Follow us on social media
Showing 81001 words to 84000 words out of 93041 words
Chapter 28 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ Sirrin Soyayyar Aljani By AMEERA ADAM
mu, zan ƙara miki tuni idan kun wayi gari da mutuwar wani bawan babu ku babu cin kayan sadakar inba haka ba zaku bishi, ku fice daga kogon dutse kuna masu ambatan sunan mu " yana gama faɗa ya ɓace daga gurin, Jakadiya da Fulani tashi suka yi suka fita, suna zuwa bakin kogon dutsen Fulani ta kuma runtse idonta tana karanta ɗalasiman tsafin, atake haske ya kuma mamaye su suka ɓace daga gurin.
Lokacin da suka koma cikin Masarautar tuni dare ya tsala babu motsin komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabobbi, Fulani karɓar Salman tayi dake hannun Jakadiya sannan ta ce mata, " Ƙuda wajen kwaɗayi akan mutum ina fatan baki manta maganar boka ba " rissunawa Jakadiya tayi ta ce, " Ina ankare ya shugaba ta "
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[3/8, 5:46 PM] AU MARYAM: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
*ANYA BAIWA CE?*
Na
*AMEERA ADAM*
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
FREE PAGE 4
Fulani taɓe baki tayi ta ce, " Yayi miki kyau ai kowa rai ya yiwa daɗi baya mai shi ba, magana ta ƙarshe da zan gaya miki, kiji ki ƙi ji ki gani ki ƙi gani, zaki iya tafiya " tana gama faɗar haka ta juya ta shige ciki ta bar Jakadiya a tsaye.
Jakadiya bin bayanta tayi da harara sannan ta juyo ta fi ce daga sashen Fulani Maryama ta wuce cen sashen su.
Washe gari tun Asubar fari Lantana ta ƙaraso ɗakin Jakadiya hankali tashe tana kwala mata kira tana bubbuga ƙofar, kasancewar bacci bai ishi Jakadiya ba taji haushin tashin da Lantana ta yi mata, cikin masifa ta fara magana, " Ke Lantan wannan kiran mafarautan da kike mun da farar asubahi na lafiya ne? Sai kace naci na wani ban biya ba, Mtsswwww jaraba kai ko yaushe baka da hutu " ta ƙarasa faɗa tana zare sakatar ƙofar.
Lantana haushi ne ya fara kamata cikin tsiwa ta ce, " Ke Jakadiya kullin cikin yiwa mutane jaraba kike to kizo kiga abunda Sahura take yi muma farkawa mukayi muka ga tana wani irin abu " gaban Jakadiya ne ya yanke ya faɗi da sauri tayi gaba Lantana na biye da ita.
Suna shiga suka samu idanun Sahura sun kakkafe jikinta sai wani irin karkarwa yake bakinta na fitar da dafara, Kuka Jakadiya ta fashe dashi tana rungumo Sahura dake cikin wani hali, lokaci ɗaya taji Sahura na shaƙuwa jikinta ya sandare daga nan numfashin ta ya ɗauke.
Jakadiya rungume Sahura tayi tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya, sai da tayi mai isarta cikin jimamin rashin jikarta ta fara magana, " Shikenan ni Kubura bani da kowa Sahura ke kaɗai kika rage mun yanxu kema babu ke kin mutu kin barni kaico mutuwa baki mun adalci ba, babu Ƴaƴa babu Jika, Allah ya jiƙanki Sahura " haka Jakadiya ta dinga surutai da ƙyar aka raba ta da gawar jikarta, ba ƙaramin tausayi Jakadiya ta bawa mutane ba musamman yanda kowa yasan irin ƙaunar da ke tsakaninta da jikar ta ta ɗaya tilo, kafin wani lokaci tuni mutuwar Sahura ta ƙaraɗe cikin gidan, bayan ansallaci Sahura mutane suka shiga sintirin zuwa yiwa Jakadiya gaisuwa.
Jakadiya ce durƙushe a ɗakin Fulani Maryama har zuwa lokacin hawaye ne kwance a fuskarta, Fulani ce ta fara mata magana, " Jakadiya ya ƙarin haƙuri? " Jakadiya goge kwallar idonta tayi sannan ta ce, " Da godiya Ranki shi daɗe "
" To Allah jiƙan musulmi, ga wannan ayi sadaka da shi " wata jaka ce ta miƙowa Jakadiya, Jakadiya da tsanar Fulani ta ɗarsu a zuciyarta ji tai kamar bazata karɓa ba, amma gudun kar Fulani Maryama ta ganota yasa ta miƙa hannu biyu ta karɓa tana zabga godiya, zuciyarta a dagule ta fito daga sashen Fulani Maryama.
Jakadiya haka ta shafe kwanaki bakwai cir bata cin abincin sadakar da akeyi, da yake ma tana cikin jimamin mutuwar ko yunwar bata cika damunta ba inma taji yunwa sai dai ta nemi gasara ta dama kunu ko tayi farau-farau, a duk duniya yanxu babu wacce Jakadiya ta tsana take jin haushin ta sama da Fulani Maryama dan gani take ta sanadin ta ne ta rasa Ƴar jikallenta guda.
Bayan kwana biyu Fulani Maryama sai saƙa da warwara take a cikin zuciyarta, tana tuna maganganun da Boka ya sanar mata fargabar abin da zai biyo baya.Ta kaɗu sosai da yadda karon farko Boka ya bankaɗo wani muhimmin ɓoyayyen sirrinta, amma data tuna irin tuggun da zata shirya sai ta mayar da komai ba komai ba, ta zubawa sarautar Allah ido tayi da jiran tsammanin lokacin haihuwar Fulani Zaliha. Domin a nan ne zata aiwatar da dukkan ƙudurinta.
Bayan kwana biyu Mai Martaba na zaune a turakarsa Fulani Maryama na gefe a zaune, ta kalleshi sai dai gabaɗaya baya cikin walwala cikin kissa ta ce. "Mai Martaba wannan yanayin sam bai kamace ka ba, Allah ƙara lafiya da nisan kwana shugaba kamar kai wannan yanayin bai dace da kai ba, Bango madafar bayi idan har zaka dinga shiga cikin damuwa, to mu da sauran talakawanka ya zamu kasance." Mai martaba cikin damuwa yace. "Wallahi ina yawan yin mummunan mafarki akan ƙanwarki Zaliha ina yawan mafarki mara kyau akan cikinta" gaban Fulani Maryama ya faɗi ɓaci rai ya sauka a zuciyarta amma da yake ta iya duniyanci sai ta aro damuwa ta yafa a fuskarta ta ce. "Haba taƙamar bayi adalin Sarki mai adalci, ai zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi, ka kwantar da hankalinka Fulani Zaliha zata sauka lafiya tunda alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, nidai a iya sanina Fulani Zaliha tana cikin ƙoshin lafiya kuma zata haife mana ƙanin Yarima lafiya" farinciki ne ƙarara ya bayyana a fuskar Me martaba, janyo hannunta yayi ya sumbaceta yace.
"Allah ya yi miki albarka Maryama ke ɗin ta daban ce saboda haka kike ƙara birgeni, naji daɗin yadda kika riƙi ƴan uwanki da zuciya ɗaya kuma kika riƙe girman da Allah ya ɗora miki, hakan ne yake sa nake tunanin ko bayan raina zuri'ata zata haɗa kanta." Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. "Dole ƙanwar naƙi wa ya isa ya ja da abin da Mai Martaba yake so, ai duk abin da ka nuna kana so har bada ina ƙaunarsa"Mai Martaba daɗi yaji sosai yadda take bashi kulawa akan sauran matansa. Cikin zuciyarta Fulani Maryam ta ce. "Da ikon Allah bazai zo duniya lafiya ba mu zuba mu gani"
*BAYAN WATA UKU*
Fulani Zaliha ce durƙushe tana naƙuda, gefenta Marka ce sai Jakadiya dake riƙe da ita, daga bakin zaure Shamaki ne yake sallama, da sauri Jakadiya ta fita gurinsa, ƙwarya ce da rubutu aciki ya miƙa mata yana faɗin, " Gashi Takawa ya ce a bata ta sha ashafe cikin da shi " karɓa Jakadiya tayi ta koma ciki ta ɗago kan Fulani Zaliha da ta haɗa uban gumi, a wahalce ta sha bayan ta gama sha aka Shafe cikin da sauran.
Bankaɗa labulen ɗakin akayi ko sallama babu, Jakadiya na ɗago kai tana shirin masifa suka haɗa ido da Fulani Maryama fuskar nan tata babu annuri, wani tunani Fulani Maryama tayi lokaci ɗaya ta sauya yanayin ta cikin ruɗewa ta ce, " Jakadiya ashe Fulani na kan gwiwa amma ba'a turo ansanar mun ba sai yanxu labari ya je mun " Jakadiya cikin rawar murya ta ce, " Ai wato...Nima zuwa na kenan, na fito zanje wajenki Takawa ya ayko da rubutu "
Marmushin Markirci Fulani Maryama tayi ta ce, " Bari nazo na riƙeta kije ki kawon garwashi yanxun nan ga ragowar turaren da akamun lokacin naƙudar Yarima " Suna haɗa ido Fulani ta watsawa Jakadiya mugun kallo ba shiri Jakadiya ta fice.
Fulani na shiga ta riƙe Fulani Zaliha tana mata sannu.
Jakadiya na kawo wuta Fulani Maryama ta kunce turaren wajen boka ta barbaɗa, ba'a jima Jariri ya faɗo yana tsanyara kuka, Fulani Zuwaira da Fulani Bilkisu na kawo kai suka ji kukan jariri, da sauri Fulani Bilkisu ta ce, " Lallai mun shigo a sa'a Barka da arziki " suna shigowa kowa yayi turus saboda ganin Abunda Fulani Zulaiha ta haifo, sai dai kowannen su haɗiye abinda ke ransa yayi gudun kar afuskanci halin da Suke ciki.
Bayan an yanke mabiyar angyara gun ruwa aka kawo na wankan jariri. Kasancewar Fulani Maryama ita yaro ya faɗo a hannunta ita aka bawa ruwan, fakar idanun su tayi ta damƙi garin gurin boka haɗe da ƙafar jaririn ta sa acikin ruwan wankan.
Lokacin da garin maganin ya garwaye jikin sa wani irin kuka ya fashe da shi, amma babu wanda ya kawo komai sai ma tsokarsa da Marka ta ke cikin waƙa tana faɗin, " Ka zama Jarumin maza karka zama rago mana matsoraci bashi zama gwani, jinin Aminullahi yafi ƙarfin wasa kyawun ɗan ƙwarai ya gaji ubansa"
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[3/8, 5:46 PM] AU MARYAM: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
*ANYA BAIWA CE?*
Na
*AMEERA ADAM*
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
FREE PAGE 5
Fulani Maryama zuciyarta fes wani shu'umin murmushi tayi har ya bayyana a fili ta ce. "Marka ai ɗana jarumi ne kamar yadda ɗan uwansa salman yake" Jakadiya ce ta fita ta yiwa Sarki albishiri Marka ta fara ƙoƙarin gyara Fulani Zaliha. Har aka gama yiwa Jaririn Fulani Zaliha wanka bai daina tsanyara kuka ba, tana gamawa ta gyarashi sannan ta ce. "Fulani barka da arziki bari na ƙarasa ciki na bar yarima yana bacci kar ya tashi ki samu ki ci abinci ki kwanta ki huta." Fulani Zaliha ta ce. "To na gode Yaya Allah ya huta gajiya" Fulani Maryama ta wuce sashenta.
Kafin wani lokaci tuni haihuwar Fulani Zaliha ta zaga cikin gidan masarautar, sanƙira bi yake ko ina yana shelar sanar da ƙaruwar da Mai martaba ya samu , cikin lokacin ƙanƙani cikin garin Kano ta samu sakon haihuwar da aka yiwa Sarkin Kano Aminullahi.
Jaririn Fulani Zaliha tun ranar da aka haifeshi yayi wannan kukan bai ƙara wani kuka da ƙarfi yadda wani zai iya ji ba, Fulani Zaliha bata kawo komai ba saboda wannan ce haihuwarta ta farko kuma bata taɓa kawowa ranta komai ba, tafi alaƙanta haka da yaro ne shi mara rigima saboda wasu jariran basu cika rigima ba. Matan cikin masarauta da sauran bayi tsegungumi sukeyi akan Fulani Maryama na rashin nuna matsanancin kishinta akan ɗan Fulani Zaliha duk da yadda kowa yasan Fulani Maryama da matsanancin kishi. Fulani Zaliha ba ta shan wahalar rainon Jaririnta dukda akwai masu kula dashi amma sam bashi da rigima. Tun daga ranar kuma Fulani bata ƙara takawa ta leƙa saahen Fulani Zaliha ba har sai da yayi kwana uku, da wata yammacin ranar ta shirya cikin shiga ta alfarma irin ta jiƙaƙƙun matan sarakuna, tafe take cikin takun ƙasaita da taƙama kamar ba zata taka ƙasa ba. Ga duk wanda yayi arba da Fulani Maryama kallo ɗaya zai mata ya tabbatar da ita ɗin tabbas jinin masarauta ce gaba da baya, duk yadda ka kai ga kallan ƙurulla zai yi wuya ku haɗa ido da ita batare da janye idanuwanka ba kuma duk sanka da ka fahimci a wane yanayi take zaiyi wuya ka fahimci halin da take ciki. Tana tafe kunyangarta na biye da ita da Salman a hannu har suka ƙarasa sashen Fulani Zaliha, lokacin da ta shiga sashen Fulani Zaliha na zaune tayi kwalliyar ta fito shar da ita ga wani kyau da ta ƙarayi irin na masu jego, Fulani Maryama zama tayi kan lallausar shimfiɗar Fulani Zaliha baiwar ta tsaya daga rumfa.Da fara'arta Fulani Zaliha ta ce, "Barka da shigowa Yaya da fatan kin wuni lafiya ya kwanan Yarima" Fulani Maryama wani murmushi tayi mai wuyar fasaltuwa ta ce. "Lafiya kalau masu jego ya kwanan ɗannawa" Fulani Zaliha kunya taji bata amsa ba ta ƙwalawa baiwarta kira tana bata umarnin kawo Jaririn, a fakaice Fulani Maryama take ƙarewa Fulani Zaliha kallo tana ƙara jin wata irin tsanarta a zuciyarta.
Lokacin da aka kawo mata Jaririn karɓar sa tayi tana murmushi sai dai ƙasan zuciyarta har wani zafi take ji saboda yadda taga kamaninsa dana Mai martaba na ƙara fitowa, a fili ta shafa fuskarsa ta ce. "A jinjira baƙwan duniya yana rigima kuwa?" Fulani Zaliha ta ce, "Tun kukan farko da yayi bai ƙarayi ba bashi da rigima" Fulani Maryama na shirin yin magana taga hawaye na gangarowa daga idanuwansa, buɗe baki yakeyi yana ɗan juya kansa wanda yake nuna yunwa yake ji, Fulani Maryama murmushi tayi me sauti ta ce. "Ai dama bazai yi ba indai ya biyo gida kinsan Yarima ma haka nayi goyonsa, ungoshi naga kamar yunwa yake ji" a kunyace Fulani Zaliha ta karɓeshi miƙewa Fulani Maryama tayi tayi mata sallama zata wuce har ta je bakin ƙofa ta juyo ta ce. "Sai fa kinsa ido akansa saboda ɓoyayyun maƙiya duk yadda kika kai ga ganosu sai kin gaza a masarautar nan dan haka ki bi sannu" murmushi Fulani Zaliha tayi ta ce, "In sha Allah Yaya kinsan zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi" Fulani Zaliha zuciyarta ɗaya ta faɗi haka ita kuwa Fulani Maryama juyowa tayi amma sai ta wayence da murmushi ɗauke a fuskarta ta ce. "Kinyi gaskiya kuma nasan da haka amma duk da haka tsugunne bata ƙare miki ba amma fa shawara ce na baki." tana kaiwa nan ta fice daga ɗakin.
Tun daga ranar Fulani Maryama bata ƙara shiga sashen Fulani Zaliha ba, kuma zuciyarta fes ta fita daga ɗakin saboda yadda da dukkan alama haƙanta ya cimma ruwa. Shirye-shirye ake ta gudanarwa na shagalin suna daga sassan ɓangarori na cikin masarautar. Ranar suna Mai martaba ya raɗawa Jariri sunan Saifullah suna kiransa da Saif, anyi shagali sosai ɓaki daga garuruwa suka kawo ziyara wajen taya Mai Martaba murnar samu Ɗa namiji a karo na biyu.
Anyi taron suna angama lafiya kuma daga ɓangaren Mejego da jaririnta suna cikin ƙoshin lafiya. Bayan wata uku Mai Martaba ne zaune a fada shi da Waziri, ga duk wanda ya dubi yanayim Mai Martaba zai fahimci tsantsar damuwar da yake ciki, amma da yake namiji ne jajirtacce farat ɗaya bazaka fahimci ainihin yanayin da yake cikin ba. Waziri ya ɗuƙar da kai cikin sigar girmamawa yace. "Allah ya taimaki takawa ya ƙarawa Sarki lafiya, Muna zaune aka aika da saƙon kiranmu" Sarki Aminullah ya jinjina kai sannan ya ce.
"Waziri wani abu yana damunmu kuma babu wanda muka aminta da mu tattauna dashi sai kai" Waziri ya ɗago yace. "Wannan haka haka yake" Sarki yace. "Mun lura da yaron wajen Zaliha kamar bashi da wadatacciyar lafiya, kuma na lura da yanayin Mahaifiyarsa ita kanta ta fahimci haka sai da tana shakkun sanar dani. Waziri ina san maganar nan ta zama sirrin saboda kunnuwa da idanun Fada suna bibiyar halin da ake ciki, banasan a fuskanci halin da yaron nan yake ciki inasan ka nemo min mai magani a sirrance ta yadda babu wanda zai fahimci halin da ake ciki."
Waziri ya numfasa yace. "Allah ƙadiran alamanyasha'u gaskiya akwai matsala babba dukda kasancewar ba shine Yarima ba, amma sirrantawar yana da matuƙar fa'ida. A cen garin Zaria akwai wani mai magani dana sani yana bada magunguna sosai, dan haka insha Allah zan shirya naje na karɓo maganin sai a jarraba da ikon Allah za'a dace." Mai Martaba yace. "Waziri me zai hana ya gayyato mana mai magnin ina ganin kamar hakan zaifi" Waziri yace, "Duk yadda kace haka za'a aiwatar da kai da kaya duk mallakar wuya ne" Mai Martaba yace. "A shirya tafiya gobe aje a gayyato mana shi" Waziri ya amsa daga nan ya fice daga fadar."
Da daddare Fulani Zaliha ce zaune a turakar Sarki ta zuba uban tagumi, Sarki Aminullahi ya kalleta yace."Me yake damunki Zaliha" idanunta ne suka ciko da ƙwalla muryarta na rawa ta ce. "Mai martaba Saif ne nake lura da yanayinsa bashi da ƙosasshiyar lafiya, na lura fa ko gani kamar ba ya yi, gashi har yanzu kansa baya tsaiwa hatta irin gwarancin yarannan banji yana yi ba, abu ɗaya kawai nasan yanayi idan na kira sunansa zan ga yana ɗan motsawa." Fulani Zaliha na kawo nan a zancenta ta rushe da kuka. Rungumeta yayi ajikinsa tsam kamar wani zai ƙwaceta ya fara rarrashinta, yana buga bayanta harta lafa da kukan sannan yace. "Ina lura da halin da kike ciki kuma na