Follow us on social media
Showing 9001 words to 12000 words out of 12469 words
Chapter 4 - My Uncle Aure Cikin Hawaye Complete Hausa Novel by Aishatu Haliru Bissalam
zance kakeyi Aliyu yafada
Hakadai salim yaruhuta musu maganin ciyon marar atarema sukaje suka siyo sanda suka dawo har ankaita dakin Hutu babu jimawa tafalka dai2 su Aliyu sundawo Dr salim yaruhuta musu sallama suka wuce gida
Basu jima da isaba bakon nata ya isoπdama kuma tana dan ciyon Mara amma na wannan watan saiyasha banban da sauran
Wannan kenan
****************
Kwanaki sundan ja har bakon nata yayi mata sallama yafece tacigaba da al amurranta domin ita har mantawa takeyi wai akwai igiyar auren Aliyu akanta
Aliyu kuwa ciyonshi sai abunda yakaru amma sabida taurinkai yaki ya nemi iman asasanta sai kara jida kaima dayakeyi
Ko sakar mata fuska bayayi yayi tafiya abuja wurin aiki yakai sau biyu acikin watannan
******************
Yau saura wata daya iman ta tare Gidan Aliyu sai kara gyaranta aunty keyi domin wani irin shu'umin turare aunty tasa aka kawo mata daga Niger turaren wani irin sirrine dashi domin gudun matsala ma aunty bata bata turarenba ta ajiye ahannunta sai ranar daza akai iman Gidan Aliyu shima idan tashiga Gidan kafin Aliyu yashigo zata shafa
Drawer aunty ta janyo tasanyashi sabida tsaro badan tsoroba π
***************
Yau Saturday bamakaranta su iman nagida gashi islamiyyarma sunyi Hutu aunty batanan tafita imance kawai sai salma
Ganin komai nagidan sun kammala iman taci wani mayen wanka na English Wear kayan sunyi matukar karbar jikinta
Riga da wandone wandon yabi fatar jikinta saika rantse da Allah ajikinta akayishi sai rigar itama tayi mata kyau kasancewarta mai karamin hannu powder kawai tashafa da Dan kwalli sai man baki amma masu karatu kuzo kuga wani masha hurin kyau datayi masha Allah ko hula bata sanyaba kawaidai ta taje kanta tayi parking dinshi tasakoshi har gadon bayanta kayan nata maroon ne shiyasa kalar ta amshe jikinta sosai abunka ga farin mutum
Sanin Dan masifa bayanan kanta tsaye tafito falon salma naganinta tace
Wow masha Allah wlh mom kinyi kyau (haka take kiranta wani lokacin idan nakwaran na kanta)
Masha Allah irin wannan kyan haka ai sai kirikitamin uncle takarasa fada cikin zolaya
Iman kam tabe baki tayi tana cewa kanki akeji
Har kuma tazauna tatuna ba agyara dakin aunty ba Dan haka tanufi dakin tafara tsabtaceshi tagyara gado tana kan gayaran gadon taga dan kunnen aunty dan haka tadakko tajanyo drawer aunty tasanya harzata rufe idonta yakai kan wani turare dayayi matukar daukar hankalinta dan haka ta janyoshi takaranta sunan dake jiki bata fahimci ruhutunba sai kawai tashiga feshe jikinta dashi domin kamshin yayi mata sosai Wanda tagama wanka da turaren lungu da sako najikinta sannan tamayar tanajin wani irin nishadi nashigarta
Tafito falon salma batanan tashiga daki tana fitowa wazata gani uncle nan danan kuwa tanemi natsuwarta tarasa
Bakinta narawa tace uncle inawuni kallonta yakeyi from up to down sa annan yatabe baki ke maza kawo ruwa kintsaya kina kollona kinsamu TV agabanki sususu tawuce yabi hips dinta dakallo yanajin yanayin jikinshi nacanjawa gawani fitinannen kamshi dayake kara tada mishi da hankali yarasa ta ina kamshin ke fitowa ruwan takawo mishi aikuwa fitinannen kamshin yakara yo mishi sallama har zata juwa yakirata ke zonan
Bamusu kuwa tajiyo amma kuma bata daga daga wurin datake ba
Kobaki jiba
Ahankali take matsowa kusa dashi kamshin nakara kai mishi ziyara aikuwa yayi saurin fizgo hannunta akan tsautsayi bata dire ko inama sai akan faffadan kirjinshi wani irin shock gaba daya yakaimusu ziyara iman tashiga kokarin barin jikin nashi
Aliyu dagaba daya kamshin yabirgita mishi kwakwalwa yakuma rikita mishi lissafi yayi saurin sanya hannayenshi ya kara rungumota jikinshi kamar zai tsaga jikinshi yasanyata
Iman dataga abunda yafi karfinta tashiga kokawar kwatar kanta amma ina takasa
Jikinshi har rawa yake unexpected yayi saurin hada bakinshi da nata
Salma data fito falon danjin iman shuru tayi mugun gani tayi saurin komawa inda tafito
INA MAIBAKU HAKURI MASOYA LITTAFIN MY UNCLE KUNJINI SHURU KWANA BIYU MUNDANYI BIKINE AMMA YANZU KOMAI NORMAL ZAKU DINGA JINA KULLUM
I love you all my fans
ππππππππππππππππππππππππ
[4/1, 6:20 AM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: ππππΉπΉ
MY UNCLE
ππππΉπΉ
Writing by:-sholy
Wannan shafin sadaukarwa ne ga Yayanah daya tamkar da dubu kuma jigo da Karin karfin Gwuiwa ga littafin my uncle ina matukar godiya da irin gudummuwar da kake bani akan wannan book din nawa DR MUHAMMAD also known as (M K) inayinka over over Yayanahπππ
Ina godiya sosai masoya littafin my uncle naga comment dinku kuma naji dadi sosai Allah yabar kauna ana mugun tare irin over dinnanπππ€π€π€π€π€π€
Page 17
Salma data fito danjin iman shuru tayi mugun gani tayi saurin komawa inda tafito
Cikin tsananin rudewa iman tawani irin zazzaro idanuwanta tana kokarin kwace jikinta
Aliyu da gabadaya yagama fita hayyacinshi jiyake kamar yana shan wani sweet mai mugun dadi Wanda kuma baya son abunda zai tsaidashi daga wannan zumar dayake xuka
Kissing dinta yake kamar zai cire mata lips
Hannunshi iman taji yana yawo agadon bayanta kamar yana Neman wani Abu zip din rigarta ya lalubo π
Iman da wani irin karfi yazo mata tayi saurin kwace bakinta tareda fashewa da kuka
Cikin wani irin Hali Aliyu da sai ayanxu yadawo hayyacinsa yayi saurin barin falon yana dafe da mararsa da take wani irin mirda mishi
Iman kuwa kuka kawai takeyi salma dataji alamun bude kofa tayi saurin lekowa gani ba Aliyu tafito tana tafa hannayenta cikin wata irin dariyar mugunta take cewa ahhh lallaisu momy abun ba sassauci kenan yanzu bazaku jira akaiku gidankuba afalonmu ma
za'a nuna mana love kinacewa bakyaso toshima wannan duk cikin kiyayyarne
Iman data karajin wani irin haushin Aliyu gakuma lips dinta dasuke mata Dan Karen zafi sabida shiga hannun Aliyu da sukayi sannan kuma wai yanzu salma tazo tana mata wannan zancen aikuwa takara sautin kukanta
Ahaka aunty tazo ta tarar da ita saifaman tambayarta take meyasameta take kuka amma tayi mata shuru kan salma aunty takomarda tambayarta itakam salma cewa tayi bata saniba itama ahaka ta tarar da ita amma dasun hada ido da iman sai tayi mata gwalo ranar dai ahaka iman tawuni data tuna abunda Aliyu yayi mata dazu saitayita kuka gashi tayi brush yakai sau goma wai wlh bazata sha miyan wani katoba hardasu cewa kazami kawai tanajan tsaki taredayi masa Allah ya'isa tafi cikon kwando
Wannan kenan
Tabangaren Aliyu kuwa yana fita yabude motarshi yashiga yajima aciki yana mayarda numfashi kafin yatada motar yabar gidan akan hanyarshima tunanin abunda yafaru kawai yakeyi sannan yana yiwa gangar jikinshi Allah ya isa domin gani yake ita ta ingizashi ga wannan abun kunyar da ya aikata
Kanshi yadafe yana fadin
Why! Why!! Why ni Aliyu zan aikata hakan salon wannan yarinyar ta rainani shutttt!!!!!!!!!!!!!!!! Yafada dakarfi
Aikuwa baidawo gidanba sai 11:30pm sabida bayason wani Abu dazai sake hadashi da wannan yarinyar harta kawo mishi raini
Bayan yagama duk wani Abu dayasabayi kafun bacci yafeshe jikinshi daturare yafada kan gado tareda janyo blanket yarufe jikinshi kasan cewar lokacin sanyine aikuwa bacci yagagare Aliyu domin kuwa daya rufe idonshi siffar imance kemishi yawo a kwakwalwa dakuma moment dinsu nadaxu saiyayi saurin bude idonshi
Dayaga abun banayi bane yamike ya dauro alwala yafara jero salloli shine bai kwantaba sai 1:22am Inda wani daddadan bacci yayi awon gaba dashi cike da mafalkai masu dadi dakuma wuyar mantawa
Saidai muce gudnyt Aliyu &imanπ
************
Tun lokacinda abunnan yafaru tsananin Aliyu da iman suka shiga wasan buya danshi gani yake yarinyar tagama rainashi
Ita kuma batama kaunar ganinshi
Aunty kam bata saurara wurin gyaran kanwar tataba domin sotake takama Aliyu da hannunta
Saidai kash tuni su Aliyu suka sami wani kiran gaggawa a abuja wani gagarumin daji da ake zargin kidnappers naciki gobe zasu wuce
Dan haka Aliyu yakira Abba da baba yasanar musu Dan haka aka dage tarewar iman harsai yadawo
Wannan kefans
10:43pm abisa tsautsayi suna kallo a falo domin kuwa ita iman harma tayi shirin bacci wani Indian film yadauki hankalinsu suka tsaya su kalla sai aunty tatuna sababbun cups dinda tasiyo dazu akasuwa ta aiki iman dakinta tadauko matasu cikin wardrobe tanazuwa kuwa taga turaren ranar datake masifar son kamshinshi Dan har akasuwa tabincika bata samuba aikuwa cikin murna tadakko tafeshe jikinta dashi sannan tadauko cups din tafito
Takawowa aunty tana zama aunty da Sam tamanta da wani rurare tace kekuwa iman a ina kika samo wannan turaren
Adakinki Aunty wlh turarennan namin dadi kibanishi Dan Allah tunda naga bakyama amfani dashi
OK zanduba ingani idan bawanda nasiyowa Abba bane
Toh aunty kawai tace
Yawwa iman dan Allah tashi maza kikaiwa Aliyu abincinshi adaki domin yanzunnan yashigo yace yagaji bazai iya fitowaba akawo mishi
Haka kawai iman taji gabanta yayi wata mummunan faduwa amma haka tadaure domin kada aunty tafahimci wani Abu
Tace toh tareda mikewa tahado abincin tanufi dakin Aliyu kirjinta nakara matsanincin bugawa
Bayan falon nashi tayi tunanin ko harya shige Dan haka ta isa Kofar bedroom din taredayin sallama amma shuru kakeji ganin jinshuru tadauka ko harya kwanta Dan haka tatura Kofar bedroom din wata irin kara iman ta kwalla tareda sakin tiren dake hannunta taduke kasa
Aliyu da fitowarshi kenan daga ban daki dagashi sai Dan karamin towel ya dakko jallabiya tareda sakin towel din jikinshi dai2 iman tashigo gashi kofar yajiyo yana kallo danshi kwata kwata baiji ma sallamartaba kuma yasan shikadaine adakin bamai shigo mishi komai nashi kai tsaye yakeyi shiyasashi sakin towel dinπππππππππππππππππ
I love you all my fans
ππππππππππππππππππππππππ
[4/1, 6:20 AM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: ππππΉπΉ
MY UNCLE
ππππΉπΉ
Writing by:-sholy
Page 18
Aliyu da fitowarshi kenan daga ban daki dagashi sai karamin towel ya dakko jallabiyya tareda sakin towel din jikinshi dai2 iman tashigo gashi kofar yajiyo yana kallo danshi kwata kwata baiji ma sallamartaba kuma yasan shikadaine adakin bamai shigo mishi komai nashi kai tsaye yakeyi shiyashi sakin towel din
Iman data wani irin duke yarada sakin tiren hannunta ta kwalla kara
Hakan yasa Aliyu saurin kallon kofa
Aliyu yayi saurin kallon kofar cikin razana da tsananin tashin hankali yaxura jallabiyarshi ko boxer baitsaya sawaba yayi saurin isa wurin iman tagaba daya tawani irin rikice
Tsawa yadaka mata keee maza mike
Jikinta narawa tayi saurin mikewa
Ido yazuba mata yanajin fitanannen kamshin ranar yana kaimishi ziyara dakuma rikirkita mishi lissafi Wanda kafin ya iso wurinta marinta yasoyi amma ina Sam yakasayin hakan
Dan Allah uncle kayi hakuri iman tafada muryarta narawa
Shut up nonsense kinga wani Abu ne
Bakinta tarufe domin jin kuka nason kufce mata tana girgiza kai alamun a a
Karya kike kinga wani Abu bazaki gayaminba saina mareki awurin ko
Kuka iman tasanya
Allah ni uncle komai banganiba
Nizakiyiwa karya yafada yana kara matsowa ita kuma tana ja da baya tareda girgiza kanta
Sanda ta hade dabango shikuma yakara matsawa har numfashinsu nahaduwa dajuna
Please uncle kayi hakuri bazan karaba
Dankin rainani shine zaki shigomin daki batareda Neman iziniba ko
A a wlh uncle nayi sallama baka karbaba shiyasa
OK to zakiyi bayanine domin tunda kika ganni wlh kema sai kincire naki kayan stupid girl
Duk abunda Aliyu yakeyi cikin karfin Hali yakeyi domin wannan kamshin bakaramin kara rikita mishi lissafi yakeyiba
Iman tawani irin zaro ido please uncle Dan Allah kayi hakuri wlh bazan karaba sorry
Kima daina wahaladda kanki akan bani hakuri
Oyaaaaaa cire kayanki yafada yana zare mata hijab din jikinta kyawawan kayan baccinta suka bayyana
Yasubhanallah ai saida Aliyu yayi danasanin cire mata hijabi lokacinda yayi tozali dasurar iman wadda tasanya nufashinshi daukewa na wucin gadi kafin yaja wata doguwar ajiyar zuciya
Iman kam duk addu'ar datazo bakinta yi kawai takeyi bata Masan metake fadaba kafin inkirga uku you remove all your clothes
Fara counting yayi
One!!!!!! Two!!!!!!!!!! Thr
Aunty dataji iman shuru bata dawoba sai hankalinta bai kwantaba tanufo dakin Aliyu din
Tareda knowing kofa tana kiran sunan Aliyu
Wanda yatsayadda Aliyu daga counting din yabude idonshi cikin wani irin yanayi had idonshi sunsauya kala zuwa red har muryanshi tasauya cikin karfin Hali yace
Karkiyi tunanin kintsira kinganni haka kinci bulus zankama kine
Kuma wlh kikayi tunanin gayawa wani wannan maganar sainayi mugun saba miki bace mun dagani stupid girl kawai
Iman da jikinta har rawa yake tayi saurin barin dakin cikin tsananin sauri hartana tuntube tana bude kofar tayi kicibus da aunty
Ke lafiyarki kuwa meyafaru ko Aliyu yayimiki wani abunne gayamin mana kikamin shuru
Aunty saifaman tambayarata take amma tace mata bakomai cikin sauri tawuce dakinsu aunty ma bayanata tabi itama tawuce nata dakin
Iman kam yau bacci yagagareta domin datarufe ido Aliyu ake hasko mata ayanayin data ganshi daxu saitayi saurin bude idonta
Har saida salma tagaji da motse motsenta ta tambayeta
Ke lfy wai miye hakan kindame mutane nikin hanani bacci Allah wlh matarnan nakusa koraki dakin mijinki kijecan kidameshi kinaha mishi bacci amma nikam bazakizo kitakuraminba
Iman kam har tabude baki zata gayawa salma sai kawai ta tuna da gargadin Aliyu tayi saurin kama bakinta domin itakam yau wani sabon tsoron aliyune yashigeta dakyar bacci barawo yayi awon gaba da ita
Tabangaren Aliyu kuwa dakyar yasamu adafe da Mara ya isa wurin fridge dinshi yabuda lemon tsami yadakko batareda wata wataba yamatsashi abakinshi sanda yashanye yayi saurin fadawa kan gado yana mai danasanin haduwa da wannan fitinanniyar yarinyar sunan da ya lakawa iman kenan yau domin gaba daya ta rikirkita mishi lissafi tunani yake wani irin hukuncima zaiyiwa wannan yarinyar idan yadawo murmushi naga Yaya kamar ba Wanda yake acikin tsananin ciyoba kome yatuna ohoooo shima dai bacci barawone yayi awon gaba dashi bayan yadan samu sauki
Sai dai muce gudnyt iman Aliyu salma & auntyππ€ͺ
**********
Bayan Aliyu yagama shiri yayiwa aunty sallama domin tunda safe zasu wuce lokacin kosu iman basu tashiba
Salim ne yakaishi airport saida jirginsu yadaga sannan yadawo
Inda Aliyu yatafi da kudirirrika masu yawa aransa Wanda shikadai yasani saikuma mahaliccinsa
Saidai muce Allah yakiyaye hanya Aliyu
CHAKWAKIYAR YANZU TASOMA MASU KARATU
SHIN YA ALAKAR IMAN DA ALIYU ZATA KASANCE
IMAN KUWA ZATA AMINTA DA ALIYU AMATSAYIN MIJINTA
ALIYU FA SHIMA ANYA ZAI AMINTA
SHIN WAYANNI KUDIRIRRIKA NE ALIYU YATAFI DASU
MENENE SHIRINSHI AKAN IMAN
ANYA KUWA ALIYU ZAIYAFEWA IMAN GANIN DA TAYI MISHI BATAREDA YADAU FANSABA MA'ANA YAYI RAMUWAR GAYYA
TAB AKWAI CAKWAKIYA KUDAI KUBIYONI DOMIN JIN AMSOSHIN WAYANNNAN TAMBAYOYIN INSHA ALLAH A PAGES MASU XUWA NAGODE
I love you all my fans
ππππππππππππππππππππππππππππππππ
[4/1, 6:21 AM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: ππππΉπΉ
MY UNCLE
ππππΉπΉ
Writing by :- sholy
Page 19
Inda Aliyu yatafi da kudurirrika masu yawa aransa Wanda shikadai yasani sai kuma mahaliccinsa
Saidai muce Allah yakiyaye Aliyu
***************
Iman kam karatunta tacigaba dayi hankalinta akwance saidai wani lokaci idan tana ita kadai takan Dan tuna Aliyu dayanayin da taganshi a Daren ranar da zaitafi
Wani lokacin haka kawai idan suna zaune tareda salma idan tatuna da yanda taga Aliyu kawai saita fashe da dariya salma kam kallonta kawai take ta girgizakai tarasa meke damun iman
Yauma kamar kullum suna zaune suna cin abinci haka kawai iman ta fashe da dariya salma data gaji da halin iman tace waike mekikewa dariyane kullum sai kitasani agaba kitamin dariya
Iman data kara fashewa da dariya acikin dariyar tace Allah ko salma wlh matar uncle tashiga uku
Salma tajuyo tana kallonta salma ta dago takalle iman acikin mamaki tace waike dama duk wannan dariyar uncle kikema to tsayama meyasa kikace matarshi tashiga uku
Hmmmm kedai kawai salma bari wlh ninasan me nagani amma wlh matar wannan bawan Allah tabanuu tafada tana dariya
Salma data kulu iman taki fada mata komiye tace wace matarsa kuwa banda ke aikuwa idan hakane kece kika banu
Iman tajuyo tana dariya hmmm salma kenan ai wlh wannan mutumin yafi karfina kedai bari kawai
Haka suka cigaba da firarsu salma natason jin miye iman tagani amma iman taki fada
Dan haka suna gamawa salma ta tashi tayi shigewarta daki iman kam remote tadauka tacanja tasha zuwa mbc Bollywood domin tana bala inson Indian film
***************
Haba Aliyu wai miyake damunkane haka kullum cikin tunani muba haka muka sankaba Dan Allah kagaya mana abunda yake damunka ko kadawo yanda kakeda please Aliyu Jibril yafada cikin tsananin damuwa(Jibril aminin Aliyu ne wurin aikinsu daya sunshaku sosai Jibril namatukar son Aliyu sabida hakayenshi shiyasa yanzu dayaganshi cikin damuwa shima yashiga damuwar )
Bakomai Jibril insha Allah zanyi kokari inga nadaina katayani da addu a please
Insha Allah zantayaka da addu a aminina
Nagode Aliyu yafada
Yawwa kokaifa kasan kaine babban aminin ango da munkoma daga wannan aikin da sati daya za afara biki kasan wlh namatsu inga Teema acikin gidana ina bala'inson yarinyar wlh Jibril yafada
Hmmm aikuwa naga alama gara mumika mata kai muhuta domin ita dinma naga alamar haka takeso domin wannan wayar dakuke ba kakkautwama ta isa tashaida mana hakan
Ai inaganin yanzu saura kwana goma shadaya mukoma ko
Eeh hakane mana yaza ayi namanta nida nake shirin angwancewa inbarku da rungumar filo da matse matsen kafafuwa Jibril yafada cikin tsokana
Lallaikuwa to kasani ko narigaka Aliyu yafada
Ahaba ahaka dinne zaka rigani kaida bakama San yanda zakayi tunkare mace mace kana sontaba inagafa sai kaje gidanmu nida teema na kayi mana sati daya mu koyamaka yanda ake love
Aliyu kam kafadar sa yadaka yana fadin to oga kada kayi mamakin inriga shiga daga ciki wlh
Yawwa dama ina so intambayeka Dan Allah meye alamar mutum yakamu da so
Aikuwa dariya Jibril ya fashe da ita ba kakkauta har saida Aliyu yasha omo yamike zaibar wurin
Jibril yayi saurin rikeshi please sorry abokina wlh dariya kabani yihakuri zangaya maka sorry duk da dariyar tashi taki tsayuwa
Aliyu yadawo yazauna domin yanason jin amsar da Jibril zabashi amma cikin daure fuska yazauna
Please Aliyu meyasa kayimin wannan tambayar
Malam Zaka bani amsar tambayatane ko a a
Zanbaka amma naso nasan wannan wace mai sa ar ce wlh
**************
Lallai kuwa iman wlh kinbani mamaki ace duk yanda muke dake kikasa gayamin wai zakiyi aure sai yanzu daga baya nakeji amma wlh iman bakida mutunci kumani nasan zamana dake ayanzu shiyasa wlh nakiraki nagaya miki kizo gidana yau akwai labari domin insamu damar gayamiki abunda yake raina vatareda kowa yajiba domin. Wlh idan akaji wai kinyi aure bansaniba dariya za amana suhaila ce kewannan masifar
Haba suhail kiyi hakuri wlh bahaka bane Nima abun abazata yazomin nan iman ta labarta mata yanda abun yakasance
Salma tasake shewa tareda rungume iman Dan farin ciki a kai haba wlh naji matukar dadin abunnan su abba