa a sake take, da wuya kaga bacin ransa, sabanin Malik da Goggoji kemai kirari da 'Sa kake baka dariya sai hamma, duk wanda yaga dariyar ka yaga mutuwa' wannan kuwa haka yake dan idan kaga Malik na murmusawa to tabbas ya gano wani salon muguntar.



Abangaren ra'ayi ma sai aka samu banbanci, dan Ahmad koda ya gama karatunsa sai ya fara aiki ne da matattarar man fetur na kasa, inada ya koma Delta da zama bayan sun bashi gidan zama da masu mai hidi ma, ga kuma albashi mai tsoka, shi kuwa Malik koda yai digirinsa na biyu a business sai ya bige da buga kwallo, inda yake a babbar kungiya ta Arsenal, ba yanda iyayensa basuyi ba ya sake sana'a, amman sai ya nuna wannan din yake so, hakan suka kyale sa bayan sun mai fatan alkhairi.



Abangaren Safiyya ma tana zaune lafiya da maigidanta, domin irin tuzuran nanne, wanda sukan dade basuyi aureba, sosai kuwa yake nuna mata kulawa, dan har lokacin bata haura sha bakwai ba, suna cikin shekara ta kusan goma da aure sannan ta haifi danta namiji,inda yaci sunan Muhammad, bafa kuma ba sai daya shiga firamare sannan tayi mace, inda aka samu Maryam, irin yawon arba'in da ake bayan an gama wankan jego shi taje gida alokacin, kwanan ta daya da zuwa ta shirya zuwa inda Hajja take aure awani gari tsallaken ruwa, dukda Goggoji taso hanata zuwa amman sai ta nuna tana son zuwan tunda ai daman yawon arba'in ta fito, ba yanda Goggoji tayi haka ta hakura ta barta suka tafi, ita da dan autansu Abdulmalik, tafiyar da bata dawo ba kenan sai gawarta aka kawo, shi kuwa Abdulmalik ma ba'a gansa ba duk neman da akayi, kuma abin ta'ajibi shine 'yar tata babu abindaya sameta sai ruwa data sha.



Asibiti aka kai yarinyar inda Aisha matar Badan tayi zaman jinyarta, sukuma anan gidan sukayi zaman makokinta, lokacin kam Malik yaji mutuwar sosai, dan kaf kannen babannasa babu wadda suka shaku kamar Safiyya haka shima Ahmad sunan ji da ita sosai, bayan an shafe zaman makoki ne Maman su Malik ta nemi alfarmar Goggoji ta bar mata Mairoji ta ci gaba da riketa, duk da anga yanda ta rike Ahmad cikin gaskiya da amana kamar dan cikinta, amman haka Goggoji ta hana ta Mairoji dan Allah ya dasa mata kaunar yarinyar ne.



Malam Saje kaf cikin jikokinsa da yake dasu dana dan uwansa day mai dasu nasa, babu soyayyar wanda tafi ta Malik girma awajensa, yana son shi kamar ya maidasa ciki, zuwan da Malik din yake yi wajen sa yin hutu tun yana sakandari yake cemai"kaga Audu....indai ina da rai da lafiyata naga aurenka, to ka tabbata bakada mata sai Mairoji, ita nake son ka aura ka tsaya mata arayuwa, dan Allah ko bayan ba raina ka cika min wannan buri nawa kaji".



Ire-iren wadannan maganganu tun yana boyesu har ya samu Mamansa da maganar yake sanar da ita, sau tari idan yazo yana fada mata sai dai tayi dariya kawai, dan itakam Ahmad dinta take wa sha'awar aure Mairoji, yanda yarinyar take nitsattsiya ba tada rayan kai na yaran zamani ai da salihin dan ta ta dace ba da wannan baudadden ba, wani zubin idan yazo yana bata labarin hirar da sukayi da Mallam sai dai tayi dariya kawai, ko kuma tace"babana dan Maliki.....uwata fa babbar macece, ba matar yara bace, tanadin da nake mata babba ne yaro dan haka kaja baya".



Shima idan ta fadi irin hakan dariya yake yace"Mama ada idan Mallam yana fadamin Mairoji ce matata anan gaba, bana jin komai, amman yanzu idan naji bai fada ba har haushi nake ji, ajiyar Malam yanzu ta dawo ajiyata, ni ne dai wanda kike wa wannan tanadin".



Arananr daya fada mata haka, yini tayi tana mamakinsa, dan itace ta haifesa amman ba zata yarda ba idan wani yace mata shi ya fadi haka ba, yanayin sa kadai ya isa ka gane waye shi, irin yananin fuskarsa ma babu alamun wasa ko wargi aciki, amman wai shi yake fada mata abunda yazo masa haka kai tsaye, kenan soyayya ya fara ko me, ko kuma dai yanajin Mairojin ne aransa bawai yana sonta ba.





Rayuwar Mairoji ta tashi ne rabinta agidan Mama rabinta wajen Goggoji, da taimakon Allah dasa bakinsu Mama da Ya Ahmad Mairoji ta yi firamare, dan Goggoji da hanawa tayi, dakyar ta yarda tayi to kuma kutso kai da Mamuda dan gidan Tako yayi da sunan yana sonta sai, Goggojin ta kuma matsawa lallai aure za'a mata ai ta isa, tunda kawayenta wasu duk suna dakin miji, da kyar ta bari tayi karamar sakandari, tana gamawa kuwan ta fara neman yan uwa don maganar aurar da ita.



Hamma Gid'ad'o, watau Madakin Darai kusan shi yake tsayawa akan komai na gidan, dan tun bayan mutuwar Mahmud shi Malam Saje yake ganin amatsayin dan uwansa.



Agarin Hadejia akwai wani abokin Malam da yake aurar da jikokinsa, to ya gayyace shi, da fari ma yaki zuwa saida Goggoji tayi magana sannan ya shiryawa tafiyar, ranar daya tafi da kwana biyu mahara suka ritsa Ruggar inda auka yi ta'adin da barna sannan suka wuce da yan mata uku.



Yana can yaji labarin abindaya faru ba shiri ya juyo gida amman sai yazo ya tarar da wayam, dole shi ma sai gidan Tako yaje amman ya ce bazai zauna mata anan ba zai koma can garin Darai ya zauna kafin aga yanda hali zaiyi.







+++++++



Atafi-tafi dai su Maoroji sun dau wani lokaci agarin kano, dan sosai Ammy take basu kulawa da nuna kauna, yanzu har Mairoji ta fara makaranta ita da Salme, sai dai kayan da aka basu ne na makarantar har yanzu basu yawe da saka shi ba, siket ne iya gwuiwa grey calour sai milk din riga da grey din baby hijab, da safa doguwa da kombas.



A amakartar da Mairoji take akwai wani Fahad daya masifar takurata da shirar banza wai shi sonta yake, tun bata kulasa har tazo tana dan tsayawa suyi yar magana ta wuce.



Yauma sun fito break kawarta wata yar gayu yar kyakkyawa haka ta kamo hannunta tana mata nuni da kai, kallon wajen Mairoji tayi suka hada ido da Fahad daya harde yana kallonta, karasawa wajensa sukayi da sallama, amsawa yayi yana kafita da ido, kanta ta sunkuyar tana wasa da hannayenta, kallon wajen yayi yaga ba yawaitar mutani ya kamo hannunta ya na dan murzawa, cikin kasa da murya yace"baby...kullum kara kyau kike, kuma har yanzu kinki yarda mu zama abu daya, nifa dan love ne ya kamata ki gane wannan, gashi gobe ne birthday dina ina gayyatarki kizo, ki shirya zan aiko a daukeki za'a kawo ki wajen da muke, idan kinzo na tabbata kina so na, idan kuma baki zo ba, jibi zaki xo jana'izata dan zan ahi poisen ne, gwara na mutu na huta da naganki akoda yaushe amman kuma baki amshi tayi na ba".



Sakin hannun yayi bayan ya sunbata, ya kashe mata ido adaya yace "ina jiranki pls...hatta kayan da zaki saka, zan aiko miki dasu, bye" 'yan yatsu biyu ya dage mata ya wucewarsa, numfashi itama ta sauke, tana jin wani bakon yanayi akan Fahad din, hanyar da yabi itama tabi da kallo murmushi na musamman yana kubce mata.



Ko da ta koma gida bata boye wa Aunty Huda ba ta fada mata komai, shiru Hida tayi kafin can tace"ki bari kafin goben zan yanke shawarar zuwannan ki ko kuma ah ah".





Da dare yayi kamar ko yaushe bayan an kallama yin dinnar Kawu ya tambayesu ko da mai bukatar wani abun kafin ya wuce sama, duk amsawa sukayi da babu, sannan ya musu sai da safe, Ammy ma bayansa tabi, bayan ta mikawa Bad'ejo furar da ta dama mata, dan ko kadan bata fiya zaman falon ba, ta fi gane zaman daki, hakan ne ma yasa Kawu ya hada mata kayan kallo adakin daduk wani abun da zai debe mata kewa.





*RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman

Wattpad#nusysa.

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango



*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*





–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo



*œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_



_6_

Tun safe take baza kunnen ta inda Anti Huda zata kirata tace ta amince da zuwan ta wajen partyn, amman shiru har kusan la'asar, gashi taji tana cewa tana da bikin kawarta da zata da yamma.



Ganin magariba ya kawo kai sai kawai ta hakura ta sallame da zuwannata, bayan sun idar da sallah ne suna zaune kamar yadda aka sabar musu, duk bayan idar da sallah Huda tana biya musu karatun kur'ani da sauran litattafan addini, bayan sun gama ne suka nufi dinning dan cin abinci, gani yanda Mairoji take tsakura ne yasa Hudan yi mata magana tace "wai kin fasa zuwa ne, naga sai wani nuku nuku kike?".



'Dagowa tayi ta kalleta tana sakin murmushin jin dadi tace" ah ah Anti zani".



"To kiyi ki gama, ga kaya cen an aiko dasu dazu kuna sallah lokacin, amman tare da Salme zaku".

Salmen da take kara miya akan farar taliya tace" Anti ina da Homework wllh, kuma ne zanyi submiting, taje kawai".



Badan Huda taao ba ta amince da Mairojin taje ita kadai, dan bata son suna nisa da gida babu wani akusa dasu, da haka dai tasa Mairoji ta shirya cikin kayan da Fahad din ya aiko mata, riga ce gown pink sai takalmi da yar porse, passion na sarkan wuya da d'an kunnaye da abin hannu duk kalar blue ne mai haske, ba laifi tayi kyau, dan Huda harda daukarta ahoto, tace ta samu nayin status, dariya suka sa dukansu sannan Hudan ta rako ta har bakin mota dan direban gidanne zai kaita.



Sai da tayi mata kashedi sosai akan karta sake takai dare, duk inda tara da rabi tayi ta tabbatar sun dauko hanyar dawowa, tana tsaye har suka fice daga get din gidan sannan ta koma tana sauke ajiyar zuciya, inda Allah ya taimakesu Kawu bayanan, sai Ammy da suka shirgawa katuwar karya.





++++



Wajen ya hadu sosai, duk da babu wadatar haske, abakin wajen shiga ta tsaya tana kallon tsirarun mutane masu wucewa, kowa sai harkar gabansa yake, ji tayi an kamo gefen kugunta ta baya, azabure ta juya dan ganin waye, ido hudu suakyi da Fahad da ya gama hadewa cikin blue suit sai baza kamshi yake, matsawa tayi tana dan zame hannunsa daga jikinta cike da kunyar kallon kurillan daya ke binta dashi.



Murmushi kawai yayi yana shafa kansa, iska ya furzar yana kuma kafeta da ido, cikin kasalalliyar murya yace"Baby....kinyi kyau fa, badan agida ance nayi kankanta da aure ba, da ba abinda zai hana ni mallakarki acikin satinnan, da ganin ki zaki bada cittahhhh".

Yaja kalmar karshe din yana murza hannun ta daya kamo, yana mata kallon kasa kasa, ita dai ta kasa magana dan wannan bakon abu ne awajenta, duk da tana da yan uwa maza, da suka taso gida daya ma dasu, amman irin haka baya shiga tsakaninsu, ko Ahmad da tafi sakewa dashi fiye da kowa ma, basa irin wannan wasan tsakaninsu.



Maganar sa ce ta dawo da ita , kallonsa tayi yai mata nuni da hanya akan su shiga, ba musu ta bisa hannunta cikin nasa, sai dai ganin sun ahiga duhu yasa ta dan tsorata har ta kamo dantsen hannunsa ba ta sani ba, dai dai lokacin haske ya gauraye wajen tare da zubowar wasu abu masu kyalli kansu, sai muryar mutane tare da tafinsu na taya Fahad din murnar cikar shekara sha takwas.



Abin daya bata mamaki, tayi zaton ganin yan makarantarsu da aiya abokansa kadai, sai dai taga harda manyan mutane, wasu ma data gani kamar iyayensa ne, matar sunyi matukar kama da Fahad din da ita, ceke din daya yanko ya kai bakin ta, rasa makamar dafawa yasa ta bude yasa mata, cike da kunya ta sunkiyar dakai.



Nan aka fara miko mai kyaututtuka yana karba sai ya bata ta rike, sai wajen tara wani abun sannan aka fara watsewa, anan ya gabatar da ita wa iyayensa, cikin sakalci yace"Dad....ita nake so, idan na gama makarantana na fara aiki ita zaku auramin, dan Allah Dad kar sai lokacin yayi kuce min ba haka ba".



Matar dake gefe da alama itace mamansa tace "idan kuma ita taki fa Son? idan lokaci yayi dakan mu zamu nema maka aurenta ka dena damuwa"

Kallon ta yayi ya dauke kai, ya mayar ga Dad din sa yace"ka fadawa matarnan ta dena shigar min magana,